← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 177 OF 218

Sashe 177

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sau biyu aka buga kafa'dar tasa tamkar irin ana jinjina masa 'din nan.
Cikin zuciyar sa kuma ji yake kamar ana yi masa magana ne da sauti mai shiga can cikin zucia, bai isa ya misalta yanayin sautin ba, ya dai yi kokari wajen ko kalma guda bata kubce masa na daga kalaman dake shigan sa" Kaje 'dana, kar kaji tsoro! kar kaji shakka, kai 'din jarumi ne, kuma namijin dunia ne, tafe kake da sa'a da 'kwarin gwiwar ka tun kana zanin goyo, ka tsaya akan gaskiyar ka, ka fiddo da ita fili, ba tonan asiri bane..ba kuma 'kiyayya ba, zallar shari'a ce da kuma hukunci, da iznin ubangiji kuma zakayi nasara yaro na! nasara taka ce, nasara ba tare da kai har abada Muhammad Rayyan...fatan alkhairi....".
Daga haka bai sake jin komai ba illa wasi- wasi daga cikin zuciyar sa..amma still kwarin gwiwar sa na nan..sam babu karaya ko tsoro a tare da shi.

Tamkar kuma an cirewa hannayen sa da jikin sa wani abu mai mauyi haka yaji shi ko ina nasa sakayau.

Hannayen sa duk biyu ya sa atare ya kamo gaban rigar yana gyara mata zama idanun sa 'kur a cikin madubin..ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya.

'Kafar sa ya 'daga ya 'danja baya ka'dan taki 'daya hakan bai masa ba, baya ya sake yi zuwa bakin gado batare da ya juya bayan sa ba, da baya yayi tafiyar zuwa inda wasu tarin takaddu ke ajiye kusa da pillown sa yasa hannu ya 'dauko su ha'de da makullin motar sa.

Sai da ya rungume su tare da lumshe idanun sa saman la66an sa ya furta sunan da shi ka'dai yasan me ya fadi..sai dai in kana kusa da shi ne zaka iya tsinkayar sautin sunan... _Zaitoon_ acan 'kasa.
Daga hk yy waje batare da ya sake waigowa ba.

'Karfe goma za'a fara shari'ar, dan haka bai yadda yy latti ba, duk da bai so hkn ba, bai so tafiyar da shari'ar a yadda yake ganin dole hakan zatazo ba, yaso tun a hannun hukuma Sultan ya amsa laifin sa amma taurin kai da kafia ya hana shi, dole sai ansha fama yasan dashi, sai dai sanin da yayi cewar ya tara 'kwararan shaidu da hujjoji yasa yake 'dan jin sanyi aran sa domin shi ba burin sa ayi doguwar shari'a ba, ba burin ayi ta kaiwa ana kawowa tsakanin.sa da Sultan ba, burin sa kawai ayi ta ta kuma 'kare batare da anaki ruwa rana ba, da so samun sa ne ma bai 'ki a yau kadai bama a kammala shari'ar sai dai yasan mawuyaci ne, ita shari'a sa6anin hankali ce dole sai an bi a sannu.

Yadda yaga kotun cike da mutane tun daga haraba abin yaso bashi mamaki amma mamakin sa bai tashi tabbatuwa ba har sai da ya dangana kansa da cikin kotun a lkcn da mai girma alkali ya iso.

Ji yayi tamkar ya wakilta wani a madadin sa amma wata zuciyar tasa ta garga'de shi da hakan nan take.

Bayan gabatar da wasu sha'riah har guda biyu sannan mai gabatar da shari'ah ya gabatar da tasu shari'ar aka fara fafatawa tsakanin lauyan Sultan da kuma lauya Muhammad da Rayyan.

Kotu tsit tayi tun daga lkcn da aka fara gabatar da shari'ar har zuwa lokacin da mai sha'ria ya 'dage 'kara zuwa zama na gaba.

