Sashe 152
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zani ne da riga ajiki na sai kuma wani hijabi na na roba mai ratsin ba'ki- ba'ki, idanuna lumshe suke yayin da fuska ta ke fuskantar 6angaren gefen bango, cikina ke matsanancin ciwo amma saboda karfin hali yasa ko ka'dan a duba na farko bazaka ta6a fahimtar halin da nake ciki ba, ta 'kar'kashin ciki na na cusa hannu ina mammatsa cikin da shi wai ko zan 'dan ji sassauci amma ko gezau, yanzun nan fa shigowa ta 'dakin bayan na samu na kammala ayyukan cikin gidan a daddafe, barka na ma yau Ummaru bai kwana gidan namu ba, yau Khausar ma azumi take yi sa6anin jiya da batayi ba, hakan yasa yau 'din babu batun karin safiya tunda ma Ummaru baya nan, jan ruwa shine abu na 'karshe da nayi wanda kuma shine ya haddasa min jin jiri sosai har yawun bakina na nake jin na ka'fewa, da 'kyar na samu na lalla6a na kammala ina yi ina hutawa har na samu na shigo 'dakin.
Tun daga 'kirji na nake ji a tokare, zuciya ta kuma na min 'kuna, ga ciki na da ya kumbura sosai rabon da na iya sanyawa cikina wani abin tun jiya da akayi bu'da baki, ko da aka tashi sahur ma kasa cin komai nayi.
.....Ina daga kwancen nake iya tsinkayo muryar Iyami dake zaune gefen Khausar daga ba'kin 'kofar ta, daga nan 'din take karantowa min abinda zan yi na gaba wato na tashi na tafi jeji na 'debo mata ganye.
" Tun wuri ki tashi ki wuce kafin anjima azumin ya fara ratsaki kije baki 'debo min abin kirki ba...".
Abinda Iyami ta fa'di kenan wanda yasa ni lumshe idanu, cikin zuciya ta nake jin wani turnu'kin ba'kin ciki da takaici na taso min, banda tsoro da fargaba da ya cika min zuciya tun cikin dare ban kuma san na menene...wasu hawaye ne suka cika min cikin idanu ina jin zuciya ta na tsananta bugawa a fili na furta" Har abada Iyami bazata canza ba...".
Haka na furta batare da nayi yun'kurin motsawa ko kuma tunanin wani zai ji ni ba dan nasan ni ka'dai ke rayuwa cikin akurkin 'dakin nawa
Wannan zuwa jejin gaba 'daya ya ishe ni wallahi, kullum ina zuwa meyasa yau ka'dai bazata yimin uzuri ba, shin da wanne zanji?
Da ciwo da nake ji ko kuma da fargabar dake damun zucia ta.
Ga tabon da hakan ya jaza min har yau 'din nan bashi da alamun 6acewa, ko jiya mafa da naje jejin sai da naci karo da wani al'ajabin mai ban tsoro, shi kansa ya kasa barin raina, tsoron saoe komawa nake har zuciya ta.
Gaba 'daya sai naji duniyar ma ta ishe ni gaba 'daya, mafita nake nema amma na rasa ta, ban ta6a sanin cewa gata abin nema bane sai yau din ka'dai, ban ta6a sanin cewar rashin gata babban 'kalubale bane sai yanzu.
Juyi na sake yi ina mai tunano abinda ya faru jiya a jeji da ya matukar tsaye min zuciya....da yake Ummaru ya raka ni jiyan hakan ya sa da ya hango tsuntsu a 'kasa yana fikim-fikim ya tafi da gudu yana murna da fa'din" Yaah Zaituna kizo ki kamamin shi..."
Da murmushi na 'karaso inda yake hannu na ri'ke da buhun da muka taho da shi dan 'debo ciyawan dabbobi da kuma ganye a ciki.
Gefe na ajiye buhun ina mai tsintan zuciya ta na cika da tsananin fargaba, kallon tsuntsun nayi na kuma kalli Ummaru da ke ta washe ha'kora yau ya samu tsuntsu.
Yana shirin 'dago wa ya mi'ka min nayi saurin dakatar da shi da fa'din" Kai!..kyale shi, kar ka ta6a shi baka ga bashi da lafiya ba ne?"
Na fa'di hakan ne dan in hana Ummaru ta6awa amma a zahiri ba hakan ya sani hana shi 'dago tsuntsun ba, jikin sa da na gani duk layu shine ya bani tsoro.
Ummaru kam kuka ya fara min wai shi sai ya 'dauka jin hakan yasani fa'din" To duba abu ko ma 'dan kwalba idan ka gani mu cire masa wannan abin in yaso sai ka 'dauke shi...".
Nayi maganar ina 'dan dube-dube ina wara idanuna a 'kasan wurin..." Yauwa ga can wani fasashshen kwalba 'dauko".
Na nuna masa in da na hango kwalbar, da 'dan gudu ya tafi ya kawo min sannan na maida kallo na izuwa ga tsuntsun da ke kwance a 'kasa har yanzun yana ta bori da alamu ma mutuwa zai yi.
Tausayin sa sosai naji ya kamani, hakan yasa cike da tausayawa na 'dauke shi a hannu na, durkuso nayi na ajiye shi gaba na, la66ana duk na shigar cikin baki na ina tunanin ta inda zan fara yanke masa wannan sar'kewar dake jikin sa, zuciya ta cike da mamakin inda ya har'de har haka shi da ke tafiya a sararin samaniya me ya ha'da shi da shrigin layu? gashi har yana neman rasa ransa abanza.
Cikin natsuwa da takatsantsan nabi duk na yan-yanke masa layun dake jikin san, Allah cikin ikon sa kuwa duk da hakan be yi rai ba, dan ina gama cirewa shima yayi 'dif.
