← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 218

Sashe 31

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......" Ba'kin talauci, fatara, damuwa da matsalolin rayuwa ne suka da'kushe komai da ya dangance ta suka kuma 6oye duk wani sirrin kyawun da Allah ya bata, dan bana jin ko ita kanta tasan ta mallaki wannan sirrin, amma wlh da zarar duk wa'dannan sun kau abu ne mawuyaci Dr Rasheed ya sake yimin duba irin na 'ya mace cikakkiya da daraja matukar yana ganin yarinyar nan gaban idanun sa kuma yasa ta a zuciya...tsoro nk ji kar abin yazo yafi karfi na watarana Anty...".
Bayanin Hameeda kenan da ke zaune kan 'daya daga cikin kujera mai zaman mutun 'daya dake madaidaicin Parlon da ya kasance maha'di ga bedroom din ta, kuma tayi duk wannan bayanin ne ga 'yar uwar ta Anty Saleeha wacce ta cika alkawarin kiran da tace zatai wa Hameedan washegari bayan ta samu isasshen lkcn da zata iya ganawa da ita.
" Ki kwantar da hnkalin ki nace, amma tuntuni kin kasa yin hakan kan wani abu da bai taka kara ya karya ba ki ke ragewa kanki daraja da baiwar da Allah ya baki, abu mai tsananin saukin da ke da kanki ma zaki iya samawa kanki mafita idan kin nutsu kk bi a hankali.."
" Kar kice haka wlh Anty Saleeha dan baki ga yarinyar bane kk ganin kamar abin ba na kirki ba, ki dai na ganin abin kamar me sauki, ni nasan halin da zuciya ta take ciki a yanzu, wani baiwar kyau Allah yy mata da duba 'daya zakai mata ba sai ka 'kara ba za ka fahimta matukar kana da kula, taya zan iya zama da ita cikin gida na Anty na kuma kasance cikin natsuwa da kwanciyar hnakalin da kk fada alhali nasan shi kansa Rasheed 'din abinda nk gani game da yarinyar shima hkn ya fahimta ne yasa shi ajiyan ta zuwa wani lkc, abin takaicin ma fa har yarinya gare ta Anty, kuma na tabbata garin biye- biyen tituna da kwararo ta samo cikin har ta haife, sai ma kin ga yarinyar...wlh duk lkcn da na tuno da su bama na gansu ba sai gaba na ya fadi bazan iya jure yawan ganin suna wulgawa gaba na ba wlh, ina kishin miji na sosai....".
"...Shin ke Hameeda kyanta ne ka'dai ya dame ki..?, baki tunanin makomar ki bayan abubuwan da ake gudu sun gudana, bakin tunanin cushewar al'amura da canzawar su? baki tunanin me ze biyo baya? da bakin ki fa kk ce har yarinya gareta bakya tunanin cewa ta fiki sanin dunia da budewar ido? ba mmk lamfo kawai take mk amma da zarar ta saita komai zaki yi mmk, irin su bada wasa ake bin su ba, domin su 'din tamkar maciji suke, dole sai an musu tashin wuf lokaci guda, cire batun kyawun ta a lissafin ki, kiyi tunanin makomar ki da ta yaran ki anan gaba...a lokacin nasan zaki fi fahimtar duk wasu bayanan da zan mk..."
Da gama fa'din hakan ta fara kokarin datse kiran, fahimtar hakan da Hameeda tayi ne yasa ta zabura ta dakatar da ita da sauri " wlh Anty yanzu ma a shirye nk zan fahimce ki, me zan tsaya jira da har sai nayi tunani?.."
" Naga kamar inda tunanin ki ya tafi daban da inda nawa yk...".
Cewar Anty Saleehan cike da gatsali..cikin ranta kuwa ayyana irin tagomashin Nairori da zata samu take matukar Hameeda ta amince da batun ta.
"...Na dawo daidai nima yanzu, fada min koma menene..."
Cewar Hameeda tana gyara zama cikin 'kaguwa da son jin mafita me 6illewa daga yayar tata.
Murmushi Saleeha tayi sannan ta 'dora da fa'din " Nan kusa da ni ne ba nisa da gidan nan, kisan yadda zaki yi kawai ki taho da ita gida na, chamber ce da ake tara irin su ake mi'ka su aikatau ko wani abin daban ga masu bukata amma za'a yi komai ne bisa tsari da kuma sirrantawa kar ta fahimta kar kowa ma ya fahimta sbd rufin asirin ki, da zarar ta shiga hannun su an dam'kata gare su shikenan bata kuma da wata mafita, dan suna da tsaro sosai, chamber ce da wani attajiri ke jagoranta kuma be 'dauki abin da wasa ba...da zaran ta shiga hannun su shikenan tunanin ta zai canza sai yadda suka yi da ita, sai abinda suka ce da ita zata yi, wannan shine ka'dai mafita agareki in kinga zaki iya amma..."
Sosai Hameeda tayi na'am da zancen sbd a ganin ta yama fiye mata sau'ki akan shawarar da zuciyar ta ta fara yanke mata na yiwa Zaitun korar kare a gidan, sbd in korar tata tayi gateman zai iya fallasa ta ga maigidan, kuma bata da ikon aiken sa ko'ina domin Rasheed bai yadda ya matsa ko nan da can ba daga jikin gate din, da yake ma ba sallah zai yi ba dan ba musulmi bane..baya ga haka ma in korar tata tayi ba mamaki ta sake komawa can asbitin wajen sa ya kara dawo da ita aikin banza kenan tayi, amma in tabi shawarar Anty Saleeha zata kashe maciji ne tare da sare kansa duk lkc guda dan haka sosai shawarar tayi mata.

