Sashe 151
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.......Kwanaki na ta tafiya lokaci na shu'dewa, amma an dauki tsawon lkc ba'a saka ranar auren mu da Babagana ba, Baffah Liman cewa yayi ko ma shekaru nawa ne za'a 'dauka suna nan bazai ta6a bawa bawa Babagana aure batare da ya ri'ki kwakwarar sana'ar yi ba, sbd har alkcn Allah bai nufe shi da dacen sana'a ba, yayin da Baffa Liman ke ganin kamar da gayya yake yaki.mayar da hankali ya samu sana'a tunda ga sa'o'in sa nan duk suna da abinyi sai shi.
Ni kuwa zuwa lokacin sosai na 'kagu inga anyi auren duk dama ban furta hakan ga kowa ba hatta Dije bata sani ba, amma ina da dalilai na da ni ka'dai na barwa kaina sanin su...ba wai dan ina 'kaunar sa ba ba kuma wai dan sbd bu'katar kaina ba..amma sosai na 'kagara inga na bar gaban Iyami ko dan in samu 'yancin kaina da kaina.
Gashi yanzu Babagana ya fara zuwa zance, Iyami sai ta tayi min habaici wai sai dai muta bin bango ni da shi kullum amma bata ga ranar auren ba, ni fa bansan me hakan ke nufi ba a zahiri amma har ga Allah maganganun nata na matu'kar 'kona zucia ta.
Shi kansa Bbgana idan yazo ro'ka na yake akan in taimake sa in sanar da Baffah cewa ko babu sana'ar ma zamu iya zama tunda yana nema kullum kuma baya rasa na rufin asirin da yasan zai iya rike mu da shi.
Yace shi bai san meyasa Baffa ya zafafa da yawa ba, ba dan.shine ya haife shi.ba da ya sai yace Ni 'din.ce Baffah baya son bashi, amma mahaifi yake agare shi da ya tabbatar bazai cutar da shi ba.
Ni kaina nasan hakan, na kuma san gata Baffah ke son masa ba komai ba, a yadda yake a yanzu idan aka cigaba a haka har aka yi kasadan bashi aka kuma fara ciyar masa da ita to kuwa zuciyar sa mutuwa zata yi bazai ta6a yun'kurin neman na kansan da gaske ba, amma ya kasa ganewa.
Ni dai idan ya fa'di cewa in samu Baffan kallon sa kawai nake yi da mamakin sa, taya yake yake tunanin zan iya hakan, wace iriyar rashin kunya kenan zan ce na aikata?
Wani sa'in idanu nake 'kwalalowa sai in girgiza masa kaina.
Wani sa'in kuwa ce masa nake ni gaskiya bazan iya ba, sai yace wai in fadawa Yaa Bukar to...sanin da nayi cewa shi ka'dai zan iya samu da maganar ne ya sani amince masa a tunani na zan iya shi 'din sai dai koka'dan da ya dawo naji bama zan ta6a iyawa ba, shine ma ke min mitar hukuncin da Baffah ya yanke kan batun auren namu dan shi a fa'dar sa wai duk shirin sa ya kankama Baffa kadai ke son mayar da shi baya, sam a ganin sa bai kyauta ba, shi aure ai haske ne, yace ko muma lokacin da mukayi auren ai babu wani abin arziki, kusan kullum ma agida muke cin abinci musamnan idan damina ta tsaya dan a lokacin ko'ina babu sau'ki, to da ikon Allah ba gashi tun ba aje ko'ina komai ya daidaita ba har muma zamu iya aurar da wasu..."
Yayi maganar yana kallona ni dai ban iya na kalle shi ba illa murmushi cikin raina nake ayyana da alamu dai Yah Bukar bu'di ya samu.
Bana yawan shiga gidan sa amma a bakin Ummaru nake yawan jin zancen.." Sun ci abu kaza da kaza nakan ji da'di har raina da jin cewa rayuwar 'dan uwa na ta fara sauyawa, ko muma agida ba laifi abincin mu ya 'dan sauya salo ba kamar baya ba gaskiya, hatta Yaaganan mu ma idan taji labarin yazo ta kanzo yayi mata ihsani ta koma gidan ta cikin jin da'di..Iyami kam ai ba'a cewa komai, ni kuwa duk lokacin da ya bani ku'di idan na ajiye bana sake ganin su koda kuwa na canza wurin ajiye ne, to ma ina ne lungu da zan wani iya ajiye ku'di a 'dakin, daga gadon kwangwalar da ke 'dakin da 'yar tabar ma akai shike nan sai jakar kayan sawa na...daga haka 'dakin babu komai to a ina zan ajiye da baza'a gani ba.
Sittira wannan idan sabuwa ce ya siyomin da kasafai ake bar min nema nake na rasa ta, shiyasa kullum nake nan.cikin tsummokarai, idan ya lura da haka ya tambaye ni inda kayana suke kuwa sai ince masa suna nan kawai.
Ban ta6a damuwa da rashin ku'din ba dan dama ni saba kashe su nayi ba, amma rashin kayan na matukar kona zuciya ta, duk yawancin zuwan sa kuwa sai ya kawo mana kaya ni da Khausar da Ummaru a hakan dai nake 'dan samun nasawa.
Bansani ba ko ya lura da hakan ne yasa yanzu idan yazo da kaya zama yake cikin gida yace kowa yayi wanka ya sanyo kayan yana so ya tantance wanda bai iya kwalliya ba.
