← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 218

Sashe 163

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya kusa barin gidan sai Abban mu ya fito daga 'dakin sa, nan ya zauna bisa kujerar sa da yake zama irin ta dattawa...yayin da Hamma ya isa ya tsugunna gaban sa daga 'kasa kan 'kafafuwan sa...
" Abbah barka da yamma, fatan ansha ruwa lpy ..?"
" Kira min Zaituna".
Abbahn mu ya fa'da batare da ya bi ta kan gaisuwar Hamman ba.

Hamma Bukar ne yaje ya tashe ni daga baccin da nake muka fito tare da shi..jiri sosai nake yake shirin 'diba na saboda zafin ciwon kai 'din da nake son takurani.

Amma ganin inda Hamma ya tunkara wato wajen Abban mu da ko alamun fara'a babu saman fuskar sa yasa take na nemi ciwon na rasa har na isa gaban sa nima nayi zaman dirshan zucia ta na harbawa da 'karfin da bana jin na ta6a fuskantar irinta.

Lokacin da kunnuwa na suka jiye min kalamin mahaifi na agare ni ba ciwon kai ba natsuwa ta ma gaba 'daya rasa ta nayi na fara rarraba idanu.

Addu'a nk Allah yasa ba dai-dai kunnuwa na suka jiye min ba, Allah yasa ba Abbah na bane ya furta.

Amma duk yadda naso 'karya sautin muryar ban samu canji ko guda ba..abin nan dai da najin shi yace..wanda tashin farko na fahimci cewa yana tafiya ne bisa ra'ayin matar sa Iyani.

" Mahaifiyar ku tace bazata zauna da shege a gida ba, dan haka kafin yamma bana so in dawo in same ki cikin gidana..ki tattara ki san inda zaki saka wannan abin kunyar da kk kwaso ko kuma ki kaiwa ubanta ya ri'ke abinsa tunda na tabbata kinsan waye ubanta, ni ke ka'dai na haifa ban kuma haifi shege ba balle in raini na wasu, dan haka baza'a tayar min da hankalin gida ina zaman zama na ba..".

Hamma Bukar shiru yayi yana tunanin ta inda zai 6ullowa lamarin.
Ni kuwa kuka ne kawai ya 'kwace min bayan tabbatar da cewa mahaifi na da gaske yake...ina girgiza kaina nake fa'din" Abban mu wallahi ni bani na haifi yarinyar ba, kuma ina zan ga ubanta balle in sanshi har in bashi 'diyar shi, Abbah uwar ce fa kawai muka ha'du da ita kuma bata yi min bayani cikakke kan asalin su ba, dan Allah Abbah kayi min rai kar ka kore ni da 'yar yarinyar nan, idan ka kore ni ina zan saka rayuwa ta..wallahi Abbah ka tambayi Hamma Bukar kaji.. shi ya sani ba nice na haifi yarinyar nan ba Abbah..dan Allah kayi ha'kuri..."
Na 'karashe ina mai komawa bisa gwiwoyi na.

Kafin Abbah ko Hamma 'dayan su yayi magana sai ji muka yi Iyami na tafa hannuwa tana fa'din
"...wallahi Zaituna bazaki zauna min agida da ''diyar shege ba, ban gaji hakan ba dan haka bazan zauna gida 'daya da mai shi a gur6ata min zuri'ah ba, kina nan kullum 'kunsun-'kunsun cikin hijabi ashe na munafurci ne sai ga sakamakon hijabin ya bayyana 'karara...kima san yadda zakiyi tun wuri da shegen abin nan matu'kar kina son zama agidan nan sa6anin hakan kuwa wallahi terere zan cigaba da yi miki kowa sai yaji me kika aikata da kuma sakamakon da kk samo, kema da kanki kin san sauran kin kuma san iya fin hakan ma..."

