← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 218

Sashe 113

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gira 'daya ya 'dage ya dubi Sultan 'din sama zuwa 'kasa 'karshe ya sau'ke idanun sa kan Arfan dake hannun sa yana mi'kawa Rayyan da alamu so yake ya amshi yaron.
'Karfi da yaji yake son ya sake karfafa bond 'din dake tsakanin su...fahimtar haka da Rayyan yayi ya sashi ha'de rai sosai, wani tukukin takaici ya taso masa, da 'kyar ya iya dannewa sai dai bai ma san lokacin da bakin sa ya furta..." Get out of my way..." a tsawace ba.
Ya fa'da ne yana tsare Sultan din sosai.
Ba shi Sultan ka'dai ba, hatta Amrah sai da tayi mamaki matuka, iya tsawon rayuwar da tayi tare da su, bata ta6a ji ko ganin abu makamancin irin haka daga Rayyan ba akan 'yan uwan sa, 'kaunace mikakkiya mai tushe yake nuna musu, amma yau din ta rasa mai ke damun sa kwata- kwata, sai kace wani mai aljanu...?
Ta tambayi zuciyar ta.

Rayyan kam da fa'din hakan yabi gefen Sultan da ya 'dan kauce agaban sa yayi gaba abinsa ya nufi 6angaren sa.

Duk 'din su da idanu suka rakashi har ya kusa shigewa wato Amrah da Huzaifa sai dai banda Sultan da tuni kallon sa ya dawo kan fuskar Arfan.
Fuskar sa babu yabo babu fallasa, kai baka ce ga yayanin da zuciyar sa take ciki ba.
Amma he is burning inside da wannan tsawar da Rayyan ya buga masa...idanun sa akan Arfan yake tunanin...dole akwai wani abu, Rayyan bazai ta6a yi masa tsawa haka nan kawai ba..."
Amrah ce ta matsa kusa da shi cike da damuwa tace
" Sultan wai meke faruwa ne?...na kasa gane kansa tun bayan isar mu hospital ya canza gaba 'daya anya Baby bashi da aljanu kuwa...?"
" Nima aljanun gare ni Amrah zan kuwa tabbatar muku da hakan..."
Zaro ido tayi sosai tana bu'de baki.
Sai ya girgiza kansa.." Kuma dayake ke 'kwa'kwalwar dusa gare ki ni kk tambaya abinda ke damun sa..? Matsayin ki na mata agare shi baki san meke damun sa ba taya kk tunanin ni kuma zan sani..?"

" Haba Sultan bayan ba fa'da min yayi ba ya kake so nayi toh..."
Ta bashi amsa cike da tsantsan damuwa.
" Sam ke de na rasa wace iriyar macece, mijin ki ne fa amma tun ganin sa cikin wani yanayi ai sai ki matsa masa da tambaya ke ko irin kissar nan ta mata baki iya bane...?"
Rai ta hade.
" Kar ka fa'da min magana mana Sultan, Rayyan ne baka sani ba ko halin sa, naga kaima gashi ya maka yanzun nan, shi in ba niyyar yin abu yayi ba ana sashi ne...wannan aikin ai sai dai Ammin sa kasani.."

" Dama daga ina kuke..?"
" Asbiti"
" Doing what..?"
" Allura aka wa Arfan.."
" Kin tabbatar abinda kawai kuka yi asbitin kenan..?"
" Noo...anja jinin mu duka..."
" Har Arfan...?"
" Erh hadda shi..."
Idanu ya lumshe cikin zuciyar sa yace" Tafaru ta 'kare..."

Tsaki Sultan yaja a fili yana bugawa Amrah banzan kallo.
" Allah ke jaka ce...tunanin ki sam baya aiki, ki zauna har lkcn da zai fito fili ya bayyana mk cewa ga damuwar sa nan, a time din zaki fi yadda da cewar ke din jakar ce dagaske kamar yadda na fadi...".

