Sashe 123
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
Ha'ki'ka a wasu lokutan 'kaddara abu ne mai matu'kar ban mmk, mai rikitar da tunani sanya ru'dani da kuma haifar da kwanciyar hankali ga wasu yayin da ga wasu abin ba hk yk ba, sai dai a mafi yawan lokuta 'kaddara takan riski bawa ne cikin yanayi na bazata ko rashin shirya zuwan ta, kuma ta kan zo ne cikin siga guda biyu da suke mabambantan juna, inma kayi farin ciki da zuwan ta ko kuma akasin haka, sai dai ga Zaitoon sam abin ba haka yake ba, sam ko alama har a yanzun ta kasa hasaso yanayin 'kaddararta ta kasancewar ta gidan Ammi Aseeya, ta kasa hasaso karshen 'kaddarar tun daga farkon zuwan ta har zuwa yau 'din nan, har a yanzu da take amsa suna matar Rayyan bata san wani gurbi zata sanya wannan karkatacciyar 'kaddarar ba.
Abin ya kasance mata ne tamkar wasa ko shirin drama, yayin da ta wani 6angaren take gani tamkar a gaske.
Ga dai ta a yanzu tana nan na da wani gagarumin abu akanta mai suna aure, auren da ta kasa tantance matsayin sa wajen ta kamar yadda ta kasa tantance asalin dangantaka da kuma halayen ahalin gidan Ammi Aseeya.
Tuni ta gama fahimtar mafiya yawan ahalin sun yi na'am sun kuma yi farin ciki da wanzuwar auren, yayin da 'kalilan daga cikin su a fili suka nuna 'kiyayyar su bata kuma san dalili ba.
Abin kuma bai kasance abu mai saukin fahimta ba kwatankwacin yadda auren ta da Rayyan ya kasance mai sauki kuma ya faru cikin sauki, illa bride price da ya kasance mai nauyin da ya bata matu'kar mamaki.
Da ace saukin fahimtar su ya kasance mai sau'ki kamar yadda sau'kin kasantuwar auren ta yake da sai tafi kowa farin ciki sbd cikin kalilan din lkc zata fahimci inda ra'ayin kowa cikin ahalin ya fuskanta....amma ina abin ba haka yake ba, shiyasa duk suka bar zuciyar ta cikin kokonto da wasi- wasi, banda tsoro da fargaba dake 'kara shiganta kusan kowani lokaci.
Cikin lokaci 'kan'kani duk wasu hidindimun Rayyan a hankali kaf suka dawo hannun ta, ita ke masa komai, tun tana jin nawi har tazo ta dan saki jikin ta ganin babu wani mai bi takan kunyar ta.
Baya ga haka ma ita da kanta tasan dalilin da yasa aka hada auren kenan dan haka itan tamkar baiwa ce ga shugaban ta, bata da iko, matsayi ko damar da zatace shi ya hanata aiwatar da aikin ta.
Hatta da Fawwaz ma yanzu sun saba da shi sosai, domin wasu abubuwan ma da kanshi yake 'kara koya mata yadda zata yi da kuma bi da Rayyan 'din.
'Bangaren Ammi ma hakane, domin a yanzu ta kan 'dan ji natsuwa da kwanciyar hankali duk da ba wai na wani can can bane amma dai da sau'ki fiye da baya.
Saboda kusan kowani lokaci gani take tamkar an takura Zaitoon ne, an kuma shiga hakkin ta, duk da Zaitunan ta tabbatar mata da cewa ba yadda take tunani bane amma ta kasa fitarwa cikin ranta.
A halin yanzu ba Rayyan kadai ke bata tausayi ba hadda ma Zaituna, shiyasa itama take biye Anty Madeena gaba 'daya sun 'dauke mata hidima da kula da Mufeeda a wuyan ta, gudun wai kar abubuwan suyi mata yawa, wani sa'in ma hatta kwana Mufeeda batayi wajen Zaitoon kuma bata damu ba.
