Sashe 217
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani tangamenen gida aka kai Marwa da fa'dar irin tsari da girman sa ma 6ata lokaci ne.
Amma su Anty da kansu sun yaba sosai tun ma ranar da suka kawo kaya.
Sun kuma samu tarba mai kyau daga Hajiyar Adam, domin gidan ta aka fara kai Marwa kafin gidan mijinta.
Kuka kawai Hajia Talatu ta sanya, lokuta da dama idan ta tuna abinda ta yiwa Zaitoon ko ita ka'dai ce cikin 'daki sai taji kunya ta kamata.
Sai gashi ashe ma Shaheed din Zaitoon tsoka da jini suke ta yadda babu wanda ya isa shiga tsakanin su sai wanda ya ha'da.
'Karin abin kunya ma yau gashi dalilin ita Zaitoon din Adam ya samu kamilalliyar matar aure 'yar gidan mutunci da nagarta.
Hakika kowani dan Adam nada tashi kalar tasirin cikin rayuwar kowa.
Matukar mutum ya shigo cikin ka rayuwar ka toh ka mutunta shi, domin Allah shi kadai ne yasan manufar shigo da shi cikin taka rayuwar.
Anyi addu'a sosai da fatan samun zaman lpy ga juna sannan aka mika amarya gidan mijin ta.
Gida kam tabarakalla komai yayi...hadda abinda bai yi bama yayi sbd kyau da tsaruwar sa.
Sauran abubuwan da ba'a kammala gyara mata bane washe gari aka tashi da aikin su nan ma Anty Madeena tayi kane kane ta hana Zaitoon yin komai.
Taso taje taga maman Abdul amma Rayyan yaki bata dama acewar sa babu inda zataje dan yasan aikin kuka kawai zata je tasha abanza.
Kafin la'asar suka fara niyyan komawa.
Domin Rayyan ne zai koma da su, ya kuma fara azazzalan su akan su fito su wuce.
Marwa kuka, Zaitoon kuka, Anty Madeena har haushi suka bata tamkar ta doke su hk taji.. tun tana ban baki da rarrashi har ta fara masifa.
Dama tun agida wajen yiwa Marwa nasiha tafara masifa ganin yadda Marwa ke kuka 'karshe ba ama kammala da ita ba ta fito.
Sanin halin Rayyan da tayi yasa tun ma kafin ta isa wajen Mota ta rage kukan sai dai Marwa kam babu ma alamun zata tsagaita.
Rayyan sau 'daya ya kalli Marwa bai 'karaba sbd wani mugun tausayin ta daya fizge shi.
Abinda yayi niyyan fada mata ma kasawa yayi.
Sai dai kukan nata ya mugun tsaya masa arai sosai.
Shi dai ga Ubangiji ya dam'ka ta, amanar ta ya bawa Allah sannan Adam, yasan duk abinda zai same ta sai in Allah yaso, so babu wani mahalukin da zai iya cutar masa da yar uwa face da yardar ubangiji...dan haka yana mata fatan dacewa, yana mata fatan alkhairi, fatan zaman lpy da kwanciyar hankali, fatan wannan auren ya kasance mata yanki na jin dadin rayuwar ta ya kuma sada ta da aljannar sa ma'daukakiya.
Tunda suka 'dauki hanya babu wanda yace komai acikin su.
Hatta da Anty Madeena ma shiru ba ta furta komai ba, Zaitoon ajiyan zuciya kawai take saukewa, yayin da Anty Madeena ke sauke gauron numfashi.
Zaitoon kam tasan ba 'karamin kewar Marwa zatayi ba, domin tun ranar da Allah ya ha'da fuskokin su basu sake rayuwa a mabanbantan waje ba har sai da ta tafi garin su sannan...a koda yaushe suna tare da juna...suyi shawara tare, suyi sirrin su tare, suyi fada su kuma yi dadi.
Marwa bata ta6a nuna mata banbamci ko girman kai ba shiyasa take kaunar ta sosai...amma karo guda an 'dauke mata Marwa an kaita wani gari can daban.
Suna shiga Kano Rayyan ya dire su a 'kofan gidan Ammi yayi gaba da matar sa.
Dayake lokacin dare ya riga yayi wanka suka yi suka ci abinci dan sun taho da take away sai kawai sukayi shirin bacci.
Ita Zaitoon ko abincin ma ba wani na kirki ta ci ba yana lura da ita.
Ga haushin 'kin barin taje taga Maman Abdul da yayi banda masifar da yayi mata ma hakan yasa ta juya masa baya.
" Kinsan ban so ko?"
Ya fa'da batare da ya waigo ya dube ta ba.
Da sauri ta juyo tana tura baki gami da 'ku'k'kuni taki ma duban fuskar sa.
" Wai fushi ake da bawan Allah..?"
Kawai sai ta sanya kuka.
" Ohh Allah Zaitoon me ke damun ki ne kwanan nan..abu kadan sai kuka..".
matsota yayi sosai jikin sa ya rungume ta, cikin kunne ya ra'da mata" kin wani damu akan Marwa.. ba aure tayi bane, kiyi mata fatan alkhairi yafi kukan nan, ke da kika yi auren ki kika ce kinji kin gani zaki bar kowa kizo ki zauna da Rayyan waye yace miki zai biyo ki ko ya mk kuka...? "
Ture sa ta fara yi tana mai 'kara sautin kukan ta sosai..." Ni yaushe nace zan zauna da kai?"
" In tuna mk ne?"
Shiru tayi ta cigaba da kukan ta.
" Still dai..bana son kukan sam..in wani abu kike so pls ki sanar da ni..".