Cikin ransa yace" Zan kuwa yi maganin Rayyan wallhi...da ni yake magana.."
Amrah dake bin Sultan da banzan kallo cike da takaicin zagin da yayi mata ji take tamkar ta rufe shi da duka.
Mi'ka mata 'dan ta yayi.." take ur Baby ku shiga ciki..."

Daga 'karshe dukkan su babu wanda ya bar wajen cikin da'din rai.."Amrah ciki tayi tana ayyana" Wallahi kaci bashi Sultan..".

Huzaifa kuwa dake daga daya can 'daya 6angaren shima cikin mota ya koma yana kya6e baki, dan Rayyan yace masa ya jira shi fita zasu sake yi, bai zago ta inda suke ba sai dai duk dramar tasu a kunnan sa ne...shima Sultan yasan duk yajin amma bai damu ba domin duk tamkar madubin sa suke...photo kawai suke ga Rayyan batare da ya sani ba.

Yanda Sultan ya fizgi motar a zuciye har abin zai baka tsoro da mamaki ga wanda bai san abinda ya faru ba.

Huzaifa kansa le'kowa yayi yabi bayan motar da kallo haka Amrah ma dake kan.m hanyar 6angaren ta, sai da ta waigo ta dubi bayan motar tana girgiza kai ta juya ta cigaba da tafiyar ta.

" Ku dai Allah ya shirya, kowa zuciya akan abinda bana kirki ba...".

Tana isa Palor shi kuma yana fitowa, ko kallon inda take bai yi ba yai waje abinsa da dukkan wayoyi da system dinsa dama wasu abubuwan da bata san komene ba.

" Baby fita zaka sake yi kuma...?"
Bai kulata ba yaci gaba da tafiyar sa.
Tasan dama wannan halin sa ne amma still sai ta sake fa'din" Baby magana nake fa ina zaka je haka...?"
" Inda kika aike ni"
Inda yayi maganar yana me cigaba da tafiyar sa tamkar bashi yayi ba.

Haka nan kawai ta tsinci zuciyar ta cikin rashin sukuni da fitar tasan karshe da idanu tabi sa har ya 6acewa ganin ta.

" Allah ya kyauta."
Tace a fili tana me zama bisa kujera mai zaman mutum biyu.

Rayyan kam sake fita suka yi da Huzaifa da niyyar sa Huzaifa ya kaisa inda za shi amma tuno maganar ta kwanaki... _Ka canza masu Kula da kai._ da yayi ya sanya shi dakatar da Hauzaifan, dama driving yake tunanin kamar zai bashi wahala but dole zai daure yayi da kansa.
A hanlin yanzu baya son kowa ma ya san inda yake balle a dame sa, sosai yake so ya samawa zuciyar sa hutu na wani lokaci.

Ku'di kawai ya Huzaifa da sunan ya samu abin hawa ya koma shi zai 'karasa inda zashin kawai.
Huzaifa ba 'karamin mamaki yayi ba da jin sauyin ra'ayi da ga Rayyan din sai sai dai sanin da yayi cewar hakan ba sabon abu bane a wajen sa ba ya sanya shi watsar da batun ya tari adaidaita yayi gaba abinsa.

Rayyan haka kawai yanzu yake ji har cikin zuciyar sa bai yadda da kowa ba, kuma ya tsani duk wata mu'amala da zata ha'da shi da wani na daban.

Bai zame ko'ina ba sai can gidan sa da ya bari tun bayan rasuwar Nadia, Nadia matar sa mafi karamci cikin matan sa, ya san dama yayi rashi tunda Nadia ta barshi yasan yayi rashi matuka, yayi rashin macen 'kwarai da baya jin har abada zai samu makanciyar ta, har abada kuwa bazai daina nema mata gafara wajen mahalicci ba, ya tabbata da Nadia ce mazaunin Amrah bazata ta6a iya cin amanar sa da wani namijin ba ballantana 'kani ma awajen sa irin Sultan.

