← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 202 OF 218

Sashe 202

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin takun sa na isa da 'kasaita ya iso gaban ta ya tsaya cak...hannu ya mi'kawa Mufee batare da wani musu ba kuwa ta tafi wajen sa.

Hankici ya ciro yana tsane mata zufan dake saman goshin ta yake fa'din" sarkin yawo...bb ko gaisuwa ne...?"

Ya 'karashe maganar da jan hancin ta, Mufee murmushi kawai tayi masa dan baccin bai sake ta.
Yace" baki tambayi Ammi da Antyn ki Marwa ba...?"
Jin sunayen da ya ambata yasa ta saurin darawa a hankali tace" Anty...".
Yace " tana gaida ki itama"!

Zaitoon kam hanyar waje tayi ganin ko ta kanta bai bi ba, 'diyar sa ce kawai agaban sa...wani ajiyan zucia ta sau'ke Jin Bai bi ta kanta ba da alamu zuwan nasa Mufeeda yazo gani.

Har ta kusa fita ta tsinkayi muryar sa yana fa'din.." Ki ha'do min kayan ta...zan wuce da ita yanzu tunda yawo kawai kk iya koya mata..da zaman hira da wasu gardawa".

Wani irin juyowa tayi ta jefa masa kallon firgici...bai kalli fuskar ta ba amma ya jinjina mata kai alamun dagaske yake.

Bata san lkcn da ma tayi masa kallon baka isa ba tayi kicin kicin da fuska, bama shi ba hatta ita kanta sai da ta bawa kanta mamaki, bata san tayi hakan ba, Mufeeda ta kalla tana ji tamkar taje ta 'kwace ta a hannun sa..meyasa bai yi maganar ba har sai da ya tabbatar yarinyar ta shiga hannun sa? shin hakan adalci ne? Meyasa zai ce yawo take koya mata bacin tana da tabbaci Innani ta sanar da shi can gida suka je.

Idanu ta lumshe ta kuma bu'de su akan sa suka ha'de idanu...zirrr kawai sai ga hawaye sun gangaro mata da gudun su.

Bata furta komai ba kawai tayi waje da gudu ta nufi 'dakin Innani ta sha kukan ta son ranta.

Ita kanta Innar bata san cewa tana 'dakin ba balle tasan abinda ke faruwa dan a lkcn tana cikin kitchen tana ha'da abinci.'

Sai da ta kammala ta koma 'dakin da fatan Allah dai ya jeho mata wanda zata samu ya mi'ka masa abinci anan taga Zaitoon.

" Ke kuma kukan me kk anan..yaushe ma kika shigo min 'daki..?"
Cikin kuka tace
" Innani wai tafia zai min da yarinya fa..kuma wlh bashi da kirki idan yy niyyan abu...".
" Toh fa!..shin in tambaye ki mana?
"..shin 'diyar nan taki ce ne ko kuwa tashi...?"
" Innani ai dai tawa ce tunda tare ya gan mu da ita..ni dai dan Allah ki ce ya bar min kaya na..indai zaman hira da wasu ne bazan sake ba, kuma bazan sake zuwa ko'ina da ita ba"
Tana kuka sosai take maganar.
Cike da mamaki Innani ke duban ta..ganin yadda take kuka gami da ro'kon nata.
" Wannan 'daurawa kai 'din har ina wai...mutum da 'diyar sa?"
" Dan Allah Innani kice kar ya tafi min da ita.."!
" Me yasa shi baki ro'ke shi da bakin ki ba sai ni da kika raina zaki zo nan kina wani yimin kukan banza...Ni tashi kije ki 'dauki abinci ki mi'ka masa kafin yace yanzu zai wuce..".

Kamar bazata tashi ba sai kuma ta mi'ke simi simi...ta nufi hanyar waje.
Innani ta cigaba da mita..." Yarinya sam bb wayo...kowa ma sai kin bari ya gano raunin ki...shiyasa zaki ta shan wahala a rayuwa ai..."
Ko da taje 'dakin da sallamar ta ciki ciki ya amsa mata kamar yadda tayi tata sallamar.

