← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 218

Sashe 159

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sassarfa na isa gidan Innah ta duk da Abbab mu ya hana ni zuwa amma inaji cikin raina cewa na yau ka'dai kam bazai zame min matsala ba, kuma ko bazai saurare ni ba zan bashi ha'kuri duk da ban san takamammai dalilin hana ni zuwan ba sai dai inaji araina cewa wannan taimakon Inna ce ka'dai zata iya yi min shi cikin salama har na mayar wa Nadia diyar ta batare da an samu matsalar komai ba, dan sarai nasan halin Iyami bazata ta6a yi wa yarinyar wankan ba 'karshe ma 'kila ta tara min jama'a ne akaina kawai.

Ita kanta Inna ta da ta ganni haka sai ta rikice musamman da yake tasan gari babu lafiya ga kuma jikin hijabina da hannayen na duk jini.

Lokacin da ta lura da jaririyar dake 'dauke ahannun na kuwa sake rikicewa tayi tana tambaya ta inda ta samo.

Sama- sama nayi mata bayani tare da sanar da ita abinda nake so ayiwa yarinyar nace mahaifiyar ta na can tana jira na maida ta...dama tare zamu zo amma an harbe
ta a cikin ta".
Sam ban 6oye wa Inna ta komai ba, kamar yadda ban fada mata 'karya dai dai da kalma guda ba.
Salati Inna kawai ta fara jerowa zuciyar ta cike da tsoro da fargaba tace" Ke kuma ina kuka ha'du da ita?"
" Iyami ce ta aike ni jeji ciro ganye na ma barshi a can jejin idan nayi zan 'dauka in kai mata..Innani har yara biyu fa ta haifa amma tace 'dayan wai bashi da rai yana can tare da ita.".
" Allah sarki..."
Inji Inna ta cike da tausayawa.
Hakan sai ya kara min kwarin gwiwa...nace
" Sai ma kin ganta Innani, wallahi 'yar gayu ce fa jikin ta 'kamshi mai da'di".
Nayi maganar ina cire lully6in jikina, take na ja ruwa na wanke shi kafin ma ruwan da innani ta dora yayi zafi ni har na gama wanke kayan da suka 6acin na shanya..gefen Innani nazo na zauna..ina fa'din" Ayi mata da wuri Innani tace in koma zamu zo tare...".

Innani dai bata ce komai ba ta tashi ta ha'da ruwa ta wanki yarinyar.
Wanda ya rage bisa wutan ta saka na 'debo ta 'dan sanyatar da shi dai-dai ta bawa yarinyar tasha..ko kukan kirki kuwa batayi ba ana wankan ma tana 'ko'karin yin bacci.

Sai da ta gama bata ruwan kafin ta dube ni tace" Sai dai babu riga kuma da za'a sanya mata".
Kai na dafe da alamun tunani wanda ganin hakan yasa Innani kawar da kallon ta daga gare ni tace" Akwai rigar salisu jikan maigidan nan da jiya suka zo suka yini anan sai suka manta.."

Ban ma bari Innani ta kai 'karshe ba na saki fuska nace" Yauwa Innani a sanya mata dan Allah, idan mahaifiyar ta ta ganta da rigar zata ji da'di..."

Koda aka gama shirya ta nice na sake rungume ta bayan na saka 'daya daga cikin hijaban Innani dayake yawanci hijaban ba wasu manya bane su, so ko wannan 'din ma bai fi wanda ni nake sanyawa ba.

A hanya ne nake 'dan bawa Innani labarin yanda muka yi da matar hadda kyauta da amanar yarinyar da uwar ta bani kamar almara.

Ita dai Innani kallo na kawai take yi amma tasan in ba wani ikon.Allah ba da kyar ne in har yanzu matar nan na raye..maganganun nata duk sun yi mata kama ne da wasiyya.

Ai kuwa muna zuwa muka ci karo da wasu motocin da tun daga nesa muka fara hango su a wurin, su uku na jami'an tsaro guda biyu da na asbiti guda 'daya(Ambulance).

Bamu san takamamman meke faruwa ba, mun dai fito muka ga mutane tsatstsaye amma da nisa basu isa kusa da jami'an tsaron ba.

Bazan iya bambance tsakanin jam'in tsaro da kuma 'yan ta'addan ba saboda kamanceceniya da suke da shi, sai dai daga yanayin tsabtar motoci da kayan dake jikin su na fahimci wa'dannan daban da suke da wa'dancan..hadda wata mota blue wanda nake kyuatata zaton ta ma'aikatan Road Safety ne, balle kuma da maga har mutane na tsaye suna kallon su daga 'dan nisa sai na fahimta dagaske cewa ba makasa bane jami'an gwammati ne...tunda wa'dancan idan an gansu ko jin labarin su guduwa ake yi.

Tsayuwa muma muka yi kamar yadda kowa dake wurin yayi..in ba kasani ba bazaka ta6a fahimtar cewa da mutum a hannuna ba.

Babu wanda yayi gigin zuwa kusa da mu dan duk sun tsatstsaya da bindigu muna rarraba idanu.

Daga inda muke tsaye ina iya hango yadda aka ciro gawar wani drivern da sai a lkcn ma na tuno abinda matar nan ta sanar da ni game nata drivern, babu mamaki shi din me.

Gaba 'daya ya koma bakikirin ashe ma motar 'konewa tayi bayan tafiyar ta.

Rintse idanu mayi sosai, take naji zuciya ta ta bushe gaba 'daya, Innani kanta bata san lokacin da ma bar gefen ta ba dan baki ta sake tana ganin ikon Allah.

