← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 218

Sashe 180

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihana bata san lkcn da ta sau'ke mata mari lafiyayye ba a zuciye, cike da ba'kin rai tace..." Akan wancan 'dan iskan yaron kk wannan haukan Marwa...?
Hala bakiji cewa da akayi shine makashin 'yar uwar ki Safaa ba..? Batare da tausayi ba ya kashe mana Zamrud ya kuma kashe mana Yah Kabir da Abban mu..bayan cin amanar da yayi ta mana a 6oye duk kin manta?..akan sa kike wannan haukan kukan kuma Marwa...?"

Baya taja tana mai dafe kuncin ta tace" Anty ai babu wanda ya tabbatar cewa shi Sultan din ne ko wani daban..kawai dan an tsane shi sai ace shine...".

Hannu Raihana ta sake 'dagawa zata zabga mata wani marin Ammi ta ce" Kulll..Raihan.."!
Tare da shiga tsakanin su.

Tsaki Raihana taja cike da masifa da kumfar baki tace" Waye ya tsane shin..? Marwa anya kina cikin hankalin ki kuwa..? Wai Sultan dai Sultan dai...? akan Sultan kk so ki nuna mana wace ko? Toh ga hanya nan..sai kije can wajen Amra ki amso muku 'dan ku Arfan da ke wajen ta ki tattara ki bishi gidan prison din ku rayu acan da yaron ku tun da ke soyayya ta riga ta rufe miki idanu baki ji baki gani..."
Daga haka taja tsaki ta juya ta fita ranta a matu'kar 6ace.

A hanya suka ci karo da Rayyan da ya taho da Mufee bisa kafa'dar sa sun yi kyau gwanin birgewa.

Kallo 'daya da yy mata ya fahimci ranta 6ace yake bai kuma san menene ba sai dai ya 'dan zargi ko itama ta goyo bayan Marwa ne tunda yaga ko kallon arziki bai samu daga wajen ta ba.

Ita yy niyyan bawa Mufee amma ya fasa sai da ya wuce ma kafin yace" ki turo min mamin Mufee...."
Inda yayi maganar yana hayewa saman Ammin shima.

Tuni ma'aikatan sun koma bakin aikin su tun bayan fitowan Raihana.
Dan haka tasan da ita yake ba da wasu ba, bada son ranta ba ta wuce 'dakin Zaitoon 'din dan sanar da ita sakon Rayyan.

A 'kofa ma suka ci karo da ita, niyyar ta dama taje ta duba Marwa ne tun 'dazun bata ji motsin ta.

" Yayah na 'kiran ki...."!
Haka kawai Raihana ta fa'da sai ta juya ta wuce abinta.

Tsam Zaitoon tayi tana tunanin dalilin da zai sa ya kira tan..sai kuma ta tuna ai 'diyar ta na tare da shi..babu mamaki bacci tayi yake so a 'dauko yarinyar shine ya kira Raihana a waya.
Wannan duk zuciyar ta ne ya raya mata hakan ba dan tana da tabbas kai ba, amma dari bisa dari zuciyar ta tayu na'am da batun.

Ji tayi badan tana son 'dauko abarta ba da bb abinda zai sata zuwa.
Bada son ran ta ta fito ta nufi 6angaren na sa ba.

Tunanin ta kawai ne ya bata har yanzu suna can tunda duk iya da'dewar da tayi bakin window bata ga fitan su ba.

Sai dai tana sa 'kafa a parlon nasa ta fahimci manufar 'kiran da akai mata...dan babu laifi 6angaren yy 'kura...a tunanin ta dalilin kiran kenan..domin rabon ta da 6angaren har ta mance.

Ba wai wani 'kura ne na har azo a gani ba, amma a yanayin da tasan yake tafi da rayuwar sa tasan dole  zaiga muhallin nasa tamkar dattin dunia aka tara masa.

