Sashe 169
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abinda ka'dai Zaitoon bata sani ba shine bata fa'da musu ba...'daya daga cikin su kuwa shine rashin son mage da Mufeeda bata yi bata san da shi ba, bata san a hannun mahaifiyar Dr Rasheed ta fara reacting ba domin basu samu lkcn da har zasu labarta mata ba suka rabu, so bata da labari har sai bayan zuwan ta gidan Ammi da suka je gidan Dada...ta kuma yi mamakin da har ta kasa 6oyewa, bayan ji da tayi daga bakin Ammi cewa Yaranta ma na da irin wannan abin a jinin su, baus 'kaunar mage, similarities din da take gani tsakanin 'diyar ta da yaran Ammi sai suka 'kara hauhawa amma still bata ta6a tunanin shi zai iya zamtowa mahaifi ga Mufeeda ba domin acewar ta baya 'kaunar yarinyar sam, 'kiyayyar da yake nunawa a gare ta me girma ce da ko nawi da kunyar bayyanawa baiyi koma a gaban wanene.
Tace na jima da yin nadamar baro iyaye na da nayi tun lkcn da tashin hankali ya kusan yin awon gaba da numfashi na, ga zaman prison ga rashin Mufeeda ga kuma takaicin tuhumar da ake min da bansan ina makomata zata kasance ba uwa uba babu kowa nawa da ya san inda nake balle akawo min 'dauki, a lkcn Allah na fawwalawa dukkan lamari na, a kullum kuma na kan nemi gafarar sa cike da burin komawa ga mahaifana da zarar na samu damar barin prison 'din, Allah maji ro'ko ya amsa min, ya kuma dube ni a lkcn da bani da kowa sai shi, bani da gata sai wanda shi ya wadata ni da shi, cikin ikon sa kotu fa wanke ni, aka kuma dawo min da 'diya ta cikin kyakkyawan yanayi, sai kuma haduwa ta da Ammi...ko a lkcn idan baki manta ba Ammi na nemi da kawai idan taimako na kk son yi kawai ki bani kudi kk ce a a, ba komai zanyi da su ba face komawa mahaifata, sai dai Allah bai bani damar haian ba.
Na yi 'ko'kari sosai wajen ganin na rufe mana sirrin rayuwar mu ba dan komai ba sai dan cewa da kaina nasan na aikata ba daidaiba, nabi son zucia ta akan rike Mufeeda ina kuma gudun ranar da asirina zai tonu irin hukuncin da zai iya hawa kaina shiyasa ban ware ko mutun guda da zan iya sanar da shi wannan sirrin ba na fitowa ta, na yi matukar mamaki da ku da kanku kuka fahimta, kuka fahimci cewa Mufee na 'diyar ku ce, kuka fahimci cewa ta ha'da jini da ku a zahiri duk da yake nasan akwai wasu abubuwa da kai tsaye suka bayyana hakan amma ni kaina ban saka su a mizanin da zai iya zamowa ta ha'din jini ba....amma ayau na tabbatar da cewa bani da wayo ba kuma ni da dogon nazari sam sam...
Abu guda da zan iya nema agare ku ahalin yanzu shine afuwar ku bisa abinda na aikata, ina kuma rokon sassauci bisa duk irin hukuncin da kuka ga zaku iya yi min shi, hakika ban aikata hakan da in cutar da wani ko kuma ita Mufeeda ba, hasalima nayi ne domin ina kaunar ta shine na sadaukar da komai nawa sbd ita...ku yafe min kan hakan da na aikata koda bazaku yafe min kan dukkan laifuka na ba, bama ni da bakin cewa ku yafe min gaba 'daya domin nasan ban muku adalci ba, na wahal muku da yarinya na sa ta sha gwagwarmayar rayuwa tare da ni wanda nasan da ace tana wajen ku ko sanin cewa akwai irin wannan rayuwar bazata yi ba, a ashirye nake da na kar6i dukkan hukunci na domin nasan na cancanci koma wani rin hukunci ne...".
Ta 'karashe da 'dauke siraran hawayen da ke bin kuncin ta.
" Dalla rufewa mutane baki, munafuka kawai algunguma, wa zaki ajiye ki cika shi da 'karya da tatsuniyoyin bakin ki irin naku na mutanen karkara?...kin je kin kwaso cikin ki kin haife kin zo nan kina wani shirya 'karairayin da ko ma'ana babu balle 'kamshin gaskia ke har kin isa?...toh tun wuri kisan inda dare yai mk, kisan inda zaki nema wa 'diyar ki dangi amma ba nan gidan ba...domin duk zuriar nan babu sa'anki, mun wuce sanin ki balle wata banzar 'diyar ki can....".
Cewar Amrah kenan tana mai nuna ta 'dan yatsa a hassale cike da kumfar baki.
" Shut up..."!
Rayyan ya doka mata tsawa da 'karfi ransa a matu'kar 6ace.
Ita kanta Zaitoon kuka take sosai, sam kalaman Amrah basu dame ta ba, domin tasan babu mai goya mata ba, babu mai yafe mata, kalaman Amrah kuwa bata ji matsayin komai ba face tuni ga zafin da ha'da musu cikin ransu, ta kuma san cewa da tun farko itace ta kawo zancen da fiye da hakan ma zataji amma da kansu suka fahimta suka kuma nemi 'karin bayani daga gareta toh me zata 6oye kuma, ita dai tasan bata yi munafurci kamar yadda Amrah ke tunani ba, kuma babu abinda ta canza ko 'kara cikin labarin da ta bayar.