Rintse idanu nayi ina jin wani suka a cikin zuciya ta, nasan babu abinda zan iya fa'da a wannan halin wanda zai yi tasiri akan Iyami har yasa ta canza ra'ayi, dama Hamma Bukar ne 'dan gaban goshin ta shima 'din yanzu idanun ta sun rufe akan sa, Abbahn mu kansa maganar ta yake bi kuma abu ne me wuya ya canza maganar sa shima.

Idanu Hamma ya zuba mata har takai 'karshen maganar ta a hankali ya furta " Dan Allah Iyami kiyi ha'kuri....".
" kar ma ka fara..."
Iyami tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fa'din hkn gami da 'daga masa hannu.
sannan ta cigaba da fa'din" ai na riga na bata za6i..sai ki za6a ko shegen abin nan ko kuma zama a cikin gidan uban ki.."
Sunkuyar da kai nayi hawaye na na sau'ko min sosai, Abban mu, na kalla naga yadda shima ya tsura min idanu yana kallo na bansan tunanin me yake yi ba, ban kuma san damuwar da ta dame shi cikin ransa ba.

A hankali na kalli Hamma da naga ya shiga alamu na rashin mafita" IYami ni dai ina son ta dan Allah ki barni in zauna da ita.."

Baki Iyami ta kya6e gami da karkata kanta tana fa'din" asararriya kawai, kin dai cuci hijabi wlh...kuma ba dai a gidan nan ba in sake nanata mk, sau 'dari idan zance wani abu kan zancen nan toh kuwa abu guda zan yi ta nanatawa ..".

Hamma na kalla na lumshe idanu na kuma bu'dewa sannan na kalli mahaifi na a hankali na furta" Shikenan Iyami, zan tafi, zan bar gidan nan Insha Allahu bazan zauna da ita anan ba...".
Yadda na 'kurawa mahifina ido nake maganar ya sani fahimtar wani 6oyayyen abu cikin idanun sa, domin da jin zan bar gidan naga ya lumshe idanun sa da 'karfi ya juyar da kai gefe.

Nasan bai ji da'din magana ta ba, sannan da za'a tona zuciyar sa ba son ransa bane hakan ya faru amma sam bashi da damar dakatar da komai, biyayya yake yi tamkar yadda mu 'ya'ya muke yi.

Ga Hamma Bukar na dawo da duba na da tuni ya mi'ke tsaye ban ma kula ba sai a lkcn.

Nima tsayen na mi'ke nace" Hamma na zan tafi....zan bar gidan nan, zan tafi wajen...."
Bai kai ga rufe baki na ba naji ya saukar mari gefen kunci na, kafin in yi kyakykwan motsi na sake ji ya sharara min wani marin nan na tashi da mari har guda biyu.

Da duk hannuwa na na dafe kunci na hawaye na sakko min nk binsa da kallo.

Shi kansa idanuwan sa hawaye ne a cike taf... amma ko 'diss bai bari ya sauko ba.

Zuciyar sa ke yi masa tafarfasa da jin kalaman Iyami da kuma furuci na na cewar zan bar gidan, amma ya kasa furta komai a zahiri....

Hannu ya kuma 'dagowa ya nuna ni da 'dan yatsa yana kallon cikin idanu na.

Jikin sa rawa yake domin ko hannun nasa ka duba zaka fahimci hakan.

Yarfar da hannun yayi gami da juyar da kansa gefe cike da tashin hnkl.

Da gudu na juya na wuce 'daki na na 'dauko yarinyar da jakar kayan sawa na, dama su ka'dai ne suka kasance mallaki na a gidan...ina dawowa tsakar gidan na tarar da Hamma gaban Abban mu ya dur'kusa bisa gwiwoyin sa yana rusa kuka tamkar wanda akayi masa mutuwa gagaruma...cikin kukan yake fa'din" Abbah kana ganin abinda ke faruwa da idanun ka? Abbah kana ji kana gani mai yasa bazaka bu'di baki kayi magana ba Abbah, wallahi Abbah ba Zaituna ce ta haifi yarinyar nan ba na sani, dan Allah kuyi mata uzuri mana, me yasa bazaku fahimci irin yarinyar da kuka haifa kuka kuma raina agaban ku ba....?"