Zagawa mayi bayan na 'dan yi tafiya mai 'dan tsayi, ina rungume da jinjirar har yanzu, burina bai wuce na ga na sada ta mahaifiyar ta ba kamar yadda ma yi al'kawari.

Can nesa sosai da jami'an tsoron na ratsa na shiga jejin, haka ta ringa ratsawa har na kusan isa inda na bar Nadia kwance cikin jini da jaririn ta.

Har a lkcn kuwa kwance take sai kamar yadda na barta sai hijabina da aka sake rufe mata jiki da shi.

Hango wani jami'in da nayi tsaye kanta ya sanya ni dakatawa na lafe bayan kananun bishiyu ina sakin ajiyar zuciya.

Sam bana jin wani tsoro ko fargaba cikin zuciya ta, cikin sa'a ma babu wanda ya lura da ni hakan ya sa na sake baro bayan bishiyar na fito fili, haka na ringa lalla6awa cikin dogon ciyayi dake wurin ina sake matsawa kusa da su.

'Buya nayi cikin ciyawan na dur'kusar da kaina ina hango Nadia da har yanzun take kwance yadda na narta babu wata alamun motsi tattare da ita.

Jami'ai biyu ne tsaye kanta ..ban san me ya faru ba kam amma haka kawai sai naji karaya ta ziyarci zuciya ta lkc guda.... hawaye ne na ya gangaro min, dan ko ba'a fa'da ba nasan da 'kyar ne idan matar nan tana numfashi.

Nasan banda 'kaddara babu abinda zai ha'da ni da matan nan, nasan ayadda take din nan ko a hanya ta ganni ba lallai ne idan ko kallon arziki zan iya samu daga gare ta na balle har muyi magana na tsawon lokaci..amma ji inda kaddara ya kawo ta, gata can yashe tamkar marar gata..." _Aisha 'diyar ki ce, na baki ita halak malak, ki kula min da ita ki bata tarbiya kamar yadda aka baki..."_
Kalaman matar da na tuna kenan wanda suke tai min yawo a kwanya ta...sai nayi saurin share hawaye.

Ban gama tunanin ba naji muryar wani dake tahowa ya tambaya " wannan fa?
Inda yayi maganar yana Nadia.

" She is dead".
'daya ya amsa shi yayin da 'dayan ya furta" Oga gawa ce ta riga ta rasu".

Kuka ne naji zai kwace min da karfi kuma lic guda, sai nayi saurin toshe bakina, hawaye na na zuba kan jikin yarinyar dake hannuna

Daga wajen da nake 6oyen ina iya hango duk abinda suke yi amma duhun ciyayin ya hana su su hango ni.

Yarinyar da ke rungume da 'kirji na na sake rungumewa wasu hawaye masu zafi suna gangaro min..." Yah Allah ka bayyana min abinda ya dace na aikata.."

Abinda na furta kenan ina kallon sama sai na sake sau'ke idanu na akan jami'an tsaron ganin an taho da wani abu kamar gado wani daga cikin su na shirin 'dauke gawan Nadia da 'dayan jinjirin ta.

Sosai ta rungume ta 'kirjina ina jin 'kaunar ta na tsarga min a zuciya.

Fuskar ta na duba cikin zuciya ta na furta" Hajia ta bani ke, tace ta bani ke halak malak, idan na bayyana musu ke ma 'kwace min ke zasu yi har abada kuma bazan sake ganin ki ba, da waki rayu da wa zako tashu ban sani ba tunda ance ita ta rasu...da muryar kuka nake fa'din..." Bana so in rasa ki, wallahi bana so kiyi nesa da ni daidai da rana guda, bana so in yi butulci bisa amanar ki da na kar6a, na ba Kano bane balle in ce ga mahaifin ki za'a kaiki, kuma bani da tabbacin haduwar ki da shi..." Yah Allah ka bu'de min 'kofar da zata 6ille mana gaba 'daya ni da yarinyar....".
Kuka nake sosai, kukan da ni kaina bazan iya na menene ba, kusan tun haduwa ta da Nadia idanu na basu bushe babu hawaye ba.

Ina nan ina le'ken su har suka gama duk abinda zasu yi suka kwashe gawawwakin suka sanya cikin mota.

Wa'dannan biyun dake tsaye kan gawar Nadia ne kafin a 'dauke ta naga sun tsaya 'yan dube-dube...kamar babyn da ke hannu na ta sani sai ji nayi kawai ta 'dan yi motsi sai kuma ta fara mutsu- mutsu sosai da alamu kuka take da niyyar sakewa, ai kuwa take nayi saurin 'dago ta na sanya mata le6en baki na na 'kasa cikin bakin ta ta fara tsotso.

Bugun tara- tara zuciya ta keyi ina hango su da gefen idanuna ina kuma Addu'ah cikin zuciya ta Allah yasa kar su gano ni.

Daa zararren idanu 'dan 'dan sandan nan ya dubi 'daya da niyyar tambayar sa ko kunnuwan sa sun jiyo masa abinda shi ya jiyo sai dai bai kai ga furta abinda yayi niyya ba wani Inspecta ya basu umarnin barin wajen....kowa yasan jami'in tsaro suna matukar biyayya ga duk manyan su mawuyaci ne kaji sun yi musu ga duk umarnin da aka basu.

Hakan ne ya sasu watsar da batun suka juya duk suka isa inda shugaban nasu ke tsaye.

Da ganin hakan sai na sau'ke ajiyar zuciya mai sanyi...a fili nake sakin murmushin jinda'di.

Sai kuma naji hankali na ya tashi sosai..tambayar kaina nayi ina mai duban fuskar yarinyar" _Shin yanzu sata nayi ko kuma taimako?"_
Chapter 159 · 0% Book details