Sashe 97
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Bangaren Rayyan koda ya koma sashen sa kan kujera ya yada zango zuciyar sa na masa tu'ku'kin ba'kin ciki da takaicin Zaitun..a ransa yake jin haushin ta sosai kan yarinyar tata...bai cika shiga sabgar da bata shafe shi ba but akan yarinyar nan duk sun dulmiyar da shi cikin lamuran su bai kuma san yaushe hakan ya faru ba, haka kawai yake tsintan kansa cikin lamuran rayuwar su, ko yanzun ma kwafa yayi cikin ransa ya gama yanke hukuncin sai ya sa an kai yarinyar makaranta kodan ya ga yanda zatayi in ma mutuwa ne sai dai tayi sai kace 'diyar ta ce ka'dai 'ya a dunia.
Washegari da safe da ya shigo gaida Ammi nan cikin natsuwa ta ringa nuna masa rashin dacewar abinda ya aikata jiyan inda Tace dashi kar wai kaga dan ta haihu ta hanyar da bata dace ba ka ringa aiban ta mata abinta, babu wanda zaka ga ya haifa kuma yace baya so balle ma ita da nake da ya'kinin zargi kawai muke har 'din nan bamu san gaskiyar lamarin ba, babu mamaki 'kaddara ce ta hau kanta har hakan ta kasance, iya zaman mu ban ta6a cin karo da wani abu da ya shafi rashin natsuwa tattare da ita ba, shiyasa idan ka zauna da mutun ba wai halayya ta zahori ce kawai abin dubawa ba, akwai halayyar ba'dini da wani lokaci kai da kanka ma baka san kana aikatasu ba kuma Alhamdulillah ban ta6a samun Zaitoon da halin da bai dace ko guda ba dan haka bamu da hujjar aiban tata ni dai har ga Allah ban ta6a yi mata kallon watsatsiya ba..."
Baki ya kya6e gami da fa'din " Ammi ai ba gane su ake yi a fuska ba...domin munafukai ne".
" Ba ka dai da hujja tunda baka san komai game da ita ba"
" Munafuncin kenan ai Ammi bayaga haka meyasa zata 6oye miki asalin ta iya zaman nan..da tana da gaskia bazata ta6a yi hakan ba.."
" Ba ni kadai bace, bama najin ta ta6a bawa kowa cikakken labarin asalin ta hakan ta za6a, ta za6i sirrinta tarihin ta ne kaga kuma bamu da hujjar tilastata.
" Kuma Ammi haka zamu cigaba da zama da ita bayan bamu san wace ita ba...?"
" Da me hakan zai rage mu..?"
" Babu komai, kuma har azuciya ta naji na yadda da ita dan haka sanin asali kowace ita bashi ne gabana ba, duk lokacin da ta shirya sanar da ni nima a shirye nake inji..nasan halin 'yan Adam yanzu sai.a hankali sam baka sanin mai kaunar ka amma na jima da kyuatatawa yarinyar nan zato kuma Insha Allahu bazata bani kunya ba, kaima abinda nake so da kai shine please Rayyan ka tsarkake harshen ka bana jin da'di ace dan cikina ke yin irin hakan, abinda kk yi 'din sam baya mata da'di haka kuma nima idan bazaka tayata son 'diyar ta ba toh pls ka cire idanun ka akan su sam banso in sake ji ka aiban ta mata yarinya.. shiyasa fa ta wannan fannin Sultan yayi maka zarra, sam babu ruwan sa da rayuwar kowa, yanzu agidan nan ka ta6a ji ko ganin sa yana ma wani fa'da ne, babu ban ta6a ji ba..amma kai indai akaji ko ganin tashin hankali daga yarinyar nan in aka bibiya da sa hannun ka aciki, 'kaddara ai tana kan kowa kuma babu wanda ya san ta inda nasa 'kaddarar zata zo masa so ka daina 'kara mata zafi..."
Shiru yayi ya sunkuyar da kansa.