Tun daga lkcn kaso mafi rinjaye daga cikin damuwar ta ya kau, tana jin cewa matsalar ta tazo karshe ne baki 'daya.
Sai ma taga waitar ta da har tayi zancen da kawar ta Nabeela tuno yadda tattaunawar ta su ta kasance, sunyi sec. schl ne tare da ita acan Kano dan itama daga can aiki ya dawo da mahaifin su nan, kuma shine abinda ya raba su da kawar tata sai dai sukan yi waya lkc zuwa lkc, duk da yk ita kawar tata Allah bai mata mijin aure ba har yanzun amma ya bata tarin nagarta, ilimi da sanin ya kamata bata da banzan hali da kai tsaye zaka nuna game da ita.
"...Dan Allah Hameeda ki kwantar da hankalin ki, me yasa wata can zata dame ki? kin manta mijin ki ne shi? Ke ce fa kk da damar sarrafa tunanin sa duk ta yadda kika ga dama matukar zaki bi komai a sannu, ki daina bari damuwar da bata kai a 'kira ta damuwa ba tana hana ki sukuni da yin abinda ya dace, yanda kk ganin tana kyau ba mmk ma kin fita kowa nada nashi kyawun ai a yadda Allah ya halicce shi, kuma nasan ba za'a rasa abubuwa da yawa ba da kk fita da su a fili da 6oye kyawun ta da ya mk karan tsaye shine zai hana ki fahimtar hkn, ki nutsu ki daina damuwa da batun kyawun yarinyar zai iya yiyuwa hassada ta kamu da zuciyar ki batare da kin fargaba karshe har kizo ki kasa aiwatar da abinda ya dace...ki nutsu kiyi ta addu'a kibi komai a sannu Insha Allahu bb abinda zai faru sai Alkhairi, kamar yadda ya kawo ta hk zai kara dauke mk ita gaban idanun ki ki huta ganin ta har abada dan Allah ki daina damuwa kinji...."
Kwata-kwata shawarar kawarta ta bai mata ba, abu guda ma da ta fi ri'kewa a ciki shine kalmar hassada da ta anbata..ta nisa ta zurfafa tunani amma ita bata ga abinda za'a ce take wa hassada game da Zaitunan ba, hakan ne yasa ta kasa tankawa kawarta ta ko da ta gama bayanin ma..." Nagode Nabeela..".
Shine kadai abinda ta iya furtawa, tasan cewa Nabeela bata san zafin kishi bane shiyasa, ko kuma dan bata da aure shiyasa bata san yadda ake ji game da faruwar irin hakan ba.

Sai ma taga wautar ta da tun farko ta nemi shawarar Nabeelan...karshe da zazzafar kalma kwara daya ta bar zuciyar ta abin kokawa.

Ta yi alkawarin bazata sake tunkaran Nabeelan da duk wata shawara tata ko neman mafita ba, tunda ba fahimtar ta kwakwalwar Nabeelan take ba.

Duk da 'dimbin farin cikin cikin da zuciyar ta cika da shi, hakan bai sa ko alama ta nunawa Rasheed ba, hk ta cigaba da 6oye farin cikin ta dan kar ya zargi wani abu har zuwa lokacin da zai dawo gidan bai tarar da Zaitun ba, dan sarai ta sanshi, ba 'karamin jaa kwakwalwar sa take ba, cikin sauki zai iya gane shirin ta.

Washe garin ranar kafin ya wuce wajen aiki da kansa ya dubo su Zaitun 'din cikin 'daki dan tabbatar da lafiyar su, karshe sai gashi ya fito da Mufee a hannun sa yanai mata wasa, Hameeda bakin ciki duk yabi ya baibaye ta kawai ta kawar da kai gefe, bata so abin nasu ya ringa girmama fiye da na baya.

Haka Wildan da Naina suka baibaye Rasheed ganin sa da yarinya kowa na fa'din ra'ayin sa, Wildan ne yace laa Abbah tazo wajen ka..?
ranar da ka aike ni wajen maman ta kin zuwa waje na tayi dana ce zan dauke ta ta makalewa maman ta, itama maman nata ta hanani ta6a ta...".
Gajeruwar murmushi Rasheed yy bai kuma yi mmk ba dan ya san hatta shi da tana da iko bazata barshi ya ta6a yarinyar ba talkmore of ya dauke ta gaban idanun ta ya fito da ita, wani dalili ya sa take barin sa take kuma shakkan hanasa ta6a yarinyar da tankasa akan komai.
" Bata sanka bane shiyasa, amma idan ta saba da kanta ma zata zo wajen ka.."
Rasheed ya fa'da wa Wildan yana shafa kansa cike da kulawa yana 'yar dariya.
Naina kam hannun Mufee ta kamo cikin hannun ta tana makale jikin Rasheed din tana wasu surutai da bakowa ke gane mata ba kasantuwar nauyin harshe da take da shi.

Wildan ne yana tura baki yace" Toh Abba yaushe zamu saba? "
" A hankali ka ringa ka na mata wasa wataran ko ka dauke ta bazata ki ba har ka kawo ta wajen Naina kuyi wasa..".
" Abba ai in na ce zanje wajen su Mummy ke hana ni shiyasa bata sanni ba har yanzu...".
A fakaice ya harari Hameedar tai kamar bata ji tattaunawar ta su sai ma ta kara 'dimewa cikin ranta take ayyana cin uwa da zata yiwa Wildan din in Rasheed ya fita.
Chapter 31 · 0% Book details