Sashe 187
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Karamin tsaki kawai yaja ya nufi hanyar fita dai- dai lkcn da jami'an tsaro ke bawa Sultan umarnin komawa ciki shi kuma yana fa'din babu wani sauran sirri da ya rage min Amra...ban san amfanin ko wani sirri tattare da ni ba a halin yanzu, Arfan ka'dai gare ni sai Allah na, dama bani da kowa taimako na akayi aka bani dangi aka bani muhalli, aka bani sittira aka bani gida aka mutuntani aka mayar dani 'da amma na butulce...ban sani ba ashe tun farkon rayuwa ta ni ba mai sa'a bane, ni ba mai nasara bane tunda banyi nasarar fara rayuwa da mahaifa na bama, ban san jinsin ina ne ni ba, ban san matsayi na cikin al' umma ba, ban san matakin daraja ko kaskantar ahali na ba, tun afarko na rasa wannan damar, na rasa damar sanin asali na, yanzu nazo ga6ar da ko da ina dasu ma basu da wani amfani gare ni balle ma babu su, toh me zan rufe, me zan rufe a rayuwata, na riga na lalata jiya na, yau da gobe na kuwa duk anan gidan suke me zan rufe da zai min amfani? Da kaina na jawa kaina, da kaina na ja wa kaina sake rasa wata damar ta daban....."
Bai gama magana ba aka tisa 'keyar sa ciki.
Bayan sa kawai da Amra ta hanga shigewar sa ya sake sawa ta rushe da kuka, ba wai dan tana tausayin sa bane a a, kuka ne ba'kin ciki tsamtsa, kuka na takaicin wautar ta tun a farko, yanzu ace wannan shine mahaifin 'dan ta? 'Dan da ta bi ta Dunia ta kara'de ko'ina da hoton sa da 'karyar cewa jikan Marigayi Sa'ad Auta ne..? Meyasa ban ta6a tunanin rana irin wannan ba? Meyasa ban ta6a hasaso faruwar makamanciyar irin wannan lamari ba?
Haushin kanta da kanta take ji sosai, sai ma ta rasa tun farko me ya ru'de ta har ta fa'da son shi, ta kuma biye masa har suka yi ta aikata alfasha sau aadadin da ita kanta bata san iyakar su ba, ta banzatar da auren ta sbd shi, meyasa bata yi tunani mai tsawo ba a lkcn...meyasa ta biyewa son zuciyar ta ne? Meyasa!...meyasa!!..meyasa!!!...tambayoyine ke barazanar tarwatsa mata kwanya.
Wata zuciyar ta ce ta bata amsa da fa'din shai'dan ne hakika shaidan ne yy nasarar afkar da ita...a fili da kuma 'karfi ta furta" Shai'dan ka cuce ni...shai'dan baka yi min adalci ba...yanzu gashi ka kaini ka baro...hakan ta ringa nanatawa a fili ta na tafia tana dukan kanta tamkar mahaukaciya, ko tuna cewa da mota tazo ma batayi ba, key 'din motar ma da takalmanta anan ta anan ta barsu tayi gaba.
Lkcn da ta fito tuni su Rayyan sun yi nisa dan ko 'kurar motar su bata gani ba.
Kuma har a lkcn kuka Marwa take yy mata tsawan tayi shirun har ya gaji.
Domin kamar ma bada ita yake ba..rana na farko da Marwa ta kasa bin umarnin Yayannata, rana na farko da sam tsawan sa yaya kasa daidaita ta...rana na farko da ta kasance da shi wuri gguda cikin irin wannan yanayin bata re da fargaba ko kuma tsoro ba...sam ta hankalin da zata nemo tsoron kansa bata ganshi ba... 'karshe shima Rayyan kansa tausayi ta koma bashi, hakan yasa bai sake kula ta ba har suka iso gida...ga Mufee ta koma jikin ta ta lafe sbd kukan da take yi ba hakan ta saba gani daga gare ta ba...Bai zame ko ina ba sai can gida yana isa kuwa ya cire key 'din ya bar su amotar bai san ma lkcn da suka shiga ciki ba shima damuwar dake ransa ta ishe sa ba a daidai yk jin natsuwar sa ba.
Babban haushin sa ma yadda Amra taje cikin 'dimbin alumma ta fa'di wancan maganar take sirri ce gare su...tuni ya gama yanke shawarar zama da ita ya 'kare masa tun daga wamcan lokacin...sam bazai iya ba, bazai iya cigaba da zama da mace irin Amra ba ko da ace ita ce 'karshen matan dunia zai iya yafe ta.
Haka nan Amra ta na'di hanya ta ringa yawo tana nanata wannan kalmar tamkar mahaukaciya, gaba 'daya ta zauce ta fita a hayyacin ta tamkar wata zararra.
Ta kai kusan awa biyu tana yawo bata san ina hankali da tunanin ta ya tafi ba sai bu'de ido tayi ta ganta kwance a 'dakin asbiti kakkarfan haske a kanta...wani abokin Abban ta ya ganta ya dawo da ita gida duk bata san anyi hkn ba.
Ko a lkcn kuma sumbatu take...ina son shi, amma naci amanar sa, ban kyauta masa ba, na haihu da 'kanin sa, Shaidan bai min adalci ba...shaidan ka gama cutata..."
Jin irin kalaman bakin ta da yanayin da ya 'dauko ta yasa da kansa ya wuce da ita asbitin Dawanau dake nan cikin garin Kano sannan ya sanar da mahaifan ta.
