← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 218

Sashe 165

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yy 'yar murmushi sannan ya 'dora da fa'din" a gaskiya ni dai banda shi irin wanda kk so 'din, amma kuma munyi magana da Habu ma ai ya bani sa'kon madarar yaran, rashin samun hanya ne kawai ya hana sa'kon isowa amma tuni..ku'din yana can na tura...".

Da jin hakan na washe ha'kora, godiya sosai nayi masa tamkar wacce ya bani wani gagarumin kyauta.

Shi kanshi yaji da'din godiyar da nai masa domin a saman fuskar sa na fahimci hakan.

Sai yace" Kafin isowar wancan 'din ina ga zaki iya bata wannan glucose 'din.. yana 'dan 'karawa yara kuzari sai adinga sanyawa cikin ruwan da ake bata zuwa yammaci ma idan sa'a kayan zasu iso"...godiya sosai nayi masa tare da mi'ka masa ku'din hanni na yace a a na barshi kawai in koma gida.

Haka na koma zuciya ta fal farin ciki da 'kaguwa sa'kon salele ya iso.

Sale kam ko bayan tafiya ta ma kai ya girgiza cike da tausaya wa.

Wani da yazo siyan magani bayan na bar wajen shine ya bi baya na da kallo har na 6acewa ganin sa.

Dogon tsaki yaja yana mi'kawa Salele ku'din hannun sa yake fa'din" Dunia ta zam abinda ta zama wlh yanzu"

Salele yace" Sai Addu'a kawai".
" Badole ba! Ai dole ma mu tsananta addu'a in ba hk ba dubi 'yar yarinyar nan amma har tasan tayo ciki ta haife babu ko kunyar Allah balle ta mutane har da fitowa cikin gari yawo tamkar wacce ta aikata wani abin aba mata?".
Ransa 6ace sosai yk maganar nan yana kuma yin ta ne cikin harshen Kanuri.
Kai Salele ya girgiza yana duban sa yace" Kana da hujjar da zai tabbatar da cewa itan ce ta haife 'diyar...?"
A hassale yace da shi" Wace hujja kuma Sale kk nema bayan wanda ya riga ya bayyana..?"

" Wannan ba hujja ba ce sam, ku sake tsananta tunani mana, yaushe tayi cikin yaushs ta raine shi kuma duk bb wanda ya ta6a lura har sai da haife? Ku ringa shaida akan abinda kuke da tabbaci dan Allah, ina tabbatar mk cewa yadda wasu suka 'dauki abin ba haka yake ba, na tabbata da Zaituna ta haifi yarinyar nan dagaske da babu abinda zai sata fitowa ina cigiyar abinda zan bata matsayin abinci alhali abincin ta na nan tare da ita kasani nasani, indai zata iya haifewa toh menene kuma shayarwa ai bazai bata wahala ba, sannan kowa yasan halin ta fannin, natsuwa, hankali da sanin ya kamata ta riga ta ci tuta ta wannan fannin, bai jima bama fa muka yi musu akan 'yan matan garin nan kaf amajalisar mu kan wacce tafi hankali da natsuwa kowa Zaituna yake yaba sai gashi jiya- jiya kuwa baki ya sauya hatta Modu da shi zai aure ta ma zagin ta yake yi da sunan da bai dace ba, dama dunia da mutanen cikin ta sam basu da tabbas, da bakin sa yake cewa shi dama da jimawa ya kasa gane kan yarinyar kuma fa 'karya ce kawai, wai kullum tana 'kunshe cikin hijabi ashe ba abin arziki take kunshewa ba, jifa kayan takaici irin ta Modu, jiya baki na kamar zai yi tsayi, a gani na ai ko bata ci darajar matar auren sa ta gaba ba ya kamata taci darajar matsayin 'kanwa da take da shi a wurin sa..."

Shiri yayi yana duban gefe tsawon wasu mintina, sannan ya saki ajiyar numfashi.
Abinda yk so ya sanar da Sale ya bashi ya juya yana fadin" Allah ya kyauta..." Ameen" Inji Sale.

Da gaske shi bb ruwan sa dan hatta Hamma Bukar shi ya kai masa lbrin kuma bai canza komai ba cikin abinda na fa'da masa.

Ya kan yawaita yin musu da mutane kuma akan hkn.

Yace" _ni kaga yarinyar nan bazan ta6a yi mata mummunan shaida ba, domin da bakin ta bani labarin duk abinda yake faruwa tun ranar da abin ya faru, kuma ni banga alamar 'karya tattare da ita ba har ga Allah.._ "

Ko da yaji cewa mahaifina ya kore ni ma ba 'karamin tausayi ne ya kama shi ba, sosai abin ya tsaye masa a zuciya har sai da ya yiwa Hamma Bukar maganar inda yace masa yana bibiyan lamarin dai a hankali tukunna Insha Allah zai shawo kan Abbahn, sai da yaji hkn sannan hankalin sa ya kwanta.

Kafin yammaci Hamma Bukar yazo ya kawo madarar da kansa, farin cikin da naji kamar in rungume shi, bayanin yadda za'ayi amfani da shi yayi mana sannan ya 'dauki yarinyar yana kallo na yace" wani suna zaki saka wa 'diyar ta ki ne 'kanwa ta..?"
'Dan murmushi nayi ina yin 'kasa da kaina nace" naji Mahaifiyar ta ambace ta da suna Aishatu ".

Murmushin shima yayi yana gyara ri'kon yarinyar a hannun sa.

Ba 'karamin da'di nake ji ba da yadda Yayana baya nunawa yarinya ta 'kyama, hakan yasa yake 'kara samun wata gurbi cikin zucia ta gagaruma.

