← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 218

Sashe 132

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Ko da ta fahimci nufin sa akan itama ta ci abincin ne sai taji sam bazata iya ba yau 'din, dan ba hk suka saba ba, ganin bazata cin ba take nufi ya sanya shima yin baya ya jingina da jikin kujera alamar shima kenan bazai ci ba sai ta ci.

Tasan yana jin yunwa sosai tunda da kansa ya zo dinning 'din batare da an gayyato shi ba balle ya 6atawa mutane rai, har ma ya riga ta zuwa kuma gashi da rana bai ci abinci ba, hakan yasa taji hankalin ta ya kasa kwanciya, kallon 'yan da'ki'ku suka yiwa juna sannan ya lumshe idanun sa alamun" ba ruwa na ni..."
Dan ya karanci ro'kon da tayi masa cikin idanun ta hadda ma karya wuya gefe.

Abincin ta tsurawa idanu tana tunanin yadda zata yi da shi, ita har ga Allah ba wani son cin abinci da take a yanzu, a hankali ta kai hannu ta 'deba ta kai bakin ta...idanun sa a lumshe amma hakan bai hana shi 'kare mata kallo ba, yana matu'kar son natsuwa a rayuwar shi, shiyasa sau da dama yake shagala wajen kallon ta batare da yasan yana yi ba, yadda take taunan abincin ma wani salon yake badawa, wani kalan atsuwa ne tattare da yarinyar da ya tabbatar ba kowa ke da irin ta ba...wanda hakan ya kuma kara bada babban gudun muwa wajen ingiza sa ga son kusanta kansa gare ta...bai kuma yaushe ya fara jin hakan game da ita ba.

Zuba mata idanu yy wanda bai masan lokacin da ya bu'de su tarwai akanta ba...ita kam bata kalle shi ba sai da ta tabbatar ta ha'diye abincin sannan ta 'dago suka ha'de idanu.

Murmushin gefen baki yy sannan ya sake 'dagowa ya gyara zaman sa, da idanu yy mata alamar ta bashi shima, cike da natsuwa ta 'debo ta bashi abincin tana lura da yadda yau 'din ma yake ta faman tsare ta da manyan idanuwan sa, sai dai ita ko ka'dan bazata iya jurewa kallon sa ba, hakan yaso yasa ta daburce nan gaban sa but bata bari hakan yy tasiri gare ta ba, kawai ta riga kauda idanun ta daga ha'de idanu da shi, yasan dama bazata yi hakan ba, ko da da take iya 'kure shi da kallo ma yasan sbd yarinyar ta ne kuma takan yi haian ne out of 6acin rai, sbd zargin da take ne na ya cutar mata yarinya, wanda ya tabbatar a lokacin ji take da ita ce sama da shi ko kuma zata samu dama da ba 'karamin bugu zata yi masa ba amma bb damar haka.

'Daya ya kar6a ya kuma no'kewa, dole sai da ta sake ci sannan ya sake kar6a...
tasan shi ma'abocin shan ruwa ne idan yana cin abinci kamar dai ita dan wannan ga6ar kam tarayya suka yi kan 'dabi'a guda.

Cup 'din abin shan da ta 'dazun ta 'dago ta nufi bakin sa da shi amma sai ya rintse idanu gami da 'dan ja baya ka'dan cikin ransa yace" Idan kk shayar da ni wannan kuma ai kin yi dani 'yan mata".

Bu'de idanun sa yy akan ta dan ita ma shi take kallo da mamakin sa, sai dai a fili ta fahimci cewa madarar ce baya ra'ayi...

Hakan yasa ta 'dan kalle shi sai kuma tayi 'kasa da idanun ta zuwa kan lips 'din shi dake motsi.." Exotic zaki bani..".
Yace a hankali kamar wanda bai son yin maganar.

Tsaye ta mi'ke ta je ta 'dauko masa mai sanyi cikin 'dayan cup 'din ta tsiyaya sannan ta koma ta zauna, da kansa taso yasha amma yayi fuska dole ta 'daga ta kai bakin sa, ka'dan ya kur6a ta cire ta sake mayarwa ganin tana son sake cirewa ne ya sanya shi 'dago hannun sa na hagun ya 'daura saman nata wanda hakan ne tilasta mata tsayar da cup in abakin sa idanun sa na kallon nata idanun amma ta ki yadda su hade ido.
Sanyin hannun sa da sanyin jikin cup 'din a hankali yake ratsa mata jiki har 'kwalwalwa..hannun nasa ta ritsa da idanun ta, ita dai wannan gargasar da ke jikin sa ba 'karamin tafiya da imanin ta yake ba...sosai yake birge ta ta yadda bata iya hana zuciyar ta bayyana 'kaunar sa.

Shi kansa ma Rayyan ya riga ya gama 'dago ta tunda jimawa, cuz idan tana shafa masa magani ya kan lura da ita yanda take wasa da gashin hannun san wani bin har shagala take batare da ankare ba, balle wancan hannun da ba amfani yake da shi ba 'din shi nashi wani luf yy ya kwanta gwanin birgewa...Wani bin addu'an da take yi masa ma da biyu ne, idan ta na son ganin hannun san ne take zuwa ta janye rigar ta fara tofa masa addu'ah tana shafawa a hankali batare da ta yadda ta kalli fuskar sa ba, shikam har lumshe idanu yake yi domin ba'kon yanayi ke ziyartar sa.

