← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 218

Sashe 69

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi tana lumshe idanu tace " Baby wai yau me ke damun ka ne haka, in na fada maka abincin da nike so zaka kawo min ne kai da kake can wata uwa dunia..?".
Murmushi yayi daga inda 'din da gaskiyar ta kuma fa amma jindadi kawai ya sahi tambayar.
" Babu ruwan ki Babyn Baby ke de fa'da min kika sani ko zan iya tura mk daga zuciya ta...".
Yayi maganar cike da shauki cikin wata kasalalliyar murya.
Sosai maganar tasa ta sata jin dadi.
" Baby..when ar u coming back..?"
" Sai jibi my dear..fa'da min abinda duk kike so 'din zan sa Sultan ya kawo miki yanzun nan..".
Idanu ta lumshe cike da jin dadin furucin sa.
" Bakomai Baby..alele naji nake so kuma zan wa Zaitun magana ta dafa min.."
" Sai kuma me...?"
Ya sake tambaya cike da kulawa.
" Babu..".
Tace
Tuno kafin tafiyar sa abinda tafi son sha yasa yace...
" Berries....?"
Da sauri tace
" Mai tsami...".
Daria Rayyan ya kwashe da shi jin yadda ta responding kamar dama jira take...yace " Na kamo ki..yanzun Sultan zai kawo miki, Zaitun kuma kice tayi mk abun mai da'di fa...ya ma sunan sa...?"
Tace " Alele..."
Yace " Good..ayi bacci lafia my dear.."
Daga haka ya yanke kiran cike da jin dadi, fatan sa Allah ya tabbatar masa da zargin sa gaba 'daya ya 'kagu ya bar wannan garin amma abu ya faskara sun rike shi dayawa.

Kamar yadda ya fa'da kuwa Sultan ya kawo mata sa'kon har a lokacin kuma fuskar sa babu walwalar kirki.bai ma zauna wajen ta ba ya tafi 6angaren Ammi nan ma gaishe ta kawai yayi ya fito tana tambayar abinda ke damun sa yace bakomai gajiya ce kawai.
Ammi tace " Ai dole ".
Addu'ah ta bisa da shi tare da fatan alkhairi.

Ranar ko takan Marwa bai bi ba ya koma gida sai Zaitun ta raka ta daga baya.

Sai da aka 'kara kwanaki biyu kafin Rayyan ya dawo, da dawowar sa kuwa washe gari yasa Amra tayi gwajin fitsari idanun sa suka gane masa abinda ya jima yana muradi dan tabbatar da zargin sa ya sanya shi daukan ta zuwa asbitin su, Fawwaz abokin sa ya sa yayi masa gwajin da kansa aka.kuma tabbatar.

Rayyan ji yayi tamkar zai maida Amra cikin sa sbd farin ciki.
Cikin sati guda da bayyanar cikin hatta Raihana da bata kusa sai da ta samu labarin cikin nan..kowa yayi murna musamman ma Marwa da itace gwanar 'kiraye kiraye da labartawa.
Duk yadda bata shiri da Amra sanadin cikin nan sai da suka fara magana sama sama, Anty Madeena da Ammi kam har 'kwalla sai da suka zubda sbd farin ciki.

Tako ina kaffa kaffa ake da Amra, ita kanta Amran mamaki take, bata ta6a zaton 'kaunar su da samun jika har ya kai haka ba sai yanzun, ji tayi ai da tasan hkn da duk shekara tayi ta hahife musu jikoki, amma da yake masu tawakkali ne basu ta6a nuna damuwar su ba suka barwa mahalicci.

*****
Tun fara aikin Zaitun 6angaren Amrah ta fuskanci wasu abubuwa, dama can ba shiri suke ba, haka itama Zaitun yarinyar batai mata ba sam, yanzu kuwa da suke kusan yini a 6angaren ta sakamakon bayyanar cikin ta da hidimar ta 'karu fin na baya, sai rashin shirin nasu ya fito 'karara tamkar masu ganin hanjin juna, hantara kyara dungurin kan Moopy kusan kullum sai Amra tayi su.

Yayin da Zaitun take jin haushin ta badan komai ba sai dan abubuwan da take yiwa yarinyar ta sosai ta tsane ta, bata ko 'kaunar ganin ta sbd bata son 'yar ta, ko da yaushe idan hakan ya faru sai dai ta bita da mugun kallo ta rungume 'diyar ta dake kuka sosai dan babu yadda zata yi...sbd kowa yanzu Amra ce gaban sa, ita kanta ta taya su farin ciki har zuciyar ta abu guda ne yasa Amran ke bata haushi shine yadda ta tsani Moopy..amma cikin jikin ta har zuciyar ta taji tana 'kaunar sa.

Kamar dai yau ma, Amra kunun tsamiya tace take so, Zaitun ta ha'do mata lafiyyan kunun tsamiya da yaji kayan yaji ta kawo mata.

Ta ha'da tasa sugar da komai ta gauraya tana shirin mikewa amra ta sake fa'din ta 'dauko mata zuma a kitchen na kan dinning ya kare.
Dole Zaitun ta bar Moopy ta tafi 'dauko mata, kafin ta dawo ne yarinyar ta fara bin bayan ta.
Amra wani tsawa ta bugawa yarinyar " Toh makalemata dallah can dawo ki jira ta nan cinyeki zanyi ne..?"
Tsawar ce ta firgita Moopy ta saki kuka harda fa'duwa, duk maganar Amran kan kunnen Zaitun ne, hakan yasa ko da tazo yarinyar ta 'dago tana ajiye mata robar zuman.
" Malama bude min zaki yi ba cewa nayi ki ajiye min ba.."!
Cewar Amra tana sake juya kunun ta a cup.

