← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 218

Sashe 33

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk 'din su babu wanda zaka gani kace 'dan dama dama dan gaba 'dayan su ba cikin nutsuwa suke ba, har gara ma Zaitun ita da taji dalilin tuhumar bata yi mamaki ba, dan dama tana da 'dan sani akai kadan bata san komai ba kam amma ta dade da dasa ayar tambaya akan Dr Rasheed 'din.
Anan nema ta fahimci Hameeda bata san komai akan lamarin ba.

Motar da suka fita da ita kwanaki an sace 'diyar wani hamshaki da ita, sai shekaran jiya da yamma aka saki yarinyar bayan an biya kudin fansa da kwanaki hudu, toh inda aka samu akasi wajen da akai garkuwar gaban wata Plaza ne kuma akwai 6oyayyar cctv ita ta bayyana musu lambar motar bayan dogon bincike da akayi, sosai suke bin diddigin lamarin an baza numbern motar ga dukkan jami'an Jahar gaba 'daya...sai yau Allah ya bayyana musu motar...kuma ita din ce ba wata ba.

Bayan 'yan bincike da akai musu nan aka gano Dr Rasheed shi ke da hannu dumu- dumu cikin lamarin.
Ba'ayi 'kasa a gwiwa ba aka cafko shi, kafin wani 'dan lkc iyaye da dangin su Hameeda duk sun cika ofishin.

Sun nemi abasu bailin su Hameeda amma bb wata kofa data bada damar hakan, abin tun daga sama ne, babu bailing har sai anje kotu.

Sai dai an sanar da su baza'a dauki dogon lkc kan zuwa Kotun ba sbd case din ya hada ne da babban mutun.

Dama ance rana dubu ta 6arawo....yau dai ga Dr Rasheed ga Hameedah ga kuma Zaitun garkame a bayan kanta.

Ba 'karamin wahala suke sha a hannun jami'an tsaron ba musamman da yake Hameeda da Zaitun sunki amsa laifin sai kuka, ko abincin kirki basa iya ci, gefe guda kuma ga wari da uban sauron da cizon su kadai ma azaba ne.
Zaitun ba karamin damuwa ta shiga ba, taci burin barin gidan Dr Rasheed cikin ko wani irin hali ba tare da tayi tunanin neman za6in Allah game da alkhairin kasancewar ta a gidan ko akasin hakan ba, yau ga shi Allah ya cika mata burin ta ta fita a gidan Dr Rasheed amma sai ta sake fadawa wani wurin da ta kwammaci rayuwa gidan Rasheed sau babu adadi akan nan 'din...duk lkcn da ta tuno hakan kwalla kawai take sharewa...ta sa aranta cewa bazata sake yin irin wancan fata da addu'an ba, zata roki Allah alkhairin abu kafin ta aiwatar da koma menene.

Mahaifiyar Dr Rasheed ce ta roki a fitar mata da Naina da kuma Mufeeda wannan ma sai da aka kai ruwa rana kafin aka amince aka bata yaran ta tafi da su.

'Bangaren Zaitun ai 'karin kuka da tashin hankln ta kenan, ita kanta bata son zaman yarinyar a cikin Cell din sbd azabar sa amma rashin sanin inda za akai mata ita kuma shiyafi tada mata hankl.

Dagasken gaske Zaitun ta shiga tashin hnkl, tun tana kuka har tazo zuciyar ta ta bushe, dukan su ake bada wasa ba karfi da yaji wai sai sun amsa laifin da basu san tushe da makamar sa ba.

Ita har Hameedan kuwa sun ki amincewa kowa ya kafe kan ra'ayin sa...kusan sati biyu ana abu 'daya, tuni an gama baza hotunan su a media gidan Television da Redio duk labarin su ake...mafi yawan mutane in sun budi baki sai dai suce an kama gawurtaccen 'dan fashi da garkuwa da mutane shi da mukarraban sa, abin mamaki ma wai har da mata ne.

Dan duk yadda aka ka'da Dr Rasheed bai yadda ya tona asirin yaran sa ko guda ba..yasan shine ya ja ra'ayin su har ya gur6ata musu tunanin su suka biye shi dan haka bai tozarta rayuwar su ba a wannan hali, yadda babu wanda yasan da su haka yk so su kasance 6oyayyu ga kowa.

Dalili kenan da yasa ranar da aka fito da shi dan yimasa tambayoyi ya mi'ka musu sako cikin azanci da yasan su kadai ne zasu fahimta..ishara yy musu ga barin harkar da ya 'dora su akai din su nemi sana'a dan shine kwanciyar hnkl da zaman lpyr su, matukar kace ta mummunan hanya zaka nemi arziki to ka sanyawa ranka faruwar rana irin tasa, ranar tonon silili, ranar da kowa zai san me kake aikatawa, ranar irin wannan me tafe da tarin abin kunya tozarci da kuma dana sani marar amfani, ban da ma ranar da Allah da kansa zai yi ram da kai.

Al'umma duk sun dauki maganar tasa ga cewa nadama ce yake kuma tunatar da mutane akan irin halayyar tasa amma su wanda yy dan su din fahimce shi sarai.

Dr Rasheed bai yi wani dogon jayayya ba ya amsa laifin sa, shiyasa tuni asbitin da yake aiki ma suka buga stamp din dakatar da shi wajen aiki...abin bai musu dadi ba musamman da yake har cikin asbitin jami'ai suka zo suka kama shi sun dole hakan.sai ya ta6a mutunci da kimar asbitin su in suka yi sa'a ma gwabnati bata rufe asbitin ba kenan.

