Sashe 79
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai take zuzuta girman da Moopy ta kara a idanun ta,
round face ne da ita da manyan idanuwa da hasken fata dan Mufee fara ce tas ba kamar Zaitun ba take choculate ba fara sosai ba, yanayin shape din fuska da yanayin jikin su iri daya ne haske ne dai ya bambanta su hakan yasa tace ko batace ba ba kasafai ake tantama wurin bayyana Mufeeda 'diyar tace ko ba tata ba.
Wannan zuwa na Marwa shi ya 'karo sha'kuwa mai 'karfi tsakanin su da Zaitun dan Marwa har ta fara zancen zasu shiga Islamiya tare.
Bacci ka'dai ke raba su da Zaitun, hatta abinci tare suke ci da Marwa adakin ta, kokadan bata nuna musu kyama.
Suttura kuwa yanzu Zaitun sai dai ta bada ga wasu, duk wani nauyin kayan 'kawa na rayuwa itama yanzu kewaye take da su.
Sosai ta kara samun wayewar rayuwa, ta murje ita da Moopy tamkar basu ba.
Tare suke komin su da Marwa hatta unguwa tare suke zuwa har gidan Anty Madeena da ta kasance kanwa ga mahaifin su.
Aikin da yaka ma su suyi tare suke yi, in an gama abinci ma suci cikin plate guda hatta Moopy yanzu sun kara sha'kuwa da Marwa sosai, yarinya ta fito tsab ta juye kalar 'yan gayu.
*****
Misalin sha 'daya ne safia, cikin 'dakin Ammi suke suna canza masa fasali, kasantuwar a ranar zata dawo daga tafiyar da tayi zuwa Abuja wajen kaddamar da wani tallafi da suka wallafa na kungiyar su ta taimakawa gajiyayyu a Abuja.
Aikin suke amma komai cikin sanyi Zaitun ke yin sa, Marwa duk na lure da ita amma ta saka mata ido, ganin kamar yanayin kara shigan ta yake ne ya sanya Marwa jefa mata tambayar abinda ke damun ta da wannan lokacin.
Kai ta girgiza tana duban Marwa" Me kika gani..?"
" Babu abinda ma ban gani ba ai, ni dai dan Allah fada min meke damun ki, bana son muna zaune da mutum inga yanayin sa ya canza wlh sai inji babu dadi...".
Ajiyar zuciya Zaitoon ta sauke kana ta tabbatar wa Marwa cewa babu komai banu abinda ke damun ta.
Shiru Marwa tayi tana duban ta ga dukkan alamu bata ji dadin amsar Zaitoon din a gareta ba.
Kawar da kai tayi ta cigaba da aiki itama, babu wanda ya sake tanka kowa tsakanin su sai dai Zaitoon da ta fahimci tamkar itama Marwa yayanin ya canza zuwa sabon yanayi duba da yadda taja baki ta gimtse sa6anin yadda suka saba tayi ta mata hira, wannan karon sbd ta kawar da shirun sai ta ringa 'ka'kalo 'yar hira amma Marwa ta'ki tankata ta karshe ma ficewa tayi ta koma dakin ta ta bar Zaitoon bayan ta tabbatar sun kammala aikin.
Bayan ta Zaitoon tabi da kallo...saman la66a ta furta" Fushi kenan...?".
Sai da ta tabbatar ta kammala komai kafin ta nufi wajen Marwa dake kwance saman gadon ta rike da wayar ta a hannu.
Tura 'kofan tayi ta shiga da sallama amma Marwa tamkar ma bata ganta ba balle ta nuna taji abinta ta fa'di.
Daf da ita ta isa ta tsaya tana duban fuskar ta da bakin ta dake bin wa'kar Mr Meddy da ke tashi cikin wayar ta.
" Marwa wai fushi kike dani kome...?"
" Me yasa zan yi fushi da ke kuma..?"
Ta bata amsa batare da ta dube ta ba.
'Yar daria Zaitoon tayi.." Baki saba ba shiyasa sam bai kar6e ki ba yanayin..."
" Ai ko ban saba dole zanyi tunda iya zaman mu baki yadda dani ba balle ki iya sanar da ni damuwar ki duk da cewa kuwa da kaina na tambaya..."
Ta 'karashe maganar gami da mi'kewa zaune.
" Kai Marwa ta, kaddai akan maganar 'dazun ce, indai itane kiyi ha'kuri zan sanar dake komai.. amma kafin nan dan Allah ki sanar dani ya asalin rayuwar gidan ku ke gudana...?"
Idanu Marwa ta fitar sosai..." Rayuwar gidan mu?, tamkar na kowa take mana..meyasa kika min wannan tambayar...?"
" Ina mamaki ne kawai"
Zaitoon tace tana shirin zama bakin bed din kusa da Marwa...sannan ta cigaba...
