← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 218

Sashe 153

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda naso katange kaina da kunnuwa na daga sauraren masifar da Iyami ke sauke min abin ya faskara.

Da 'kyar na bawa kaina 'kwarin gwiwar da har na iya sakko da kafafu na na zauna da 'kyar ina me sakin wahalallen numfashi.

Na 6ata kimanin mintina uku kafin na iya mi'kewa tsaye saboda yanda nake jin 'kirji na, banda jiri da nake ji na shirin 'diba na.

Gyara zaman hijabin da ke kaina nayi idanu na kokarin lumshewa..bango na dafe na fara takawa a hankali, amma bazan iya mi'kewa tsaye tsaf kamar yadda na saba ba.

Sam bana so, bana so bana 'kaunar wannan dambun da Iyami ta nacewa yin sa kullum, watan azumi fa muke amma dan mugunta irin ta Iyami sai dai ta dafawa mutane dambu shi kuma Abbah ba zai ce komai ba.

Hamma na ne ma idan ya sani zai yi magana amma shima gidan sa yake bu'de baki sai dai ya aiko mana 'dan abinda ya sauwa'ka wanda ni kam ma ban ta6a gani da idanu na ba sai dai in ji 'kamshi ko kuma Ummaru ya bani labari ko ka'dan kuwa ban ta6a sawa raina damuwa ba, ni Hamma na ya wanke min komai, dalilin sa nake yiwa Iyami uzuri bisa abubuwa da dama ban fiya ganin laifin ta ba.

Shi da kansa yanzu ya hana ni wanke-wanke yace sai dai Khausar ta ringa yi ai itama ba yarinya bace tunda shekarun ta goma sha biyu yanzu..dole badan sun so ba Khausar 'din ke yi amma 6angaren Iyami da Khausar 'din kuwa tsanata ne ya 'kara ninkuwa musu a zuciya.

A hakan ma ba bari nake kullum tana yi ba na kan kar6a in tayata kusan kowacce rana amma maganar kirki bata hada ni da ita.

Haka na tabbata da Hamma na ya san ba'a bani abin da yake aikowa da zai ringa kawo min nawa ne daban, amma ban damu ba, ban kuma ta6a 'daura aniyar sanar da shi ba, na riga nasan komai da lokacin da Allah ke 'debar masa, ko babu aure akwai mutuwa ai, watarana sai labari...dole sai dai wani ne zai tuna da wani, ni kuwa ko da wani lokaci fata na shine a ko'ina a tuna da Alkhairi na ba sharri ba.

Kaina a 'kasa na tako da 'kyar 'kafafuna na har'dewa, wallahi lokuta da dama har fargaban shigowar yanayi na damina nake yi saboda irin wannan lamari.

Ga shi ni a rayuwa ta babu abinda nafi tsana cikin abinci sama da dambu, ban sani ba ko sanin hakan da Iyami ta yi ne ya sanya ta nacewa yin sa kullum ta kuma tilasatwa kowa cinsa domin daga shi bata sake dafa wani abin sai ta ga dama....kowa ma agidan yanzu ya saba hatta Abba cin abin sa yake yi ya sha ruwa hankali kwance.

Ni ka'dai ce wacce ciki na ya kasa sabawa da shi, ban kuma san ta yadda zan 6ullowa Iyami ta fahimce ni ba, ban kasance ma'abociyar cin abincin gidan mutane ba duk kuwa da irin shige-shige da muke yi ban fiya shan ko da ruwa ba har sai na dawo gida...ba tun yau Iyami ta fahimci bana so ba amma ta kawar da kai ta cigaba da yin abin ta duk lokacin da ta ga dama, kafin watan azumi ya tsaya ma sam bana kulawa idan tayi da rana to bazan ma kalli inda yake ba kawai sai injira abincin dare inci in kuwa da rana tayi sa to haka nake kwana banci abinci ba..yanzu kuwa da ya kasance yanayi na azumi dole ne sai ka ci abinci shiyasa nake tilastawa kaina cin sa duk da kuwa nasan illar da yake wa ciki na.

Kaina a 'kasa na fito ina jina tamkar zan fa'di idanu na na zuvar da hawaye, da ganin fitowa ta Iyami sai taja tsaki....inda ta cigaba da masifa" Shashancin banza da wofi, ina fatan dai kin ji abinda nace kika wani zo kaina kina 'kif'kifta min idanu iwa mage...da shegen munafukin hijabin ki na gadon tsiya kamar sanin Allah kika fi mutane...."

Yaa Bukar da shigowar sa kenan turus yayi yana duba na sannan ya dubi Iyami...a hankali ya 'karaso yana daga tsaye yake tambayar Iyami me ke faruwa kuma da safen nan Iyami?"
Ya 'karashe maganar yana me sau'ke idanun sa akaina, 'kasa na sake yi da kaina daidai lokacin da naji wani suka a 'kirji na amma ko motsin kirki ban yi ba balle in nuna alamun jin hakan da nayi ko kuma yin yunkurin dafe 'kirjin nawa, hawaye na kawai ya gangaro da gudun gaske sanadiyyan rintse idanu da nayi.

Iyami maimaita abinda ta fa'damin tayi na zuwa mata jeji amma bata maimaita zagin da tai min ba, da yake sarai tasan halin Hamma Bukar yanzun sai yace sam bazani ba, hakan yasa ta canza salon sautin ta izuwa ga lafazi mai sanyi ta kuma 'karashe maganar tana mai kawar da kanta.

Da jin abinda ta fa'di kuwa take ya ha'de fuska sosai yana duban ta yace" Haba Iyami..."
" Sannu Uba na...".
Ta furta a fusace ranta a matukar 6ace...batare ma da ta bari ya kai karshe ba, domin ta riga tasan karashen zancen indai Hamma Bukar akan Zaituna ne.