" Banga Inna ta ba, kuma naga kowa amma banganta ba...".
" Abban gidan ta ne bai da lafia shiyasa bata zo ba ki kwantar da hankalin ki..."
Ya bata amsa nan take.
" Ka min masifa kuma ka hana ni zuwa in ga maman Abdul...?"
" Wannan kam ban amince ba, nasan in kun hadu banda kuka babu abinda zakiyi shiyasa bazan yadda kije ba...ki bari ba yanzu ba..kinji..Insha Allah watarana zaki je idan na tabbatar kin girma kin daina kuka".
" Ni nace zanyi kuka ne?".
" Da ban sanki bane yarinya..sai kice komai..".
" Hope ba abinda ke damun ki, naji jikin ki da zafi sosai..".
Shiru tayi.
" Ko in mk allura.."
Da sauri ta girgiza kanta.
Shiru ya dan biyo baya.
" Kinsan mene?".
Ta girgiza kanta.
" Kina bani mamaki wani lokaci"
Da sauri ta 'dago ta dube shi yace" Yes mamaki sosai fa..".
Cigaba da duban sa tayi, duban da shi da kansa yasan 'kage take taji abinda zai fito bakin sa.
" Abinda har kullum nake tsammanin inji ya fito bakin ki ban ta6a ji kin furta ba...ban kuma san dalili ba, ko baki da ra'ayin sane ban sani ba..".
Duban fuskar sa kawai take yi tamkar ance mata amsar maganar tasa na kwance saman fuskar sa ne.
Saman idanun ta ya sumbata ta lumshe idanun sai dogayen eye lash dinta dake dan motsawa
" Meyasa baki ta6a yi min magana akan karatun ki ba? Ko baki ra'ayi..?"
" Kai nake jira inji kayi maganar ai..".
" In kuma ban yi bafa?".
Tace" Shikenan"?
Hancin ta yaja, nifa ina so kiyi karatu ki zama likita kamar ni, Feefy na ta zama Barrister kamar ni itama m...sannan zaki haifa min sojoji da yawa inta ganin su ina jin dadi...".
" Hmm" Kawai tace bata ce komai ba.
" Amsar ki kenan..hmm?".
" Toh ni me zance?"
" Kice toh Insha Allah sai nace sun isa...kice kinji kin gani sai kin cika min burina kamar yadda kk jajirce kk ce kinji kin gani sai kin cika min burina na kasanewa tare da ke.."
Da sauri taja hancin sa.
" Sannu sarkin sharri..."
Ta fa'da tana mai dan jin nawi gami da murmushi.
Yace
" Ba wani sharri...barni in fada gaskia..ni kadai nasan irin jajircewan da kk fa".
Ita dai in ba sharri irinta Rayyan ba yaushe tace taji ta gani sai shi.
Ranar sun sha hira sosai kafin sukayi bacci.
Washegari kuwa sassafe ta danna 'kiran Marwa...bata same ta kan layin ba.
Kira kusan uku babu respond...hankalin.ta sai ya kasa kwanciya.
Shaheed ta 'kira yana 'dauka tace ina kwana Yayah..wai ina Marwa ne sam na kasa samun ta kan layin ta.
" Bacci take Zaitoon sai dai ko zuwa anjima kadan".
" Bacci kuma har yanzu, Marwa fa ba haka take ba Yayah...".
" Kinsan in ki'da ya canza dole rawa ma zai canza, barta tayi bacci sister..anjima zan ha'da ku...".
Alhamdulillah duk yadda 'yan uwan Marwa ke mata fata da buri samun sauyi sama da gidan ta na baya Alhamdulillah Adam bai bar burbushin da zai basu damar tunawa da baya har ace gara na baya ba.
kowa sai san barka yake, ana fadin Allah yasa a 'dore haka nan, domin Marwa ta samu farin ciki da kwanciyar hankali.
Soyayyar su suke zubawa gwanin birgewa.
Ita kanta Zaitoon abin na birge ta sosai, duk da itama yanzu ba baya ba wajen kula da mijin ta...amma tafi kaunar ta kira waya taji Marwa ta kyalkyata daria fiye da komai..ji take duk damuwar ta ta yaye tass..a kullum burinta shine taji Marwa cikin farin ciki.
A hankali cikin ta ke 'kara girma dan a halin yanzu wata bakwai kenan cikin amma inka gansa bakace ya kai hakan ba, sai dai ya hura ta tako ina, kuma babu abinda ya canza mata abu guda ne kawai bata so shine kifi..amma normal take cikin bai takurata ta kowacce fanni ba.
Tuntuni aka dawo da Mufeeda wajen ta, domin Ammi tace gidan zai na mata shiru tunda shi Rayyan ba mai zama bane, amma tana tunanin hidima da Mufee ga kuma ciki ma.
Hakan yasa ta ha'do su da 'daya daga cikin masu aikin mai 'dan madaidaitan shekaru kuma wacce tasan sun riga sun sha'ku.
Batun makarantar ta kuma Ammi tace da zaran ta haihu zata fara shi.
Hakan bai kawo ma Zaitoon matsalar komai ba domin ita ba mai shiga sabgar mutum bace kuma abu da yawa bata bari ta jira sai anyi mata tuni zata mi'ke ta aiwatar sai 'dan abinda ba a rasa ba.
Mufee yanzu an girma baki ya fito sosai surutu kuwa sai abinda ya yi gaba.
Kusan kullum sai sunyi waya da Antyn ta, ayi video call da sauran su idan ta dawo School.
Marwa kam ta murmure abinta da ka ganta kasan ta samu kwanciyar hankali.