Kukan da take ya ta'allaka ne da tuno wasu abubuwa da ta jima da binne su aranta, tuno wasu mutanen da suka kasance maha'din rayuwar ta ne, mutanen da bazata iya raba zuciyar ta sam sam da tunani da kewar su ba.
Kallon wajen da Ammi take tayi ganin yadda ta rungume Mufeeda ajikin ta da tuni ma tayi bacci, wani kauna da tausayin yarinyar ya sake ratsa ta...amma yanzu da sauki tasan koda bata tare da ita atleast tana da nata dangin na kanta da kanta.
Tsaye ta mi'ke duk da tana jin babu da'di cikin ranta kan tona sirrin rayuwar su da ta da'de tana 6oyewa, 'kafafun ta kansu sun yi sanyi sanadiyar da'dewar da suka yi tan'kwashe kuma bata motsa su ba..hanyar 'dakin ta tayi dan zuwa 'dauko musu shaidar da ita ka'dai ce agare ta da zai tabbatar musu da abinda take fa'da gaskia ne ba 'karya ba.
Bata so dai dai da 'kwayar zarra suji cewa akwai 'karya cikin abinda take fada kamar yadda Ammi ta fara hasashe tun farko...ga kuma Amrah, bata kuma san meke cikin zu'katan sauran ba.
Sai dai tun kafin ta bar parlorn baya kawai ta juya kafin ficewar ta taji an rungumo ta ta baya har abin ya 'kara bata tsoro.
Yanayin 'kamshi da zubin halittar ya sa ta saurin fahimtar cewa Rayyan ne.
'Ko'karin fizge jikin ta ta fara hawayen ta na tsiyaya amma ya ki bata wannan damar sam.
Shi kansa bai san me ke damun sa ba, amma ayau 'din kawai yaji aran sa cewa ta cancanci appreciation ba 'dan ka'dan ba..ta cancanci dukkan wani nau'in yabo daga gareshi, bai kuma san meya dace shi a matsayin sa na mahaifi ga Mufeeda yayi mata ba illa hakan.
Tausayin ta gami da wani girma da daraja nata yaji ya shige shi nan take.
Idanun sa lumshe ko kunyar sauran mutanen dake parlorn bai ji ba tunanin sa ma bai bashi hakan ba sam.
Sosai ya shigar da ita cikin jikin sa, ba kuma yaso ya bu'de idanun sa balle ta fahimci halin da yake jin zuciyar sa a ciki, tsananin tausayin halin rayuwa da suka fuskanta da kuma tuna cewa wai da gudan jinin sa akayi wannan fa'di tashin sosai ya karya masa zucia, ga kuma 6acin ran kalaman Amrah abin duk sai suka taru sukai masa yawa, idanun sa sun ka'da sunyi jajir, jijiyoyin kansa suka fito sosai...mutsu mutsu ta fara jin irin ri'kon da yy mata amma still ta kasa raba jikin ta da nashi.
Cikin kuka tace" Zan 'dauko jakan da mahaifiyar Mufeeda ta barmin ne, shine ka'dai shaidar da ke tare dani wanda zai tabbatar da gaskia ta....".
" Ba bu'kata!"
Ya fa'da da wata irin muryar dake tabbatar mata da cewar tun daga zuciyar sa ne.
Duk da hkn bata fasa 'ko'karin cire jikin ta daga nasa ba domin ta kasa tantance manufar sa....
" Nagode!"
Ya furta huci na biyo bayan maganar sa..." Thanks..so very much Zaitoon...Allah ya saka mk da alkhairi fin alkhairin da kk nufi 'diya ta da shi....".
Ya ra'da mata cikin kunne yana mai rarrabe maganar da 'daddaya.
Yana kuma gama fa'din hkn ya sake ta yayi gaba bai ko sake waigowa ba.
Jikin ta sanyi yayi sosai, har ma ta kasa motsin kirki har 'karasa ficewa.
" Meyasa zae gode mata? Meyasa zai zayyano mata kalaman godia irin wannan? aganin ta sam bata cancanci hakan ba! bata cancanci irin kalaman nan ba, Ita da take tunanin tayi laifi ta sace musu yarinya ta raba su na tsawon lkc?
Ita da ta riga ta shirya kar6an hukuncin ta sanin da tayi ta wahal musu yarinya da irin tata salon rayuwar? Kullum sai tayi tunanin irin hukuncin da mahaifan yarinyar zasu yi mata idan suka ganota ashe ma cikin su take rayuwa bata sani ba, ashe suke ciyar da 'diyar su bata sani ba, sai kuma gashi suna gode mata...she is totally confused ita bata ga abin godia da tayi anan ba.
Kalaman Amrah sun riga sun yi mata tasiri a zucia, hakan ya sa ta zubewa bisa gwiwoyin ta tana mai jin zuciyar ta na harbawa.
Marawa ce ta taso da gudu ta rungume ta tana kuka take fa'din" Hakika Zaitoon ke 'diyar halak ce, wai dama duk wannan kaunar da kk yiwa Mufee ba kece kk haife ta ba Anty Nadian mu ce...? Ashe Mufeeda jinin mu ce ban sani ba...?"
Kuka ta cigaba da yi tama kasa cigaba da magana.
Haushi sosai ya kama Amrah ji take tamkar ta zo ta make su dukkan su.
So take ta bar parlorn sbd tsananin takaicin da take gani amma tafi so taga 'karshen komai da idanun ta shiyasa ta kasa tafia ko ina.
Ammi ce ta yi 'ko'karin daidaita muryar ta hkn kuwa ya jawo hankalin dukkan su gareta.