Sashe 5
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai taji dadin ganin yadda yarinyar tayi bacci sake a ranar, sau daya tak ta farka kamar yadda ta saba tun farko tun ma a gida kafin suzo nan dan haka bai zamewa Zaitun wani sabon abu ba, haka ta tashi ta bata madarar ta ba'a jima ba kuwa ta koma baccin har wayewar gari.
Gari na karasa wayewa yau din ta kuduri aniyar fita ta nemo abinda zata karya da shi da 'dan canjin dake hannun ta dan bata so ta daurawa Maman Abdul nawi da yawa kocdaren jiya ma ragowar abincin da Maman Abdul din ta aiko mata shi taci tayi bacci.
Waina ta siyo ta naira dari sannan ta fara laluben inda zata ga shago, ba karamin wahala tayi ba kafin ta gano inda shagon yake anan ta sai sabulu da omo anan shagon taga ana saida tsintsiya dan haka shima ta siya guda daya...hatta baho anan ta siya dan madaidaici ta hada hadda bokiti ta siya karami da yake shagon na yorubawa ne kusan komai suna saidawa.
Kafin ma ta samu ta dawo gida har rana ta hau kadan shiyasa ko lokacin da ta dawo gidan shiru ta jisa da alamu su Siyama har an wuce makaranta.
Gidan basu da matsalar ruwa sam sam dan haka tana gama cinye wainar ta ta tattaro kayan yarinyar kaf da nata da suka yi datti ta fito da su.
Wajen Maman Abdul tayi tunanin zuwa ta gaida ta dan ko bakomai matar nan ta nuna mata halacci da kauna daga ita har yarinyar ta.
Bayan sun gaisa din ne Maman Abdul take mata tayin abinci tace a a taci abinci ai.
Maman Abdul bata takura ta kan hakan ba sai cewa da tayi toh ga ruwan wanka nan tun dazun ma ya tafasa na leka naga bakwa nan.
Ahmad dake shan Mama a cinyar Maman Abdul Zaitun ta 'dan yiwa wasa cikin ranta take jinjina tsabta irin na matar nan yaron tsab da shi alamun har an mai wanka, tun zuwan ta gidan bata ga alamun datti ko kazanta tattare da yaranta ba"..an gode sosai Maman Siyama, dama inaso nayi dauraya ne yanzun inyaso idan na kammala sai muyi wankan daga baya"
" a a ke de kije kiyi wankin naki ita yarinyar kawo ta in mata wankan zata fi jin dadin jikin ta idan an mata da wuri".
Zaitun bata yi musu ba ta kwanto yarinyar daga bayan ta ta mikawa Maman Abdul ita.
Cikin kwanaki kalilan shakuwa ta shiga tsakanin Zaitun da Maman Abdul, 'dan ragowar kudin da ya rage mata tuni ta tanadarwa Yarinyar ta madara da shi.
Ta siya omo wadatacce wanda tasan bazai zo ya kare mata cikin kasa da sati biyu ba ko dan saboda wankin yarinyar ma.
Tuni kuwa Maman Abdul ta kawo mata wasu kayayyakin kamar yadda ta fada ranar Zaitun har kuka sai da ta yi saboda farin ciki.
Net irin na yara wanda zai hana sauro cizan mata yarinya, kayan sanyi masu kyau wadanda take da tabbacin basu wani dade ana amfani da su ba, ragowar kayan Ahmad na jegon sa kananun rigunan da suka gaza mai hadda washin Pampers Maman Abdul ta bata.
Shiyasa matar ta gama shiga ranta ta zauna daram domin ta saukaka mata abubuwa da dama.
Wannan washin Pampers din shi take sawa yarinyar da dare shiyasa yanxu ta huta wankin kayan fitsari da ta shi tai wanka tai wa yarinyar sai ta kayan da ta cire mata da Pampers din ta shanya kafin ta dawo MamanvAbdul ta kwashe mata kayan ta adana ta mata su.
Yanzu kam bata da tashin hankali tunda yarinyar ta wadace take da komai sai dan abinda ba a rasa ba.
Dawowar Sirkar Maman Abdul gidan daga tafiyan da tayi shine babban tashin hankalin Zaitun a yanzu dan ko kadan matar bata da dadi, sosai take ciwa Zaitun mutunci ita da 'yar ta dan tun abin ba ya damin ta har yazo yana ci mata zuciya musamman da ta lura abin bana kare bane.
Gashi sai ta hana jikokin ta ra6ar Zaitun din sai dai suzo asace in dai tana gida in kuwa bata nan toh tamkar dangi suke da yaran.
Sosai suke kaunar yarinyar tata, dan haka tuni ta yada makaman ta na hana Siyama daukan yarinyar yanzu kam bata hana ta.
Sukan kira yarinyar da Mufeeda, wani lokacin kuma Muphy...yayin da Ahmad da be iya magana sosai ba yakan kira ta da Feefy ne shi bisa ga rashin kwarin harshen sa.
Sukan yi dariya sosai idan ya fadi sunan amma wasa wasa da tsokana da 'yar raha har sunan da Ahmad din ke fada ya bi bakin duk su Siyaman.
