← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 218

Sashe 131

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata fiye zama wajen sa har yaci abinci ba indai ba Mufee na nan tare da su ba, yakan ce ta bar yarinyar suci abinci, haka zai lalace wajen Mufee yana bata abakin ta tun basu saba ita da Mufeedan ba har ya zam musu jiki, Zaitoon dai na mamakin wannan sabon sauyin daga gare shi, toh in dai ba dan yarinyar ba sau tari sai ya gama take dawowa ta kwashe warmers 'din...so bata san yanayin cin abincin san ba.

Akwai ranar ta gama jera masa abinci ta harha'da duk abinda tasan zai bu'kata saman dinning ranar haka kawai taji ta tsaya har ya kallama kafin ta tafi...koda tayi serving nasa ya fara niyyar cin abincin ga mamakin ta sai taga left hand din sa ka'dai yake amfani da shi, tasan hakan yk yi idan tare suke da Mufeeda amma bata zaci ko da shi ka'dai ne hkan zai yi ba.Koda ya 'debo abincin gani tayi abin ya mata baibai sai taji zuciyar ta ya kasa sakewa.
A hankali ya taune abincin kamar bai san cin sa, sai da ya 'debo wani yana niyyar kaiwa bakin sa da sauri ta yi 'karfin halin ri'ke mai hannu cike da tausayin sa a zuciyar ta ta girgiza masa kai idanun su sar'ke da na juna.

Tausayin sa sosai ya kamata tuna kwanaki baya kadan ba hakan yake ba mutum ne shi lafiyayye amma Allah cikin ikon sa ji yadda ya canza shi, har wani ruwa taji idanun ta ke tarawa.

Rayyan sake mata spoon 'din yayi yana sakin sassanyan ajiyar zuciya.

Taso ta daburce kan shishshigin da tayi na ansan spoon 'din domin da farko rasa me ma zatayi da shi tayi, amma ganin yadda yake duban ta da sauraran dalilin ta na yin hakan yasa taji wani 'kwarin gwiwa ya shige ta da bata san daga ina ya taho ba.

Kujera ta ja ta zauna batare da ta dubi fuskar sa, abincin ta 'debo ta nufi bakin sa da shi tana me sake ssau'kar da idanun ta.

Rayyan sai yaki bude bakin sa ya tsaya bin ta da kallo.
Jin shiru bai amsa ba yasa ta 'dagowa da tunanin ko hankalin sa baya kanta ne ta ankarar da shi.

Sai dai tana 'dagowa suka yi ido hu'du.
Abincin dake hannun ta ta kalla sannan ta kalle ahi.
Gira ya 'dage yana duban ta batare da ya motsa ba.

Sai ta sake kallon abincin nan ta fahimci manufar sa.

Dagaske ba bakin sa ta nufa da spoon 'din ba wuyan sa ne.
Kunya taji sosai sai ta sake 'dago hannun ta sama ka'dan ya kuwa bu'de bakin sa ya amsa.

Dole take 'dagowa ta kalle shi badan komai ba sai dan ta saita inda bakin sa dan ko ta karkace mai mata gyara ya kan tsaya duban ta ne kawai.
Amma duk wannan bata yadda ta sake ha'de ido da shi ba har ya 'kare cin abincin sbd kunyar abinda ke faruwa.

Tun daga ranar kuwa sai ya zamana ita ta ke bashi abincin abaki, wanda hakan ya sake kawo kusanci a tsakanin su, sbd kullum tare suke zama tayi serving nasa ta kuma basa sai dai in Ammi na nan tare da su ne salon zaman ke canzawa ita ke bashi da kanta.

Ranar da ta fara ganin yadda Ammi yadda Ammi ke bashi abincin tana kuma lalla6a shi suna 'yar hira zuciyar ta cika yayi taf da mamaki, sai kuma taji wani iri cikin ranta.

Gatan da tun tasowar ta bata ta6a dacen samu ba kenan, gatan da yai mata fintinkau a rayuwa, bawai dan bata da mahaifiya ko mahaifi ba ne a a, sai dan kawai haka Allah 'kaddaro mata tata rayuwar.

Ba wannan ranar ce ta kasance farko ko 'karshe ba kuma, domin ko Ammi bata nan idan Anty Madeena na nan kusa ta kan bashi abincin itama abaki tamkar yaro 'karami, sbd sun san hannun sa da ya dace yayi amfani da shi wajen cin abinci ba lafia gare shi ba.

Bata san wani irin 'kauna da soyayya suke yiwa Rayyan ba ahalin gidan nan.

Marwa ce dai bazata iya masa hakan ba amma duk wani abinda tasan zata iya batare da ta jawa kanta magana daga gare shi ba takan yi 'kokarin ta wajen yi itama, kuma har ila yau babu abinda ya canza daga sha'kuwar su.

Suna 'kokari sosai wajen nuna kulawar su gare shi
sai dai dole a hankali wasu abubuwan sai da suka dawo hannun zaitoon gaba 'daya.

Sau tari in dai da Mufeeda tazo duk tare suke cin abincin illa na dare ka'dai da basa ha'da hira da Mufee sbd saurin bacci gareta hkn kuma shi na sanadin da ya sa basa yin dinner tare...Rayyan kansa bai so hkn ba amma yarinyar ta riga ta saba.

Ranar har fa'da yaso yiwa Zaitoon out of confusion akan wai ta koya mata baccin wuri..hk kawai salon ta maida yarinyar wata kala.

