← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 218

Sashe 107

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waje Rayyan ya nuna mata yace ta kaita waje Sultan zai zo ya 'dauka.
Hakan kuwa akayi waje ta mikata sannan ta dawo ciki.

Idanun Rayyan rufe ruf suke 'dumin jikin Mufee na ratsa shi yana kuma jin sa a zuciyar sa.

Tunani kala kala ke zuwan masa, hakika maganar Anty Madeena akwai 'kamshin gaskia aciki, dole akwai wani babban dalilin da ya kawo hakan, ba hk nan kawai Mufeeda zata yi kama da shi ta kuma kwaso yanayi da zubin matar sa ba, sannan the worse ma tayi kalar jinin su...yasan duk wannan amma ya kasa gano asalin ta inda dangantakar take.

Tsoro yake kar ace wannan yarinyar tashi ce tsawon lokacin nan...tsoron ne kuma ya sanya da ya tuno Nadia sai yayi saurin girgiza kai..." ohh no...it can't be...".
A dole yake tilastawa zuciyar sa kawar da Nadia cikin lamarin dan ma kar shi ya shigo ciki.

Bai ma san da zaman Anty Madeena wurin ba tsabar yadda ya shiga halin ru'dani, yayin da tun fitowar ta zuba masa idanu bayan ta gama 'karewa dacewa ta jini tsakanin sa da Mufeeda.

Kawar da kai tayi ganin alamun ya riga yayi nisa cikin nazari.
" Nuwaira, Nuwaira...ta fara kwalawa kira wanda hakan shine ya maido da hankalin Rayyan gare ta.

A hankali ya bude jajayen idanun sa ya sauke akan Anty Madeena.
Ji yake tamkar 'kwalla zasu zubo mishi ne musamman sbd rashin takamammen madafa.

Mintina 'kalilan da suka gabata Anty Madeena ce ke 'kage da son ji da gano dangantakar su, yayin da a halin yanzu yake jin nasa 'kaguwan ya ninka nata.

" Bari Nuwaira tazo ta tafi da yarinyar kafin ka maida ta cikin cikin ka..."
Cewar Anty Madeena tana duban sa.

Sai a lokacin ma ya lura da yadda ya 'kwa'kume Mufeeda ajikin sa, bai ma kula da cewa jikin tan tuni ya saki ba.

A hankali ya fiddo ta daga jikin sa yana shafa gurbin da ya kukkumburo a kan fatar ta da ya tabbatar kafin akawo masa ita babu shi...
" Anty kina gani ko, itama attack din ta samu kamar ni, ina jin tsoron ace duk wannan ba kamanceceniya ce da Allah ya ha'da haka nan kawai ba...inajin tsoro ace yarinyar nan jinin mu ce Anty...amma abinda ya ke daure min kai na kasa fahimta shine..."
Isowar Nuwaira ne ya sanya maganar tashi dakatawa.

" Amshi yarinyar kije ki sake mata wankA da ruwa mai 'dumi sosai kisa lalle cikin ruwan zaki ga wani magani na ajiye saman mirror na ki shafe mata jiki da shi in tayi bacci shikenan..."
Kai Nuwaira ta jinjina tana mai yin gaba dan cika umarnin Anty Madeenan.
" Ina jinka..."
Tace tana duban sa..
" Anty Zan je gida...kawai ina so in huta zuwa gobe sai muje asbitin...".
" Bazaka jira dawowar Sultan din ba?".
" A a Anty.. idan ya dawo kawai ya 'dauki magen sa ya tafi..."
Yayi maganar yana mi'kewa.
" Toh naga bamu 'karasa maganar ta mu ba kuma".
" Ma yi daga baya Anty..."

" Shikenan Allah ya tsare, amma dai ka tabbatar baka bawa kowa damar sanin komai kan wannan lamarin ba, idan nace kowa ina nufin hatta Ammi Aseeyah..biyo bayan ta kuwa babu wanda ya cancanci sani a halin yanzu, domin kasan har yanzu bincike ake bamu tabbatar da komai ba, baya ga haka ma kar ka mance akwai ma'kiya da nake da ya'kinin akusa suke, sirri nada matukar amfani a mafi yawan lokuta...ko Ammi ba yanzu ya kamata ta sani ba balle wasu daban...kar ka sake in kuma ji makamancin maganar ta fito..."
" Insha Allah Anty...".
Yace yana mai yin gaba.

Tafiyar sa da kusan awa guda kafin Sultan ya dawo dan cewa yayi Rayyan ya more da magen kafin nan ya kawo maganin dan mugunta irin tasa.

Cikin rashin sa'a kuma da ya dawo bai tarar da shi ba sunyi sa6ani, hakan ya sa ya 'dauki magen sa ya yiwa Anty Madeena sallama yayi gaba abin sa.

Anty kam da idanu ta bishi har ya 6acewa ganin ta, ita dama tun can asali haka nan kawai jinin bai hadu da yaron ba, shiyasa ko lokacin da zai auri Marwa taso hanawa amma tasan duk abinda ta fa'da za a ga kamar dan shi dan tsuntuwa ne shiyasa take kin jinin sa.
Baya ga haka ma bata da ikon sawa ko hana abu dangane da su, sai dai in ya zama dole ne ma tana iya bada shawara.

Rayyan kam daga gidan Anty Madeena YOUHEAL ya wuce wajen Fawwaz.
Shine yayi masa allura yana mitar dama yasan da yanayin sa meyasa zai je inda magen suke.
Rayyan yace" arashin sani ne..."
Fawwaz bai bar shi ya tafi ba har sai da ya tabbatar zazzafan yanayin ya sauka masa kafin ya barshi tafiya dan cewa yayi driving cikin wannan yanayin is very risk.
A hankali yake 'dan jan sa da hira, hirar kuwa bata kowa bace face ta Mufeeda..." Inda ya fara da fa'din" Ya Babyn nan?..ya jikin ta...?"
Hakan da ya fa'di ne ya sa Rayyan fahimtar wacce yake tambaya.
Idanun sa ya lumshe domin wani karaya ne yaji ya ziyarce shi nan take...har ma ya sashi ji zaman asbitin ya gundure sa.