Na jima dur'kushe a wurin ina jimami, a hankali na kai duba na wurin shirgin da na cire masa, sai a lkcn kuma na ji fargaba ganin tulin layun dake jiki, gashi kyakykywan 'dauri aka yi masa ga dukkan alamu ba da kansa yayi hakan ba.
Ummaru na kalla da shima ya zuba min idanu duk muka yi tsam da ran mu kowa abinda ke cikin zuciyar sa daban.
'Dan karkata kai nayi gami da kamo hannun sa na dama nace" Ka ga ma fa ya mutu ka bari zan kamo maka wani kwanan kaji yaro na..?"
Shi dai bai ji da'di ba amma sai ya 'dage min kansa alamar yaji.
Sakin hannun sa nayi na maida duba na izuwa tsuntsun sannan na koma kallon shirgin dake gaba na.
Cike da rigima na fara yayyanka layun 'daya bayan 'daya..wani bana ganin komai a ciki sai farar takadda, sai na ukun da na wawware ciki naga wani abu kamar gashin kan mutum abin ya bani tsoro sosai.
Cikin hannu na na hagu na tattaro su, buhun nawa na tsugunna na 'dauka sannan na fito bakin hanya da su, gefe can naga wata 'yar 'karamar bola na tashin haya'ki ga dukkan alamu an tattare wurin ne kasancewar gobe ranar kasuwa ce.
Cikin wutar naje na je fa su daga haka na kakka6e hannu na na sake kama hannun Ummaru muka muce wuce jejin.
Sai da muka koma gida ne ina bawa Hamma na labari dan nasan shi ka'dai ne zai iya zama ya saurari labarai na, a hakan ma Iyami sai hararar mu take yi tana kya6e baki.
Shi kam mamaki yayi kwarai da gaske domin ya kasa 6oye hakan cikin zuciyar sa har sai da ya furta" Allah sarki" muryar sa cike da yanayin tausayawa yace" Allah ya sakawa mai shi...".
Jin hakan yasa na 'kwalalo ido da mamaki nace" Hamma ba fa nice na kashe Tsuntsun ba, Allah ka tambayi Ummaru ma kaji.."
Na 'karashe maganar idanu na na tara ruwan hawaye.
Sai yayi murmushi mai sanyi yana kallo na yace
" Ni fa bance kiyi min kuka ba ai nasan 'kanwa ta ba zata iya kisan ko da 6era bane balle tsuntsu..ki kwantar da hankalin ki ba da ke nake yi ba...ai da alamu wani aka shilla duniya da wannan tsuntsun da kk gani..."
Da ido kawai nake kallon sa domin bangane manufar sa ba sam fahimtar hakan da yayi ne ya sashi yi min bayani filla-filla.
Hankali na tashi yayi sosai har ina hawaye domin ni Allah yyi ni da uban tausayi na masifa, har kamar zan yi sashshe'ka duk da ban san wanda abin ya faru da shi ba....amma na taya mai shi bakin ciki gaskiya, ayanda na fahimci zancen kenan an raba shi ne da gida da duk 'yan uwan sa...to duk saboda mene hakan wai?"
Kai na grigiza cikin zucia ta nake fa'din" Yah Allah ka shiryi mutane ka kuma rufa mana asiri ka raba mu da mugaye daga cikin bayin ka....Ameen.."
Iyami ce ta azazzali Hamma da fa'din" ka wani zauna kana ta surutan banza kar ka tashi ka wuce in da zaka, in dai wannan ce sai ta yini bata gaji da jero maka tambayoyi ba...mthew."
ta 'karashe da jan tsaki, ni kam murmushi nayi daga haka na tashi na shiga 'daki zuciya ta cike da tausayi tsoro fargaba gami da jimamin zalunci irin na mutane.
Salmerh😘
[27/12/2022, 8:53 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...86*
.......Ban gama watsar da wancan al'amarin cikin raina ba sai gashi yau ma Iyami na shirin turani jejin, wani lokaci sai in ga kamar da gangan kawai take yi min hakan saboda mugunta ko kuma wani abin daban.
" Zaituna!"
Na sake jiyo muryar ta a akaro na biyu.
Ko.nace zan amsa sautin murya ta bazai fito fili har ta ji sakamakon zazzafan yaanayin da nake ciki.
" Ke Zaituna!!
N sake tsinkayo muryar Iyami dake furta sunan nawa cike da izza da masifar da ya cika mata zucia.
Hakan kuwa shi ya ankarar da ni cewa ashe fa tun 'dazun take faman 'kira na ina can ina shirin zurfafa tunani.
Wani abu ne me 'daci naji ya tokare min zuciya, 'kirji na ne ya cigaba da bugawa da 'karfi yayin da sautin muryar Iyami ya cigaba ta kara'de gidan namu, masifa take da iya karfin ta tana faman aibatani.
Tsawon wani lkc tana abu guda, yayin da nake sake ji jiki na na min nawi sosai, bansan lkcn da 'kwalla ya fara kwaranyo min ba, kalma guda ce da kusan kullum sai na ambace ta har yau din kuma na rasa amsar ta.
" Shin da wanne zanji...?"
Kusan kowace rana sai abubuwa sun ca6e min na rasa mafita guda.
" Yah Allah ka dube ni, ka saukaka min al'amura na...Yah Allah idan bari na duniya shine min alkhairi kuma sau'ki ga zazzafar rayuwar da nake ciki Yah Allah ka 'dauki raina badan na gaji da yi maka bauta ko gajia da jarabtar da ka 'daura min ba, Yah Allah ka 'dauki raina kana mai yarje min cikin aminci da salama ka sani cikin bayin ka salihai..."