← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 218

Sashe 67

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zafafe ya 'daga hannu da niyyar sau'ke mata marin da zai dawo da hankalin ta ga abinda ta aikata sai dai cikin rashin sa'a yana 'daga hannun ita kuma ta sulale 'kasa dan bashi ha'kuri ganin kan 'kafafun sa ya parantin ya fa'di sannan ya gangara amma still idanun ta na akan Moopy bata ma lura mikewar sa ba balle tasan da batun mari tana sulalewa mari na tahowa suka buga sa6ani.
Sai kan iska ya sau'ke shi.
'Baci ransa ya sake yi ganin ta kaucewa wannan bai bari 'karfin marin sa ya tafi abanza ba cike da hassala kawai ya kai mata hambari da kafarsa, rashin sa'a duk yanda yy balance ya kai harbin sai ya sau'ka a gefen cinyar Mufeedah.

Wani gigitaccen kuka ta sanya da ya kusan hautsinawa Zaitun hanjin cikin ta.

Tsaye ta mi'ke nan take kamar an tsunkule ta tana rungumar Mufeedan tana bin shi da wani kallon tsana wanda ke fita tun daga zuciyar ta...ido cikin ido suke kallon juna kowa ransa a matukar 6ace.

Tsawa ya buga mata da fa'din"...Daina kallona ni mayya..kurwata tafi 'karfin manyan ki ma balle ke..useless kawai..".

Ita dai bata yi magana ba banda hankalin ta da ya 'kara kakkasuwa kashi-kashi, kukan Moopy da ke ratsa ta ga kuma takaicin babu damar ramawa Moopy wannan zaluncin da akai mata, hakan yasa ta kasa 'dauke idanun ta da suka cika da ruwan hawaye akan sa....

Kallon fuskar Moopy ta sake yi tana shafa mata gefen cinyar tata sai gani tayi fuskar tayi ja da alamu cike da azaba take kukan.

Bata ko sake kallon shi ba ta juya ta fice abinta tana sake rungumar Mufeedah ajikin ta hawayen idanun ta gangarowa.

Daf da zata bar 'dakin ta tsinkayo muryar sa yana fa'din"...wani uban ne zai gyara mk nan 'din?"
" ....Uban da ya dakar min ''diya ta.."
Amsar da ta bashi kenan daga haka tayi waje bata ko.sake waigowa ba, kuma bata yi tunanin wannan maganar me ze iya janyowa ba...ji kawai tayi cikin ranta ta maida masa martani koba komai shima zai ji zafi cikin ransa koda bai kai zafin da Moopy taji cikin jikin ta ba.

Bata ko shiga part 'din Ammi ba baya ta koma wajen lambu anan ta samu da 'kyar ta lallashi Moopy tana kuka itama.

Sai da taga yarinyar tayi bacci tana sau'ke ajiyan zuciya kafin ta samu natsuwa amma har a lokacin bata daina jin zafin wannan bugun ba da yai wa Moopy ba...yarinyar ya buga amma ita taji zafin a zuciya, dan babu mamaki na yarinyar ya washe cikin kankanin lokaci amma itace ciwon da ya ji mata a zuci game da hakan ba me warkewa ba ne har abada.

Shi kam Raina hannu ya cusa cikin gashin kansa gami da kama kunkumi da da 'dayan hannun, alamun mamaki 'karara ya bayyana kan fuskar sa.
Iska ya furzar daga bakin sa yana sake maimaita abinda kunnuwan sa suka jiye masa ta fa'da.