Cikin gidan nan yayi rayuwa da matan sa biyu bazai manta ba shekaru ne 'kalilan da suka wuce 'kasa da shekaru biyar amma yau da ya tsinci kansa cikin gidan cikin 'dakin ta ji yake tamkar ya shekara 'dari ne rabon sa da ita.

Kewar Nadia da kuma cin amanar da akayi masa ya sanya shi jin duk ga6o6in sa sunyi sanyi.

Gidan cike yake da 'kura dan ba sosai yake le'ko shi ba amma ahakan ko da ya samu ya yaye leda 'daya da aka rufe kujeru da shi yaga 'kurar wajen babu sakamakon ledar da ta musu shamaki da kurar ahaka ya zauna akai yana mai daga kansa sama dayake jin yana sara masa tamkar zai rane gida biyu.

An jima ana munafurtar sa, anjima ana masa ha'inci a rayuwa, anjima ana cin amanar sa amma in ka 'dauke ta kashe Daddyn sa da akayi wannan shine cin amana mafi muni da ya tsaya masa arai sosai, in dai har Sultan da tun tasowar sa yake yiwa kallon 'dan uwa, kuma 'kani a wajen sa na jini zai masa haka me ze hana wani ma daban ha'intar sa?
Indai har Amra da take matsayin matar sa ta iya masa haka toh waye bazai masa ba.

Turaren Sultan da ke saman mirrorn ta da ya ta6a gani da jimawa...kuma yaci gaba da gani har zuwa lkcn da cikin Amrah sannan ya daina gani, bai ta6a damuwa ko zargin wani abu da ganin turaren ba, duk zaton sa itace take amfani da shi duk da bai ta6a jin 'kamshin sa ajikin ta ba.

Ashe shi suka mayar sauna, ashe ala'kar su tayi 'karfin da ta zarta tunanin sa.
Bai san tsawon wani lokaci suka 'dauka suna wannan rayuwar da Sultan ba amma shi abinda ya sani kawai shine daga yau din nan baya jin zai iya sake rayuwar aure da ita har abada.
Har cikin zuciyar sa yake jin ta fita daga ransa ya kuma cire ta cikin tsarin rayuwar sa kwata- kwata.

Hankalin Amrah bai sake tashi ba har sai da taga dare yayi babu Rayyan babu alamar sa, ta kira wayar sa fin a 'kirga amma duk numbers din sa basu tafiya...wasa- wasa har sha 'daya babu shi, bai ma ta6a yi mata irin hakan ba tun farkon auren ta da shi sai yau din..shiyasa hankalin ta ya tashi.

Tuni ta 'kira Ammi ta sanar da ita, itama tayi ta 'kiran sa numbern sa bai tafiya.
'Karshe Sultan Ammi ta tambaya yace shi bai san inda yake ba amma zai bincika Insha Allah.

Sultan baccin sa yasha haka ma Marwa da bata san meke faruwa ba dan lokacin da Ammi ta 'kirasa Marwa na bathroom ne, ko da ta fito kuwa bai sanar da ita ba, yayin da Ammi da Amrah suka yi kwanan fargaba.

Zuwa lkcn Amrah ta gama fahimtar akwai wani abu, dole akwai abinda Rayyan ya sani musamman ma idan tayi fashin baki ga kalaman Sultan da tun jiyan bata yi nazarin komai akai ba lallai dagaske itan sauna ce bata san inda wayo da tunanin ta suka tafi ba.

'Bangaren Zaitoon kuwa da farin ciki ta kwanta da yasa har ta 'kagu gari ya waye sbd tsabar zumu'di.

Tun kafin yammacin ranar ta roki Ammi adawo da Mufeeda haka, agaban ta Ammi ta 'kira Anty Madeena dan ta lura Rayyan bashi da niyyan dawo da yarinyar...Nan Ammi ta roki Anty Madeena kamar yadda Zaitoon itama ta roketa kan dawo da yarinyar.
Chapter 113 · 0% Book details