← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 218

Sashe 23

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaitun bata ji zuciyar ta ta sake ba har sai da ta tsinci kanta a bakin layin da ya kasance shine gaba da na Hajjaju, tayi hakan ne kuma saboda ta jirkita tunanin duk wanda ya fito da niyyar neman ta, tayi tafiya me nisan gaske da har duhun maghriba ya riga ya gauraye ko'ina sai hasken farin wata, tabbaci da taji cikin zuciyar ta cewa ta yiwa Hajjaju nisa ya sata sakin ajiyar zuciya, kuma sai a sannan taji natsuwa ta 'dan shige ta, ko ba komai ta rabu da masifa, ta rabu da mugun iri ita da 'yar ta, ta rabu da makasan farin cikin ta...domin aganin ta duk me niyyar raba ta da Mufee toh shine babban makashin farin cikin ta a duniya, _marar 'kaunar Mufeeda kuwa bata jin har duniya ta na'de itama zata kaunace sa_ .

Da yake tana hutun sallah hakan yasa bata yada zango ko'ina ba tafiya take batare da waiwaye ko 'dar ba har akayi sallahr isha'i tana kan tafiya, tun tana ji da ganin hayaniyar mutane har ya fara tsagaita, gari ya fara yin shiru, bataji tsoro ko 'dar ba wannan karan ma, dan tasan itace 'kwarin gwiwar duk su biyun, idan ta karaya tun yanzun bata jin zasu iya cimma nasara, amma har sai yaushe zata bar wannan guje gujen?, har sai yaushe natsuwa zata same su itada Mufee..?" wannan abin na cimata rai ba 'dan kadan ba.

Bata so Mufeeda ta taso ta tarar da su cikin wannan halin, bata so rayuwar yarinyar ta 'kuntata...bata so sam taci amanar da Allah ya bata.
Ba Zaitun ta dakata da tafiyar ba har sai da taji ta gaji da tafiyar, taji 'kafafun ta sun gaza tafiyar kafin ta sarara karkashin wata rumfa da ta kasance majalisa ce ta wasu manyan mutane amma da rana suke zaman majalisar ba dare ba..nan rumfar take gefe daf da titi..kuma anan Zaitun ta yanke shawaran kwana dan aganin ta yafi mata musamman da taga tabarmi ninke ajiye a gefe..zuciyar ta taji tafi kwanciya mata da nan din, dan zuwa yanzu ta gaji da halin mutane, bazata sake neman alfarma wajen kowa ba matukar ba ya zam mata dole bane, mutane 'daya suke duk karshe tsagwaron butulci suke nuna mata..gara tayi rayuwar ta, zata nema da duk karfin ta, da lafiyar ta da lokacin ta, zata yi duk wani aiki ko min wuyar sa dan tseratar da rayuwar ta data 'yar ta.

'Bangaren su Oganniya Hajjaju da 'yan matan ta kuwa, duk wani shirye shirye sun kammala dan Hajjaju ta riga tayi magana da Hajiyar Bangis, ta kuma amince zata kar6i yarinyar, dan haka a yau din nan ba sai gobe ba zasu kai mata Mufeeda.

Maganin bacci aka shirya cikin abincin Zaitun wanda da zaran taci babu 6ata lokaci bacci mai nauyi zai 'dauke su daga ita har yarinyar matukar abincin ya ziyarci cikin su, koda 'dan ka'lilan ne kuwa sai ya bugar da su, a fa'dar su hatta ita yarinyar sai dai ta budi taga babu uwarta haka ma Zaitun zuwa lokacin da maganin zai sake ta Mufeeda tai mata nisa...shikenan an musu farraqu.

Duk da Na'eema na jin babu dadi cikin ranta na yadda duk yinin yau din ita ke ta hidimar abincin Zaitun tamkar wata baiwar ta sai dai na yanzun bata ji wancan damuwar tayi tasiri cikin ranta ba musamman sbd yadda take ganin nasara ga cikar burin su, ba 'karamin 'kaguwa tayi taga wannan Zaitunar ta dulmiya cikin harka irin tasu ba, duk da kwanaki data kwankwasata ta fahimci kamar ba'kuwa ce a harkar sai dai ta kasa yadda sam da hakan musamman kuwa data ke ganin ta hadda yarinya.

