Sashe 201
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ilai kuwa su 'din ne dai, mamaki sai ya cikata, toh me ya kawo su gidan nan? Ta tambayi kanta.
Abinda tuntuni take so ta fahimta kenan ta kuma gaza yin hakan domin sam Yah Bukar bai bata damar fahimta ba, shin dama ya sakko daga fushin da yake ne ya amshi Zaitoon bayan yawon iskancin da ta tafin ko kuwa dai.
Tana so ta fahimta ta kuma 'kara sanin wani abu daga Zaitoon amma sam ko hirar ta 'dauko masa sai ya kawar da ita ya kawo wata.
Ko sallamar tasu ma kasa amsawa tayi sai tsawa da ta buga wa Umaru da fa'din" Kai dallah can, ka bi ka ishi mutane da korototo sai kace wasu mutanen kirki ka gani..idan baka rufe min baki ba zakaci dukan tsiya wallahi a waje na...".
Murmushi Zaitoon tayi da jin kalaman Azeeman, sai kuma ta sake doka wata sallamar...ta daban.
" Lafia kam, ina fata ba makauniya bace ke?"
Tayi maganar a zafafe tana duban ta.
Kai ta girgiza mata sannan tace" Ko 'daya, gani nayi ita sallama cike take da manufofi na alkhairi wanda fa'idar amsa ta baya da iyaka".
Bama ta bari ta gama ba tace" Toh ri'ke abar ki ni ba ita nake da bu'kata ba...ita alkhairi kewaye da ita nake kusan kowacce rana...Allah dai yasa lafia na ganku gidan mutane da wannan tsakar ranar..?"
Kafin Zaitoon ta bata amsa Yah Bukar ya 'daga labile yana yi musu iso, domin duk abinda ake yi 'din a kan kunnuwan sa ne.
Wajen zama ya basu fuskar sa babu yabo babu fallasa ya kuma 'kwala 'kiran Azeema akan ta kawo musu ruwa.
Kwafa tayi sannan ta 'kira Ummaru tace ya kawo kofi...'debi ruwan can ka kai musu kai..."
Yace" wannan?"
Tace" Erh..shi nace"
Tana mai tsare sa da idanuwan ta.
Yace " Wannan fa ruwan..."
Bata bari ya 'karasa ba ta watsa masa wata uwar harara.
Hakan yasa shi yin gum da baki ya 'diba ya kai musu.
Yana ajiye ruwan ya fara jan Mufee da wasa da yake ta sanshi da kansa ma ya sha zuwa can gidan Inna..yau 'din ma rashin 'karfin jiki ya hanata sakewa tayi wasan.
Itama yau Zaitoon taka tsantsan take da yarinyar sbd masifar mahaifin ta..sosai take gudun duk wani abu da zai tta6a lafiyar ta..hkn yasa bata damu da rashin sakewar ta suyi wasan ba..tafiso dama ta ri'ka ganin motsin ta baya ga hk ma sam bata gane inda Azeema ta dosa game da su ba.
Garin wasa 'kafar Ummaru ya ture cup 'din ruwan da ya kawo ya kuwa malale a 'kasa baki 'daya tun kafin su kai ga shan sasa.
" Subhanallah" suka ce atare, fa'da Yah Bukar ya fara yi masa akan rashin natsuwa...sannan ya 'kara da fa'din maza je kawo abinda za'a goge ruwan da shi.
Allah ma yasa leda carpet ne a 'dakin..Zaitoon da kanta ta ansa ta goge shi tass sannan ta shanya sa.
" Daga zuwan mutane ka sasu aiki Ummaru, gashi ko ruwan basu sha ba ka malalar da shi, maza je ka 'debo musu wani ruwan su sha".
" Yayah babu wani ishi ma fa, dayake dg gida muke ai"
Ummaru ne yy caraf yace" Abba bama ruwan ai ya 'kare, waccen ma ragowar awaki ne da suka rage fa akace na 'debo musu".