Zaitun ta kafe ne kan iya abinda taga zata iya sanar da su game da dangantakar ta da Rasheed din daga ranar da ya taimake ta har ya kaita gidan sa zuwa ranar da aka kama su, kuma ko da wasa bata yadda ta canza magana ba.

Haka ma Hameeda ita kam dama bata san komai ba illa kasancewa matsayin matar sa da Allah yasa ta yi.

Duk da haka ba 'karamar wahala suka sha wajen Jami'an ba, duk sun fita hayyacin su sun rame sunyi baki sai tabon cizon 'kwari da sauro da kuma bugun da ake sa jami'ai mata ke musu lokaci zuwa lokaci already kuma an saka ranar da za'a fara gabatar da su gaban kotu dan ansan hukunci daidai da laifin su.

*******
"...Shiyasa aka ce yaro yaro ne, yanzu ba ga irin ta nan ba, ka na dai sane da yadda duniya ta dauka an kama Zaitun cikin masu sata da garkuwa da mutane...kuma da ahakan kk so ni in barka ka aureta Shaheed? yarinyar da babu wanda yasan asalin ta balle tsuhen ta, ko kashe ka tayi ta gudu babu ta yadda zamu iya binciko ta har mu kamo ta tunda bamu san wace ita ba...yanzu da asalin wace ita ya bayyana ai sai ka saki ranka nima ka barni na nutsu, ka hana kanka farin ciki, ka toshe dukkan wata hanya ta walwalar ka, 'karshe ma karatu ma gagara tafiya kayi duk dan sbd ita, ni dama tun gani na da yarinyar wlh bata kwanta min ba...".
Furucin Hajiya Talatu kenan ga Adam Shaheed dake kwance kan kujera yayin da yasa daya hannun sa ya dafe goshin sa da shi sakamakon sara da kansa ke faman yi masa, 'daya hannun kuma na rike da wayar sa da ya kife ta bisa kirjin sa tun wasu mintina baya.

Sam zuciyar sa ta kasa yadda da wannan batun, shi yasan Zaitun, ya kuma san halin ta, duk da akan ce zuciya na gurbacewa amma yasan dai bata da mummunan tunanin da zai sata aikata irin wannan 'danyen aikin...taya ma zai yadda? taya zai amince? Zaitun da ko wani lkc damuwar ta 'diyar ta ce yaushe zata amince ta fa'da harkar da tasan a kowani lkc tashin hnkl na iya riskar su.

Bai ce da Hajiyar tasa komai ba har ta 'karaci bambamin ta tayi shiru...ko fita baya kaunar yi waje, balle yaci karo da muggan kalamai ga Zaitunan.
Shi dai Allah ne ya dasa masa kaunar ta, kuma ba wai ya kasa yadda da zancen sbd kaunar ta da yk yi ba ne, ya kasa yadda ne kawai sbd ya san nagartar ta da halayen ta...duk tashin hnkln da ya riski kansa abaya dalilin rabuwar su bakomai bane compared to tashin hnklin da yake ciki a yanzu.
Dalilin kuma shine sani da yy cewar Zaitun bata da kowa babu wanda zai tsaya mata, gata yarinya ce 'karama me kuma 'karancin shekaru, dole tana bukatar wani nata kusa da ita, dole zata nemi tallafawa, agaji ko kuma kalaman kwantar da hankali daga wani makusancin ta.

A yanda dunia ta gurbace ma tsoro yk kar rashin gata ya sanya shari'ar tasu juyewa kar a dorwa Zaitun laifin da yasan bazata iya aikatawa ba.

Cikin ransa ya ayyana lokaci yayi, lokaci yazo dole a wannan ga6ar ya neni taimako, ya nemi tallafi da saka hannu a karo na farko kaf 'din rayuwar sa zai nemi taimakon wanda ya kasance mahaifi ne agare shi ba dan kansa ba, ba dan jin dadin sa ba, ba kuma dan farin cikin sa ba sai dan Zaitun.

Wannan dalili ne ya sanya batare da sanin Hajiya Talatu ba ya tafi cikin babban birnin jahar tasu ya isa ga station 'din da aka rufe su Zaitunan amma duk yadda ya buga ba'a barshi ganin ta ba dole ya ha'kura bai kuma yi mmk ba dan irin tuhunar da ake musu dole tana bukatar tsatstsauran tsaro, ba mmk ha'duwar su yanzu sai kuma a kotu.

Mmn Abdul da mijin ta hatta Hajja duk abin ya ta6a su sai dai dole damuwar na wani yafi na wani, Bbn Abdul hnkln sa ya tashi sosai dan har yau har gobe yana jin Zaitun cikin zuciyar sa, amma tashin hankalin da Mmn Abdul ta shiga har zai baka mamaki, abin kamar 'yar uwar ta jinin jikin ta ya shafa, yadda ta 'daga hnklin ta ma yasa Hajja da tausayin Zaitun din ya 'dar su mata tuni tai gefe da tausayin ta fara sirfawa Mmn Abdul ruwan masifa dan har zazza6i sai da tayi sbd kuka da damuwa.

Ita kanta Hajja tasan mawuyaci ne Zaitun ta aikata abinda ake zargin, amma tsana da haushin yarinyar sun riga sun gama rinjayen zuciyar ta hakan yasa tayi fatali da duk wani tunanin cewa bazata iya din ba.

Hajjaju da mukarraban ta kuwa da suka gani cewa sukai Allah shi kara dai dai kenan..sosai faruwar lamarin yai musu daidai.
Chapter 33 · 0% Book details