Bata wani jira ko neman inda suke ba kawai ta fara aikin ta tana yi tana tura baki cike da jin haushi...( Ni kuwa nace kede kk sa kanki 'yan mata...).

Rayyan kuwa ko da ya hau saman Ammin Marwa ka'dai ya tarar dukun'kune tana ajiyar zucian kukan da tasha.

Yayi tsayuwan kusan mintina uku batare da ya furta komai ko kuma motsin kirki ba.

Duban Marwa kawai yake yana jin tausayin er kanwar tasa na ratsa shi.
Bai san cewa har haka take so da 'kaunar Sultan ba sai yanzu, ya kuma gama fahimtar ko a zaman auren su zama ne sukai na triangular ita kadai ke son shi shi hankalin sa na wani waje can daban.

Sai yanzu ma ya fara tunanin tabbas akwai wata manufa game da zaman auren Sultan da Marwa ba sbd Allah ya nemi auren ta yake kuma zama da ita ba.

Tausayin ta ne ya kama shi sosai, yana son sistern sa yana kuma tausaya mata..hakika so masifa ne.

Mufee ma Marwa ta 'kurawa idanu sbd 'kanta na 6oye cikin 'kafafun ta da farko bata gane wace bace.
Sai daga baya ta fahimci Marwa ce.

Nuna ta tayi da yatsa ta dubi fuskar Rayyan tace..." Anty..."!
Tana mai nuna masa ita.
'Yar murmushi yayi kawai ya juya ya koma 'kasa bai tsaya ba kawai ya sake komawa 6angaren sa ganin bai ga Zaitoon din ba sai yy tunanin ko batanan ne ko kuma wani uzuri daban ko kuma halin ne ya motsa, cikin ukun dole yasan daya, hakan yasa ya yanke shawarar komawa da yarinyar 6angaren sa idan ya gama shiryawa sai su fita tare dan shi kansa yana bu'katan hutu, ko kuma kawai ya mi'ka ta gidan Anty Madeena...tunda bai ga alamun akwai mai cikakkiyar natsuwa cikin gidan ba a wannan rana.

Yana shiga yaga yanayin iskan 6angaren ma ya canza banda tsab da ya ga ko'ina a parlon yayi.

Dube- dube ya fara dan gano wanda ya aikata hakan bai ga kowa ba..a hankali ya fara takawa har ya kai rabin parlon sai yaji motsi daga bayan sa.

Yana shirin juyawa sai yaji Mufee tace" Mammiii..."!
Cike da farin ciki cikin sautin muryar ta.
Waigowa yayi da sauri, nan yaci karo da ita, daga kitchen ta fito hannun ta rike da roba da mopping stick.

Yadda Mufee ke zillo a hannun sa ya sa ya sau'ke ta da gudu kuwa ta 'karasa wajen Zaitoon dama gatanan ne tamkar a takure tun dazun bata saki jikin ta da shi ba, shi kuma a dole me 'diya 'karfi da yaji yake 'kokarin janta a jiki.
Dan ma yanzu ba kamar baya ba, bata gudun sa sai dai akwai rashin sabo.

Zaitoon rungume abarta tayi tana mai dur'kusawa gaban yarinyar ko sake kallon inda yake ma bata yi ba.
Murmushi kawai yayi har ya juya zai shiga 'dakin sa sai yaji abin da Zaitoon ke tambayar yarinyar.

Domin hannu ta kai cikin rigar ta ta shafo cikin ta...a hankali tace" _Kin sha Tea din...?"_
Yaso yaji amsar da Mufeeda zata bayar amma bai ji ba sbd da kai ta amsa ta.

Kuncin ta Zaitoon ta kamo duka biyu har sautin muryar ta na canzawa dan bata ji da'di ba har ranta.
" Ai ke 'din ce mama na, son yawo ne da ke, kinsan Tea kk ce min zaki sha har na fito dan ha'da mk tea din kuma sai ki kama ki bi wani mutum can daban alhali ba lalle ne ya fahimci abinda kk so ba.. yanzu gashi kin zauna da yunwa tun 'dazun abanza..."