Saurin rage sautin muryar sa yayi yace
" Kiyi ha'kuri Iyami, ba haka nake nufi ba, amma ki tausaya mata mana, da bakin ki fa 'dazu kike ce min ko sahur bata tashi tayi yau 'din ba kuma kinsan ba haka nan kawai a banza taki tashin ba sai dan rashin jin da'di da take yi, yanzun ma ita na shigo dubawa kafin in wuce, kuma fisabilillahi ahakan zaki sake tura ta jeji Iyami?..ki duba lamarin dai...".
" Ke kinsan Zaituna bata da son jiki, yau ka'dai ayi mata uzuri mana dan Allah Iyami..."
" Yo ai gani nayi jinyar ba kwantar da ita tayi ba kawai fa tsirfa ce da shegen langwami da ke damunta..".
" Ko ma dai menene Iyami zuwa jejin nan kiyi ha'kuri da shi, ki barshi zuwa gobe idan ta samu sauki ba sai taje miki ba, amma yau kam gaskiya babu inda zata je, yarinyar nan idan tana da lafiya bata yi miki musu kullum na yau ka'dai kam ba zai zama abin damuwa ba...dan Allah Iyami kiyi mata uzuri ki barta na yau ka'dai...".

Yana gama fa'din hakan bai ma jira amsar ta ba ya dawo da kallon sa gare ni yace" Ki koma 'daki ki kwanta idan na fita zan aiko miki da magani sai kisha kinji.. ba dai cikin ki ke ciwo ba?"
Ya tambaye ni cike da kulawa.
Kaina na 'dage masa batare da na kalli ko da 'daya daga cikin su ba.

Daga haka ya sa kai yayi waje Iyami ta raka shi da doguwar harara, ni kam raina fes dan nasan ba zuwan kuma zanyi ba tunda ya hana nasan ya hanu...tsaki ta saki bayan ya 'karasa ficewa sannan ta dawo gare ni ta bankamin wata uwar hararar da ya sanya ni jin 'kafafuna na rawar mazari. .'kasa na sake yi da kaina sosai wannan karan hawaye na bai sakko ba jin bazan je jejin ba.

" Dama me ke damun ki?"
Ta tambaya a matu'kar hassale, dan ji take tamkar ta make ni.

" Ciki na ne ke ciwo Iyami".
Na bata amsa da sanyin murya ta batare da na kalli inda take ba.
Sake hassala tayi ta hayyako kaina wanda ya sani takure kaina waje guda yayin da ta cigaba da fa'din.
" Shegiya munafuka, in ma mene ke damun ki ke kika sani, mutum kullum 'kun'kunsun cikin hijabi kamar wata mutuniyar arzi'ki, saura kuma goben ma ki tsirfo min wata 'karyar kiga maganin ki da zanyi, dambun da kika raina kike yangar ci 'din wataran fin 'karfin ki zai yi matukar ina numfashi, ba dai Babagana kike 'kwa'kwa ba.. muna nan ai...".
Ta 'karashe da yin 'kwafa gami da juyawa tayi gaba.

" Ki yi ha'kuri Iyami...".
Na furta cike da sanyin jiki da marairaita dan har ga Allah banji dadin furucin ta ba, kuma kalmar ha'kuri da na furta ya taso min ne tun daga can 'kasan zucia ta.

Sai dai ban san takamamman dalilin da ya sani furta shi gare ta ba.

Ban kai ga rufe baki bama Iyami tayi saurin waigowa a hassale ta tare ni da fa'din" Uwar ki zanyi munafuka...bazan yi ha'kurin ba 'yar iska kawai...annamimiya".

Ni dai ban damu ba na juya na koma cikin 'daki na ina mai jin farin ciki da hana fita ta da Hamma yayi, dan nasan ko da ma na fita yau 'din da 'kyar ne in iya yi mata abinda ranta ke so dan sosai nake jin babu da'di a jiki na

Ba dan ba zai yiwu ace kayi azumi baka ci abinci ba ai da banga abinda zai sani cin wannan abin ba, sai ma naga na yau 'din yafi wahal da ni fiye da kullum kasantuwar rashin be ta6a yi min irin hakan ba, kuma fa har a lokacin banji mur'dawar ciki ba balle inyi gudawa, 'kirji na kawai naji ya tokare ni sai ciki na da ya kumbura sosai gashi idan zan yi tafiya jiri ke 'diba na.

Lumshe idanu na nayi bayan nazo na mi'ke a 'kasan 'dakin nawa sanyin simintin na ratsa ni, tuno cewa jiya dambun Iyami ya samu kuskure da nayi shine ya sani bu'de idanu na, sam jiya dambun Iyami bai tiraru da kyau ba, sanadin ruwan sama da ya sakko da maraicen jiyan bayan har ta hura wuta, sosai kuwa aka shirga ruwa haka da 'kyar a daddafe ta kammala.

Ina da ya'kinin rashin dahuwar dambun ne ya haddasa min wannan ciwon da ya kasance min na daban kuma zazzafa.

Ummaru Hamma ya aiko da maganin ya kawo min amma sai naji sam bazan iya karya azumi na sbd wannan ciwon ba, hakan yasa na ajiye sai ansha ruwa sai na sha.

Ranar a 'daki na yini bana fitowa sai in alwala zanyi, karo na farko kenan a rayuwa ta da Dije tazo min da labarin anyi haihuwa a makwabtan su amma ban samu damar zuwa ba nace da ita bana jin da'di bazan iya doguwar tafiya ba.
Chapter 153 · 0% Book details