← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 218

Sashe 86

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayyan idanu kawai ya lumshe gami da jingina kansa da jikin kujera, 'kauna da begen 'yan uwan sa na 'kara shigan sa ta kowani kafa na gashin jikin sa suna yi ha'de masa a zuciya..babu wanda ya sake magana a cikin su illah aikin zuciya da 'kwa'kwalwa sai 'karar fan dake aiki...asali ya tsani aikin force shi a rayuwar sa amma baya jin zai iya ture wannan muradi na Sultan kwata- kwata.

Sultan kam zuciyar sa sai bugawa take da tsoron kar Rayyan 'din ya'ki amincewa, sbd yasan halin sa da kafiya, dalili kenan ma da ya sanya shi shigar da batun a wannan ga6ar da yasan mawuyaci ne ya'ki amincewa.

Tun zaman a wancan gidan tunanin mafita da dacewar lokacin yake tunani sai gashi cikin sauki Allah ya bashi dama, ba burin sa yayi aikin soja dan kare ahalin gidan ko dan fansa ga Abbah ba, burin sa na ganin ya shiga aikin soja manufa ce tashi ta kashin kansa ta yadda zai kawar da duk zargin da zai iya biyowa ta kansa ne.

Tsawon mintina takwas suna a haka, Sultan yafi Rayyan shiga 'dimuwa dan yasan kalma guda ta Rayyan na iya ruguza duk shirin sane gaba 'daya, tsoron abinda zai fito bakin sa yake yi...a hankali Rayyan ya saki ajiyar numfashi.
Idanun sa ya bu'de ya sau'ke su kan fuskar Sultan da ya tsura masa idanu yana jiran amsar sa..a hankali cike da mazantaka yace" Kaje kaga Ammi..."

*****
.....Daga wajen Ammin Sultan bai zame ko'ina ba sai 'dakin sa, a zahiri bama ya son ha'duwa da kowa, bayan haushin dramar da yayi a wajen Ammi na nuna mata damuwar sa da yake 'karara kan lamarin, babban damuwar sa itace rashin jin gamsashshiyar amsa daga bakin Rayyan ne, hatta Ammi bayaso taji 'kudurin sa har sai ya tabbatar ya samu amincewar Rayyan 'dari bisa 'dari dan yasan shine 'kwarin gwiwar sa, idan Ammi ka'dai ya tunkara yasan bazata ta6a amincewa masa ba dan a halin yanzu bata kaunar guda cikin su yayi mata nisa.

Wannan dalilin ya saka shi sake killace kansa domin kawai ya nuna wa Rayyan damuwar sa akan zancen da suka yi...baya ga shi da Ammi cikin gidan babu wanda yasan ya dawo.

'Bangaren Rayyan kuwa tun fitar Sultan tunani yake to in dai har Sultan dake 'kasa gare shi kuma bare a cikin su yake da wannan shau'kin har yayi tunanin nan saboda mahaifin su shi kuma mecece tashi gudummuwar kenan?"
Wata zuciyar sa ta bashi amsa da fa'din" addu'ah..." Tabbas hakane..yana wa mahaifan su addu'a sai ma abinda ya 'karu a halin yanzu, kuma Insha Allah zai 'kara kaimi sosai wajen ganin ya ninka akan wanda yake yi abaya.

Har ga Allah shi bai ta6a zargin wani ko wata kan mutuwar mahaifin su ba, haka kuma ko a baya ma bai taba tunanin akwai wanda ke bibiyar mahaifin sa ba, domin Abbah bai ta6a barin wata kafa da zasu zargi faruwar wani abu daban ba...'karshe sai gashi a hannun sa Mahaifin sa ya cika batare da ya iya dakatar da makiyan sa ganin bayan sa ba..".
Wata zuciyar ce ta tuna masa cewa..." _Ai mutuwa daga Allah ne, kuma dolen kowa ce...in lokacin mutum yy kuma babu mai iya hana shi tafiya..._ "
Yasan tabbas hakane
Amma yanzu fa?
Bayan mai afkuwa ta afku, bayan sanin cewa mahaifin sa na da magauta sai kuma ya na'de hannu ya zuba musu idanu su cigaba da aikata munanan ayyukan su?"
" _Bazai yiyu ba_ "
Yace a fili.