Fuskar sa wasai tamkar ba shi ba yana ta hira da Mufee duk da ba komai da take iya fa'da yake ganewa ba koda ta fa'da amma duk da hakan biye mata yake yana kuma jin nisha'di sosai..musamman da yaga yadda take 'dan sakin jiki da shi ba kamar baya ba.

Ganin shigowar Zaitoon ne yasa shi canza akalar maganar tasa izuwa.." Mamana...dole zan tafi dake fa..bazan iya barin ki ana koya miki yawo a banza ba..."!
Wani duka da zuciyar Zaitoon yayi ita kanta sai da ya bata tsoro, kuma ko da wasa ya'ki duban inda take..balle su ha'de idanu..take har ji tayi kanta ya fara sarawa.
Kar dai da gaske yake tafiyan zai yi da ita.

Abin hannun ta ta ajiye sannan ta zuba masa abincin dai- dai yadda tasan zai iya ci, kuma duk abinda take hawaye bai bar zuba mata ba bata kuma 'daga ido ta dubi fuskar sa ba sbd tsananin haushin sa da take ji..sai da ta ha'da masa komai kafin ta mi'ke tsaye..shima mi'kewar yayi ya tari gaban ta, bisa kafa'dar sa ya kwantar da Mufee ta kuwa yi luf.
Sai ya zamana shi ka'dai ke fuskantar Zaitoon.

'Kasa sosai tayi da kanta wasu sabbin hawayen na sake sau'kowa.

Ido kawai ya zuba mata ya'ki cewa komai.
So yake kawai ta ro'ke shi da bakin ta amma taurin kai ya hana ta.

Salmerh😍
[23/01, 6:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...104*

........" Kukan fa...duk na menene haka?"
Bata ce komai ba sai ya cigaba.
" Baki so zuwa na ba ko?...nasani ai..fa'da min toh waye shi..mecece ala'kar ki da shi da har ya samu daman ta6a min kayan sawan matata da hannayen sa.."

Ba shiri ta 'dago ta dube shi..suka hade idanu.
Da sauri tayi 'kasa da nata idanun.

Sai lokacin ma ta tuna..." Yah Adam wai?"
Ta tambayi kanta.

Sassauta muryar sa yayi.
" Kina son shi ko?"
Bata san lokacin.da ta sake 'dagowa ta dube shi ba hawayen dake idanuwan ta suka tsaya cak...tabi sa da kallon mamaki.

Shi kuma ya cigaba.." Kar ki damu fada min waye shi, nayi mk al'kawarin..daga yau ma bazan sake zuwa ba..dama ita ke kawo ni..kinga idan na tafi da ita ai shikenan...sai kiyi ta yawon ki son ranki, ki yi walwalar ki da samarin ki son ranki babu mai hanaki..."!

Gefen sa tabi da gudu ta fita tsakar gida ta zauna tana share wasu zafafan hawaye cike da tashin hankali.

Rayyan bayan ta yabi da kallo tsawon mintina biyu yana tsaye a wajen sannan ya sake komawa ya zauna..zuciyar sa cunkushe yake jin ta.

Sama- sama yaci abincin wannan ma sbd Mufeeda ne dan ya lura tana da bu'katar abincin, yana ci yana bata a baki, ka'dan ya ci bai sake kaiwa bakin sa ba sai dai ita, dan ji yake tamkar 'kaya yake taunawa sbd bakin cikin da ya riga ya cika shi, sai da ya tabbatar ya ishe ta sannan ya fara shirin tafia.

Zaitoon ko tarin kirki bata iyawa sbd yadda ta matsu taga ya bar gidan ta 'dauke 'diyar ta zuwa jikin ta...addu'a take yi Allah yasa ba dagaske yake ba.

