← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 218 OF 218

Sashe 218

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

wata uku da auren su Adam ya kawo ta da kansa suka gaida su Ammi da sauran yan uwa kwanan su 'daya suka koma ai kuwa tun lokacin Zaitoon ke faman tsokanar ta wai bata yadda da ita ba.
" Za ma kiyi ki gaji ne yan mata...ni babu wani abinda nake da shi, sai kace ke..".
Duk da maganar nayi mata wani iri amma haka take chigaba da tsokanar ta..amma inta kebe banda tunani babu abinda take yi.
Wai dagaske ashe itace zata haihu, shine da farko Rayyan yace mata shine ba ita ba...." banda shirmen ki Zaitoon ina kk taba jin namiji ya haihu".
Wata zuciar tata ta ankarar da ita.. a lokacin duk tunanin hakan bai zo mata ba ta amince da maganar sa sai daga bata ta sake tabbatar da cewa lallai shirmen ta ya kai intaha.
Ita bakomai yake bata tsoro ga haihuwa ba sai yadda taga Mahaifiyar Mufeeda, abin idan ta tuna yakan bata tsoro.

Domin Rayyan tun bai fahimta ba har yanzu ya fahimci manufar tsoron nata ya kuwa yi mata nasiha sosai, ya nuna mata bambancin zanen 'kaddara, kowa da kalar tashi yake tafe, ba duk Allah ya halicce mu da 'kaddara iri guda ba kamar yadda bai yo mu da kalar fata, hali da zucia iri daya ba.
Ba lallai bane dan abu ya sami wanin ka kai ma kayi tunanin zai iya samun ka.

Da irin nasihun nan ya ci galaba akanta ta fawwalawa Allah komai.
A halin yanzu fata da burinta kawai shine Allah ya sauke ta lafia sai kuma tsananin son ganin Innar ta da take.

*****
" Ki cigaba da 'daga min hnkl kiga ko hkn zai baki nasara...zancen zuwa ko'ina ai ba tun yau na sanar mk babu shi ba, na soke ba yanzu ba kin manta hk nace...?"
Ya 'kare maganar da zuba mata idanun sa masu matukar tasiri a zuciyar ta.

Kasake tayi tana kallon sa itama, dagasken kuma yanzu hawaye ke sau'ko mata bb 'kakkautawa.

Bata san cewa la66an ta sun motsa har ta jefeshi da tambayar da ke cikin zuciyar ta ba sai lkcn da taji cikkakkiyar amsa daga bakin sa.
" Kin san bana magana biyu Precious.. pls ki bar zancen nan ba yanzu ba...".
A iya sanin ta Rayyan ba ya son ganin ko kwayar zarra na hawayen ta musanman na bakin ciki, amma meyasa yau 'din yy mata banza ya manna mata hauka har hk.

Tashi tayi kawai batare da ta sake tanka shi ba ta fice fuu ranta na sake yi mata 'kunci.

Rayyan sai yy 'yar murmushi cikin ransa yk jinjina rigima irin tata, wani lkc in tayi abu ko Mufee ma albarka.
Bayaga hk taya take tunanin zai 'kara barin iyalin sa 'daukan wancan hanyar with that same yanayi? Sam abu ne mai wahala ya iya barinta tafia cikin wanna halin...zasu je amma ba yanzu ba..yau kam kici kukan ki ki more yan mata".

Maganan sukayi da Marwa ashe ita kuma ta labartawa Ammi.
Tana zaune sai ganin 'kiran Ammi tayi nan take bata baki da ban hakuri akan ta bari ta haihu tukunna, ta daina 'daga hankalin ta, ai kamar yanzu ne zata je, amma ta tabbatar duk yadda zata kai ga 'daga hankalin Rayyan bazai bari taje a wannan yanayin ba, ba kuma wai dan bai san 'kaddara bane a a kawai bazai samu nutsuwa bane koda ya barsu tafiyar sannan zai ri'ka tuna baya.

Gashi ma doguwan tafiya ce babu dadi...".
Tace" bakomai Ammi...nima ban matsa ba..kawai dai..".
" Nasani Zaitoon..ai nasan halin ki, ki 'kara hakuri kinji, kuma kar ki riqa biyewa fushin Rayyan har kike sawa aranki irin na baya, kinsan shi zafin rai gare sa amma yana da sanyin hali a mafi rinjayen lokuta".

" Hakane Ammi..
Nagode sosai" .
" Bakomai 'diyata...Allah ya albarka ce ku baki daya..."
" Ameen Yah Allah".
" Agaida min waccen yar jaridan idan ta dawo"
Suka yi daria atare.