Hajja itace kakar su Siyaman wadda ta kasance mahaifiya ce ga Baban su Maman Abdul ke fada min cewa zaman su tare ya samo asali ne tun lokacin da ta haifi Ahmad saboda gargadar da haihuwar tazo da shi har sai da akai mata aiki tun lokacin da Hajja ta dawo zama da su bata sake komawa ba sai dai taje ta ziyar ci dangin nata ta dawo kamar dai wannan tafiyar da tayin kafin zuwan Zaitun gidan.
Baban Abdul mota yake ja daga gari zuwa wani gari har kudu yakan kai kaya dayake babbar mota ce yake ja, kuma mutun ne shi mai zuciya ga kokari, dan ya kan wadata gidan sa da komai da komai na bukatan rayuwa duk da yake ba zaman wuri daya ya cika yi ba amma hakan bai sa ya rage abinda yake musu ba, dan tun zuwan Zaitun gidan bata ta6a ganin sa ba, kamar yadda bata ta6a ji ko ganin Maman Abdul sun nemi wani abu sun rasa ba.
Gudun kar ta zame musu tamkar karin nawi ta 6angare guda ya sanya ta ma rage zaman gidan gaba daya.
Sati guda ya rage ta fara fita aikin ta dan haka ta shirya taje wajen Hajiya Talatu gudun kar ta manta da batun ta.
Ai kuwa batayi mamaki ba lokacin da Hajiya Talatu ke sake tambayar ta wacece ita sai da ta yi mata bayani dalla dalla kafin ta gane ta.
"...ai kuwa na ma manta dake...amma dai babu damuwa tunda kika dawo da kanki da alamu shirte kike, Allah de yasa zaki min aiki yadda ya kamata dan ni bana daukan wargi...wanke wanke ne amma duk lokacin da Customers suka ci abinci atake ake wanke min su babu 6ata lokaci dan banason kazanta...fatan kin fahimta?..aikin ki zai fara ne daga safe har zuwa lokacin da za'a rufe wannan wurin...sannan kudin aikin ki dubu shida ne duk bayan wata guda".
Sosai Zaitun taji dadin yadda Hajiyan ta kar6e ta cikin sauki take ta nuna godiyar ta a fili duk da kuwa cikin zuciyar ta lissafi take na yadda kudin zai ishe ta dawainiyar yarinyar ta.
Tana shirin juyawa ta tafi bayan Hajiyan ta sanar da ita lokacin da ya kamata ta fara zuwa aikin Mufeeda dake bayan ta ta dan yi yunkuri gami da sakin kuka kadan irin na jirajirai.
Ido Hajiya ta waro akan Zaituna gami da fadin" Zaitun wannan fa..me nake ji haka?"
Murmushi Zaituna tayi tana girgiza Mufeedan tace.." Hajiya 'YATA CE".
" Wai dama kina da goyo?"
Cike da mamaki hajiya ta tambaye ta tana me bin ta da idanu.
Da kai Zaitun ta bata amsa..yayin da mamakin Hajiya ya kasa 6oyuwa.
"...kuma da ita zaki yi aikin..?"
" Hajiya saboda ita ma na nemi aikin ai...".
Shiru Hajiyan tayi illah idanun ta dake yawo jikin Zaitun din tana kissima abubuwa da dama, hakika zamani ya gama lalacewa, baya ga haka ace kamar wannan yarinyar har ace tana da goyo.
Ita fa bata mata kallon wata aba ba, kuma ko ranar can sam bata kula da cewa Zaitun din dauke da goyo take ba shiyasa ma ta rage asalin kudin da take biyan masu wanke wanken nata dashi ganin yarintar Zaitun din ashe ta wuce ma tunanin ta.
Daga shagon nan Zaitun bata koma gida ba kamar yadda ta saba...gida gida take bi tana tambayar in suna da bukatan ai musu wanki, wanke wanke, shara ko wani abin daban sai tayi a biya ta, da kudin take samu take siyan abinda take ci kullun gefe guda kuma take ajiye wani abu kalilan daga ciki dan kula da yarinyar ta, da yake har yau din nan Zaitun bata ta6a hura wuta ba..toh ina ma taga tukunyar da zata dora din bata da shi, dawainiyar da zata yi kafin fara dora girki kuwa a gida ta kwammaci kullun kawai ta rika siyan abincin tana ci yafi mata sauqi.
Babu abinda ya dame ta yanzu tunda asirin ta a rufe yake yanzun a ganin ta.
Damuwar ta bai wuce zagin da Hajja ke yawan yi mata ba ita da yarinyar ta, ta tsani kalmar nan da Hajja ke jifan ta da shi ta kuma kira yarinyar ta da shegiya...Hajjan na cin darajar Maman Abdul ne da kuma yawan shekarun ta baya ga haka da sam bazata iya cigaba da barin ta tana aibanta mata yarinya ba. Dalilin kenan da ya sanya zuciyar ta za6a mata daina zama a gidan tana fita yawon neman aiki yafiye mata...Hajja bata gansu bama balle ta bisu da kalami mummuna.
Sai daga baya ma ta fahimci rashin zaman nata ba karamin taimakon ta yayi ba domin ta koyi abubuwa da dama daga cikin halayyar mutane wadanda ada sam bata san su ba.
Cikin ikon Allah kwanakin fara fita aikin ta yayi ta fara zuwa tana aikin kamar yadda Hajiya ta tsara mata.