Mummyn ta rikice sosai itama ta ringa kuka da tsoron abinda ya sa canza mata yanayin yarinya da har za'a kaita Dawanau....dan da farko ma taso ta yi masa masifan meyasa zai kai mata yarinya cikin mahaukata amma bai tsaya ya saurare ta ba ya kaste wayan yayana jan tsaki.
Aanayin da ta ga Amra bayan isowar ta yasa taja baki tayi gum kawai ta ri'ka kuka a bayyane dan ta kasa yin na 6oye..sai da hana ki, sai da nace kar ki koma Amra dubi abinda kika jawa kanki..."..kin biyewa soyayya kina neman haukata kanki...haba Amra..sai kace ba raino na ba..akan namiji...namiji dai..."
Bayanan bakin likitoci ne ya sanya ta 'danji kwarin gwiwa.
Duk da hakan ta sha wuya kafin ta samu Amra ta dawo dai-dai ba kuma kananun kudade ta kashe ba akan 'dan zarewan da Amran tayi...nan ta turke ta sai da tayi mata bayani dalla dalla.
Ita kuka mummyn ta kuka tana fa'din ta cuce ta, dama duk wannan fama da 'daga muryar da take sata yi ashe zaman cin amanar mijin ma take yi...wannan abin kunya da me yy kama...innalililahi wa inna ialhi raji un...
Tace shiyasa da ta sanar da shi batun rashin lafiyar fatan samun sauki kawai yy mata ya kashe wayar sa, kuma har suka dawo gida bai sake 'kira yaji yanayin jikin ba balle akai ga batun ba zuwa duba su ba.
Mummyn Amra zaune take a 'dakin ta amma kunya da nauyin ahalin Sa'ad Auta take ji na shigan ta ta ko'ina.
Sam sam bama tasan ta iina zata fara ba.
Kunyar abubuwan da ta ringa yi musu akan 'diyar ta take ji... Sai gashi babban abin kunyar da 'diyar tata ta kwaso mata, ashe gwara shima auren yar aikin Amra kawai yayi aure kuma mai cike da shaidu ba haikewa yarinyar yayi ta haifa masa 'da ko yarinya ba.
Gaba 'daya Amra tasa mahaifan ta cikin zullumi, kar ma mahaifinta bawan Allah yaji labari.
Gaba 'daya ya kaurace musu, hatta gaisuwar su bai amsawa ita Amta har Mummyn nata, baya cin abincin ta fushi sosai ya 'dauka da ita, dama yasha fada mata batun yau ba akan zata 6ata Amra da matukar dai bata canza yanayin da take tafiyar da rayuwar ta ba, indai bata canza kalmomi da lafazi game da auren Amra ba tace sam dole ne ta kwatarwa 'diayrta 'yanci...sai gashi rana tsaka abinda ya tsinkaya...sam irin 'yancin da take ikirari akqi din bashi ya tsammata ba kuma bai ji da'di ba.
Arfan kam tuni shan nono ya 'kare masa, tunda mahaifiyar sa ta shiga wani hali bata 'kara shayar da shi ba..toh ina ma zai ganta.
Baki 'daya rainon sa sai ya koma hannun Nannyn sa dan guidan ahalin yanzu bb ma mai lkcn tunawa da shi.
Zaitoon kuwa itama tun fitar su take kuka cike da haushin an hana ta tafiya tare da Marwa, haushi sosai take ji na hana ta da Rayyan yayi, gashi dalilin hanawan ba wani muhimmanci ta basa har a ranta ba, kusan kullum ma tunani da burin ta taji an yaye mata amma shiru sai ga wata sabuwar tsirfa wai bazata je waje ko kuma aikata abinda ranta ke so ba sai da iznin sa.
Har suka dawo gidan bata huce ba, amma ganin yanayin Marwa ya sa ta tuni tayi watsi da nata takaicin ta rungumi na Marwa.
Bata samu natsuwa ba har sai da ta ta tabbatar ta kwantar wa Marwa da hankl ta kuma samu bacci kafin ta nustu.
Ta tausaya mata matuka, sosai ita kanta taji bb dadi, jikinta duk yai sanyi..taji ta karaya...ashe nata ba ma komai ba ne... dan sun tattauna batun da Marwa kafin baccin ya 'dauke ta.
Ammi kanta bata san da dawowan su ba sai ganin Mufee kawai tayi nan ta fahimci ashe sun dawo.
Rayyan ma bai je 6angaren ta ba yana can nasa 6angaren shima da nashi kalan damuwar dake nukurkusan shi.
Kusan ilahirin ahalin kowa da nashi tashin hankalin kunshe a kirjinsa.
Sai dai wannan karan ba Marwa ka'dai ba hatta Rayyan bai sake tattauna batun da Ammi ba sbd matakin 'karfin lafiyar ta sosai ya raunata cikin kwanakin...ita Marwa kam bama zata iya sake maimaita maganar gaban Ammi ba, kunya sosai take ji na borin da ta ringa yi musu akan Sultan...sai gashi da kansa ya tabbatar mata komai.
Sai dai wani abu guda da ya 'daure mata kai har a lkcn ta kasa jin haushin sa, gani take kamar gazawan da tayi wajen haihuwa ya sanya shi neman Amra har suka haihu...soyayyar da take masa daga cikin zuciyar ta ne, ginin da soyayyar sa tayi cikin zuciyar ta yy girman da bazai iya misaltuwa ba...kuma bata jin zai iya barin ta a lkc guda.
Da Zaitoon ka'dai ta iya tattauna batun kuma Alhamdulillah ta fahimce ta ta kuma samu natsuwa...dama can suna shawartar junan su idan abu yasha wa 'dayan su kai shiyasa yau din ma direct wajen ta tayi...akwai fahimta da shakuwa tsakanin su biyun fiye da zaton mai karatu.