Sashe 172
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fahimci 'yan uwan Mufeeda ba sake bar mata yarinyar ta tafi da ita zasu yi ba, ta kuma san ita har Mufeedan zasu yi kewar junan su sosai, yau ka'dai ma da take ganin yadda kowa ke son janta ajiki ana nan nan da ita sai take jin ranta bb da'di ba wai dan tana ba'kin ciki da bayyanan 'yan uwan Mufee ba hasali ma bata jin akwai wanda ya kaita farin ciki a cikin su illa tsoron da bata san takamammai na menene ba daya cika ta.
Har wata 'yar rama tayi, amma hakan bai sa tabi son zuciyar ta ba, da kanta take lalla6a Mufeedan idan wani ko wata na son 'daukar ta.
Ayau 'diyar ta ta zam tauraruwa, Mufeedan ta ta zama yar dangi itama hakan ka'dai na sa taji alfahari sai dai tsoron dake ranta shi ya hana farin ciki da alfaharin nata bayyana kansu a fili.
Duk wannan hayaniyar da ake agidan bb wanda ya kalli ko 'kwayar idanun Rayyan balle fuskar sa tun bayan fitar sa.
Ko farin ciki da ake son taya shi ma babu wanda ya samu arzi'kin yi masa shi sbd rashin ganin sa.
Har washegari kuwa bai yadda ya bayyana kansa ga kowa ba.
Sultan ka'dai ne damuwar sa, burin sa kawai ya ga anyi ram da shi.
Sultan kuwa bai samu isowa Naija a ranar da ya tsara ba har sai washegari sannan ya iso, a lkcn kuwa Anty Raihana ma ta iso ita har da mijin ta, Bassam ma 'kin zama yy duk kuwa da cewa yana makaranta dole sai da aka taho da shi.
Kuma a washegarin ranar dangin Nadia suma suka iso hadda mahaifiyar ta, mahaifin ta ne ka'dai bai samu zuwa ba sbd yanayin 'karfin jikin sa sai a hankali a hakan ma Rayyan bai ta6a mancewa da su da taimakon su ba, sun sha kuka, sun nuna tsantsan farin cikin su a fili.
Da farko ma duk basu lura da rashin Amra cikin gidan ba har sai da aka kwana aka kuma 'dauki hanyar yini da basu ganta ba sannan suka ankare da cewa bata nan, Rayyan ne yy musu bayanin cewa ai tana can gidan su ta tafi.
Shima ya samu cikakken bayani ne daga bakin Nanny sakamakon kukan Arfan da yy yawa.
Babu wanda ya damu duk cikin su illa Ammi sai ma kya6e baki da kusan dukkan su sukayi.
Sbd suna ganin kamar gata ne yy wa Amran yawa da ke sata iskanci da raina mutane.
Rayyan na komawa 6angaren sa bathroom ya shige ya sakarwa kansa ruwan sanyi, zafi yake ji kansa na 'dauka sosai hk ma zuciyar sa suya take masa sosai, sam ya rasa dalilin da ya sa aka daina samun wayar yaron nan kwata- kwata.
Isowar mahaifan Nadia da wasu daga cikin 'yan uwan su yasa dole ya fito izuwa 6angaren Ammi.
Sun gaisa cike da mutuntawa da karamci domin koda wasa bai bari an karanci 'kalilan 'din damuwa saman fuskar sa ba illa Ammi da ko batayi magana da shi ba duba 'daya take yi masa ta fahimci in ma akwai abinda ke damin sa ko a a.
Sun masa barka da samun lafiyar sa sun kuma jimanta domin tun baya da suka zo duba shi daya ke kwance a lkcn ma bai san da zuwan su ba sai yanzun suka dawo, bayan wannan batun Mufeeda ne ya biyo baya.
Mahaifiyar Nadia kuka ta ringa yi rungume da Mufeeda tana jin tamkar ta maida ta cikin ta sbd tsananin farin ciki da kauna.
Ranar kam Nadia tasha Addu'o'i kowa dole sai da ya tuna da ita da mutuwar ta, yadda akayi kuka kuwa sai ka rantse aranar ne ma ta rasu.
Kwanan su 'daya suka koma sbd sun bar mahaifin su a gida shi ka'dai, amma kafin tafiyar su sun ro'ki da a taimaka akai musu Mufeeda suma watarana ta 'dan yi musu kwana biyu.
Rayyan dai bai ce komai ba illa murmushi da yy har suka tafi kuwa basu 'kara ha'duwa da shi ba, ya dai bar musu sa'ko a hannun Ammi.
Irin tarin kyaututtukan da 'yan uwa da abokan arziki suka rinka kawo wa Mufeeda abin ba'a cewa komai, ciki hadda iyalan Alhaji Barau dan su ma ba'a bar su abaya ba..abokan Rayyan tamkar zasu maida ta cikin su...Mufeeda dai taga kaunar da koka'dan ita ba damun ta yy ba balle tasan muhimmancin sa, illah Zaitoon da abin ke matu'kar tsorata ta.
Har fargaba take idan taga zuwan baki gidan sai taga tamkar zukatan wasun su zai iya tunzura suce sai an kulle ta sbd raba su da 'diyar su da tayi na tsawon lkc, wani bin ma tunanin ta bata yake akan ta gudu kawai kafin akai ga rufetan, sai dai sa6anin hakan sai taga wani girma da daraja ake bata da bata ta6a zato ko hasashen samu daga gare su ba, abu na biyu da ke 'kara tsaye mata arai shine batun auren nan da har yanzu bata ji wanda yy maganar sau'ke mata shi ba.