A wannan ranar da akayi mata huduba da suna Aishatu...kwana nayi banyi bacci ba sbd tsananin farin ciku, tana rungume da jiki na, idan na kalli fuksar ta sai inji sanyi a zucia ta, in gaji da rikon ta sai in kwantar da ita saman ciki na, gani nake tamkar idan na ajiye ta wani abin zai zo ya 'dauke min ita...balle yadda nasan kowa 'kaunar ta yasa dole nake kaffa- kaffa da abuna...kuma tsayin daren kaf murmushi bai bar saman fuska ta ba.

Kafin gari ya waye babu tunanin da banyi ba game da sunan ta, na kasa tantance wani suna ya kamata in kira ta da shi, cewa nake yadda take da kyau din nan toh suna mai kyau mai dadi nake so na 'kaira ta da shi amma na rasa wanne yafi dacewa ..'karshe dole na hakura domin da gaske ni ba sanin sunaye nayi ba sai dai irin namu.

Kullymum addu'a ta shine..Allah ya taimake ni ya bani ikon kulawa da ita, yah Allah ka hana kowa raba ni da ita, Yah Allah ka sada mu da alkhairin dake tattare da junan mu tsakanin ni da ita.

Ko cikin sallata addu'a ga Mufeeda shine abu na biyu da ke biyo bayan addu'a ta farko...bayan na yiwa iyaye na Yayana da kaina Mufeeda nake 6ata lkc wajen yiwa addu'a...babu kalan addu'ar da bana mata, Allah ya raya ta, Allah ya sa kar idan ta girma ta 'kini, Yah Allah yadda ya kawo kaddarar da ta ha'da ni da ita a lokacin da bana zato Yah Allah ya 'daura ni kan hanyar da ta dace da mu koda ban zaci hakan ba...Allah ya kawar da duk sharrin dake tattare da ita....

Washe gari ranar kasuwar garin mu ne, haka na 'dauki wannan dubu biyun da na fitar cikin jakar Nadia na nufi kasuwa.

A hanya na ha'du da Dije 'kawata amma ta kawar da kai tamkar bata sanni ba, turus naja na tsaya ina duban gefen fuskar ta, ga mamaki na idanun Dije hawaye suka fiddawa.

A hankali na isa bayan ta na tsaya.
Sai kuma na kasa fadin komai..baki na naji yai min nauyi.

Sam banga laifin Dijeh ba domin nasan ba ra'din kanta ne ta yanke 'kin kula ni ba babu mamaki umarni take bi kamar yadda nasan dole sai an gindaya mata akan tarayya da ni.

Da kanta ta juyo ta kalle ni idanun ta na zubda 'kwalla sosai jiki na yayi sanyi.
" Zaitoon kina nan? Ina yarinyar ki...?"
Ta tambaye ni da muryar kuka amma cikin sautin muryar ta na fahimci alamun farin gani na tattare da shi.
" Abinda ya dace ki fara tambaya ta kenan kema Dije...?"
Wani hawayen ne ya sake biyo kuncin ta masu gudu.
Sai ta daburce, na riga na gama fahimtar ta rashin sanin abinda zata fada ne ya sata furta hakan.

" Kiyi hakuri, ki yafe min kinji Zaituna, ni ban guje ki ba, kuma har abada bazan ta6a guje ki ba musamman akan abinda nasan bazaki ta6a aikatawa ba, shaidar da nayi mk cikin zucia ta ina da yakinin da shi zan mutu babu abinda zai canza shi.. nasan 'kaddara ce ta ha'da ku,
sai dai wannan 'kaddara ce zazzafa Zaituna tunda gashi tayi nasarar shiga tsakanin mu...ki rike amana kuma tsananta addu'a ta Insha Allah 'diyar ki alkhairi ce agare ki, da iznin Allah kuma bazaki ta6a yin danasanin kasancewa da ita ba...".
Daga haka ta juya bata 'kara waigiwa ta dube ni ba.
Dije na kenan, itama mun rabu kenan...?"
Na tambayi kaina.

Kafin in dawo daga 'dan guntun tunanin da na fa'da Dije har tayi nisa.

Bansan lkcn da na kwasa a guje nabi bayan ta ba.

" Dijeh..!"
Na 'kira sunan ta da 'karfi.
Cak ta tsaya amma bata waigi ba, 'ko'kari take ta cika umarnin mahaifan ta amma abin na neman gagarar ta.
" Dije nagode sosai...!"
Kawai na furta bayan fahimtae da nayi cewa ba tsawaita zance take da bu'katar yi da ni ba.

Sai a licn ta waigo, hawayen idanun ta sun bushe, ni kuma a lkcn nawa suka sakko.

Hannu ta 'daga min alamun bankwana, amma ni na kasa maida mata martani.
Kai na juya mata kawai alamun amsawa.

Daga haka tayi tafiyar ta, shikenan Dije na ta barni kenan, daga ranar ban sake saka ta a idanu na ba.

Na jima tsaye a wurin ina zubda 'kwalla har na daina hangen Dije kafin na 'daga 'kafafu na da 'kyar na shiga kasuwar da na fito da niyyar zuwa.

Riguna na siyowa Aishatu kala uku sai Panties guda hu'du, farin Powder da man shafan ta, kwalli da safa 'kafa uku da huluna guda biyu..sai omo da sabulu na wankin kayan ta.

Salmerh😘
[17/1/2023, 10:38 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...93*

.......Bani da matsalar komai yanzu sai damuwar rashin makusanta na.

Kuma akai- akai Hamma ke kawo magunguna, madara da Glucose 'din yarinyar, ko baya gari kuma ba'a fasa kawowa domin ya riga yayi magana da Mai Chemist abokin sa.

Hatta kayan sallahn mu ni da Aishatu duk ya tanadar mana tuntuni.
Chapter 165 · 0% Book details