Kallon ta Zaitun ke yi shi bata kuma yi niyyar bude Zuman ba, kallon sai ya hassala Amra ta mike tsaye tana nunata da yatsa take masifar wai Zaitun ta gama raina ta akan me ne..hadda zata harareta.
Tace " Bafa na son iskanci da rainin hankali, da alamu jin kanki kike dan kinga an taimaka an wayar da ke ko, to wlh ki kiyaye ni in ba haka ba sai nayi sanadin da zaki koma bin kwaroro kina tara yara tunda haka kika fi so..a bu'de min zuma nace ba a tsaya a kaina ba...Moopy da ta tsura mata idanu ta 'karashe da buga mata tsawa bayan ta sauqe idanu akanta..." Daina kallo na ni banza Shegiya dangin 'yan titi...".
" Kar ki kuskura...'yarinya ta ba shegiya bace daraja ce da ita na musamman in baki sani ba ni nasan abu na".
Tsayuwa Amrah ta gyara tana tafa hannuwa tace" Hehehehe...yau naga rasar kunya ta zahiri, wato an fara yiwa shegu lasisi a 'kasanan nan ne ban sani ba har haka...ke ko kunya bakiji kike neman kare wannan abar.."?
ta 'karashe da nuna Moopy.

Zaitun kam bata kula ta ba sai ma gyara rikon da ta yiwa Mufeedah da tayi izuwa gefen ta na hagu.

Bata tankawa Amrah ba illa juyawa da tayi tana 'daukan wani al'kawari cikin ranta...yayin da ta bar Amrah na ta sababi da kunfar baki.

Kafin su bar Parlorn sai ga Rayyan ya fito yana 'daura bottle 'din hannun longslip shirt dake jikin sa.

Gaban Amra ya dawo ya tsaya batare da ya furta komai ba.
Da ganin sa ne sai ta 'dan sassauta ihun da yake tasan baya son hayaniya kuma itama ya hane ta.

Shi kam baki ya kya6e sam ko da wasa bai ta6a yin tunanin dakatar da Amrah daga cin zarafin da take yiwa wannan mai aikin ba, dan shi baya saka kansa abinda bb ruwan sa.
Labari Amra ta 'dan fara bashi bayan sun zauna bisa kujerar tana 'karasa sanya masa botiran da yake da magana a bakin ta sai ta saki ranta tana bashi labarin duk abinda ya faru" To ke ma ina ruwan ki da rayuwar su Amrah plz ki daina shiga sabgar su kinji...".
Ya 'karashe yana 'dan ha'de rai gami da saukaka muryar sa.
" Bazaka gane bane Baby yarinyar ce 'yar rainin hankali wlh".
Bai sake magana ba har ta gama masa ta 'daure masa sannan ya mi'ke yana ayyana yau yaci sa'a kenan an masa babu tura baki.
" Tashi muje ki gaida Ammi...har cikiyar ki take yi fa...ke har yanzu baki jin magana ta ko...?"

" Kai Baby, toh jira in shirya sai muje..".

Ido ya 'dan fitar.." Wani shiri kuma again...".
" Ni dai please Baby..."
Ta fada cike da shagwa6a tana bubbuga 'kafafu.

" Toh kawai same ni acan..".
Ya fa'da yana ficewa daga gidan ya nufi 6angaren Ammi anan yaci karo da ita a hanya ta jingina kanta da bangon da zai shigar da kai parlorn Ammi ga dukkan alamu wani abu ke cin zuciyar ta, kawai da kai yayi tamkar bai ganta ba kawai ya shigewar sa ciki.

Har Amra ta fito Zaitun na nan, abin dunia duk yabi ya isheta bata kuma san ta ina zata 6ullo musu ba.
Amrah cikin takun ta na isa da birgewa take tafiya bayan shigewar sa da ka kamar mintina sha biyar sannan ta fito tana wucewa tana taunar cingam 'kas 'kas musamman da ganin Zaitun tsaye daga waje tasan damuwa ce ta cika ta, tana tafiya tana ha'de hanya 'kamshin ta na mara mata baya.
Sai da tazo dai dai Zaitun ta wani tauna cingam ya bada 'karacsosai da tasan dole hankalin Zaitun zai dauku gareta sannan tace" Waya fa'dawa yarinya ana ja da isashshiya matar Rayyan ne?"

Salmerh😘
[2/10/2022, 11:28 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...43*

.....Ta 'kofan kitchen Zaitun tabi ta wuce 'dakin ta bata kuma san lokacin da suka bar 6angaren ba.
Babu wanda ya san abinda ya faru tsakanin ku hatta da Marwa Zaitun bata bawa labari ba..haka kuma bata fasa zuwa dan yin aiki ba.

Bayan kwana Biyu Ammi ta tafi Abuja Marwa taje Zaria yin clearance na makarantar ta.
Zaitun sam sai taji gidan yayi mata fili sosai sbd bata ganin Marwa yanzu, sanyin ta ma sai ya 'karu, yanzu duk abinda Amra zatai mata bata ko 'daga idanu ta dube ta ma balle mayar da martani.

A hankali Mufeeda ta fara er zazza6i, tun abin bai yi zafi ba har zazza6in ya shiga jikin ta sosai, Zaitun ta rasa yadda zata yi da yarinyar.

'Daya cikin sabbin masu aikin gidan ne ta bata shawarar bata paracetamol amma still jikin sai a hankali.

Zaitun kuka sosai take zaunawa tayi haka duk dare ita kanta sai da tayi 'yar rama.
Ko 6angaren Amra ba zuwa take yi ba yanzu ita kadai tasan damuwar da take ciki.
Gashi har yanzu Ammi bata dawo ba haka Marwa ma...Sultan ma yanzu ba sosai yake shigowa ba.
Chapter 69 · 0% Book details