Daga baya ta fara zaton ba mamaki ta haifi yarinyar ne ta hanyar aure tunda ba wata wayayya bace kila auren kauye ne ko kuma dai wani abu haka har 'kaddara ta jefo ta cikin su.

Koda Na'eema ta 'karasa bakin 'kofar ta turawa tayi gami da 'yar sallama, baki ta kya6e ganin babu kowa a dakin ba da alamu suna bayi ne, dan ba tun yau ta fahimci wannan 'dabi'a ta Zaitun ba, ko wanka zata bata barin yarinyar da ita take shiga abin ta, ta kuma rasa wannan dalili sai kace akan ta aka fara haihuwar kyawawa, inda ta 'karashe tunanin nata da sakin gajeruwar tsaki..(cKowa da abinda ya dame sa kenan... Ita kuma Na'eema kyawun yarinyar ya dame ta..)
Baki ta kya6e a fili ta furta" Yau dai zamu ga 'karyar soyayya..."

Ajiye abincin tayi da nufin anjima zata dawo bayan ta tabbatar sun gama ci, da yake ita ce mai kula da al'amuran Zaitun din ya sanya ba'a saka kowa ba sai ita gudun kar Zaitun ta gano wani abu..a yanda suka shirya sai in Na'eema ta koma ta tabbatar sunci kuma sunyi baccin kafin ta. kai rahoto wajen Hajjaju...wanda a lokacin ne komai zai kammala.
Cikin rashin sani basu san cewa Zaitun tai musu nisa ba zuwa wannan lokacin.
Bayan kusan mintina ashirin kafin Na'eema ta dawo, ga mamakin ta babu abinda ya canza, kofar 'dakin nan nan a yadda ta bar shi, kofan bayi ma haka, uwa uba abincin da ta ajiye shima haka.

Idanu ta waro ta tafi ga abincin ta bu'de ko 'dis baiyi ciwon kai ba, 'kofan bayin ta 'dan buga.."Zaitoon..!"
Shiru ba amsa..."..Zaitoona!!" Ta dan 'kara karfin sauti...." Maman Mufeedah....."
Ta 'kara 'kiran sunan ta akaro na uku.
Still shiru babu amsa, dan haka sai ta tura 'kofan bayin...wayam taga bama alamun an shige sa awanni ka'dan baya..duba da yadda yake a bushe kamas.

Cikin 'dakin ta dawo da kallon ta...tabi kwantacciyar katifan da kallo gyare tsab yake babu ko alamun an a hausa mintina kadan baya.." .toh ina suke...?"
Ta tambayi kanta.
Baya kadan ta matsa sai taji 'kafar ta take abu a 'kasa da sauri ta kai duban ta wajen abin, sai taga wata 'karamar takadda ce, saurin kaiwa hannu tayi ta 'dago shi sai a sannan ta fahimci katin receipt ne na wata Pharmacy "..Zaitun Ahmad...". Ta karanta a fili sai kuma address 'din inda Pharmacyn yake.

" Ina suka shiga ne..?"
Ta sake tambayar kanta karo na biyu.
Komawa tayi gaban waldrop din kayan su ta bu'de...sai taga jakan kayan su nan kamar yadda yake a kullun.

Tuno Pampers din Mufee dake nan gefen jakar 'dazu da safe da ta ganshi yasa takai duban ta wajen wayam tagani babu shi babu alamun sa...." Zaitun ta gudu..."!
Ta furta a fili tare da maida kofan waldrop din da karfi ta rufe.
Dole yadda tayin da ace da wani cikin 'dakin sai ya firgita amma da yake babu kowa ita kadai ce hakan yasa bata damu ba, Sameera da dakin ta ya kasance daura dana Zaitun din itace ta farga da tashin karan da tajiyo wanda hakan yasa ta lekowa.