Hakan kuwa ake yi duk sai mu shiryo cikin sabbin kayan mu dan ya gani, yakan kuwa yaba mana baya yadda a kushe kowa sai dai zai gyara maka inda ka kuskure.
Kayan nan kuwa idan an saka shi sai na kwana biyu nake cirewa, na kance ko da na rasa ma ai dai na mori abu na.
Cikin ikon Allah kuwa sai na lura idan na sanya kayan bana rasa shi ni ke kashe abina...anan na fahimci manufa da dabarar Yayan nawa.
Da wannan dubararcta Yaah Bukar na 'dan fara saka kaya mai kyau nima.
Matar sa ce ma naga tana 'kara wani shan 'kamshi idan tazo gidan namu sai ta ta wani harha'de rai tamkar dole aka sanya ta zuwan bansani ba, a ahakan kuma Iyami tai ta ji da ita tana jan ta a jiki ana nan nan da ita, ni dai kya6e baki kawai nake yi idan yaron ta yazo kusa da ni in 'dauke shi in yi masa wasa idan kuwa bai zo ba nima ban zuwa in 'dauke shi saboda nasan masifa za'a min idan ma naje dan 'daukar sa.
Hamma Bukar bai sake samun damar jimawa a gida ba sai da lokacin damina tayi, lokacin kam ya dawo ya zauna saboda noma amma jefi-jefi sukan je su yo kwana biyu su dawo.
*****
......Lokacin damina lokaci ne mai matu'kar ni'ima da haka kuma mafi yawancin mazauna karkara kan ji da'din yanayi na damina, musamman saboda sukan wadatu da kayan ganye su sarrafa zuwa nau'ika daban- daban...sukan sarrafa su a duk nau'in da suke bu'kata suci su sha ruwa.
Kusan kowa na jin da'din wannan yanayi...sa6anin ni ka'dai, domin mu a gidan mu da zarar damina ta kama to fa babu wani abinci da Iyami zata ri'ka da ya wuce dambu...ni kuma har ga Allah bana so, bana 'kaunar cin dambu sam kuma duk.wanda ya sanyi ya san hakan...amma ita ko ajikin ta sam bata damu ba, inci ko kar inci ba damuwar ta bane ban sani ba mugunta ce ko ra'ayin ta ne hakan kawai.
'Karin abin takaici kuma nice mai 'debo mata ganyen a gonar Abban mu, kusan kullum da na kammala ayyuka na na gida zata tura ni jejin, yakuwa, kalkashi ko kuma zogale in ciro in kawo mata ta shanya wasu wasu kuma ta sarrafa su zuwa wani abin da ciki zai iya 'dauka aci ayi bacci, ba wai dan bamu da abincin da zamu ci ba sai dan iko da isar da Iyami ke da shi a gidan...Yah Bukar yayi yayi da ita akan ta daina tura ni jejin nan musamman saboda abinda ya faru dani shekarar da ta gaba ta amma abanza Iyami kam babu ruwan ta, haka zanje in ciro mata ganyen kullum ta shanya wanda zata shanya wasu kuma ta bawa sirkar ta Azeema yayin da wani kuma ta kanyi amfani da shi a cikin gida.
Abin har ya fara zame min jiki, ba na ma damuwa yanzu, ba kuma sai ta maimaita min ba tuni na saka shi cikin jerin ayyukana na kowace rana.
Shima Yah Bukar gajiya yayi da magana ya 'kyale ta..hakan ma gara shi akan Abban mu, dan shi tamkar ma babu shi cikin gidan namu yanzu, abin nasa ma sai na lura kamar gaba gaba yake 'karawa, yanzu fa komai ma sai abinda Iyami tayi a gidan ta kafa doka ta kuma shimfi'da shara'din ta yadda taso, shi dai nashi ido ne na amsawa yace to ko kuma ya sake jaddadawa.
*****
......Kwance nake rub da ciki saman gado na da shikan sa zan iya cewa 'kara min ciwon jiki yake, wata shekararriya kuma yamutsatstsiyar tabarma ce akai sai wani bargon da ni kaina bazan iya fa'din shekarun sa ba, sam 'dakin babu komai da zaka gani na jin da'din rayuwa amma hakan bai sa 'dakin ya kasance 'kazantacce ba, kullum tsab zaka gansa a share hatta samintin 'kasan 'dakin bazaka ta6a yin shayin zama akai ba saboda yadda nake 'ko'karin goge shi..babban abinda yasa Hamma Bukar ke ji da ni kenan, saboda tsabtar da yake ce ina da ita, har fa'da yake da alfahari akan sam Zaituna bata da 'kazanta shiyasa ko ka'dan bai jin shayin siya mata ko wani irin kaya, baya shakkan wadata ta da sabulai dan yasan ba asarar ku'din sa yake yi ba..idan na tashi wanki kuwa agidan hatta kayan Iyami da su Khausar bana bari kaf nake wanke musu da na Ummaru dake gidan, shima Yayan nakan sha damun sa akan ya kawo kayan sa na wanke masa mana sai yace a a na bari ai Azeema na wanke masa kuma shima 'din duk ranar da ya samu zama da kansa yake wankewa...ni dai ban ta6a yin kwanaki biyar batare da nayi wanki ba sam bana barin kayana su zauna da datti.