Sashe 192
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu guda ne yafi tsayawa Innani arai shine batun auren nan da taji cikin labarin da Ammi ta bata...sai kuma batun cewa wai Aishatu 'diyar su ce ta halali...zallan iko da 'karfin mulkin Allah ne yayi aiki a wannan waje, bayaga haka taya ma hakan zai kasance? tace a can Bauchi ta tsinto ta ta kai ta gidan ta sai kuma daga baya suka fahimci ashe ma 'diyar dake tare da ita tasu ce...taya duk hakan ya faru cikin sauki haka..?anya ba wayo suka nunawa Zaitoon akan yarinyar ba, in kuma watarana dangin ta na asali suka bayyana fa...? wa za'a kama?"
Sake kallon inda Rayyan yake zaune tayi Mufee na lafe a jikin sa...sam yarinyar bata tare da damuwar komai, kama ce kuma sosai ta jini a tsakanin su amma ta yaya toh suka gane ta...?"
Irin duban da Innani ke binsu da shi yasa Ammi ta fahimci cewa bata fa yadda da su bane balle maganganun su domin a fili zaka fahimci shakkun dake tattare da ita.
Ammin ce dai ta sake bayyana mata duk yadda abubuwan suka kasance bayan fahimtar yanayin Innanin duk da hakan kuma sai taji ina kanta ya ma kasa 'dauka sam sam.
Nan ta ce ita bazata iya ba dan Allah su tafi wajen mahaifin ta tunda yana nan raye ko bashi nan ma akwai babban wanta wanda shine makwafin mahaifi agare ta, zai ma fi fahimtar su.
Ammi duban Zaitoon tayi a hankali tace" Yah Bukar".
Da kai Zaitoon ta bawa Ammi amsa tana mai share 'kwalla.
Lokacin da zasu tafi Ammi tace" ai kamata yy dukkan mu mu je har ke Innar mu tunda kema ai 'diyar ki ce".
Innani taso 'kin bin su kamar yadda Ammin ta bu'kata amma kwarjini da kamalar matar ya hanata musawa duk da tasan ba lallai ne zuwan ta gidan ya haifar mata kyakkyakyawan sakamako ba amma babu yadda zatayi, a hakan dai ta bisu suka je.
Iyami na tsakar gida tayi biji biji da ita, ciwo take a tsaye da bata san kansa da tushen sa ba.
Duk ta rame ta koma tamkar ba ita ba, ga cikin yarantan kaf bb mai tausaya mata illa Bukar, shi Goni kam ma tun lkcn da ya bar gida a wancan lkcn bata sake jin 'duriyar sa ba shekara biyu kenan yanzu idan watan Ramadan ya kama.
Can take jin kishin- kishin din wai ai ya zama 'dan fashi da makami kuma an kashe shi ma.
Damuwa tai mata yawa sosai, tana jin jiki amma ko tsinke sai tayi da gaske sannan Khausar ke taya ta dagewa cikin gidan, hatta wanke wanke yanzu ita ta ke yin abinta da kanta.
Ga Abban su babu lafia shima babu mai kulawa da shi sai Yah Bukar, hatta Iyami wani sa'in sai ta yini bata leka inda yake ba, abinci wannan sai in Yah Bukar ne yazo sannan za'a bashi, shiyasa yanzu ya rage tafiye tafiye sosai, sai ya zam masa dole ne sannan yake tafiya kuma baya ta6a wuce kwanaki uku zuwa sati 'daya, ba kamar abaya da har wata guda yana iya yi ba, bubuwa duk sun dagule masa, 'ko'karin da yake kan jinyar mahaifin san yasa kullum Azeema ke faman yi masa fitina a gida and ba sosai take samun abubuwa kamar baya ba shiyasa rashin zaman lafiyar gidan ya rinjayi zaman lafiyar.
Shi kanshi Yah Bukar din duk ya kare a tsaye sbd damuwa.
A hkn ma wai batun auren Khausar 'din ake da Babaji tsohon saurayin Zaitoon, dan tunda ta 'kyalla idanu taga yanzu yana kashe 'yan canji Iyami tayi ruwa tayi tsaki sai da aka bashi auren khausar, sai daga baya take jin ashe wai ba a ma san sana'ar da yake ba, Iyami tayi banza da zancen ita dai in zai kashewa 'diyar ta ai shikenan..not knowing that 'kasurgumin 'dan ta'adda ya koma shima...duk wasu hare hare da aka kai a yankin su shi ke jagoranta...'dan ku'din da ake basu yake zuwa yy ta musu bagu da shi.
Khausar banda 'dan banzan yawo bb abinda ta iya, ita kuma iyami bata iya tankata sai dai a bayan idanun ta tayi ta 'kananun maganganu, yayin da shi Yah Bukar tafi rainawa sama da kowa, shi ne me 'ko'karin yi mata amma kuma duk wani burbu'din masifar ta kansa take sau'kewa.
Sai dai kawai yayi ta bata hakuri, shi dai fatam sa ya rabu da su lafia ne kawai.
Ko yanzun ma masifa take faman zuba masa bisa laifin da yasan ita karan kanta tasani bashi ne ya aikata ba.
Daga nan ta gangara wai baya kula da ita yanzu sai dai ubansa ka'dai, dan ya raina ta.
Shi dai hakuri kawai yake bata...dan zuwa lkcn ya gama sabawa da 'daukan laifin da baisan mafarin sa ba balle 'karshen sa.
Sallama suka ji daga bakin 'kofa atare dukkan su suka 'dago kafin su kai ga amsawa sai ganin wata matashiya suka yi ta bayyana.
Gaba 'dayan su idanu suka zuba mata suna mata kallon sani banda Iyami da mi'kewa ma kasawa tayi.