Na'eema waje tayo da gudu tana kwala kiran sunan Hajjaju....

Salmerh 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...15*

"...Hajjaju Zaitun ta gudu..."
Shine abinda take fa'di tun ma kafin ta isa ga Hajjajun...
Sameera da ta leko bayan ta tabi da kallo cike da rashin fahimta...
Yanayin yadda Na'eema ke maganan da karfi ya sanya duk wani dake cikin gidan ankarewa lokaci guda duk akayi haduwar kaska a babban parlourn Hajajjun..kowa na son jiyewa kunnuwan sa rahoto...." Wlh bata 'dakin kaf na bincika Hajjaju.."!
Cewar Na'eema tana duban Hajjaju.

" Kamar ya bata dakin?...kin tabbatar bata bathroom...?"
" Hajjaju duk na duba da alamu ma ta dade da barin dakin dan hadda wasu kayan amfanin su ma babu...".
'Dunguma duk suka yi tamkar umarni ne ya riske su kowa so yake ya gani da idanun sa ba sai an bashi labari ba.

.....Wayam suka ga 'dakin kamar dai yadda Na'eema ta labarta musu..." Zonan ina Sa'eeda? je kira min Baba Habu da Allah...yaushe yarinyar nan ta bar gidan nan fisabilillahi babu wanda ya sani...wannan wani irin asara take shirin janyo min...?"
Tayi tambayar tana duban 'yan matan ta yayin da Sa'eeda tayi hanyar waje zauwa wajen mai gadi dan cika umarnin Hajjaju.

Tare suka dawo da Sa'eeda yana bayan ta inda ya same su tsatststaye kan kafafuwan su illah Hajjaju da tsayuwan ya gagare ta ta zauna bakin katifa.

Tun kafin ya kara sa isowa gaban su Hajjaju ta jefa masa tambaya," Baba Habu an samu matsala, ya akayi ka bar yarinya ta bar gidan nan batare da ni na sani ba..?"
" Yarinya kuwa Hajiya...wlh bansan anyi hakan ba.."
" Ga shi dai an duba bata nan Baba Habu, kuma dole nasan ta 'kofan gate ta fita tunda ba wata 6oyayyar hanya bace ta daban a gidan".
" Hajiya wlh ni dai ban ga fitan yarinya ba, ban san kuma yadda akayi hakan ya faru ba, amma ki kwantar da hankalin ki Hajiya bari a dubo ko batayi nisa ba....."
" Daga haka ya juya ya fita abinsa dan baya so maganar tayi tsayi da shi, cikin ransa yake mitar kun kawo yarinya taga bazata iya irin hallayar ku ba badole ta gudu ba, babu wani inda zani neman ta Allah ya kara rufa miki asiri yarinya..."
Ya fada cikin ransa yana me nufar bakin gate, shima kansa zaman dole yake saboda rashin madafa amma me za sa ya tsaya zaman gadin karuwai 'yan iska...shi be san yarinyar da Hajiyan ke magana akai ba dan bai san an kawo ta bama sauran 'yan matan Hajiyan ne duk ya san fuskar su kuma sukan fita koda su kadai ne su kuma dawo abinsu....koda ya fita yawata wan sa yaje yayi ya dawo yace bai fa ganta ba shi kam.
.." Wlh Baba Habu yarinyar asara zata ja min, da yake ban fara saka ta cikin harkoki na ba kafin yau din yanzu ne na gama komai akanta har an shigar da sunan ta alayi amma ta gudu yaushe ma na maida gurbin asarar da 'yan fashin nan suka jaza min sai ga wani kuma...?"
Hajiya ta fada da raunin murya.
" Sai hakuri Hajiya Insha Allahu za aganta ".
Daga haka ya juya ya fice abinsa.
Yana Allah wadaran halin su.
Chapter 23 · 0% Book details