Zaitoon bata sake tada maganar ga kowa ba hatta shi Rayyan din.
Da kansa sai da yayi mamaki.
Haka kuma yadda take kulawa da shi da bukatun sa abin ba karamin birge sa yake yi ba..ya kuma kara dawwamar da kaunar ta cikin ransa.

Shi fa har kullum ya kan zauna ya ta tunanin me zai yiwa yarinyar nan ne ya biya ta abinda ta yi masa, ta bashi 'diya akaro na farko domin bisa taimkon ta ne Mufee ta rayu, ta kula da shi a lokacin da shi kansa bai san waye shi ba, ta bashi farin ciki, ta zauna da shi ta jure dukkan damuwa da bukatun sa sannan gashi tana shirin bashi kyautan wani diya ko 'dan abinda yafi muradi a ahalin yanzu.
Hakika ita din wata ni'ima ce ga rayuwar sa da bazai taba iya raba zuciyar sa da begen ta ba.

Rayuwa na tafia al'amura na tafia musu normal ko ta ina farin ciki ke wanzuwa, hakika bayan wuya akwai ni'imar Allah idan akayi hakuri, ayau ga Zaitoon da yaron ta santalele da shi wanda yaci sunan mahaifin Rayyan Wato Muhammad Sa'ad ita kanta ayadda haihuwar tazo mata abin ya bata mamaki.

Hakika Allah gwanin baiwa ne da hikimomi.
Sosai take godewa Allah idan ta dubi yaron nan, wai ita ta haife shi.
Haka ta hada su da Mufee ta rike abinta tsab.

Sunje gida bayan ta haihu suka yi kusan wata biyu sannan suka dawo gida.

Da yake Marwa bata zo sunan Muhammad ba wai bata da lafia ashe ashe wata 'karuwar suka samu.
Dan kuwa Muhammad nada wata takwas Marwa ta dire musu santaleleliyar 'diya kyakkyawa da ita...Yarinya taci sunan Zaitoon dan Adam cikin ransa yayi al'kawarin sai yawa 'yar 'kanwar nan tasa takwara..ya kuwa cika burin sa cikin yarda da amincewar ubangiji.
Abin ya yiwa Zaitoon da kowa ma dadi, da'din da'dawa ma Shaheed ya hana a 6oye mata suna..little Zaitoon ake kiran ta wasu kuma suce little Zee.
A hankali Little Zee yabi yarinyar dole ya kyale su.

Tuni Zaitoon ta fara makarantar ta, domin SS2 ta fara tana kaiwa karshen shekarar kuwa ta zana waec ta cigaba da karatu.

Tuntuni kuma take wa Rayyan magana akan Arfan amma yaki bata hadin kai kan maganar, bawai dan yana jin haushi ko ya tsani yaron ba, kawai baya son wata harka ta sske hada sa da Amra ne sam..shiyasa yake sharewa.
Kuma yasan Arfan bazai ta6a neman abu ya rasa ba tunda yasan waye mahaifin Amra kuma yasan karkashin sa suke.

Dai- dai da rana guda bai ta6a zuwa duba yaron ko kuma neman jin ya yake ba, kwatsam bayan haihuwar Marwa labari ya iske su cewar Allah ya kar6i ran Arfan sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da yayi.
Mutuwar ta dokesu baki dayan su, domin duk sun san basu kyauta ba yadda sukayi watsi da lamuran sa, basu yi kasa a gwiwa ba suke je gaisuwa Ammi da mukarraban ta amma Rayyan bai yadda Zaitoon ta bisu ba..haka shima bai je ba.
Sai daga baya ya kira mummyn Amra yayi mata ta'aziya.

Ranar da Amra taga su Ammi ba 'karamin kukan nadama ta sha ba, duk da kuwa ta jima da yin nadaman amma ganin su sai ya dawo mata da komai sabo, a duk lkcn da idanun ta zasu kalli wani ko wata cikin ahalin Rayyan bakinta baya iya rike neman afuwar ta kamar yadda zuciyar bazai taba iya danne damuwar ta batare da ta bayyana shi ba.