Baya so zuciyar sa ta shirya masa 'karya kan abinda yaji amma ai in dai ba yaudarar zuciyar sa zai yi ba babu shakku kan abinda kunnuwan sa suka ji daga sautin muryar ta.
Wannan yarinyar da alamu hankalin ta barin jikin ta yake yi akan wannan 'diyar tata, har ni zata mayar wa magana..ni ta zage ni..?
Wata zuciyar ne tace da shi ai laifin kane malam da baka ta6a 'diyar ta ba da bazata ta6a iya yi maka ko da tari bane akan ka balle abu irin hakan.
"..to ai ni ba niyya ta in bugi yarinyar ba yar ta ba ido na ne ya rufe da takaicin abinda tayi min shiyasa ban ko lura ba 'kafar yarinyar ba, amma ai komiyene nafi 'karfin ta mayar min magana da zagi tunda ni ba sa'an ta bane, wannan yarinyar yarinyar da bata fi karfin ace na haifa ba, ko su Safaa da Marwa fa sun girme ta nesa ba kusa ba.
Jikin sa yabi da kallo yana aiyana tsadar sittirar da ke jikin sa..ya tabbata zai iya 'dauke cimar gidan su na kwana biyar lafiyayyu....

Wayar sa ya lalu6o ya danna sunan Ammi daf da zai tsinke ta 'daga, bai jira tace komai ba ya fara fa'din" Wallahi Ammi duk masu aikin kinnan basu da tarbiya kokadan...".
" Me kuma suka yi maka Rayyan a ringa hakuri dai dan Allah haba Ammi...Ammi.."
Sai kuma yayi shiru rolling idanu yayi cike da rashin madafa.
Ammi dake can 6angaren yanayin muryar sa ka'dai ya tabbatar mata da cewar ya gama 'kulewa yau 'din..ta kuma san halin fushin sa hukuncin sa ba ya yin kyau matukar aka kai sa ma'kura.

" Bana son fushin nan naka fa Rayyan..Kwantar da hankalin ka kai min bayanin komai insha Allah zan yi wa tufkar hanci."
Hannu ya 'daga ya nuna mata 6angaren stained tiles 'din hadda jikin kujerar sa da kuma carpet in dake 'kasan 'dakin tamkar Ammin na gaban sa ne.

" Kalli abinda tayi min Ammi duk da bata min parlour da lemo sannan akan wata shegiya banzar 'diyar ta zata gane ni...ni fa Ammi nayi mata magana sai ta zage ni.."
Tsaye ya mi'ke yana zaro jajayen idanun sa ya sake maimaita " Ta zagi ubana Ammi..ni Muhammad Rayyan".
Ya 'karashe da nuna 'kirjin sa...." Wallahi Ammi na kama yarinyar nan sai ma canza mata kamanni.."

Ammi kam yanke wayar tayi gaba 'daya jin yadda yaje buga mata tsawa ba mamaki ya mance da ita ce tai masa laifin ba.
Dole ta 'dau mayafi ta nufi 6angaren da rabon ta da shi bama zata iya tunawa ba, ba kasafai take zuwa ba sai da dalili kwakkwara.

Da idanu kawai take bin sa bayan ta shigo parlorn da 'yar sallamar ta, bata ga Amra ba, kuma bata yi mamaki dama dan tafi zaton cewa bata a gidan.

Duba 'daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa har can zuciyar sa yake jin haushi...kuma zuwa yanzun Ammi ta gama fahimtar da Zaitun suka samu matsala, amma ita ta yadda da yarinyar da kuma yadda da tarbiyar ta, abu 'daya kawai zaka mata ka fahimci 'daya bangaren halayyar ta shine ka ta6a mata yarinyar ta tana kuma da yi'kinin shima ya ta6o yarinyar ne tunda har ta shigo cikin zancen, akan Moopy ka'dai ne Zaitun bata iya sarrafa 6acin ranta kuma ita kam bata ga laifin ta ba tayi mata uzuri akan hakan domin duk wata uwa burin ta bai wuce ta kare martaba da asalin yayan ta ba.....