" wai zafi....hmm ai sai dai ta 'kone amma sai yaga 'kurewar iskancin ta...
Ammi kuwa ta cigaba
" Yanzu alal misali kai, matarka ba ciki ne da ita ba, Allah ya sauke ta lafiya ace wani ko wata ya sa ma 'dan agaba da zagi, cin mutunci ko aibantawa da sunan shege ya zakaji..?"
A zabure ya dubi Ammi yana fa'din" Haba Ammi...haba dan Allah, da kanki kike fa'din irin wannan maganar kuma..?"
" Misali na baka, ba gashi kaima kaji babu da'di ba, ai haihuwa duk haihuwa ce, 'da kuwa ko wani iri ne abin 'kaune yake ga mahaifan sa, 'kaddara kaine Zaitoon yanda zaka rinka ji idan ana kira ma 'da da suna shege kusan kowacce rana...?".
" Insha Allahu ma babu wanda zai zagar min da, ai akwai bambamci..."
" Hmm "
Ammi tace
Yayin da shi kuma ya shiru kawai ya kawar da kansa gami da lumshe idanu, imagining yake irin hukuncin da zai iya yiwa wanda ya aibanta masa 'da kamar yadda Ammi tace..sosai yaji babu da'di amma hakan bai sa ya mance da 'kudurin sa ba..A hankali la66an sa suka motsa wajen furta" Ammi tog batun makarantar fa..".
inda yy maganar yana murmushin mugunta da shi ka'dai yasan ma'anar ta...ba abinda yafi 'kauna irin yaga ya 'kuntata zuciyar Zaitun yaga tana zubda 'kwalla sbd wannan 'diyar ta ta abin na sa shi nishadi matu'ka.
Toj akan irin yarinyar nan ma ana 'kwalla ina ga in ya kansace ta hanyar halak
Aka samu haihuwar?
Ajiyan zuciya Ammi ta sauke sannan tace" Ranar monday Insha Allah za'a kai Mufeeda makaranta.."
" Monday..ta amince kenan..? dan nasan dole sai da amincewar ta sannan zaki yanke hukunci.."
" Ba dole ba Rayyan ita da 'diyar ta, ita ke da iko da abar ta ai.."
" Lalle kuwa, ta kyautawa kanta ai, amma ni ko bata amince ba na riga na yanke hukunci domin haka kawai nake ji araina inada iko da yarinyar dan haka ta amince ko bata amince ba za'a kai yarinyar skul ba za'a biye shirmen ta ba".
Da sauri Ammi ta kalle shi..." Did I heard u said ko bata amince ba..? thaugh yanzun nan muka gama magana da kai kace ka daina irin abin nan...?"
Murmushi ne ya wadaci fuskar sa, yatsan sa 'karami na 'karshe ya 'dago yayin da saura ke kalmashe yace da Ammi" Wannan ka'dai ne kuma Insha Allah shine na 'karshe.."
Yayi maganar yana 'ko'karin mi'kewa tsaye".
" Baka tambayi wace makarantar bace naga kana shirin mi'kewa".
Gira ya ha'de tare da fa'din " toh ni Ammi me ya shafe ni..wannan ba shirgina bane ai..ba dai ta amince ba ai shikenan".
" Um-Um fa Rayyan me yake damun kane wai?"
Kallon cikin idanun sa tayi daya zuba mata su tana 'dan ha'de rai tace..." kai nake so ka kai ta nd that's Final.."
Fasa tashi yayi ya hade rai sosai yace" Gaskiya Ammi monday kinsan banda lokaci..."
" Zan ma Huzaifa magana ko kuma James 'dayan su ya kaita ba shikenan ba.."
" Ba shikenan ba kai din dai da nace kai din zaka nemo lokacin dole Rayyan kaje da kanka...ni friday zan tafi Abuja ka sani kuma sai Upper week zan dawo badan haka ba ai da kaina ma zanyi basai na nemi taimakon ka ba amma ganin na isa da kai ne yasa na wakilta ka in kuma bane ai shikenan, Alhamdulillah ma tunda ba kai ka'dai gareni ba".
