Sashe 85
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kam Sultan ido ya tsura mata na tsawon mintina biyu...a hankali da sanyin murya yace
" Ammi..!"
" Na'am Sultan dan Allah ba dan ni ba ka bar wannan zancen kaji.."
" Kai Ammi don't tell me kinsan komai dama kike 6oye mana tun ba yanzu ba...."
Kai tayi saurin girgizawa sannan tace" Koka'dan Sultan ban san komai ba, amma na jima da fahimtar mahaifin ku na cikin tsananin damuwa amma kasan halin sa, bai ta6a ko kwatanta sanar da ni damuwar sa ba...sai dai nasan babu abinda Mutum ya isa yayi wa wata halitta matu'kar ba Allah ne ya tsara masa ba, bansan tasa kalar matsalar ba, ban kuma san ta ina ta taso ba dan haka Sultan bisa umarni na..ka rufe wannan batun ka fuskanci rayuwar ka kaji 'dana dan Allah..."
Shiru Sultan yy ya tsurawa guri guda idanu.
Rayyan kam fasa shigowa ma yayi kawai ya juya ya koma da baya, bazai iya jure ganin mahaifiyar sa cikin wannan yanayin ba sam.
Bayan kamar mintina hu'du 'dakin bb komai sai ajiyan zuciyan Ammi, tashi Sultan yayi batare da ya furta komai ba ya sa kai ya bar saman sitting room 'din.
Ammi kam tashin hankali ne sosai ya ziyarce ta, ta riga tasan halin abinda ta haifa, yaran ta duk babu mai sau'kin hali indai an ta6a su, nd bata so su saka kansu cikin abinda zai sa ta rasa ko da 'daya daga cikin su, ba Sultan ko Kabeer ne damuwar ta ba, babban damuwar tata dama Rayyan ne, tasan in dai ya riga yaji komai to kuwa kwanciyar hankali ya bar shi kenan.
Tun daga ranar bata sake saka Sultan a idanu ba har akayi kwana biyu.
Shima Rayyan gaba 'daya damuwar sa 'kara yawaita tayi har bai kula da rashin ganin wulgawar Sultan cikin gidan ba.
Abubuwa ne suka kulle kansa, bai so tun farko Sultan ya samu labari ba, amma kwatsam sai ji yayi suna zantawa da Ammi kan batun da suke faman 6oyewa tsakanin su.
Ina Sultan ya samu labari har ya isar ga Ammi..bai sani ba.
Tsawon kwanakin abinda yake tunani kenan amma ya rasa amsar sa.
Dole ya nemi ganawa da 'dan uwan sa wato Kabeer kafin ya zauna da Sultan din ma.
Da yake shima Kabeer 'din kwana biyu shiru babu labarin sa sai dai suyi waya kawai, yayin da yake can yana sake zurfafa bincike kan lamarin da iya zuciyar sa hatta Rayyan bai shigar cikin binciken sa ba.
Dan haka Rayyan ya shirya ha'duwa da shi, bayaga haka ma yanda Ammi ke damun kanta sosai akan rashin ganin sun shi har Sultan ne ya 'kara masa 'kwarin gwiwar neman sa da dan Sultan kam hatta wayar sa ma bata shiga.
Anan ya tarar da wan nasa cikin tsananin tashin hankali wanda da ganin Rayyan ya saki hamdala dama yayi kewar su sosai.
Ashe baya jin da'di ne kuma jikin yayi tsanani sosai kuma ya hana matar sa sanar da kowa.
Rayyan da kansa ya duba sa inda ya tarar da damuwa ce da kuma hawan jini suka kamasa.
Da kansa ya harha'do masa mugunguna kafin ya bar gidan 'karshe zancen da yakai shin ma bai samu damar tattauna wa akanta ba.
Shine ya kawo labarin rashin lafiyar dan uwan nasa ga Ammi.
Nan hankalin ta ya 'kara ta shi dukkan su har Anty Raihana suka je duba shi.
Yayin da shi kuma daga nan ya wuce can wani ke6antaccen gidan Abban su ya tabbatar zai samu Sultan acan, domin a mafi yawan lokuta nan ne wajen zaman sa indai har yana a yanayi marar da'di.
Yayin da 6angaren Sultan ya ke6e kansa ne da gangan sbd ya cigaba da gudanar da ayyukan sirrin sa cikin sauki da kuma sirrintaka.
Kabeer kam damuwar sa ce tai tsanani sosai, tun ranar da suka fara bincike da Rayyan ya fahimci abin kamar ba daga nesa bane kusa da yake tasowa, ansha yiwa Abbah barazana akan abubuwa da dama da ya tabbatar wanda yasan sirrin su sosai ne ka'dai zai aikata...'karshe ma hallaka Abban aka yi.
Sosai ya abin ya 'daure masa kai har ya haddasa damuwar da ta kaishi ga kwanciya musamnan saboda tsanantawa wajen gano wa zai iya aikata hakan gare su cikin makusantan su, amma ya kasa ganowa, wannan karan hatta da Rayyan 6oye masa yayi ya ta aikin sa shi ka'dai, sai da ya ga numfashin sa na neman barin sa ne kafin ya fara tunanin sanar da Rayyan cikin sa'a sai gashi yazo duba shi duk da hakan basu samu tattaunawa ba ya bari zuwa ha'duwa ta gaba, amma dole ne suyi zaman sirri da juna.
Yaso ya ha'kura da binciken amma zuciyar sa ta kasa amincewa da hakan, babban abinda ya hana shi ha'kuran shine barazanar da akai ta wa Abban su har akan su 'ya'yan sa, tunanin sa idan suka yi shiru kan al'amarin har abin ya dawo kansu fa, ta ina zasu iya 'daukan mataki..kafin a cimmasu a kassara su.
