← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 182 OF 218

Sashe 182

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

" Barka da hutawa Ammi..."
Yace yana 'dan rankwafawa.
" Barka dai" tace tana mai mayar da hankalin ta gare shi.
" Ya akayi...?"
Tace tana duban sa.
" Ko a kawo maka abinci.
" A a Ammi".
Ya bata amsa yana zama gefe ka'dan da ita.
" Kamar ranka a 6ace?"
Kai ya girgiza mata.
Ta sake fa'din " Ko batun Marwan ne?"
Sai ya yi shiru yana duban ta...Ammi kam cigaba da shan fruits 'din tayi tana fadin" Ai ta yi shiru, tana 'dakin ta, kasan dole ne abin sai ya dame ta tunda bata ta6a zaton faruwar hkn ba, abin yy mata bazata ne...kuma yarinya ce sai an bi ta a hankali....sai dai ko ni batun takaddar sakin da kayi saurin amsar matan banji da'din sa ba, sai naga kamar anyi gaggawa da yawa, da an bari zuwa wani lkcn daban..."
" Me kuma za'a sake jira ne Ammi? bb fa'idar hkn sam, tunda na gano wanene Sultan bani da wani burin da ya wuce in ga na raba shi da duk ahali na sbd ba'kar zuciyar dake tare da shi, ban san wa yake hari bayan ni ba, ina tsoron ta'sar da zata bayyana bazata a lkcn da bani da ikon dakatar da komai...itama Marwa abata hkr dama shi aure rai gare shi, toh wannan dai kam ya mutu..kuma har abada bana fata, kamar yadda ko da bayan raina ban amince a sake tayar da wannan auren ba...".

" Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi ya raba mu da mugun ji da mugun gani...".
" Ameen Ammi" Yace ata'kaice sai kuma ya mayar da duban sa kan ledar dake gaban sa.

Zama ya gyara yana mai ciro wayar sa yake tambayar Ammi ina yarinyar nan tayi ne?"
" Wace kenan".
" Zaitoon"!
Ya bata amsa batare da ya dubi Ammin ba.
'Dan jim tayi tana kallon da son karantar manufa da yanayin sa.

Kaf kuma abinda take so 'din ta karanta tsaf.
Kawar da idanu tayi daga kansa sannan tace" Me kuma ya sake faruwa ba yanzun suka shigo daga wajen ka ba...?"
" Kayan su zan basu...".
" Ohh..toh barshi anan zan sa a mi'ka musu...".

Jin amsar Ammi ya sa shi 'dagowa ya dube ta...." Ammi wai shikenan ni bani da iko da ganin iyalai na a gidan nan, sai kace baki san waye ni ba...kuma fa hakan da kk yi yasa yarinyar nan duk tabi ta gama raina ni wlh Ammi...".
Ya 'karashe maganar da rage sautin muryar sa...bai san ma ya akayi ya furta hkn ga Ammin nasa.
Kalamai biyu zuwa uku cikin maganar tasa ne yasa shi jin wani iri.

Ita kanta Ammi lafazin nasa ya bata mamaki.
Da wannan yanayin kuma ta dube shi..dai dai yana kawar da kansa cike basarwa as in baiji dadin abinda Ammin tayi masa ba...sai dai can kasan ransa nauyin mahaifiyar tasa yaji sosai.
Wani matashin numfashi ta fidda tana mai kawar da idanun ta daga kallon mamakin da tayi masa.

" Yi hakuri toh sarkin san girma..kuma daga yau kar ka sake 'daukan min yara zuwa wani wuri batare da sani na ba...".
Mai aikin ta 'daya ta 'kwalawa 'kira ko da tazo bowl 'din dake hannun ta ta mi'ka mata tana fa'din kira min " Zaitoon dan Allah...".
Da fitan mai aikin Ammi ta cigaba.
" In batun raini ne kuma ai koma me tayi maka kaine da kanka kaja...sai ka koma ta tuhumi kanka bani ba Rayyan...".

Juyowa yy ya dubi Ammin cike da mamakin kalaman ta...taya kenan za'a ce shi yaja...ta wacce hanya, me yk yi me ya aikata?
Ya kasa bawa kansa amsa.
Gashi Ammi bata sake furta komai ba ba ma alamun zata furta 'din.