Kusan kowani da'ki'ka tsoro ke sake shigan sa.
Tsoron tabbatuwar alaka tsakanin sa da Mufeeda, tsawon lokacin nan batare da yasan cewa jinin sa bace ba.

Ji yake bazai iya yafewa kansa ba, bazai iya yafewa kansa abubuwan da sukai ta faruwa abaya ba, ta ya zai iya sake duban idanun yarinyar nan banda tsananin kunyar ta da zai ji...duk da still yana kokonto, yafi bawa ikon Allah ne kawai ya kawo kamar su da yanayin jinin su, but yanayin ta da Nadiar sa ya kan sa yaji tsoro sosai ya kama shi...amma ai a pic din da jami'ai suka nuna masa yaga pic din Nadiya kwance cikin jini da jaririn da ta haifa masa kuma duk sun rasu..toh me yasa alakar su da Mufee ya ha'da da ita, sannan yadda yake jin zuciyar sa a duk lokacin da suke tare da yarinyar is something else.

Bai bawa Fawwaz amsa ba dan shi a yanzu bama ya jin harshen sa zai iya dogon magana.

Tashi kawai yayi yana 'dagawa Fawwaz hannu yayi gaba.
Bai koma office ba kawai ya wuce gida.

Nan ma tsaye ya same su kan 'kafafuwan su, mai gadi da sauran ma'aikatan gidan na compound suna jajanta wani batu, domin sa6ani suka yi, ana fita da Amrah zuwa asbiti shi kuma yana shigowa da motar sa.

Ji yayi gaba 'daya hankalin sa ya tashi sosai, sharp- sharp ya shiga ya watso ruwa da nufin bin su amma 'kiran sallar maghrib da aka fara shi ya dakatar da shi.

Alwala yayi ya fita zuwa masallaci.
Sai bayan ya idar da sallah ya komo gida, tun abakin gate ya tambye su asbitin suka ce basu sani ba sai dai a tambayi sauran dake ciki, 6angaren sa ya koma ya 'dauki wayar sa, numbern Ammi yake ta faman 'kira har alokacin amma still bata 'dagawa haka ma na Amrah ba'a 'dagawa sai daga baya ya fahimci ai wayar Amrah ma na nan gida.

Sunan asbitin da suke kawai yake so ya tambaya ba komai ba, amma ya rasa samun su, yasan ba lallai ne Ammi tasa akai su YOUHEAL ba indai taga condition din Amran ya haura sosai, bai san ma meyasa basu neme shi a waya ba kafin tafiyar su.

Keyn motar sa ya 'dauka ya nufi 6angaren Ammi da zummar ko zai samu amsa daga wajen su.
Sai dai nan ma bai tarar da kowa ba Marwa da Ammi duk sun wuce asbitin sai Zaitoon da sauran 'yan aikin gidan kawai.

Wata mai aikin ne ta bashi wannan amsar har ya juya sai kuma ya dawo ya bata umarnin 'kira masa Zaitoon 'din.
Tare suka dawo Zaitoon na bayan ta...duk jikin ta yayi sanyi da ganin halin da Amrah ta shiga, dama tun 'dazun da Ammi tasa su dubo ta suka fahimci bata jin dadi amma koda Marwa ta tambaye ta cewa tayi bakomai ita lafiyar ta 'kalau, kuma ta tabbata mijin nata ma kafin ya bar gida lafiya kalau ya barta, a hankali bakudar ta taso mata kafin yammacin kuwa har tayi tsanani.

Sosai take jin babu da'di musamman da ta tuno abinda ya faru abaya.

" Barka da dare Yah.."
Ta fa'da da sanyin murya tana yin 'kasa da kanta.
" Yauwa..barka dai, ya sunan hospital 'din da Ammi suka je...?"

" Wallahi ban sani ba sai dai ka 'kira su..."
Ta fa'da cike da ladabi dan bata jin 'kwarin gwiwa yanzun koka'dan.

Haushi ma amsar tata ta basa hakan yasa ya juya yana sakin 'karamar tsaki da tunanin tama raina masa hankali, inma 'kiran wayar ne 'karamar 'kwa'kwalwar ta bai bata akan ya 'kira bai same su bane kafin yazo tambayar, ko kuwa tana tunanin ita ta fishi sani abinda ya dace ne.

Daf da zai bar parlorn tace " Dan Allah yaushe za'a dawo min da yarinya ta..?"
Ta tambaya yanzu ne dan tasan shine ka'dai damar da take da shi.
Bayaga yaushe zata ma gansa, tsoro take ji kar tayi shiru ta kyale a kasa kawo mata yarinyar..babu mamaki kuma tana can tana kuka kullum.

Cak ya tsaya yana jin wani abu na masa yawo a zuciya, sai lokacin ma ta tunasar da shi kan ga6ar dake gudana cikin rayuwar sa kafin tasowar batun Amrah.

Kafar sa 'daya ya 'daga ya juya ta wanda hakan ya bashi damar juyowa ya fuskance ta.

Hasken 'dakin dake tarwai shi ya bashi damar 'karewa fuskar ta kallo da kyau.

Tsawon mintina biyu yana kallon ta yana kissima abubuwa da dama, sosai yake nazarin ta a zuciyar sa, bai ma ta6a tsayawa yayi mata kallon tsap irin na yau ba.
Chapter 107 · 0% Book details