Sashe 72
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hira sosai suka cigaba da yi, Marwa ke bata labarin makaranta da yadda abubuwa ke tafia mata, a hankali hankali har labarin ya gangaro na cikin gida, nan take labarta mata yadda Sultan ya damu sosai da rashin haihuwar ta, tace kwata- kwata 1yr 3mnths ne fa da auren mu amma yadda Yah Sultan ya damu zaki 'dauka kamar mun shafe shekarune, bansan miye matsalar sa da haihuwa ba, abu Allah ke bada shi.
Kai Zaitun ta jinjina tana fadin" HakaNe kam Marwa, kuma in anyi hakuri komai ai mai wucewa ne.."
" Abinda nake ta so in fahimtar da shi kenan amma Yah Sultan da alamu he is not ready yet ya fahimci abubuwa, yanzu in na yadda Ammi tasan damuwar san nan Allah ita kanta hankalin ta tashi zaiyi...bata san damuwar kowa cikin mu gaba daya..".
" Allah dai ya rufa asiri ya kawo rabon nan kusa mai albarka.."
" Ameen Zaitun, Ameen Yah Rabbi...shine ma dai da ya kasa fahimta amma ai rayuwar ma gaba daya 'yar hakuri ce, musamman idan ya lura da Yah Rayyan, da yayi hakuri ba gashi ba cikin ikon Allah Allah ya sake azurta shi da wani cikin bayan wanda ya rasa abaya..."
Cewar Marwa.
Sai kuma tayi 'yar dariya tana duban Zaitun tace" Haka fa raywar nan take, wani na nema wani na gudun sa, wani kuma bai shirya kar6a bama Allah ke bashi, kamar dai ke ba gashi ya baki baby kyakkyawa ba a lokacin da nasan ke kanki baki shirya kar6anta ba, kamar ki bani kyautar ta wlh, hk kawai nake jin ta a zuciya ta...idan na zauna fa wani lokaci Allah tunanin ki ke zuwa raina ko lokacin da nake school, sai inga gaskia kamar anyi asarar tarbiya anan...."
Kallon ta Zaitun tayi cike da mamaki tana duban ta.
Ba wai yau tasan kalaman Marwa ba, haka take wani lokaci kalaman ta na mata kamanceceniya da ta Amrah, babu dadin ji sam amma da yake azahiri bata nuna musu 'kyama shiyasa bata fiya damuwa da munin kalaman nata ba.
Balle wannan bata zaton ma da ita take yi...cigaba da magana Marwa tayi.
" Allah wani lokaci ina mamaki, Zaitun kema 'yar 'karama da ke har kin iya kiyi cikin shege kuma ki haife....."
Ta 'karasar da kya6e bakin ta amma still there is smile on her face.
" Dan ma banga laifin ki ba, kamar kinsan cute baby zaki haifa shiyasa kika haife abarki"
Shiru Zaitun tayi yau Marwa ta ta6o mata inda a rayuwa ta tsani jin sa, bata ta6a zaton Marwa zata iya furta hakan a gareta ba, iya zaman su da rashin dadin kalamanta da suke zuwa mata lokaci zuwa lokaci Marwa bata ta6a furta irin wannan maganar a gareta ba.
Murmushi mai ciwo Zaitun tayi gami da tsurawa Mufee idanun ta da tuni sun kawo ruwa amma tayi kokarin danne su...bata san me yasamu Marwa yau din ba.
" Wato ashe har a 'kauye ma ana tsula tsiya, sai dai sakamakon duk 'daya ne ai tunda gashi yanzu kema kin gani, ke da kika biyewa banzan yanzu kece aciki tunda gashi yanzu baki ga tsuntsu baki ga tarko, baki ga shi uban 'yar baki kuma ga iyayen ki kin rabu da kowa naki, shi kuwa yana can yana shanawan sa, in yana da sa'ar rayuwa ma ko 'yar sarkin garin sai kiga ya aura ya kuma zauna lami lafia, shiyasa fa ni sam ban yadda da ko wani banzan saurayi balle har a kaiga wannan shashancin...Yah Rayyan ma yaji labari ai kashe ni zaiyi ko kuma ya binne ni da raina...".