Bai san waye ne ba, bai kuma san dalilin da yasa su ka kashe masa mahaifi ba amma guarantee yasan their must be a reason but bai sani ba, bai san waye kuma zai sanar da shi ba.
Yayi bincike iya iyawar sa batare ma da Rayyan ya sani ba har zuwa lokacin da ya san zai samu wani evidence amma abanza, ba 'karamin iya taku suka yi ba...duk sun rufe hanyar da ya kamata yasan abinda yasa suka kashe masa mahaifi.
To ya zaiyi, da kansa yaji ma ya tsani kansa dama duniyar baki 'daya, yana tsoron ranar da za'a sake ta6a masa 'daya daga cikin 'yan uwan sa.
Babban burin sa shine yin ram da koma waye yake da hannu dan ya fahimci ba mahaifin su ka'dai suke hari ba, yana so ya 'daukan masa fansar abinda aka yi masa burin sa ya du'kufar da makasan agaban kuliya...amma..how can he do all this..?
bai sani ba.
Ya 'dauki a'kalla tsawon sati biyu kafin ya sami mafita dan zuciyar sa ta kasa ha'kura balle ya yafe ma koma waye yy hakan.
Aganin sa ta inda aka hau ta nan ake sau'ka...bazai ta6a ragawa koma waye ba, bashi da burin kisa ko kuma ganin ankashe amma hakan bazai hana shi 'daukan fansa ba.
'Bangaren Rayyan kuwa tunanin sa bai bashi karya ba, nan inda yake tunanin zai samu Sultan anan ya tadda shi, Sultan na ganin Rayyan ya taho ya rungume shi, tamkar 'karamin yaro haka ya ringa kuka yana fa'din basu kyauta masa ba da suka 6oye masa cewa kisan Abbah akwai hannu aciki, sosai jikin Rayyan yayi sanyi, da 'kyar Rayyan ya shawo kansa bayan sun zauna bisa kujera, anan ya sanar da shi cewa basu tabbatar bane shiyasa basu bayyana ba amma suna kan bincike Insha Allahu da zarar sun tabbatar zasu 'dauki mataki.
Tare da Sultan suka dawo gidan bayan ya ce da Rayyan su zo su sake bincika 'dakin Abbahn ko zasu dace da samun wani clue 'din.. sai dai a ba'dini duk cikin shirin sa ne.
Ai kuwa hakan akayi, kafin Ammi ma tasan da batun dawowar su gidan 6angaren Abbah suka yiwa tsinke, bincike sosai suka yi amma basu samu komai ba duk da dama already Rayyan sun riga sun yi duk abinda ya dace tare da wansa Kabeer amma tunda Sultan ya nemi ayi hakan bazai iya musa masa ba dan kar yaji babu da'di, hatta motar Abbahn sai da suka duba amma babu komai babu wani abinda zai bayyana wannan sirrin..amma kuma cikin wayar sa ga zahiri akwai matsala kama daga text messages da baya gogewa a wayar sa system 'din sa ma basu samu komai ba sai kuma 'kira da wasu numbobi, kuma duk numbobin Rayyan ya gwada 'kira tun ba yau ba amma ko 'daya basu shiga...yayi binciken duk da yakamata akan numbers 'din amma da alamu mai amfani da layukan yana da matukar wayo.
Guda 'daya ne aka samu har aka iya tressing inda yake 'karshe a wata unguwa can rijiyar lemo cikin magudanar ruwa suka gano shi, wannan binciken Rayyan da Kaberr duk suka yishi batare da sanin kowa ba...iya hangen su kuma basu tuna kowa da suka sani a Rijiyar lemo ba.
Anan ne Rayyan ke 'dan bawa Sultan labari a zahiri ya nuna hankalin sa ya tashi sosai.
Dukkan su tagumi suka yi a palorn Mahaifin nasu, sun rasa ta ina zasu fuskanci lamarin kwata- kwata daga 'karshe Rayyan ne ya fito da sharwarar kawai su share tunda basu san ta inda zasu fuskanci lamarin ba ya kuma nemi Sultan ma daya kwantar da hankalin sa ya cire komai aransa ya daina damuwa, ya nuna masa yawan damuwar su kan iya sawa sauran matan ma walwalar su ta kasa komawa dai- dai.
Sultan yaro ne amma sam baya giving up da wuri, dan ko wannan lokacin ma kai ya girgiza yace be iyawa, yace ba zai iya rayuwa cikin farin ciki ba kamar yadda Rayyan ya bukaci yayi bayan yasan mahaifin sa na da muggan ma'kiyan da har suka kaishi 'kasa kuma ace bai sansu ba, bai san ta inda zai fara kamo su ba amma yasan duk da'dewa komai zai bayyana, dan haka yace zai tari lamarin da babban makami...
Duban Rayyan yayi yace
" Ya Rayyan aikin soja nake son shiga domin bana so idan na kama ma'kiyin Daddy in yi masa da sau'ki kuma bana so case 'din ya shiga hannun kowa dan duniya ba gaskiya yanzu, bazan fa'dawa Ammi ba haka ma Yah Kabeer hanani zaiyi, ya Rayyan kai ka'dai nake neman amincewar ka nasan idan ka amince babu mai cewa a a.."
Kan gwiwoyin sa ya zube gami da 'dago hannayen sa duk biyu ya rike hannuwan Rayyan din sannan ya cigaba.." idan kana son ganin farin ciki na yaya ka amince min dan Allah wannan shine buri na a halin yanzu...."
Ya 'karashe cikin yanayi na ro'ko mai tafe da tsantsan rauni da damuwa.