Ammi tayi mata nasiha sosai itama haka suka baro gidan jikin kowa yayi sanyi.
Rayuwa kenan.
Amra duk ta lalace tayi duhu kamar ba ita ba.
Ita kuma Iyami rashin lpy take sosai, sai an daga sai an kwantar, yayin da lafia ingantacciya ta samu ga Abban su Zaitoon tamkar ba shi ba.
Komai na tafia masa normal ayanzu, sai ci mai kyau yasha mai kyau ya kishingida bisa lafiyayyan shimfida baya da matsalar komai.
Domin Allah ya sanyawa yaran sa albarka sun kuma tallafa wa rayuwar sa.
Shiyasa a kullum yake faman sanya musu albarka, haka cikin kowacce sallar sa addu'ar sa gare su baya taba gajiyawa.

Iyami anje asbiti kusan sati hudu abu babu cigaba hakan yasa likitoci suka sallamo su da shawaran su koma gida a nema mata maganin hausa.

Jiki dai yaki dadi, a kullum abinda zai bullo daban dana gobe.
Ga idanun ta rass zataji zata gani amma babu motsi babu tankawa.
Tana son yin magana akan abu da yawa amma babu dama, haushin hakan in ya cika ta sai kaga tana zubda hawaye.
Kwanakin talatin da uku kwance a gida ranar wata laraba aka wayi gari bata numfashi.
Kwanan ta ya kare, duk wani abu da aka shuka an tafi an barshi nan dunia babu amfani, an tafi can gidan gaskia gidan girbe munana da kyawawan ayyuka.
Sau fatan Allah ya jikan musulmi ya kyautata namu karshen idan yazo.

Bayan rasuwar Iyami da wasu watanni rana guda kawai kwatsam Zaitoon na zaune sai ji tayi an saka wa Bello da Khausar rana wata uku kacal masu zuwa abin yai mata bazata.

Ko da ta nemi jin ta bakin Khausar dariya kawai tayi mata.
" Khausar wai ina Babaji?"
" Yana nan Adda..Allah bai sa da shi za'a yi ba ya musanya min da wannan".
Fatan alkhairi Zaitoon tayi mata da fatan Allah ya nuna musu lkc.
Hakika tafi kowa farin ciki da faruwar wannan lamari.
Bello dan uwan ta ne kamar yadda Khausar take yar uwar ta ta jini.
Ita kam me zata ce da ubangiji idan ba godia ba.
Rayuwar Marwan ta a gidan Shaheed kadai ya ishe ta dawwama cikin farin ciki sai ga wani karin abin farin cikin ma.

Daddy 'karami yana gudun sa ko'ina yanzu dan ko School Zaitoon ba zuwa da shi take ba, Mufee da na da shekara biyar da haihuwa yanzu tana kuma kokarin shiga Nursery 3...amma shagwaban Mufee babu abinda ya canza har yanzu.

Rayyan ne ma mai taka musu birki, domin sau da dama ajiye masa Daddyn sa ake agefe a dauki Mufee a rungume har sai tayi bacci...wani sa'in kuma tace sam Zaitoon take so ta goya ta...haka nan zaka dauke ta ta goya abinta.

Rayyan abin na bashi haushi, saukin daya ma shi Daddy karami hakurarre ne, baki data ya amshe girman ya bar Mufee da shagwaba.
ko bacci suke Mufee zaka gani rungume da Zaitoon shi Dady na gefe yana bacci ko wajen mai aiki.

Da abin ya ishi Rayyan ne ya tarkata kayan ta kaf yasa akaita gidan Ammi wai ankaita hutun shekara.

Kamar wasa tun Zaitoon na ganin kamar wasa har tazo ta saduda ganin fa dagaske yake, yace abin naku hadda shiga hakki ai, bacin ni na hakura an tauye ni abaya sannan babana ba za'a barshi ba sai an tauye shi....yace daga can gidan Ammi inta gama shekarar can gidan Anty za'a mika ta..daga nan sai Bauchi sai wajen Innani, sai kuma Maiduguri..Mufeeda tabar zama gaban ta kenan har sai ta girma ta bar wannan iskancin shagwaban.
Yace Dama Raihana ma tace tana so ta dauke ta dan aikin mijin ta ya koma Italy, so basu ita zai yi su tafi can kowa ma ya huta.
" Toh kuma makarantar ta fa.".
Yace" A hakan zatayi, ba Affan ma na School ba, ko ina take zata karatu ai".
" Ni dai dan Allah kayi hakuri adawo min da yarinya ta, wlh zan daina goya ta zan daina daukan ta ma kwatakwata..".
Ta fada tana share 'kwalla.
" Yace sai kuma kiyi..".
Fita yayi ya barta a dakin taci kukan ta koshi...dan tasan mawuyaci ne ya janye abinda ya fada.

Tammat bi Hamdallah.

Salmerh😍
Chapter 218 · 0% Book details