Idanu sosai Yah Bukar ya waro akan Ummaru cike da mamakin sa.
Zaitoon dai kam batayi mamaki ba dan Azeema ba ba'kuwar ta bace..inda dai ta gode Allah da ya kasance ita har Mufeeda babu wanda ya kai ga shan ruwan.
Cike da haushi Yah Bukar ya fita waje bai da'de ba sai gashi ya dawo da leda cike da robobin ruwa da na lemo.
Azeema dake wanki cikin gida mamaki da takaici ya hanata cigaba da wankin.
Shi kuma bai ce da ita 'kala ba ya sake wuce ta yy ciki.
" Yayah duk wannan sai kace mun kai goma, ai dama baka siyo ba wlh sai kace wasu ba'ki.. "
Shi dai bai ce komai ba, domin har ga Allah ba 'karamin kunyar bayanin da Ummaru yy musu yy ba..taya Azeema zatai masa hk...ya rasa amsar sam, meyasa ta aikata hkn ya kasa ganewa...shin matsayin Zaitoon a wajen sa ta mance ko yaya, ko kuwa dai tana tunanin ya canza ne?
Dalili kenan ma da yasa shi jan su da hira duk da ba hk yy niyya ba, sun sha hira kuwa sosai irin wanda suka da'de basu yi irin ta ba.
Can gida kuwa ashe tun bayan fitar su Rayyan yazo dan hankalin.sa yaya kasa kwanciya da yanayin da ya bar Mufeeda tun ranar nan...Inna ce ta sanar da shi ai sun tafi can gidan mahaifin ta.
Baiyi 'kasa a gwiwa ba ya 'dauki hanya ko da yaje basa can.
Haka ya 'dan zauna da mahaifin na ta nan ma yake samun labarin rashin lafiyar tasa, ya tausaya masa sosai, 'karshe ku'di masu yawa ya bawa Iyami kafin ya bar gidan wai ko zasu nemi wani abin tunda yana under medication ne.
Can ya koma gidan Innani da tunanin ko sun koma ne ganin har fa ya bar gudan bai gansu ba...kuma bai ssamu labarin zuwan su ba.
Abin mmk shiru har lokacin bb su babu alamar su.
Waje ya koma cikin mota amma ya kasa zama,
hk ya riqa shiga yana fita sam yama mance da cewa gidan sirkan sa ne.
Har Innar Zaitoon ta gabatar masa da abin sha amma ya kasa yiwa abin ko kallan arziki sbd damuwa.
Bakomai yake tunawa ba sai wancan ranar, ina kuma ta sake kai masa yarinya bai sani ba...ya rasa me yake damun Zaitoon kwanan nan..gani yake ta canza masa baki 'daya...haka nan kawai sai yake tuna wancan ranar da tarar da ita da Adam.
Wannan tunanin ya hanasa sakat, ya kuma kasa tafia batare da yaga 6ullowar su cikin 'koshin lpy ba.
Koda taje gidan kuma babu wanda ya sanar da ita batun zuwan sa, Abban su ne dai kawai ke bata labarin kirkin sa yana kuma sanya masa albarka, ita dai bata san dalili ba, bata kuma san meyasa yake sanya masa albarkan ba, shi kuma Abban bai ce da da ita a ranar ya shigo ba.
Iyami kuwa tun shigar ta gidan ko gaisuwar kirki bata tsaya sunyi ba ta fice abinta har suka bar gidan kuwa bata dawo ba.. Khausar ma an shiga gari bata tarar da ita gida ba.
Da ta gaji da batun Rayyan a bakin Abban kawai sai ta kawo wata hirar ta kawar da waccan.
Basu suka koma gida ba kuwa har sai bayan sallar la'asar..Mufee rungume bisa kafa'dar ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali.
Zaitoon baki 'daya tasha jinin jikin ta tunda taga mota a waje tasan shine domin sarai tasan kalar motocin da yake hawa.
" Wannan dai anyi fitinanne.."!