Bata gama wannan tunanin ba ta tsinkayo muryar sa yana fa'din" Ammi tell her to leave this house in ba haka ba wlh zan illatata who d hell is she? akan wata shegiyar ''diyar ta?
Akan ta aka fara haihuwa ne ko me?..nima nan badan ikon Allah ba ai da ina da 'diya ko yaro na agabana, yaushe ma 'ya'yan gaba da fatiha suka samu license na zama daidai da kowa?
Ko kuma tsabar ta nuna wa mutane cewa itan cukakkaiyar mara tarbiya ce shiyasa zata budi baki zage ni bayan ta gama yawon barikin ta? Ni da ita waye abin zagi Ammi..? Wama ya bata wannan damar a gidan nan..?"

Saurin matsawa kusa da shi Ammi tayi ta kamo hannun sa, ta zaunar da shi sannan ta mi'ke frigde 'din nasu ba komai a ciki sai madara da kuma ruwa...ba mamaki 'karewa duk sukayi kuma ba'a saka wasu ba amma tana da tabbacin akwai a store.

Ruwan ta 'dakko masa mai sanyi ta bashi ya kuwa kafa kai ya shanye tas.
Baya yy ya jingina bayan sa da jikin kujera ya lumshe idanu.

" Allah ya huci zuciyar Baba na..".
Ta fa'da tana murmushi gami da duban fuskar sa.
Bai tanka Ammin ba haka kuma baiyi alamun zai tanka 'din ba.
" Ayi hakuri a kuma nutsu, kar fushi ya gusar maka da tunani Rayyan har ka dinga fa'din wasu maganganun da basu dace ba musamman wa'danda baka da tabbas akan su, shaidar zina girma ne da ita, ni kaina da kk gani haka na ganta da 'diyar ta kuma dana tambaye ta sai naga kamar bata shirya bayyana asalin labarin ta gareni ba shiyasa kawai na share amma duk da haka bamu da hujjar sheganta mata 'diyar ta, domin idan kayi mata duban natsuwa zaka fahimci Zaitun nada wani abu 6oyayyen cikin zuciyar ta wanda yake yi mata ciwo, walwalar ta fa ka'dai Mafeedah ce, idan kaga tayi murmushi to Mufeedah ce, idan kaji tashin dariyar ta to tare suke, ni da kaina na fahimci hakan, domin duk zaman mu da ita ban ta6a ganin asalin farin ciki me fita tun daga zuciyar ta ba sai ranar da na siyowa Mufeedah kaya anan na fahimci lalle farin cikin ta na manne ne da na Mufeedah, bata damu da komai ba na jin da'din kanta burin ta a kullum Mufeedah tayi farin ciki...akan yarinyar sai ta hana idanun ta bacci ko kuma wani abu muhimmi da ya danganci tata rayuwar.
Tana da hakuri, tana da tausayi sai dai Zaitun sam bata 'daukan wulakanci a wajen koma waye ne..uwa uba bata da kawaici ga duk wanda ya ta6a mata yarinyar ta, ko da bazata iya 'daukan mataki ba sai ta nuna 6acin ranta a zahiri...ko kaima 'din na tabbata ka ta6o mata 'diyar ta ne shiyasa har kaga tayi maka rasar kunya hakane ko ba haka ba.?

Shiru yy bai tanka ba kar yadda kuma bai bu'de idanun sa ba.
Banda juya kalaman Ammi babu abinda zuciyar sa ke yi.
Dama haka uwaye suke? Sadaukar da farin cikin su suke yi saboda yayan su? amma ai ita wannan natan har yy yawa.

Ammi ce ta cigaba da fa'din " yanzu dai kayi ha'kuri, irin wannan fushin ba naka bane sam bana 'kaunar sa, kayi 'ko'karin kore shi dan Allah Rayyan kaji, kuma ka manta da batun yarinyar zanyi mata magana insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba..."
Bata gama rufe bakin ta ba ya bu'de idanu ya kalle ta da alamun tambaya amma bai furat ba.
Cikin zuciyar sa ya ayyana kina nufin haka zan barta taci bulus bayan ubana da ta zaga Ammi..?
Chapter 67 · 0% Book details