Lokacin da ya fito tafia, wani shegen ajiyan zucia ta sau'ke da taji har yanawa Innani sallama bata ji batun Mufeeda ba, sai dai murnar ta ta koma ciki ne da ta tsinkayi muryar sa a 'karshen maganar yana ce da Innani Auwal zai zo 'kanin Nadia ya 'dauki Mufeeda tayi musu kwana biyu may be ko cikin Ramadan haka.

Tunda Zaitoon tayi 'kasa da kai bata sake 'dagawa ba, ashe ma an gudu ne ba'a tsira ba, bata ma san lkcn da ya gama da Innani ya fita ba sai ji tayi Innani na fa'din ai sai ki je kiyi masa sallama da godia ko...?"

Anan ta dubi Innani da idanu Innani ta nuna mata kayan da ke jibge a gefe da alamu siyayya yai musu kenan.

Kamar bazata mi'ke ba sai kuma dai ta tashi ta fita.
Ya shiga mota yana shirin tayarwa ya hango ta, hakan yasa ya dakata.
Ko da ta iso 'kin duban fuskar sa tayi shima 'din bai damu da dole sai tayi hakan ba yace " Ya akayi..."
Yana duban gaban sa.
Tace" Angode..."!
A ta'kaice
" Da akayi me fa...? Ohh da na zo?...ai ba wajen ki nazo ba nazo ganin 'YATA CE..".
Ji kawai tayi ta 'daga kai ta kalle sa anan suka ha'de idanu..sai ya sake waro mata idanun sa gami da jinjina kansa alamar tabbatarwa.
Sai tace" Allah ya 'kara bu'di ya tsare hanya..."!

Daga haka ta juya ta koma gida ko waigowa bata sake yi ba.
Shi kansa yy mamakin 'karfin halin ta ayau 'din, yarinyar ta canza masa sosai.
Ya da'de yana tsaye batare da ya ja motar ba kafin ya gathering courage yy gaba yana me amsa waya da sauti sassanya.

Sam Zaitoon bata san zancen da ake ba, bata san komai dake faruwa ba dan Innani bata wani dogon hira da ita balle taji daga bakin ta.

Haka kawai kuma tun wancan ranar bata sake fita gidan hakan nan kawai batare da 'kwakkwaran dalili ba, ko da fita ya zam mata dole ne sai ta ri'ka jin fargabar fita kar yazo yace dagasken yawo take koyawa 'diyar sa.

Kusan ko wani lkc fargaba da gudun abinda zai janyo ya furta mata wata kalma akan Mufee take..balle wasu maza daban.

Atai'kaice dai yakan yawaita zuwa mata rai duk da bawai ta tsara hakan cikin jadawalin rayuwar ta bane ko kuma a son zuciyar ta ba.

Ko ranar da Yah Adam yazo tafia da su wajen dangin mahaifiyar ta ita har Innanin zuciyar ta fal fargaba, amma har suka je suka dawo bata ji natsuwa ba, tayi murna kam ta kuma yi farin ciki, musamman yadda taga Innani cikin 'yan uwa dangi da mahaifan ta abinda tun tasowan ta bata ta6a gani ba sai a lkcn, anyi kuka sannan aka sha hirar yaushe gamo, taga dangi sosai, taga soyayya ta zahiri, taga yadda ake nuna 'kauna ta 'yan uwantaka, hakika sunyi rashi sosai da basu san juna tuntuni ba, anan tasan ashe 'yan uwa da 'dadi ashe itama tana da nata dangin masu yawa, masu son ta, masu 'kaunar mahaifiyar ta da gaskia, domin duk wani wanda keda ala'ka da mahaifiyar ta a ranar sai da yazo suka ga juna..kowa na nan nan da su, hatta Mufeeda bb wanda ya nuna mata 'kiyayya ko kyara duk da Yah Adam ya riga yy musu bayanin wace ita matsayin 'diyar mijin ta ne...
Haka ma Yah Bukar bb wanda ya ware sa.

Amma ansha kuka, kuka ne irin ajiyayyen nan, kuka irin wanda ta jima bata ga anyi sa ba.
Sosai da sosai ta tausayawa Innar ta.
Chapter 202 · 0% Book details