Bana so duk wani ma'kiyin Abbah na especially wa'danda suka yi sanadin mutuwar sa su samu sassauci ko ka'dan...

" _Zaka mutu_ ".
Shine ta'kaitaccen text na 'karshe da ya gani cikin wayar Abbahn wanda ya shigo wayar sa mintina 'kalilan kafin rasuwar sa..ya kuma kasa samun numbern bai kuma ga suna a jiki ba.

Idanuwan sa ya bu'de da suka rine izuwa jajaye, sai kuma ya sake lumshewa nan take.
" U definately win, mahaifi na ya mutu amma ya bar baya...Bazan ta6a sarara muku ba..bazan ta6a bari ku rayu cikin salama ba...but how?
ya tambayi kansa.
waye?
ina yake?
me yasa suke yi masa barazana akan 'ya'yan sa?
me yasa basu zo ga mu 'y'ayan kai tsaye ba sai shi?
menene dalilin su na kashe mahaifina?
Me ya musu?
wa'dannan tambayoyin duk amsoshin su na ga mutum biyu ne tak, Abbah da kuma makasan nasa.
ta Abbah ta 'kare domin ya riga ya tafi..kai kuma ina kake? ina zan ganka?
Ina zan ganka ka sanar da ni ala'kar ka da mahaifina da har yasa ka kashe min shi?

Ya fa'di hakan ne tare da dun'kule hannu ya buga inda hannun sa ke ajiye wato gefen kujerar...sam bai ji zafin hakan ba domin zafin da yake ji cikin zuciyar sa ya ninka wannan da yaji a zahiri.

Haka kuma bai fasa yin gaba da baya da kujerar ba.." Sam bazan bar duk mai hannu cikin lamarin nan ya tsira ba, da hannu na zan 'dauki fansa, da ilimi na, da dukiya ta nayi al'kawari sai na tozarta duk wani wanda ke da hannu wajen kisan mahaifina...zan gurfanar da ku irin gurfanar da babu wanda ya isa ya tseratar da ku...wannan al'kawarin Rayyan ne..".

Cikin kwanaki biyu duk Ammi ta kasa gane kan yaranta, ganin su ma na neman yafi 'karfin ta domin kowa cikin damuwa yake sosai, ita kanta bata da walwala tun ranar da Sultan yazo mata da waccan maganar kuma ya tafi har ya dawo 'din bata dawo da walwalar ta dai- dai ba, tana matu'kar son yaran ta tana son farin cikin su amma ta rasa hanyar da zata bi dan raba su da damuwar da suke ciki, ga Kabeer can kwance babu lafiya.
Ga Anty Madeena ma ta koma gidan ta tunda akayi 40days sai dai in ta samu lokaci tazo ta leka su ta koma gida

Ko lokacin da Sultan ya dawo fa'da sosai ta yi masa tana yi idanun ta na 'kwalla, domin ta fahimci kamar Sultan ya sanar da Rayyan komai ne bayan sai da ta garga'de shi..sam bata so hakan ba amma ganin Rayyan cikin kwanakin ya kasa natsuwa ya sata ta zargi hakan.
Batasan cewa asalin binciken ma shine da Kabeer ne mafarin ta ba.

Bata son yaran ta su cusa kansu cikin wani abu daban shiyasa ta damu, nd tsoron kafiyar su take yi tasan da wuya ne ta iya tan'kwara su domin ita tasan me ta haifa.

