Sashe 10
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( ' Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️...6
.....Wasa-wasa Bbn Abdul da ya tafi sai da ya shafe watanni uku cif bai waiwayo gida ba wanda yayi dai dai da cikan Feefy watan bakwai da haihuwa, Bbn Abdul sai dai aike kawai da ya saba yi musu ya cigaba...Mmn Abdul kadai abin ke damu domin tasan shirun nasa ba alkhairi yake shukawa acan din ba yayin da Hajja tayi mirsisi ko ajikin ta tamkar ba shi ne kadai kyautar da Allah ya bata na haihuwa ba.
Tuni Mufeedah ma ta fara takawa kadan kadan ba karami dadi hakan yayi wa Zaitun ba ji tayi tamkar zata hadiye ta saboda farin ciki, hatta Adam sai da tai masa albishir washegari cewa Mufeeda ta fara taka kafar ta, bai boye farin cikin sa ba shima in da kara da alkawarin zuwa yaga tafiyar Mufee a ranar da yamma hadda guzurin dandasheshen takalmi.
Matakin kaunar da Zaitun ke wa yarinyar bai ta6a yin kasa cikin zuciyar ta ba sai ma karuwa, zaku yi mamaki idan kuka a yadda Zaitun ke kwana da yarinyar bata ta6a bari Mufee tai juyi ba'a cikin jikin ta ba, kullun kan cikin ta take kwantar da yarinyar ta bata ta6a gajiya da hakan ba sai dai in gari ya waye lokacin in zata yi sallah sannan take kwantar da ita zuwa wayewar gari, shiyasa ko baccin rana mai kyau Mufeeda bata iyawa saboda sabo da jikin Zaitun da tayi.
Zuwa yanzun kuwa tuni Mufee ta gama sakin jikin ta da kowa na gidan banda Hajja kadai da kullun kyara da tsangwama ce tsakanin su hakan yasa Mufee kokadan bata kaunar zama inda Hajjan take, yarinya ce amma tana da tsananin wayo da takatsantsan sosai tasan me kaunar ta da me kyarar ta.
Su Siyama kadai ne abokan wasan ta sai su yini suna wasa bata damu ba in kuwa suna makaranta da Ahmad take wasan ta.
In ka jiyo tashin dariyar Feefy toh kuwa da Siyama ne ko kuma Zaitun.
Takan ci ko wani irin abinci yanzu shiyasa tuni Zaitun ta huta siyan madara sai dai dan hada mata shayi, dan kullun dare Mufee sai ta tashe ta tasha shayin nan.
Duk lokacin da Zaitun ta dawo gida daga wajen aikin ta farin cikin Mufee bai ta6a 6oyuwa haka zata zo da gudu tana " Mammi!..Mammi..!!" Tana daga hannuwa sama tana dariya.
Kamar dai yau ma hakan ne ya faru Zaitun na dariya ta dago ta sama " Oyoyo Mamana...oyoyo 'yan mata na.".
'Dago Mufeen da tayi idanun ta sak ya sauka kan gashin Mufee ta kalla ta sake kalla take sai ta dan dama fuskar ta tana duban Maman Abdul dake zaune tana jifan su da kayataccen murmushi da yake tasan me hakan da Zaitun tayi yake nufi.
" Kwantar da hankalin ki Hajjaju ba ma tayi kuka ba...ke baki ga yanayin kitson bane bafa sosai na kama mata ba.."
Murnushi Zaitun tayi itama tana lakutan kumatun Mufee tace" Kinyi kyau Feefy na, kin yi kyau sosai 'yar albarka.." Ta karashe da fadin" kuma fa kitson ya haska ta sosai, Mmn Siyama dole abaki tukuici tunda yake bata yi kuka ba...yarinya ta tayi kyau wlh.." Ta karashe maganar tana saukar da Mufee ta dago Ahmad da shima yake 'dago hannayen sa yana fadin.." Feefy.."
Da son shima a daga sa.
" Ahmadi na Feefyn ka yau an sha kitso an zama 'yan mata kyakykyawa..".
" Dama asali mai kyau ce ita, ki ringa bari ana mata kitso kiga yadda yarinyar nan zata dawo, yau ma din kawai gashin ne naga kamar idan aka biye ta taki ahaka zai ta lalacewa shiyasa na kama mata kuma ma in ba a yi mata ai bazata saba da kitson da wuri ba..".
Bata bi takan wannan zancen na Mmn Abdul ba kawai ta gaida Maman Abdul din tare da yi mata barka da gida da kuma ban gajiyar kula mata da yarinya da take yi kullun...yau din haka kawai take jin zuciyar ta wasai..shiyasa murmushi ya kasa barin fuskar ta.
Biskuit, sweet da cheese balls da ta saba siyowa yaran yauma shi ta raba musu kowa ya ansa cike da annashuwa.
" Bari in dan watsa ruwa yau din wlh duk na gaji sosai.
Ko bayan shigewar ta Maman Abdul tunani kawai ta lula tana duban fuskar Mufee da kullun asalin kyawun yarinyar ke kara fitowa, musamman yanzu da yake Maman Abdul din na kulawa da ita sosai tamkar daga cikin ta ta haife ta...idan baka san Mufee tun farko da Zaitun ba bazaka ta6a tunanin yarinyar ta bace sam.
Duba ma da yadda kalar hasken fatan su ya banbamta, hanci da idanun su kadai ne da suka zo iri daya baya ga haka babu abinda Mufee ta kwaso daga Zaitun din, sosai hasken ya kere na Zaitun nesa ba kusa ba.
