Sashe 12
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin idon mai bayanin ta duba tace" Waye yace maka yarinya ta shegiya ce marar uba..?"
Tayi tambayar ne cikin tsare su da idanun ta kai kace in aka barta zata iya tsinana wani abin kirki ne.
Tuni tama nemi hawaye ta rasa a idanun ta, hakika mutane abin tsoro ne a wannan zamani, yaushe ma aka santaa unguwar har da labarin ta zai fito ta wannan sigar.
Mai bada dogon bayanin na shirin tankata wanda aka kira da Sabi'un yai saurin dakatar da shi, sai duk suka zuba mata idanu.
Ganin bazai tanka ba yasa Zaitun cigaba da fa'din..." Daga yau ko da abayan idanu ne ka sake aibanta min yarinya da suna shegiya wlh bazan ta6a yafe maka ba kuma sai Allah ya mata hisabi da kai da ita...ka guji daukan hakkin marayan da bai ji ba gani ba...".
Daga haka ta juya ta fara tafiya da dan sassarfa tana ganin gaban ta da kyar, har tama manta da wani zazza6i ballantana jiri da take ji.
Jikin matasan nan sanyi yayi sosai kusan shafewan wasu dakiku kafin mai suna Sabi'u ya saki ajiyar Zuciya..." Babu mamaki kallon kitse kuka tsaya yiwa rogo dan ni wlh kalaman yarinyar sunyi tasiri a zuciya ta tuni naji na yadda da ita dari dari bisa"
" Ka dalla can...ashe karamin kwakwalce da kai, wannan kuma wani sabon abu ne Sabi'u? Ni nan da kake gani burga baya tasiri a zuciya ta waye ma bai san zaman kanta take cikin unguwar nan ba..".
Ajiyar zuciya kawai Sabi'u ya sauke da fadin" Allah ya kyauta".
Hajja da Siyama sun riga Zaitun kaiwa gida dan haka ko da ta karasa dakin ta ta shige bata kuma bi ta kansu ba dan ita kadai tasan yanayin da take jin kanta a yanzu...sai da ta tsinci kanta cikin dakin ta tama kafin taji wani kuka mai karfi yazo mata cike da kunar zuciya...Da hannun ta daya ta toshe bakin ta gami da kife kanta tasha kukan ta batare da kowa ya jiyo ta ba.
Mmn Abdul ke tambayar Siyama ina ta baro Zaitun din bayan ta gama gaisuwa da Hajja tana mai kokarin diban mata ruwan da zata sha take yiwa Siyama tambayar.
Amsa ta Siyaman tayi da fadin.
" Tana tahowa abayan mu...tace jiri take ji idan tayi sauri faduwa zata yi...".
" Kai Allah dai ya sawwaka ni kam wannan irin ciwo lokaci guda haka.."
Tayi maganar nan ne tana mai ajiye ruwan gaban Hajja tana sake zama bakin tabarma gefe da Hajjan kadan.
Sai da Hajja ta sha ruwa ta sauke kofin sannan cike da gatse tace" Ita waccan din me ya same ta..?"
" Wallahi zazza6i ne kawai Hajja amma kar kiga yadda ta zabge rana guda tak abinki da me kazar kazar duk sai kaji wani iri babu dadi..itama yarinyar kamar ta san uwar ta ba lafiya yau din yini tayi sukuku duk ba wata walwala sai da na goya ta ma kafin aka samu ta danyi bacci..".
Baki Hajja ta kyabe tana duban Mmn Abdul.." Wato dai Rahma har yanzu baki bar wannan bautar da kika daurawa kanki ba ko..?, Allah yasa ma ba wani abin kunyar ta kuma karo muku ba tunda taga kuna kar6a mata hannu bibbiyu hadda tayin raino..."
" Um um Hajja na tabbata Zaitun bazata aikata wancan danyan aikin ba.."
" Sai kuma kiyi, lokacin da tayi na farkon ta nemi shawarar ki ne...?"
Rauda dake gefe da Hajjan saurin jefa nata tayi itama.
" Bar Anty Rahma dai Hajja da ba'a aje shaida mun gani bane sai muce ba haka abin yake ba amma ga zahiri nan..."
Wani dan banzan harara da Mmn Abdul ta zabga mata yasa taja baki batare da ta karasa fadin abinda tayi niyya ba ta karashe da kawar da kai tana kunkuni.
Mmn Abdul kokadan bata ji dadin wannan magana ta Hajja da 'yar uwar ta ba, amma babu yadda ta iya da ita dole taja baki tayi shiru, wani lokacin bata ganin laifin su ma duk laifin Zaitun ne, da ace ta bude zuciyar ta ta bayyana al'amarin a yadda yake asali tasan da duk hakan bazai faru ba.
Kamar Mmn Abdul tasan abinda ke zuciyar Zaitun kenan adaidai wannan lokacin dan itama tashin farko ta dauki laifin karankataf ta daurawa kanta, sai dai tasan koma me zata fada musu ba lallai ne ya canza zuciyar su ba, ba kowa ne zai amince da batun da zata fada din ba kamar yadda tun a gida akai mata tawaye aka ki fahimtar ta shiyasa a kullun take ganin babu anfanin sake bayyanawa dan duk mutane iri daya suke kusan kowani lokaci.