Zaitoon kam baki ta sake cike da mamakin sa tace " Ji wani 'karfin hali.."
Rabon da taji sautin maganar sa a suna tare iya su biyu har ta mance amma wai yau shi ne ke mata mita akan 'diyar ta.
Sai ta ga kamar dagaske fa yake fadan sannan ta tankashi da fadin..." Ai baccin shine mata dai dai, in bata yi bacci ba ma zai tayi a irin wannan lkcn...kuma ta riga ta saba babu abinda zai mata ai...".

Babban ledan kayan za'ki da ya tahowa Mufeeda dashi ya cire ya tura gaban ta batare da ya furta komai ba.

Tun ma kafin ta bude ta fahimci menene dan ba yau ya fara taho mata da abubuwa ba matukar ya fita a ranar, be it asbiti yaje company ko kuma wata sabgar shi ta daban.
" An gode..Allah ya kara arziki da lfy" tace tana kawar da ledan gefe.
Hararan ta yayi cikin ransa yake " ayyana sarkin za'kewa kawai..'karfi da yaji ta hana ni ganin yarinya ta...".

Feefy bata ta6a wuce 'karfe 8 batare da tayi bacci ba...shi kuma sai bayan isha'i yake cin abinci...karfe 8:40 zuwa 'karfe 'karfe tara na dare yake cin abincin sa da wannan damar kuma yy amfani ya zuba mata maganin bacci cikin abin shan da yake zatan zata sha idan ya bata umarni.

Shigan ta ciyar da Feefy ne kafin ta fito ya 'zuba mata maganin da Fawwaz ya bashi 'dazu da yaje wajen sa, cikin cup 'din da ya 'dan yi gaba ka'dan zuwa kusa da ita yasan idan har zata sha din dagaske toh hannun ta kansa zai fara sau'ka dan zuba abin sha 'din, dan haka yy fuska tamkar bb komai a ciki, da yake yau 'din ya riga ta fitowa kan dinning 'din sai ya kasance tamkar yunwa ce kawai ta ciwo shi..hakan da ta gani yasa ta yin komai cikin hanzari dan kar yunwan ta illata shi ta riga ta kuma san ba zai ta6a bu'dan baki ya sanar da ita a zahiri ba.

Abincin ta zuba gami da ajiyewa gaban sa, kwalin abin sha 'din ta 'dago yana ganin ta a kishingi'den da yy ta 'kasan idanun sa, sai dai ita kanta ma bata san a yadda yaken duk wani motsin ta kan idanun sa bane ba.

Shi dai cikin kwanakin nan yarinyar na matu'kar birge shi, ya so ya garga'di zuciyar sa akan abubuwa da dama game da ita amma sam ya kasa.

Komin ta yake ji na tafiya dai- dai da tsarin sa, musamman yanda take yin komin ta cikin sanyi ba kamar yadda yaga wasu matan ke yin abu wufwuf kamar maza ba, yana matu'kar son mace mai sanyi shi a rayuwar sa.

Ba tun yau yasan yanayin ta ba, inda sabo ya riga ya saba amma cikin kwanakin nan ya kan tsinco zuciyar sa cikin shauki da bukatawa mai tsanani ta yadda har ya kasa iya dakatar da kansa hukuncin da zuciyar sa ta yanke masa.
" Ai matar ka ce...halalin ka..."
Jimillar kalmomin da ke faman yi masa yawo aka kenan kuma suke 'kara masa 'kwarin gwiwa.

Ganin ta cika cup 'din ta ajiye masa ne ya sashi 'dagowa daga kishingi'dar da yayi babu wata magana kawai ya 'dago ya gyara zaman sa fuskar babu yabo babu fallasa.

Haka suke tamkar kurame dan duk ba gwanayen hayaniya bane su.

Abincin ta fara bashi a baki a hankali kamar yadda ta saba, sai dai tayi mamaki da yau taga Rayyan bai tsaya 6ata lkc ba yake kar6am abincin..sai da ya amshi 'daya, biyu, uku amma na hu'dun sai ya tsare ta da idanu yana kallon cikin idanun ta, itama kallon sa tayi bata san me yk nufi da hakan ba yasa itama ta kalle shi, idanun sa ya rufe ya kuma bu'de su nan take tare 'dan dage gira da kansa atare, ita wannan yaren ba ba'kon ta bane dan ya jima da karantar da ita salo- salo, dan haka bata sha wahalar fahimtar abinda yake nufi ba, sai dai bayan fahimtar tasa 'kasa tayi da idanun ta gami da girgiza kanta alamar a a, dan ko da da take bashi abincin ma bata ta6a ci har sai ta tabbatar ya gama cin nashi sannan, domin baya tashi haka zai sata gaba dole wai sai taci ya gani shima..yakan yi mata alamun bashi da lafiyar hannu ne amma da shima zai ciyar da ita tamkar yadda take ciyar da shi..'karshe sai yy mata alamun ban ha'kuri, hakan yasa yake tsare ta agaban sa wai taci abincin...sai dai duk zai yi bata iyawa 'kar'kari ta 'dan kai bakin ta sai tasha ruwa shikenan.

Sai dai in ya matsa dole
haka zata ringa tsakura ka'dan ka'dan kamar mai shirin cin wuta, idan ta kai 'daya sai ta shafe mintina da yawa kafin take sakewa kafin ta kammala kuwa abincin yy sanyi sosai ko ka'dan kuwa Rayyan baya gajiya da zaman jiran cin abincin nata dan a ganin sa tunda shima ta juri ciyar da shi dole shima ya 'dan ware lkc cikin lokutan sa dan ita ka'dai matsayin ta na matar shi ta aure itama ya bata kulawa.

Salmerh😘
[30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...76*
Chapter 131 · 0% Book details