Da yawan mutane sun tafi ne da haushin Rayyan sbd dangantakar su da Sultan ya riga ya bayyana har su ke ganin rashin kyautawar Rayyan yayin da wasu ke tunanin dole akwai butulci ta 'daya 6angaren da har yanzun sun kasa gano daga ina ne, domin har aka tashi shari'ar Sultan ya ki furta ko kalma 'daya 'kwakkwara da yasan zata rufe shi, shiyasa wasu ke jin tausayin sa.

Hankalin Ammi ba 'karamin tashi yayi ba da ganin Sultan a kotu da kuma yanayin da ta gansa, duk da yake basu samu isowa akan lkc ba sun zone a 'kurarren lkc, amma ganin yanayin Sultan ya sake rikita mata tunani, Rayyan kuwa ana kammala sharia aka neme shi aka rasashi yabi wata hanyar yy gaba abinsa.

Duk yadda Ammi taso haduwa da shi abin ya faskara, hankalin ta ya tashi sosai, shiyasa ko fahimtar abinda ke faruwa cikin kotun batayi sosai ba.
Anty Madeena ke 'dan kwantar mata da hankali da yake su uku suka zo da wata 'kawar Ammin.

Duk yadda su Raihana suka zo zuwa Anty Madeena 'kin amincewa tayi, tace ta zauna da su Marwa a gida.

Sam yadda Ammi take tunanin sha'riar ba haka bane, Anty Madeena da ta 'dan san wani abu akai, ta kuma fahimci ka'dan daga cikin shari'ar bayan zuwan su sai taji abin ya mata zam zam, taso fahimtar da Ammi amma ta kasa bada hankali ma balle ta fahimci manufar Antyn dan haka sai ta fita hanyar ta.

Email ta yiwa Rayyan akan tana san ganin sa kota wanu hali a yau ba wai sai gobe ba, domin wayoyin sa duk" babu me tafiya.

Ai kuwa har ta cire rai da zuwan sa, bayan isha'i sosai ma sai ga shi yazo, domin bai ga sakon da wuri ba, yaso ma tun yamma.ya wuce Lagos sai aka samu akasi jirgin Lagos 'din ya riga ya wuce sai kuma zuwa shida na safia, abinda ya hana shi wucewa kenan kawai ya tsaya duba sakonnin sa na email nan yaci karo dana Ammi, batare da 6ata lkc ba kuwa ya shirya ya tafi gidan ta domin yasan darajar mahaifiyar sa ba dan kadan ba.

Fa'da sosai Anty tai masa na fara shari'ar da yayi batare da ya sanar da mahaifiyar sa ba ta kuma sanar da shi yadda duk hankalin Ammi yake a tashe sbd hakan.

Ha'kuri Rayyan ya bata sannan ya 'dora da jero dalilan sa ya kuma ce ai ke ma kin sani Anty, kinsan halin Ammi..na kwammaci a kammala komai kafin haduwar mu sbd nafi kowa so da ganin an hukunta yaron nan, sanin cewa ba'a daukan doka a hannu ne yasa nk duk wannan ba dan haka ba da tuni na hukunta dan banza, ya cuce ni yaron nan Anty, ya min mafi tsanani da munin cin amana, yaci amanar mu gaba 'daya Anty, wlh na jima banga macuci mai tsananin son kansa irin wannan yaron ba...Anty...kuma nasan Ammi bazata ta6a fahimtar duk wani karatun da zan mata bisa wannan al'amari ba indai akan yaranta ne musamman ma shi..shiyasa na biyo ta wannan hanyar.

Sai ya yi shiru ya kasa ci gaba da magana.
Anty ma jikin ta sanyi yayi sosai...a hankali tace kayi hakuri Rayyan....."
Da sauri ya tare ta yana mai girgiza kansa yace..." Not on these issue pls Anty...Ki barshi ya girbe abinda ya jima yana yiwa mutane, ki barshi ya girbe abinda ya jima yana shukawa kansa da kansa...".