Tsananin soyayyar da Zaitun ke nunawa yarinyar ne yake matukar tsaya mata a zuciya, sosai abin ke sanya. Mmn Abdul tunani, da ace bata ta6a haihuwa ba kila da zata ce dan bata da 'da ne shiyasa bata san zafin su ko dadin su ba amma abin sam ba haka bane, soyayya ce zallah da ko da wasa bata hada shi da komai ba, ta jima da fahimtar irin sadaukar da farin cikin ta da take yi saboda yarinyar, kitso wannan sai da aka kai ruwa rana kafin Zaitun ta amince ta fara yiwa Mufee shi dan har ta kai watanni bakwai da haihuwa ba'a ta6a saka hannu cikin kanta ba dan yin kitso ba kuma gashin ba laifi tana da shi amma Zaitun sai dai ta taje shi in Maman Abdul ta matsa ne sai ta sa rubber band ta daure shi manya in ta ga dama uku in yayi yawa ne guda biyar, kuma taki yadda kowa ya sa hannun sa kan yarinyar, hatta Adam ya mata complain kan barin kan Mufeen ba kitso amma Zaitun sai ce masa tayi kuka zata yi idan aka kama kan.
Babu yadda ya iya dole ya kyale ta.
Watarana da tadawo tazo ta tadda an wa Mufee kitso shuku mai kyau ibra akalla zasu kai kwaya sha takwas bakaramin zaro idanu tayi ba cike da tashin hankali, dan kallo daya ta yiwa yarinyar ta fahimci tasha kuka wanda take kyautata zaton na kitson ne...yayi kyau kam ya kuma kara fito mata da kyau da hasken 'yar ta amma ita duk wannan ba shine gaban ta ba, the fact that Mufeeda tayi kuka shine kadai damuwar ta.
Amma tayi kokari wajen ganin ta danne hakan saboda karamcin Maman Abdul agare ta yafi karfin wannan, a fili nuna jindadin ta da ganin kitson tayi inda ta yabawa Maman Abdul din sosai...
Sai dai duk Maman Abdul na lura da ita, sarai tasan kukan yarinyar ya tsaya mata arai kawai basarwa tayi domin duk wani takun Zaitun din baya mata wahalar ganewa kawai itama sai tayi murmushi.
Da sati ya zago kuwa Zaitun da kanta ta tsefe kitson nan tunda rana da yake asabar bata zuwa aiki dan haka da dare ta hana idanun ta bacci haka ta ringa lalla6a kan tamkar me lalla6a kwan da be gama kwari ba, da zarar ta motsa kuwa sai ta bari da haka har ta kammala mata kitson, kuma fa ba wai iyawa ta yi ba kawai dai bata san ganin an takurawa yarinyar ne sam shiyasa ta lalla6a tayi da kanta.
Washe gari da Maman Abdul taga kitson dariya sosai tayi.
" Wlh Zaitun baki da dama, yanzun wato rigakafi akayi mana shine kika yi wannan din ko? da ki bari ai mata mai kyau gara ki mata hana kuka da kanki.."
Murmushi kawai Zaitun tayi tana shafa kan yarinyar tace"...Toh ba gashi ba asirin mu arufe babu wanda yaji kukan mu.."
" Gara kuyi zuciya ai dan ni kam yanzu na fara indai bazaki mata da kanki ba toh kuwa kin ringa tarar da mu da jajayen idanu sai dai kiyi hakuri kawai"
" Kai Mmn Abdul baki tausayin ta ne dan Allah..?"
" Ba rashin tausayi bane ai ke ma din so nake ki rage ki na dinga sassautawa, kaunar da kike nuna mata sai inga kamar yana zarta iyaka, baki ji ba ne da hausawa kan ce kazo naka duniya ta 'kishi..."
Bata yi magana a fili ba cikin ranta tace" Ko kowa ya ki ta ni ina son kayana"
A fili kuwa daidaita zaman fuskar ta tayi da ta Mufeeda dake wasa da wani Balloon a hannun ta.
Hannayen tasa gefe da gefen fuskar yarinyar ta lumshe idanu..." Kauna bata ta6a yin yawa Maman Siyama, ni gani nake ma tamkar da saurana cikin irin tarin kaunar da nake yiwa yarinyar nan, wannan halittar da kike gani itace bugun zuciya ta Mmn Abdul, itace farin ciki na, Mufeedah wata 6angare ce daga cikin rayuwa ta, ji nake daga ranar da tayi nesa dani tamkar anan rayuwa ta zata tsaya..'digan hawayen Mufeeda jin sa nake tamkar garwashin wuta cikin kirji na..."
Cike da mamaki Maman Abdul ke duban ta cikin ranta ta furta
" Allah mai iko.."
"...Zaitun ni kam har kullun cike nake da son jin tarihin rayuwar ki ina so in san wace ke, meyasa ke baki ta6a tunanin bani labarin ki ba duk iya tsawon zaman nan da muka yi..."
Sai lokacin Zaitun ta dago ta dubi Mmn Abdul ido cikin ido yayin da nata idanun ke cike taf da ruwan hawaye da ya tsatstsafo sakanni kalilan bayan maganar Mmn Abdul na karshe.
Kafin hawayen ya gangaro ne tayi saurin maida duban ta ga fuskar Mufeeda wanda yayi daidai da gangarowan hawayen nata suka hada idanu da yarinyar, tuno abubuwa da dama take yi, abubuwa ne da bata jin har abada zata iya mancewa da su.
Mufeeda kam cikin idanun Zaitun din ta tsaya kalla ganin yana ruwa...daga ita Zaitun din har Mmn Abdul sun yi matukar mamakin ganin yadda Mufee ta saki Balloon din da take wasa da shi tayi saurin kai hannun ta ga fuskar Zaitun..." Mam..mi..!"
Ta fada tana me shafo hawayen dake gangarowa.