Da kyar ta iya budan baki ta tare dogon sharhin da Marwa ta gingimo dan sosai ta gaji da jin su.
Batare da ta dubi fuskar Marwa ba tace" Ke de kawai Marwa kiyi ta addu'a kawai kar kiyi alfahari, kiyi fatan Allah ya baki kariya, ya kuma rabaki da mummunan kaddara domin ita kaddara idan taka ce wlh ko kin binne kanki cikin 'kasane matukar mala'ikan mutuwa bai ziyarce ki ba toh kuwa binki zatayi kuma sai ta same ki addu'a kadai ke iya canza ta, ni kuma da kike gani ba wai kula na rasa ba da har yasa na haifi Mufeeda, ba tsayayye akaina na rasa ba, ba kuma rashin tarbiya ya sani samun Mufeeda ta ba, kaddara ta ce ita kuma na kar6eta, a kullum kuma fatan shine in kwatanta sama mata kula da tarbiya kwatankwaci koma fin wanda ni aka bani, kaddara ta Mufeeda ba yadda duk kike zato bane, 'diya ta 'yar halak ce Marwa, maraici ne kaddarar mu bayaga haka haka babu komai..."
Ajiyar zuciya Marwa tayi tana mai jin kunyar kalamanta ga Zaitun da ta kasance tamkar kawa agareta...ita kanta bata san me ya shiga kanta ayau ba...sai yanzu kuma taga rashin kyautawar ta.
" Gaskia ne Zaitun, Allah dai ya 'kara rufa mana asiri ya bamu ikon kar6an 'kaddarorin mu ya kuma bamu da sau'ki..kiyi ha'kuri kuma idan na 6ata ranki.."
Ko tankawa Zaitun batai mata ba cikin ranta ta amsa da" Ameen".
Yayin da Marwa itama cikin ranta take tunanin rashin kyautawar ta, yayin da wani 6arin zuciyar ta ke ganin tamkar rainin hankali kawai Zaitun ke son nuna mata baya ga haka ai yanayin su da tarihin su da ta bayar bai 6oye irin rayuwar su ba, gani na farko da su zaka fahimci inda matsalar take wato cikin shege tayi iyayen ta suka kore ta daga gidan su.
Irin hakan ba ba'kon lamari bane a wannan 'kasar ba kuma ba'kon abu ba, bata san meyasa Zaitun ta ke wani 6oye lamarin ba, hala kunya take ji, koma menene ita dai haka kawai Allah ya jarrabce ta da kaunar su musamman ma 'diyar ta.
" Nima fa wlh ina son baby, amma dai ban kai Yah Sultan ba gaskia kuma ma yadda nake jin ake fadin labarin wahalar haihuwa yasa nake dan ji tsoro..ki fa'damin ya kk ji lokacin da zaki haifi Moofy"
Kallon ta Zaitun tayi da mamaki take kuma sai ta kawar da kanta...komai idan Marwa ta riga ta furta shi ya wuce kenan a wajenta, ba yau tasan wannan halayya tata ba, bata da riko bata da jan magana, so gani take tamkar kowa ma irinta ne, yaushe ma ta gama cire wancan batun da tai mata arai da har zata kara mata da wata kuma, gaba 'daya ji Zaitun tayi hirar tasu ta ishe ta ma yau din.
Batacgama tunanin ba taji Marwa na tsakanin ta da Allah na cigaba da ro'kon ta.
" Dan Allah ki bani labari inji Zaitun nifa kullum tsoro ke kamani idan Ya Sultan yayi batun haihuwar nan".