Cak ya tsaya..batare da ya waigo ba.
" _So...wani mutum can daban!...nd she means me..._ "

Wani murmushin mugunta ne ya 'kwace masa, har ya 'daga 'kafa zai cigaba da tafia sai kuma ya juya ya dawo baya.

Tuno wani abu ya sa ya sake juyawa ya shiga 'dakin sa ya fito rike da makullai a hannun sa.

Lokacin da ya fito rungume ya tarar da Zaitoon da Mufee...Mufeeda na fa'din"..Mammi...Anty..."
Shi dai ba wani fahimtar maganar yarinyar sosai yake ba amma yaji Zaitoon na cewa" Tana can bari in gama aikin nan sai in kaiki wajen ta...".

Gaba ya wuce yana sake fa'da'da murmushin sa.
Fita yy ya rufe 'kofan ta waje ya shige motar sa yy gaba...da yake yasan kitchen 'din sa bayi da kofa ta waje dama 'kofan palor ne ka'dai mafitar 6angaren kuma ita ya rufe.

Hankalin sa kwance ya ja motar sa ya fice ya bar gidan zuwa can gidan sa na asali.

Zaitoon bata san me ya aikata ba sai da ta gama gyara ko'ina har 'dakin sa da da 'dayan 'dakin ta tsabtace su sbd ta riga ta saba yanzu 6angaren ba bakon ta bane takan iya shiga ko'ina illa 'dakin Amra ka'dai.

Kalmar ta ke faman yi masa yawo aka, yana kuma soya masa zucia, _wani mutum can daban..._ har wani 'daci- 'daci yake ji sbd takaici.

_Zanyi maganin yarinyar_ .... sai yy 'kwafa...yayi hakan yafi sau shurin masaki.
Sam bai san yaushe Zaitoon zata daina raina shi ba, yarinyar Bata girmama shi sam sam...har sai yaushe zata daina yi masa wasu abubuwan tamkar shi 'din matsayin tsaranta yake ne.

Kwata- kwata bai yi niyyan komawa ba, ada niyyar sa sai ta yini ta kwana a 6angaren ita kadai amma tuno Mufeeda dake tare da ita da kuma abinda take so ya sa shi jin bazai iya ba.

Amma dole ne sai yy maganin Zaitoon hankalin sa zai fi kwanciya...haka ya ayyana sannan ya jinjina kansa cike da gamsuwa.

Bai da'de ba ya sake dawowa gidan hannun sa rike da babban leda ya bu'de ya shigo.

Zaitoon dake zaune a palor Mufee kwance ajikin ta ta rungume ta sosai.
Ko dago idanu bata yi ba balle ta damu da sanin wanda ya shigo dan tasan shine bayan tsinkayar sautin sallamar sa ciki- ciki tamkar dole aka sanya shi.
Zuciyar ta cike take da haushin rashin samun 'kofa a bu'de da batayi ba..ta kuma san shine kuma da gayya yy, hakan yasa ko kallon inda yake bata yi ba balle ta nuna alamun tasan da shigowar sa.

Babban abinda ya 'kara zafafa takaicin ta shine duba 6angaren da tayi bata kuma ga ko alamar kayan tea ba kuma yasan Mufee nason sha ya kuma san bai da shi anan amma duk da hkn ya rufe su yy gaba abinsa batare da ko tausayi ba acewar ta.
Mufeeda kuwa da yunwa ya isheta ta da 'kananun kuka tayi bacci.

Shima Rayyan din bai iya ya mata duba sau biyu ba ya dauke kansa, amma yanajin dole fa sai ya tabbatar mata da cewa shi din fa ba wani mutumi can na daban bane kamar yadda take fa'da...dole ne sai ya koya mata hankali.
Chapter 180 · 0% Book details