Safaah ce ka'dai ke da sanyin zuciya na biyun ta itace Marwa sai dai itama Marwan ba cikakken lafiya gareta ba, kullum tana nan ne jiya i yau sbd matsalar sanyi da take fama da shi..wato Pneunomornia.
Kuma itace ka'dai a gidan bata san komai dake faruwa ba, sai dai 'karancin walwala da ta fuskanta game da sauran 'yan uwanta sosai itama yake ta6a ta.

Ga Raihana ma an 'kira ta saboda Bassam 'din ta babu lafiya da yake dama bata taho da shi ba yana can wajen kakannin sa ne a Kaduna dole ta shirya ta tafi.

Safaa data fuskanci damuwar Ammi kullum 'kara gaba yake yi sai itama ta rasa sukunin zuciya, dan ma a hakan sosai Ammi ke 'ko'karin 6oye mata.

Sultan sake zurfafa bincike yake da kulla sabon shiri bayan killace kansan da yayi dama gashi masanin na'ura ne shi, yayin da Rayyan kullum indai yana gida zaka same shi kan kujeran sa yana juyawa da idanuwa lumshe yana tunanin mafita, dama al'adar sa kenan tun a baya matukar yana cikin farin ciki ko akasin hakan zaka same shi bisa kujerar sa yana juyawa da idanuwa lumshe bambamcin kawai shine idan yana a yanayi na farin ciki zaka tsinci murmushi saman fuskar sa ne.
Sa6anin yanayin sa na yanzu da sam babu walwala saman fuskar sa, kullum burin sa shine 'daukan fansa..amma ya rasa ta ina zai fara, likita ne shi yanzu, ba hukumar bincike yake aiki ba, bai masan komai game da aikin bincike ba dan babu abinda ya ta6a ha'da shi da hakan, shi ba jami'in tsaro ba ba kuma alkali ba...to ta ina zai fara?

_Zaka iya yin komai idan kazama lawyer mai zaman kansa_
Wannan shawara ce daga wani 6angare na zuciyar sa, take kuwa ya bu'de idanu sai kuma ya sake lumshewa.

Lawyer...!
Lawyer....!!
Lawyer......!!!

Dama tun asali wannan burin sa ne, amma a wannan ga6ar hakan na da wata fa'ida ne?
Ya sake tambayar kansa...

Bai kai ga kaiwa 'karshen tunanin ba sallamar Safaah ya dakatar da shi.

A hankali ya bu'de idanu, ciki- ciki ya amsa ta.
Duba 'daya yayi mata ya fahimci damuwa ce ke tafe da ita.

Gaban sa tazo ta zauna inda ya daina lila kujerar ya zuba mata idanu.
Kanta ta kwantar saman gwiwoyin sa kawai ta fara rera kuka mai sauti ko magana ba ta iyawa.

Shi kam kanta ya zubawa idanu yana tunanin me ya sata kuka haka kuma?
Tunanin sa ya tafi ne ga Yayan sa Kabeer da kuma 'dan 'kanwar sa Bassam da Marwa da duk basu da lafiya suke kwance.
Lokaci guda sai yaji jikin sa yayi sanyi sosai...duk da yake ko ayau ma sai da ya dubo jikin Kabeer din kuma Alhamdulillah da sauki sosai sai dai still zuciyar sa babu natsuwa..kuma ba abin mamaki bane a wajen ubangiji daukan ran duk wanda ya so.

Tsawon mintina suna a hakan yama kasa dakatar da ita a hankali ya 'kira sunan ta gami da 'dora hannun sa bisa kanta alamar rarrashi.
" Me ya faru ?"
Bata amsa shi ba ta cigaba da kukan ta dan ta jima tana tarawa.
Sakanni talatin ya 'kara mata sannan ya sake tambayar ta " Safaah me ya faru ne wai?"

" Yaya..Ammi ce".
Ta fa'di da muryar kuka tana 'dago idanu jin yanayin da yy magana tasan gaf take da kaishi wani ma'kura in batai saurin bashi amsa ba.
Chapter 86 · 0% Book details