Kuka yake sosai kamar ransa zai fita irin kukan dake fita da takaici tun daga can cikin zucia, kukan da gaba 'daya ya tsinka min jiyoyin jiki na kaf, kukan da duk ya karya min duk wani 'kwarin gwiwa ta.

Ban ta6a ganin Yayana cikin irin wannan yanayin ba..sai yau ka'dai, yau 'din ma a sanadi na.

Abin mamaki ko 'kala Abbah bai ce ba tamkar bada shi ake yi ba.

Nima tuni na zube bisa sbd ganin yanayin Hamma na yake yi ya sanya ni dur'kushewa bisa gwiwoyi na ina kuka nake fa'din" Abbah ka yafe min dan Allah, ba nufi na in guje ku ko 6ata ranku ba, amana na kar6a kuma ina so in cika al'kawari na ne Abbah, Hammah dan Allah ka tsayar da hawayen ka haka nan, ciwon su nake ji a zucia ta, Hamma wlh har abada bazan ta6a yafewa kaina ba wannan hawayen da ka zubda sbd ni, dan Allah Hamma ka yafe min, duk tsawon rayuwa ta ban ta6a tunanin akwai irin wannan ranar ba, ban ta6a tunanin akwai ranar da ni zan zamo sanadin kukan ka ba...."

Kuka ya 'kwace min sosai har na kasa 'karasa abinda nayi niyyan fa'da.

A hankali na mi'ke tsaye rungume da yarinyar na sa6i jaka ta da 'dayan hannu na da 'kyar na 'daga 'kafa ta nayi gaba ban ko sake waigowa ba.

Ganin ina fita shima Hamma Bukar ya mike yabi baya na da sauri.

Kafin ya fita Iyami ta 'kira sunan sa cikin Izza da nuna ikon ta..
Cak ya tsaya amma bai waigo ba" Wallahi Abubakar idan kuskura ka kai yarinyar nan gidan ka bani ba kai har abada na fa'da maka...".

Ji yayi tamkar an 'da'd'daure shi, wani zafi yaji tamkar an zuba masa ruwan zafi saman 'kirjin sa.

Cikin ransa ya furta " wannan wani irin son zucia ne haka? Wannan wani irin shiga hakki ne..?"

Da 'kyar ya samu damar waigowa ya kalle ta da kyau yaga yanayin ta erh da gaske take yi sannan ya yi waje yana goge ragowar 'kwallan da ya zubo masa.

Taku ka'dan yayi ya cimmani sai ganin sa nayi agaba na idanun sa duk sun firfito waje sun koma jajaye.

" Hakan yafi maki ko 'kanwa ta?"
Ya fa'da yana 'kure ni da kallo.

Kuka na fara tare da sakin jakar hannu na ina shirin sulalewa 'kasa yayi saurin dakatar da ni da fa'din..." Ban ce ki tara min mutane ba, kije gidan Innani zan zo an jima na same...".

Daga haka ya bar gaba na ya kama hanyar gidan sa.

Ni kam waigowa nayi nabi bayan sa da kallo..."
'dan uwa na, abin alfahari na, sosai nake ji da Hamma na, sosai nake 'kaunar sa, amma yau ni da kaina nasan na 6ata masa ransa....
" To Hamma ya zanyi, tun jiya nake ro'kon Allah ya bayyana min abinda ya kamata inyi amma har yanzu zucia ta toshe take na rasa mafita...bani da za6i illah in barwa Iyami gidan ta kamar yadda naga tafi raja'a kansa...."
Na furta hakan cikjn zucia ta, ina hawaye na kama hanyar gidan Inna ta.
Chapter 163 · 0% Book details