*****
Lokacin da ya shigo 'kasar ji yayi ya sha'ki wata ni'imtacciyar iska mai sanyaya zu'kata, banda 'kamshi da alamun ruwan sama da iska ke tafiar da shi, sai dai ko ka'dan ji yayi bayi da lkcn 6atawa wajen bambance yanayin da yake ciki balle yanayin 'kasar, damuwar sa rufaffun asusun sa da bai san dalilin da yasa aka rufe masa ba sai kuma toshewar duk wata kafa da ku'da'de ke shigo masa suma duk ya daina jin motsin su.
Taxi ne ya kawo shi gida, domin bai 'kira kowa ba balle asan da zuwan sa, hasalima shi a fa'dar sa ma ba ya so kowa yasan da dawowar tasa shiyasa bai 'kira gida ya nemi a tura mota ta 'dauko sa ba.
Gidan sa ya fara sau'ka sai dai ban da mai gadi bai tarar da kowa ba, hakan yasa ya wuce 'dakin Marwa dan yasan mawuyaci ne ya tarar da nashin da cikakken tsabta tunda yasan Marwa bata san da da dawowar san ba.
Tuni Rayyan ya samu labarin sau'kar Sultaan dan ba 'karamin securities yasa aka zuba a ta kowace kusurwar da yasan ta dace da dawowar san ba.
Cike da hanzari yayi wanka ya fito wanda shima Sultan adaidai wannan lkcn wanka yake a 'dakin matar sa.
Koda ya shirya 'dakin sa ya koma ya duba wasu takaddu sai dai bai da'de ba ya fito hannun sa ri'ke da key 'din motar sa.
Mai gadi ya yafito da hannu yayin da ya taho da gudu dan cika umarni.
Motar dake lullu6e da tampol yasa ya bu'de masa, tayi 'kura amma ba sosai ba sakamakon rufe tan da akayi.
Sauran biyu dake fili gefe ka'dan da shi ya waiga ya kalla, 'daya daga cikin su yk son hawa amma bb key a hannun sa..dole sai dai wannan din.
Family house ya wuce domin yadda ya 'kagu yaga Amra ko Marwa baya 'daukin ganin ta hakanan.
Direct 6angaren ta ya wuce hankali kwance batare da fargaban komai ba, domin bai ta6a sanin Rayyan ya tashi ya cigaba da harkokin sa ba.
Sauri yake yaji daga ba'kin Amra sannan ya wuce INFINITY yaji dalilin da yasa kudi suka daina shiga masa asusu daga nan kuma ya wuce Banks ma yaji nasu dalilin da yasa akayi barning asusun sa da gaba daya.
A gobe kuma yk so in komai ya tafi masa yadda ya tsara Lagos zai wuce domin can ne ma yafi damun sa sbd share 'din dake shiga asusun sa daga Lagos yafi na ko'ina nauyi.
Rayyan kuwa tun fitowar sa a wankan banda amsa 'kiraye- 'kiraye bb abinda yk yi..ya 'kira a kuma yi kiran sa shima.
Ruwan sanyin da ya watsa yasa ya 'dan ji sanyi aransa ya kuma 'dan samu natsuwa.
Hatta managern can Lagos din yy magana da shi, duk da yk companyn ba'a hannun sa take ba a hannun Sultan ne, amma hkn baya hana shi tambayar su duk wani abinda yk da bu'kata sbd duk sun san shine sama da Sultan kan dukiyar su.
Tambayar su yy Sultan yaje ne suka ce a a.
Bayan wasu 'yan maganganu da ya biyo sai ya cire wayar daga kunnen sa take kuma sai ya saki ya tsaki 'yar ta'kaitacciya tuno Zaitoon da yy.
Kwanaki 'kalilan baya ita ke taya shi shiryawa, bai san matsalar ta ba a halin yanzu da duk ta 'kauracewa inda yk, duk da bawai hkn ya damesa sosai bane amma yau ka'dai da yake matu'kar bu'katan mutum kusa da shi sai yaji kewa da haushin rashin nata kusa dashi yafi shigan sa.
Cikin hanzari ya samu ya shirya gashi har a lkcn hannun sa bai gama warwarewa ba ta maza kawai yk yi yana amfani da hannun tamkar baya jin ciwon komai.
Shigowar ta kenan 6angaren duba wasu kayayyakin su, da yk dama ba 'diban kayan tayi ba in bama ya zam mata dole ba sbd Mufeeda da bb abinda zai sa ta zuwa 6angaren nan ahalin da ake ciki.
Ko yanzun ma tafiyar da take tamkar tana yi akan ruwa ne, cike da hanzari ta shiga 'dakin ta tattaro abinda ya shigo da ita, mafia yawa ma kayan amfanin Mufeeda ne tsiraru ne nata aciki, rungume da su a 'kirjin ta ta fito...turus taja ta tsaya tana duban sa da tsantsan mamakin ganin sa, a lkcn fita zatayi sai ta gansa ya yaja jacket hannun sa na hagu ri'ke da hular sa P-cap ba'ka.
Ihu tayi niyyan sawa sbd tsorata da tayi, tamkar cikin mafarki domin bata ta6a tunanin ganin sa anan ba.
Kuma tashin farko wa'dancan mutanen da suka ta6a sace su abaya sune suka zo mata rai lkc guda.
Baki ta bu'de tana duban sa da niyyan sakin ihu sai dai kafin sautin muryar ta ya bayyana a fili yy saurin rufe mata baki da hannun sa ya manna bayan ta da jikin bango.
Sam bata san lokacin da ya iso kusa da ita ba balle faruwar hkn.