Duk da zuciyar ta cike yake da fargaba amma hakan bai hana ta 'karasowa gaban su ba, da sauri ta dur'kushe bisa gwiwoyin ta ta saki sabon kuka tana mai ambaton sunan Yayan ta.
Sosai ya ha'de ransa yana duban ta, irin duban da ko ba a fa'da mata ba 'din nan tasan na menene.
Sai da ya nuna ta da 'dan yatsan sa kafin da rawar murya yacm furta" Zai..toona.."
Domin tabbatarwa.
Tace" Yah Bukar..."!
Inda tayi maganar cike da farin cikin ganin sa.
" Me ya kawo ki gidan nan kuma...?"
Ya karashe maganar yana hade ransa sosai.
Tambayar da yy matan ba 'karamin hautsina mata 'ya'yan hanci yy ba...bata kai ga dawowa daga tunanin ba ta sake jin muryar sa yana fa'din.
" Ki tashi ki koma inda kk fito Zaitoona, mu nan bamu bukatar sake ganin ki cikin rayuwar mu...kije ki cigaba da irin rayuwar da kk riga kk za6arwa kanki...ganin ki na sa inji tamkar wani babban ma'kiyi na ne a gaba na...ki bar gidan nan tun kafin inyi mk illah Zaitoona...."
Bata motsa ba illa sautin kukan ta da ta 'karu.
Tasan cewa dole zata fuskanci hakan koma fiye da shi, domin tasa duk cikin su bata yiwa kowa adalci ba tunda tayi tafiyar ta batare da sanin ko guda daga cikin su ba amma ai tana da dalili...musamman ma shi da ya bata muhimmanci fiye da kowa cikin 'yan uwan sa.
" Ki tashi ki fita nace".
Tsawan da ya sake daka mata yasa bata san lkcn ma data mi'ke 'da gudu tayi hanyar waje ko ganin gaban ta bata yi ba.
Shi kuma da ke tsaye daga 'dan waje kaydan sautin tsawan yasa shi saurin takowa dan ganewa idanun sa, domin yasan tabbas da Zaitoon ake.
Ya taho ta taho kowa da abinda ke ransa duk basu lura da juna ba karaf kawai suka yi karo, madadin yy baya shi kuma kawai sai ya rungume ta daga gefen sa yana mai bubbuga bayan ta jin irin kukan da take, ransa a matu'kar ha'de.
Zaitoon da ba hayyacin ta take ba jin an tallafe ta yasa ta kwantar da kai ta cigaba da rera kukan ta tamkar mai shirin shi'dewa.
Wanda bai san wace ita ba sai a 'dauka da gayya suka yi hakan.
Ba Yah Bukar da abin ya 'kara turnu'ke shi ba hatta Innani sai da taji kunya ta kamata.
Yayin da Ammi ta saki wani 6oyayyen murmushi tana kawar da kai gefe.
Anty Madeena kuwa yi tayi tamkar bata ma san anayi ba.
Yayin da Iyami ta fara tafa hannuwa da salallami...tace" Yau na shiga uku...wai menene nake gani haka ne? Bayin Allah nan ba gidan 'yan iska bane ba kuma dabar karuwa ba ce! mu 'din salihan bayi ne masu mutunci a idanun kowa, 'yar iskan gidan ta jima da barin sa ta tafi yawan barikin ta wata mai kama da waccan...dan Allah ku fita ku bamu wuri..kh fita ku bar mana gida bama bukatar irin ku yanzu...."
Dogon tsaki Yah Bukar yaja sannan ya nufi hanyar barin gidan a zuciye yana cije la66an sa, sam sam kalaman Iyami basu yi masa dadi ba amma yadda yaganewa idanun sa sai yaji takaicin sa ninka na baya, hakika Zaitoon ta wuce tunanin sa a halin yanzu, duk ina tarbiya da nasihar da ya sha 6ata lkcn sa yana yi mata abaya ina hankali da natsuwar ta suka tafi ne..?
Kafin ya kai ga barin gidan gaba 'daya Innani tayi saurin ri'ko hannun shi...sannan a hankali tace.
" Dan Allah kayi ha'kuri Bukar, badan ita ba, ko dan darajar bakin nan ka tsaya ka saurare su.."
Matar na da matu'kar kima da daraja a idanun sa kuma bazai iya musawa umarnin ta ba...balle kuma rokon sa tayi, hada sa da Allah tayi.
Kallo 'daya Innani tai wa gidan tasan cewa ya canza ba kamar yadda ta sanshi ada can baya ba, ita dai kam rabon ta da gidan har ta mance...ko ayau din kuma in da badan dalilin yakai dalili ba da babu abinda zai shigo da ita.
'Daga kai Bukar yyi nan yy arba da Hajia Ammi Asiya, gefen ta Anty Madeena ce da tun zuwan su garin tamkar ansawa bakin ta Padlock bin komai kawai take da idanu..sai Rayyan da ke can rungume da Zaitoon ga kuma yarinya kwance saman kafa'dar sa daga 'daya gefen tana baccin ta cikin kwanciyar hankali.
Marwa dai na can gida dan sam Rayyan hanawa yy ta biyo su sbd saurin ru'dewar ta ...dan haka babu ita wurin.
Lokacin da Bukar ya sa babbar tabarma akayi musu iso sannan Anty Madeena dake 'dan kusa da shi tace" toh sai aje a zauna idan an gama rasar kunyar".
Ta fa'da masa 'kasa 'kasa.
Wata uwar harara suka sakarwa juna shi da Bukar kowa abinda ke cikin ransa daban.
Dai dai da shigowan Khausar gidan tana 'dan rare wa'ka irin wanda ta saba.