Ba ada'de ba sai gata ta fito.
Mufeeda tafe abayan ta hannun ta ri'ke da teddyn wasanta baby pink mai kyau da shi.

Kusa da Ammi taje ta zauna daga 'kasa tana mai sake yi mata barka da hutawa.. ta sannan ta 'dora da fa'din bani ke 'kiran ki ba Zaitoon..dahauta nuna shi batare da ta dubi inda yake ba tace" Rayyan ne".

Tamkar ba ma ya 'dakin haka yayi, kacokam 'din hankalin sa duk ya tattara wajen Mufee dake tahowa a hankali tana ha'de rai.
Ita kanta Ammi hankalin ta naga yarinyar ne.

Zaitoon kuwa kallon sa tayi sai ta kawar da kai kamar yadda taga yayi.
Cikin ranta take mitar tamkar ba yanzun muka baro 6angaren sa ba inba fitina ba miye kuma yanzu...in 'diyar sa yake so ba sai yace akawo masa ita ba..ita kam menene nata kuma.
" Ina yini yaya..."
Tace da sanyin sauti duk da ba wai har cikin ranta taso gaishe shin ba amma rashin amsawar sa sai ya ba'kanta ranta sosai.
Fuska ta yamutse tayi 'kasa da idanun ta tana wasa da en yatsun ta.

Duk Ammi na lura da su amma bata tanka ba.
Shi kam bai ma san tayi ba balle yasan 'karin laifin da ya aikata.
Tana gama rufe baki kuma Ammi ta 'dora da fa'din." Hala wani abin kika yiwa Indolan nan naga tana ha'de rai.."

Abinda ya hana jin haushin nata tasiri kenan itama ta dubi Mufeedan.

Bata bawa Ammi amsa ba da yake ta riga tasan damuwar yarinyar...kawae sai tayi murmushi.

Sai ya zama na baki 'dayan su dukkan hnkln su na gareta ne amma ita kuma duk bata su take ba hnkln ta na wajen Zaitoon kuma duk 'kira da maganar da Ammi ke mata bata ko nuna alamun taji ba balle tayi yun'kurin zuwa inda take.

Jikin Zaitoon taje ta fa'da Zaitoon ta rungume abarta tana bubbuga bayan ta a hnkl alamar rarrashi.

'Yar daria Ammi tayi tana fa'din miskilar yarinya kawai..hala baki kaitaxwajen Antyn ta bane shiyasa.."
Tsaye Rayyan ya mi'ke yana fa'din " Ammi zan shiga cikin gari sai na dawo".
" A a zauna tukun ai bamu gama magana ba".
Jin hkn yasa ya koma ya zauna 'din kamar yadda ta bu'kata.
A zahiri ba hkn yaso ba, yaso ne ya kaucewa wani yanayi da yaji zuciyar sa na shirin bijiro masa da shi lokaci guda.

Sam baya so ya biyewa zuciyar sa, hkn yasa yy tsam da ransa.
Da kyar ya samu bugun numfashin sa ya daidaita duk dama yy sa'a bai 'dauki wani dogon lokaci ba... duban Zaitoon yayi yace" Ke kuma kayan da kk san na wanene bisa wani dalili zakictaho ki baro min su a can...?"

Ledan ta kalla sannan ta 'dan cuna baki tana mai kawar da kan Mufeeda daga 6angaren ledan, domin tasan abinda takewa fushi akai 'din na cikin ledar...kuma dagangan ta baro shi.

" Ai naga kayan za'ki ne duk, kuma ni ba so nk tana shan za'ki sosai ba shiyasa...".

Wani ba'kin takaici ne ya taso masa bai san ma lkcn da ya banko mata wata uwar harara ba yana shirin magana Ammi tayi saurin 'daga masa hannu sannan ta dubi Zaitoon tace" Tashi 'dauki kayan kuje Zaitoon bana son gardama, ki duba ki za6i wanda yake 'dan dai dai sai ki bata...".

Kamar yadda Ammin tace tayi suka fita itada da Mufee duk kuwa yadda Ammi taso yarinyar taje wajen ta ta 'kiya...hkn ma sai ya 'kara ba'kanta ran Rayyan..gani yake kamar koya mata kiyuya Zaitoon ke yi da gayya.
Chapter 182 · 0% Book details