" _Kinsan jiya da dare da wuri muka yi bacci, toh ni dai ban san me ke faruwa ba, cikin daren Moopy na ta dame ni da 'kananun kuka, ba kasafai take min irin wannan rigimar ba dan haka sai naji hankali na duk ya tashi, saboda bansan abinda ke damun ta ba gashi ba baki ke gareta ba ballantana ta sanar da ni matsalar ta._
_Cikin wannan daren dole sai da na goya ta, a lokacin idan ban yi 'karya ba 'karfe biyu ne da 'yan mintina na dare, jikin window na tafi ina kan jijjiga ta sai nayi tunanin da ace zata koma ma da na dan yi nafilfili sai dai tuno cewa fashin sallah nake yasa na watsar da wancan batun._
_Daga inda nake tsaye ina iya hango harabar gidan har zuwa wurin parking motoci da yake dama kinsan direct saitin windown 'dakin da nake yake._
_Ga mamaki na sai na hango kamar motsin mutum 'kar'kashin motar yayan ki..."_
Da hanzari Marwa ta mi'ke tsaye dafe da 'kirji tace" Innalillahi wa inna ilaihiraji'un..wani Yayan nawa kenan...kardai Yah Rayyaan?"
" Ki kwantar da hankalin ki Marwa ba...."
" Babu wannan maganar Zaitoon ke de 'karasa bani labarin kawai baki san yadda naji zuciya ta ba ne..."
Cewar Marwa bakin ta har na sarkewa ta wani dam'ko hannuwan Zaitoon cikin tafukan hannun ta ta rike dam tamkar ance mata zata gudu ne batare da ta karasa mata labarin ba.
Kafin Zaitoon ta fara magana suka tsinkayi 'karar wayar Marwa dukkan su duban wayar suka yi..." _Yah Sulty_ " Suka ga an rubuta da tambarin heart ajiki.
" _Kyale shi zan kira shi daga baya cigaba da ban labarin abinda kika gani kawai_ ".
" _Nima mamaki ne ya kama ni sosai, ban san me hakan ke nufi ba amma har zuciya ta sai naji na kasa samun natsuwa, kafe wajen da idanu nayi ai kuwa sai ganin mutum nayi ya fito daga wurin yana 'yan dube- dube irin na marassa gaskia...Can ya nufa wurin hanyar gate daga nan ban san kuma ina ya kuma yi ba, ban da ba'ka'ken kayan sa da hasken wutar lantarkin harabar gidan ya taimaka min wajen gani ban fahimci komai game da shi ba..._ "
" _Jiki na sosai ya fara rawa zucia ta ta cika da wasi- wasin abinda hakan ke nufi, a zahiri nasan shirin ba na alkhairi bane shiyasa aka bi dare sai dai ban san manufar wanda na gani ba, ban kuma san ta ina ya kamata in fara bayyana abinda na gani ba, nasan bani da shaidar da zan fahimtar da masu gidan tunda bansan nufin koma waye bane nagani ya aikata hakan...shiru nayi, amma zuciya ta ta kasa saituwa, nutsuwa ta ta kasa dawowa jiki na._
_Zuwa lokacin tuni Moopy na ta jima da komawa bacci amma ni na kasa barin wurin har 'karfe uku ta gota da wasu mintina...Ajiyar zuciya na sau'ke bayan wani 'dan guntun tunani da nayi..'kila gyara suke yi wa motar..wani 6arin zuciyar tawa kuma tace min..gyara da wannan tsohon daren, meyasa sai tsakiyar dare?...to ke Zaitoona ina ruwan ki ne?_
_Nima dai haka na gani shiyasa na saki ajiyar zuciya...amma duk na kasa jina dai- dai._
_Da hakan na koma na kwantar da Moopy sannan nima na kwanta..duk 'ko'karin da nake dan ganin na cire abin a zuciya ta abin ya faskara._
_Sam bacci sai ya gagara 'dauka ta har sai da akai sallah sannan bacci ya 'dauke ni batare da na sani ba._
_'Karfe bakwai na tashi a bacci kasancewar Moopy na ta riga ni farkawa sai ta ringa min mutsutstsuku a jiki na tana 'kiran Mammi dole na tashi badan na soba...amma da tashi na wancan lamarin ya fara zuwan min kwanya ta...Sai kuma nake jin tamkar idan nayi shiru ban kyauta ba musamman idan na tuno irin karamcin Ammi gare ni, kuma wannan lamarin ya shafi ahalin ta ne, ya shafi farin cikin ta ne domin nasan ahalin ta suna farin cikin ta a halin yanzu, dan nayi shiru kuma bani da tabbacin daidai na aikata, ban san ina ne karshen lamarin gaba daya ba, ta iya yiyuwa shirun nawa ya kawo babbar matsala ta iya yiyuwa akasin hakan amma dai dole sai an yun'kura kafin ake kaiwa gaci, bai kamata inyi shiru in zubawa lamarin idanu har sai ya faru ba._
_Da wannan tunanin na samu 'kwarin gwiwar mi'kewa, bayi na shiga nayi wanka sannan na yiwa Moopy na ma"._
_Shi kansa ba sosai nake ganin sa ba yanzu, na kan mance ma da lamarin sa a rayuwa ta har naji muryar ko ganin sa, wannan ma sai dai in Ammi na gida ne kawai in bata nan ba kasafai ake ganin sa ba kinsan, abinda na guda in fada miki shine kar ki kasa fahimta ta shiyasa naji zuciya ta tafi bani in fara sanar da shi tukunna, ta iya yiyuwa idan na fada mk kafin zancen ya samu isa gare shi wani abin ya faru duk ba'a fata, amma dai ganin mutum karkashin motar wani haka siddan da tsakiyar dare ansan ba lafia bane, ta iya yiyuwa kuma ba abinda nake zargi bane amma nasan shi idan nai masa bayani zai fi fahimta ta ko da ace ba hakan bane, kuma ina da tabbacin zancen bazai yi yawo ba_ .