Hakan shi ya sake haifar da wata sabuwar sha'kuwa tsakanin.su gaba 'daya.
Wani 'bangaren kuma sanin da Ammi tayi cewar Zaitoon na matukar kokari wajen kulawa da Rayyan tana kuma nan tare da shi kusan kowani lokaci yasa kullum banda albarka babu abinda take sanyawa Zaitoon... domin aganin ta tai mata halaccin da ba kowa ne zai iya mata ba, ta mata abinda tasan har abada bata da abin saka mata da shi sai dai ta bata wani babban matsayi cikin zuciyar ta da tasan zai yi wahala ya bar mata zuciya, yadda da amanar ta duk ta dan'kata ga Zaitoon da ya'kinin bazata ta6a cutar mata da shi ko watsa musu 'kasa a idanu ba.
Yawan godia da albarkar da Ammi ke sa mata ya sanya Zaitoon jin da'din ayyukan da take yiwa Rayyan.
Bata ta6a jin cewa wahalar banza take yi ba saboda tasan tana faranta ran Ammi dama sauran 'yan uwan sa..hakan kuwa na sake tsunduma ta cikin farin ciki da walwala itama...ya kan kuma kara mata karsashin aiwatar da ayyukan ta gare shi.
Shine dai bata da tabbacin zai yaba ko akasin haka, amma sam bata shi take ba, bata amincewar sa rashin sa take ba, burin ta tayi ta samu lada na biyu kuma ta farantawa mahaifan sa musamman sbd yadda taga itama suke kula mata da yarinya kamar ransu.
Har wata Nanny gareta yanzu a gidan domin kulawa da ita ita ka'dai.
Hakan kuwa da suka yi sosai ya 'kara musu daraja da kima a idanun ta.
Fatan ta da addu'an da bata gajiya da yinsa a yanzu kawai shine Allah ya bashi lafiya ya tashi kafadun sa cikin aminci domin tasan da zarar ya samu sau'ki shikenan komai zai zo 'karshe.
Aure da hidimar duk 'karshen su kenan.
Bata sake saka Sultan a idanun ta ba sai da aka dauki tsawon wasu kwanaki sannan yazo duba jikin Rayyan fuskar murtuk babu fara'ah dai dai da 'yar ka'dan, hatta gaisuwar da Zaitoon take yi masa ma bai amsa ba itama kuma hakan bai dame ta inda sabo ai ta saba da irin hakan tunda 'dabi'ar Rayyan ce ga Sultan ne dai take sabuwa a yanzu bata kuma san dalili ba.
Washe garin zuwan Sultan take jin labari a bakin Marwa wai a Amrah ta 'kira wayar Rayyan Anty Raihana ce kuma ta amsa, tsabar shiga rudu da zafin kishin dake cinta tama mance da cewar Rayyan fa ne kwance ba wani daban ba.
Da jin an 'dauki waya bata tsaya bi ta kan waye kan layin ba kawai ta fara surutai cike da 6acin rai...tana fa'din..." Yanzu Baby dagaske aure kayi? Auren ma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar aiki na dan kawai ka tozarta ni..?..'yar aiki fa Baby..? 'Yar aikin ma wai Zaitun fisabilillahi..?"
" Hakan dai ne ya kasance kuma babu ja da baya Zaitoon da kika sani mai taya ki ayyuka abaya ba ita ce Zaitoon din mu ta yanzu ba domin wannan matar Rayyan ce..".
Shiru Amrah tayi daga can 6angaren tana mai jin kukan takaici da bakin ciki na taso mata.
Da hannun ta 'daya ta toshe baki gudun kar sautin kukan ta yafito fili tama kasa cewa komai.
Anty Raihanan ce ta cigaba da magana.