A nan kwancen da take tana iya jiyo duk abinda suke tattaunawa dan bakin dakin Hajja suke zaune kuma shine daf makwabcin dakin ta.
Hannu ta kai ta dafe kirjin ta dashi saitin zuciyar ta, har ga Allah tana cutuwa a mabanbantan lokuta kuma sanadin mabanbantan mutane, bata so akai gandun da raunin dake zuciyar ta yin tasiri akanta da wanne zata ji, meyasa kowa yake aibantata sanadin Mufeeda, meyasa kowa bai kunar yarinyar ne?"
Zuciyar ta taji nayi mata suka tamkar wacce aka cake ta a kirjin da mashi..." Hajja dai bazata ta6a canzawa ba itama.."
Dakyar ta samu ta daidaita hawayen ta sannan ta lalla6a ta fito har yanzun kuma basu tashi inda suke zaune ba illa Mmn Abdul da bata gani ba tana can tana karasa gyaran da aka yiwa dakin nata a yau din.
Gaishe da Hajjan tayi bayan ta zaune gefe kadan da ita.
Sai ga mamakin ta daga Hajjan har Rauda kowa kawar da kansa yayi bacin tana da tabbacin sunji gaisuwar da tayi, sake maimaitawa tayi sai dai har yanzun Hajja bata amsa ba.
Cak Zaitun ta mike tare da kwashe rigunan yarinyar ta dake kan igiya ta koma ciki.
Dama hakkin makwabtaka da kuma girma da take bawa Hajjan dalilin Mmn Abdul ya sanya ta fitowa bayaga haka me zai sa ta 6ata lokacin ta wajen wacce kokadan bata kaunar ta balle yarinyar ta.
*****.......
Kamar hadin baki washegarin dawowar Hajja sai ga Bbn Abdul ma inda yai musu diran safiya.
Wani sabon tashin hankalin da Zaitun ta jima da mancewa da shi ne ya diran mata da ganin Bbn Abdul din.
Sai yanzu ma ta fahimci dalilin dawowar Hajja da kwalema da su Mmn Abdul suka yi a jiyan kenan dan Bbn Abdul zai dawo ne, meyasa kwatakwata kwakwalwar ta bata kai can din ba.
Toh banda abin Zaitun yaushe ma damuwar da take ciki tun jiyan ya barta ta yiwa abubuwa duban fahimta..?
Tun a jiyan bata wani nutsu ba gata nan dai kawai tunanin ta duk yana ga neman mafita ne sai ga kuma wata sabuwa.
Da ace Bbn Abdul bai nuna mata halin sa daga isowar ta shi bama da zata yi tunanin tuni labarin wancan lamarin ya shude amma daga isowan shi suna hada idanu ya wani dage mata yana mata wani kallo kasa kasa da ita kadai take fahimta sbd ba yanzu ne farko da ya mata hakan ba.
Duk tsarabar da ya kawo Mmn Abdul ta so diban ma Zaitun ko wanne daga ciki, dangin Manja, doya, irish Potato, kwakwa, doya, garin kwaki hadda tulin tsintsiyan kwakwa dadai sauran su..amma Hajja ta tsaya tsayin daka ta hana a cewar ta ma daidai kwayar tsintsiya idan aka bawa Zaitun din bata yafe masa ba.
Wannan lamari sosai ya ta6a ran Mmn Abdul yayin da 6angaren Zaitun dadi ma ya mata, dama bata ta6a jin kwadayin wani abu na Bbn Abdul din ba ko min girman abin kuwa.
Mmn Abdul tsabar kunya kasa hada idanu tayi da Zaitun ganin yadda ake ta raba tsaraba wa makwabta amma ita an hana abata.
Daga karshe dole ta daure taje har daki ta bawa Zaitun hakuri...Zaitun kam ko ajikin ta, abu ma ko an baka sai an biyo bayan sa da gori ina amfanin sa, tunda bata rasa ci da sha ba Alhamdulillah ta godewa Ubangijin ta.
Hatta Mufee Zaitun bata kara barin ta taje kofan Mmn Abdul ba gudun abinda zai iya zuwa ya dawo...Mmn Abdul ce tayi saurin lura da hakan har taso nuna 6acin ranta wa Zaitun din da fadin ko dai fushi takeyi da su gaba daya.
Zaitun rasa ma abin cewa tayi, erh mana rasa abin cewa domin idan har tace zata wanke kanta game da hakan toh sai ta hada da rantse- rantse kafin ta iya wanke kanta, yawan rantsuwa kuwa ba halin ta bane ba kuma tasan jan zance.
Wannan dalilin ne ya sa ranar da zata koma bakin aikin ta dole ta bar Mufeeda a gida badan komai ba sai dan Mmn Abdul kada ta fassara ta sigar da ba haka abin yake ba.
Bayan kwana biyu da dawowan Bbn Abdul ne ta koma aikin kuma har zuwa lokacin bata sake haduwa da shi a gidan ba, bata sanin lokacin fitan sa balle shigan sa da sauran al'amura ashe doka mai karfi Hajjan ta kafa masa game da Zaitun din bata sani ba.