" Nima ban hana ka hukunta sa ba, but why can't u expel nd replace ur self with somebody else...I think is better than kai da kanka ace kk wannan shari'ar Rayyan, bayaga haka ma kar tafia tayi tafia kazo ka karaya bcuz Sultan is still ur brother nasani, that bond is still existing sbd u all raised with it...".

Shiru kawai yayi bai ce da Anty komai ba, amma shi a karan kansa yana ji da kuma tabbatar da hakan ba tun yau ba, yana son Sultan ya na kuma kaunar sa matsayin dan uwan sa sai dai hakan bazai hana ya kasa mi'ka shi ga duk inda yasan zai samu hukunci dai dai da laifin da ya jima yana aikatawa ba....

Abu biyu zuwa uku da Sultan yai masa har baya 'kaunar tunawa da su, sbd abubuwa ne masu matukar ba'kanta rai da zucia, cin amana, ha'inci da kuma yaudara, tun asali ya tsani ma'abota ha'inci da cin amana, sannan ko da wasa bai ta6a zargin Sultan kan komai dake faruwa cikin ahalin su abaya ba, amma karo guda Sultan ya karyata mafarkin sa, ya wargaza yadda, amana da amincewar da akayi masa tun yana dan karami, ya tabbatar masa da cewa shi din ba 'dan halak bane na zahiri, ya kuma tabbatar masa da gaskiyar maganan nan da ke cewa tsintacciyar mage bata mage....

Da 'kyar da kalaman kwantar da hankali da kuma lallami Anty ta samu ya labarta mata komai da ya sani, nan ta 'kara 'daukan zafi akan Sultan, domin yanzu ta gama sanin komai ta kuma 'kara tabbatar da cewa tun da can baya ba a banza ne take jin tsanar yaron ba ashe da gasken gaske fuska biyu gare shi, ashe dagaske maci amana ne maha'inci....".

Ammi sam bata tsoma baki cikin maganar tasu ba illa idanu data tsura musu cike da mamakin su duk biyu.

A yadda ta fahimci Rayyan sam ko me zatayi bata ga alamun janyewa tare da shi ba...hakan yasa kawai ta mike da niyar basu waje tunani kawae ta fara na yadda zaymta 6ullo masa.

Ganin tashin nata yasa Rayyan saurin kiran sunan ta...bata tsaya ba ta amsa shi da cewa"Nagode sosai Babana"!
A yadda tayi maganar yasan me take nufi.
Dan hk take ya mike yana fadin Ammi dan Allah kiyi..."
Saurin tare shi tayi tana gab da barin parlourn tace" Kar ka damu jeka abinka...ngd ka kuma kyauta"!
Daga hk tayi gaba abinta shi kuma ya tsaya cak ya dafe goshi gami sakin numfashi.
Yaso yabi Ammi amma yasan ko da ya nemi dogon zantawa da ita batun dai 'daya ne indae Ammi ce shi kuma sam bazae iya ba a wannan ga6ar.

Yadda yaga Anty Madeena ke share 'kwalla ya fahimci lalle abin gagarumi ne da alama wasu abubuwan take sake tunowa.

Rayyan dai bai ce da ita komai ba kawai ya wuce ya tafi izuwa masau'kin sa.

Ranar da aka koma zaman kotu Rayyan bai bayyana kamar ranar na farkon ba, shawarar Anty ya dauka kai tsaye sbd shi kansa ya sani akwai ga6ar da bazai iya jure tunawa da shi gaban 'dumbin jama'ar ba da ganin idanun sa sun ninka na baya, hakan ne yasa ya wakilta abokin sa mai suna Ahmad Fari shi kuma ya 6oye kansa, sai dai ko kalma guda cikin shari'ar bai bari ya wuce shi ba.
Chapter 177 · 0% Book details