Zaitun idanu ta lumshe a hankali hawayen ta suka gangaro da tun dazu take danne su..sake rungume Mufy tayi cikin jikin ta tace" Bazaki ta6a ganwa ba duk yadda zan yi miki bayani Marwa amma kowa da kalar tashi haihuwar, wasu na zuwa musu cikin sauki wasu ko akasin hakan, wata zata ce miki da wahala yayin da wata zata ce mk haihuwa babu wata wahala amma duk da hakan har gobe ba'a fasa haihuwar 'ya'ya ba, toh me ze sa kiji tsoro bacin ke baki ma san wani nau'i zaizo mk yayin haihuwar..ni dai abinda kawai na sani haihuwa akwai wahala Marwa babu sauki sam ba wani gayan hakan ba kuma da kaina na fahimta...kiyi fatan Allah ya baki yara masu albarka wa'danda wahalar haihuwar ki akan su bazai tafi abanza ba..."
Cikin sanyin murya ta cigaba da fa'din" Shiyasa na ke son mufy na na kuma sadaukar da abubuwa da dama domin ta, dan ni ka'dai nasan wahala da kalubalen da suka faru yayin haihuwar ta, ni da na gani ni nasan ciwon hakan shiyasa nake iya 'kokari na wajen ganin na kwatan ta abinda nasan ko da tare take da mahaifin ta bazai ta6a bari ayi mata su ba wato cin zarafi da rashin samun kulawa, bansani ba ko haka ya kamata nayi ko kuma na gaza...".
" Wallahi baki gaza ba, tab a hakan Zaitun, ke ko mu nan da muka jima muna muradin ganin jikoki a gidannan iya sadaukarwar da zamu iya yi kenan balle ke...aikin yi kokari...ki dube mu nan kiga mun rasa, mahaifin mu da babban yayan mu,mun rasa matan yayun mu da 'diyar sa amma hakan bai sa mun sadaukar da farin cikin mu ga wasun mu ba...hakan bai hana Ammin mu fita wajen aikin ta ba, bai hana mu walwala da cigaban al'amuran rayuwar mu ba, kuma a hakan mun isa muce mahaifiyar mu ta gaza akan mu ne wallahi bata gaza ba ta ko ina..balle ke da kika sha fa'di tashi cikin rayuwar ki, kika yi ta sadaukarwar da ke kanki baki san karshen su ba..kike fadin hakan...Zaitun kenan mamaki ma kika bani wallahi..".
Da yamma lis da Marwa zata koma gidan ta Zaitun dauke da 'diyar ta suka fito dan yi mata rakiya, a daidai gaban part din Ammi suci karo da Rayyan shi kuma zai shiga.
Cike da 'kauna Marwa ta gaida shi" Yah barka da yamma.."
" Yauwa Marwa ya schl 'din..? kin kammala komai ko..?"
" Erh Yayah.."
" Toh Masha Allah..Allah ya bada sa'a ".
" Ameen Yayah..".
Yana cigaba da tafiya yace" Ammi fa..?"
" Tana ciki ".
" Ok" yace yana mai nufan mashigar da zata sadaka da babban Parlor.
Da sauri Marwa ta waigo tana duban Zaitun..." Baki gaida Yah Rayyan ba.."!
Shiru Zaitun tayi tana mai cigaba da tafiya.
Da 'dan hanzari Marwa ta daidaita tafiyar su tana maimaita mata tambayar.
Turus Zaitun taja ta tsaya tana duban ta.." Wai in rakiyar ne baki so ki sanar da ni mana kawai..".
'Yar dariya Marwa tayi
" Ni kuma yaushe nace hakan abinda nake tambayar ki daban da batun rakiya...ko de wani abin yai mk kike 6oye min...?"
Marwa ta 'karasa tana yawo da idanun ta kan fuskar Zaitun da son karantar yanayin ta amma ta gaza gano komai.
Kai Zaitun ta girgiza.
" a a kam babu komai, kawai dai shi in aka gaida shi baya amsawa ne shiyasa na daina...".