Ta furta cikin zuciyar ta tana me ha'de ranta sosai.
Yau kam 'dakin Innani ta wuce direct sbd fargaban abinda zai biyo baya, dan tasan fitina kawai ta kawosa, kuma bata mance da masifar da tasha waccan ranar ba, gashi yau ma ta fita yazo bata nan.
Ko Mufee Inna bata bawa masau'ki a 'dakin ta ba balle Zaitoon tace su koma nasu 'dakin tunda jiran su ake.
" Inna yau dai rashin kirkin ake ji da shi"
Ta fa'da cikin ranta.
A fili kuwa cewa tayi" toh Innani bari in kwantar da Mufeeda sai inje mu gaisa.."
Ta fa'di hakan ne da tunanin idan zata iya masa 'karyar ba da 'diyar sa ta fita ba.
Ai kuwa Inna tace " sam..kai ta wajen ubanta ya ganta..kinsan da'dewar da yayi ne yana jiran zuwan ku...?"
Baki ta tura ta fito tana gyara ri'kon Mufee ta sanya takalmin ta fita.
Sallama tayi ciki- ciki ta kuma sa kai lkc guda tana mitar shigan mata 'daki da yake batare da iznin ta ba.
Tana shiga kuwa ta tarar da shi tsaye hannayen sa duk biyu cikin aljihun sa.
Kallo 'daya tai masa ta tabbatar ransa 6ace yake 'kololuwa.
'Kasa tayi da idanun ta wani mugun fitsari ya kamata.
Banda 'kirjin ta dake rige rigen dukan uku uku.
Juyawa tayi da niyyan barin 'dakin domin dagaske fitsarin ya matsa ta.
Ganin ta juya 'din yasa shi yin gyaran murya dai- dai wayar sa ta 'dauki 'karan shigowar 'kira.
Cak ta tsaya sai dai bata waigo ba.
Yadda ta gyara ri'kon Mufee a kafa'dar ta da 'karfi har sai da yasa yarinyar farkawa.
Rass ta bu'de jajayan idanun ta da bacci ya rina su ta sau'ke su akan Rayyan...sake waro idanu tayi sosai tana duban sa.
Sosai Zaitoon ta ha'de ranta tamkar an yi mata wani gagarumin laifi...sam bata tsammaci ganin sa ayau din ba, sam batayi tunanin zai zo ba..toh me yakawo shi yau kuma...?..me yasa tun zaman da tayi a gida bata fita ba bai zo ba sai yau ka'dai da ta fita dan neman fitina.
Tana tura baki da haushin da ke cika ta ta waigo, da sauri Mufeeda ma ta waigo tana duban sa" Ni fitsari zani..."!
Ta furta still tana tura baki.
Bai tanka ta ba idanun sa na akan wayar sa tamkar bai san da wanzuwar ta ba..har sai dda ya gama duba abinda yake gani cikin wayar kafin ya 'dago idanu.
Mufee ma 'kura masa idanu tayi tana duban sa yana 'dago kai kuwa akan ta ya sau'ke idanun sa.
" Mama na..sarkin yawo.."!
Ya fa'da yana 'ka'kalo murmushi.
" Zo mana mu gaisa...".
Ya fa'di hk ne yana mayar da wayar sa cikin aljihun gaban rigar sa...gami da 'daga 'kafa ya tunkari inda suke tsaye.
Zaitoon ji tayi 'kafar ta ya fara rawa tamkar bazai iya 'daukan su su biyun ba, tsoron masifar sa take, balle yadda taga ko kallon arziki Bata samu daga wajen sa ba.
Duk iya sanin da tayi masa kuma a yanzun ta kasa fahimtar yanayin da yake ciki...sai dai sam fuskar sa babu walwala ma, ko wacce take gani 'din ma a zahiri kawai yk nunawa sbd 'diyar sa..sai ma taga yana ta 'kara ha'de girar sama da ta 'kasa..ko me akayi masa oho.