Ta 'karashe maganar tana kawar da kanta.
Da sauri ya gayra zama jin furucin nata abinda bai saba ji daga bakin ta ba.
" Yah Subhanallahi, Ammi maganar fa duk bata kai nan ba, indai makaranta ce wallahi zan kaita dan Allah kiyi ha'kuri"
'Yar murmushi tayi tana dawo da kallon ta gare shi.
" ko kaifa, abinda nake so da kai kawai shine kayi ha'kuri kaji? ka daina biyewa zuciyar ka kana aikata abinda nasan ba halayyar ka bace dan nasan ba haka Babana yake ba amma na lura ka jima da bawa shai'dan damar sarrafa maka zucia".
Kai kawai ya girgiza a hankali yace" ba haka bane Ammi na, amma Insha Allah zan yi kokari in ga ban cigaba da aikata abinda kike zaton na sauya ba.."
" Masha Allah..ina ro'kon Allah ya albarka ci rayuwar ka da albarka, ya wadata zuciyar ka da tsoron sa.."
" Ameen ya Rabbir raheem..thanks Ammi."
Daga haka ya mi'ke gami da barin parlon Ammin a hankali yake taka stairs 'din...ransa yake jin duk babu da'di sbd kalaman Ammin na 'dazu, sam bai saba da jin irin wancan kalamin daga bakin ta ba.
Yana zuwa gama sakkowa ya tunkari corridorn da zata kai shi uzuwa ga Parlorn downstairs anan parlorn ya tarar da ita suna wasa da Moofy tana 'dan guje mata Mufeedan kuma na binta tana son kamo ta suna dariya dukkan su...da alamun basu tare da wata damuwa.
Duba 'daumya yai musu batare da ya dakata da tafiyar tasa ba ya ratso ta tsakanin su zai wuce
Cikin rashin sa'a Moopy dake faman dariya ganin mutun kawai sai tayi saurin kama 'kafar sa 'daya ta ri'ke tana dariya mai matu'kar birgewa...shikan sa dariyar yarinyar ya matu'kar birge shi amma yadda yaji zuciyar ya amsa da fa'duwar gaba gami da bugu akai- akai ya sanya shi kawar da batun birgewar dariyar yarinyar ya bibiyi kadin zuciyar sa.
Cak Zaitun ta tsaya da tata dariyar domin tasan ba alkhairi hakan zai haifar ba ta riga tayi masa shaidar mugunta kuma bai ta6a karyata tunanin ta ba daidai da 'kwayar zarra in dai akan su ne...
A sukwane ta fara 'karasowa wurin da suke tsayen domin 'dauke 'diyar ta musamman ganin yanda Rayyan ya 'dime ya ha'de ransa sosai, cikin rashin sa'a kafin ta 'karasa tsakiyar 'dakin shi kuma Rayyan yy saurin janye 'kafar sa a hassale daga ri'kon da Moopy tai masa yayi gaba yana sakin 'karamar tsaki, take Moopy ta fa'di sanadin jan 'kafar da yayi ta buga bakin ta 'yan ha'koran dake bakin suka bugu da tiles suka datse mata la66anta sai jini.
Razanannen kuka ta sanya daya maye gurbin dariyar ta, yayin da bugun da 'kirjin Zaitun ke yi ya sanya ta zaman dirshan a wurin ta janyo ta ta rungume a 'kirjin ta itama sai hawaye...cike da tausayin 'diyar ta azuciyar ta take shafa bayan ta amma babu alamun kukan ta zai tsagaita anan kusa.
Rayyan kuwa ko waigowa bai yi ba ya fice abinsa tamkar ma bai ji kukan yarinyar ba, duk da can 'kasan zuciyar sa yana jin babu da'di, yana jin rashin natsuwa yana jin tamkar bai kyauta ba.