"...mene dama yafi dacewa da duk matar da ta tafi ta bar mijin ta cikin mugun yanayin da tasan cewa yanada bukatar ta kusa da shi? Ita matar ta mance ne cewar ba ita kadai ce mace cikin duniyar ba ko me? Ke anya ma Amrah kina da kunya kuwa, sai yanzun kika san ki 'kira sbd kinji batun auren sa daga bakin wasu amma da kanki kinsan halin da kika barshi ciki amma hakan bai sa kin 'kira ko da sau 'daya bane kiji lafiyar sa.....?"
Da sauri Amrah ta kashe wayar batare da ta jira karshen maganar ba.
Koda Marwa ta gama bawa Zaitoon labari ji tayi babu dadi, cike da sanyin rai tace da Marwa" ai da Anty Raihana bata ce mata haka ba...ayi mata uzuri mana, kinga fa itama biyayya ta yiwa mahaifiyar ta..."
" Dalla can 'kyale ta, ni wlh an min dai dai, gara tasan cewa bata kyauta ba.
Cewar Marwa tana barin 'dakin.
Nan ta bar Zaitoon zugum tana tunani a zaune, gani take tamkar itace silar komai, kuma bata so taga ta kuntatawa wani sam a rayuwar ta, sosai ta 'kara kaimin addu'ar ta gareshi ba dare ba rana.
Burin ta ya samu lafia ya sallame ta kowa ma ya huta.
'Bangaren Amrah kuwa sosai tasha kuka, taji aranta cewar bata kyauta ba sam bata kuma ankara tun farko ba sai yanzu da maganganun Raihana suka ankarar da ita.
Tun zuwan ta gidan mahaifiyar ta ta mantar da ita komai, domin duk wani abu na jin dadi wanda zai kawo mata kwanciyar hankali shi ta ri'ka yi mata take kuma sawa ake mata...dan hatta Arfan tsakanin ta da shi shayarwa shima din sai ta ga dama.
Fita ko'ina babu mai taka mata birki ko da yini zata yi kuwa.
Hakan kuwa ya sa suka cigaba da holewar su da Sultan bayan ya shawo kanta da kyar domin tsoron sake jefa kanta cikin kuskure take tunda Allah ya taimake ta ta tsallake na Arfan babu wanda ya 'dago.
Amma da yake Sultan shegen kaya ne tuni ya kalallame abar sa ya nuna mata cewar wancan ma kuksuren ta ne ya jawo, da ace tana bin maganar sa da ka'idar maganin da yake bata da duk hakan bai faru ba amma zasu kiyaye bazai sake bari a maimaita makamancin kuskuren ba.
Amrah ta kuwa amince da shi, kusan kullun sai yazo ya dauke ta ko kuma su hada appointment na wajen haduwa kawai su ha'de acan...tun bayan komawar ta gida har zuwa ranar da ya sanar da ita batun auren Zaitoon da Rayyan da gangan dan ta taya shi ya'kin 'kwato abar 'kaunar sa...so yake ta koma gidan..ya kuma yi nasarar hakan.
Domin Amrah ba karamin rigima ta yiwa mahaifiyar ta ba tana fadin ta cuce ta da ta dauko ta gashi ta ja an mata kishiya tana zaman zaman ta.
Tasan Rayyan bayi da ra'ayin aure nan kusa amma sakaci da rashin wayon ta yasa gashi an mata kishiya, kishiyar ma abin takaici wai yar aikin ta.
Duk yadda Mummyn ta taso kwantar mata da hankali abin ya faskara domin 6acin ran Ameah ya riga ya haura ta yadda take rasa control din zuciyar ta.
Fadi take ta cuce ta da tasa ta dawo hida bayan tasan mijin ta na da bukatar kulawar ta, ita da take tsohuwa ma ba ai mata kishiya ba sai ita bayan tasan yadda take kaunar mijin ta.
Amrah kanta bata ta6a sanin tana tsananin kishin Rayyan ba sai a wannan lkcn, Mummyn ta na mamakin ta itama.
Dan lkcn Nadia bata yi irin kishin nan ba sam sai yanzu.