Sai da yasha rabin cup 'din kafin ya 'daga hannun ta gami da janye kansa baya, ita kam a lokacin gaba 'daya ta shagala cikin wani yanayi, 'karamin murmushi yy cikin zuciyar sa cike da jin da'din rikita mata tunani da yayi.

A haka suka ci abincin wanda dole tasa Zaitun shanye hollandian da ta zuba masa tunda yau 'din ba ita ya shaba ya canza she'ka...

Sai dai kuma bata san dalili ba tun tana tattare dinning 'din ta fara sakin 'kananun hamma, tana zuwa kitchen idanun ta na lumshewa.

Rayyan kuwa tuni ya koma cikin parlourn yana binta da kallo a afakaice har ta gama tattare dinning 'din, zuwa lokacin gaba 'daya jikin ta ya saki bacci sosai ke damun ta har yana 'ko'karin cin 'karfin ta.

Da gefen ido ya kalle ta dai- dai lokacin da tazo zata gifta shi a hankali kamar bai son magana ya ce" Ki canza min bedsheet bacci nake ji sosai..."
Yayi maganar ne yana lumshe idanu wanda tun safe wannan shine maganar sauti da ta ji ya furta mata na biyu, dan ko gaisuwar ta ma da idanun sa yake amsa ta.

Jin yadda yy maganar ya sanya ta zubo masa lumsassun idanun ta masu cike da yanayi na bacci amma haka dole ta juya ta koma 'dakin nasa dan cika umarnin sa.

Sai dai me tun a awajen cire pillow case baccin ya ci 'karfin idanun ta bata san ma lokacin da ta sulale ta fara baccin ba da yake zaune bakin gadon take tana cire pillow cases dan canzawa sai ya ta koma ta jinginu da jikin gadon pillown na kan cinyar ta har ta cire rigar pillow 'daya saura 'daya baccin yy gaba da ita.

Bayan shigan ta da kusan mintina arba'in sannan ya shigo a lokacin ya tabbatar baccin ta yy nisa dan tun shigar ta bai sake jin motsin ta ba bai kuma ga ta fito ta wuce ba.

*****
Abu ne da bai ta6a tunanin zai faru gare shi ba ko cikin mafarkin sa, bai ta6a kawo akwai ranar da shi zai iya aikata irin hakan ba, sai dai 'kaddara, ya riga ya san komai.na.faruwa ne bisa yadda Allah 'kaddara wa bawan sa komai na rayuwar sa, sannan babban 'kwarin gwiwar sa ya samu ne daga sanin da yayi cewar ita 'din halaliyar sa ne a halin yanzu, mallakin sa take.

Yasan bai kyauta ba sam, bai mata adalci ba kamar yadda yasan bai yiwa kansa ba, amma hakan aganin sa shine ka'dai mafita domin bazai iya cigaba da jure yanayin da yake jin kansa ba kamar yadda bazai iya fitowa fili ya bayyana mata bu'katar sa gareta ba.

Sai dai ya kasa tantancewa shin hakan dai- dai ne ko kuwa kuskure ne gagarumi, duk wata natsuwar da yake so ya same ta amma can can 'kasan zuciyar sa yana jin babu da'di...gaba ya sata ya ma rasa me ya kamata ya aikata mata, wani taimakon ya kamata ya bata, shin taya zai sanar da ita akan ta tsarkake jikin ta batare da ta zarge shi ba.

Rashin mafita yasa shi yanke shawarar ya maida ta 'dakin ta kawai.

Hakan kuwa akayi, amma kafin ya maida tan sai da yayi mata allurar pain relif da yasan zai taimaka mata sosai wajen rage zafin jikin ta ko kuma ciwo.
Yadda yasan tayi shigar ta ya maida mata sannan da hannun sa mai lafiyar da ya dauke ta ya maida ta 'dakin ta ya kwantar da ita hadda rufa mata abin rufa.

Idanun sa ne suka sau'ka akan Mufeeda dake bacci tayi 'da'd'daya, gyara mata kwanciyar yayi yana mai zama bakin gadon ya sasu agaban sa, a hankali yake shafa kan Mufee yana jin wata 'kauna da soyayyar 'diyar tashi na taso masa sabuwa fil.

Rigar ta ya 'dage yana sake duban wannan ba'kin abun da Anty Madeena ta nuna masa a jikin ta.

Tabbas irin nashi ne sak, peck ya sauke mata a saman goshin ta sannan ya rufe ta itama yana tunanin yadda ya samu Zaitoon a 'danyar ta ya same ta, babu alamun ma tasan wani namijin balle har ta kai ta ga haihuwa.

Sannan dukkan alamu sun gama bayyana masa cewar babu hadin jini tsakanin ta da Mufeeda dagaske, kauna ce kawai take wa yarinyar, kauna daga indallah.

Koda ya koma 'dakin sa kasa bacci yayi, ya kuma rasa menene ya hana shi baccin, abu guda ka'dai dake masa kaikawo shine rashin sanin asali da farkon alakar Zaitoon da Mufeeda...he really want to know everything....

Bai ta6a 'dokantuwa da son jin dangantakar ta su sama da yau ba, bai ta6a jin 'kaguwa da son jin wani abu game da su sama da wannan ranar ba.

Ba shine bacci ya 'dauke shi ba har sai tsakiyar dare, ko da safe kuwa da ya fito bai ji alamun motsin kowa ba, yasan babu mamaki basu tashi bane, ya kuma riga yasan koma menene shine silar komai.
Chapter 132 · 0% Book details