Sashe 197
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Adam idanu kawai ya 'kura mata yana jin wani abu da ya jima da 6oyewa na son taso masa sabo fill, duk dama shi har ga Allah bai ta6a cire ta aransa ba dama can, amma dole ya danne 'kaunar da yake mata sbd ya fuskanci rayuwar sa...bai kuma ta6a gigin sake sanya wata 'diya mace cikin ransa ba balle yy tunanin 'kaunar wata macen zai iya danne na Zaitoon a ransa, har a yanzun dai ita 'din ce kuma ita ka'dai a zuciyar sa babu wata.
Wani gagarumin farin ciki yake jin zuciyar sa ciki tun a wancan ranar, ba 'karamin dauriya yayi bama da ya iya kaiwa kwanaki har hu'du kafin ya dawo.
Ji yake kaf a dunia babu wanda ya kai shi farin ciki..zuwan sa wajen Goggon nasa ya zame masa babban nasara a rayuwa..domin zai iya ce tsuntsu biyu ya jefa da dutsi guda..ya sada sa da farin cikin sa da har ya fara cire rai da samun sa.
A hankali tace.
" Yah Adam..kai ne ?"
Kai ya jinjina mata yana murmushi.
Tace
" Barka da zuwa.."
Ta fa'da batare da ta yadda sun sake ha'de idanu wa ba.
'Ko'karin lalu6o inda tabarma yake take yi da idanun ta yayin da shi kuma Adam ya 'kura mata idanuwan sa baya ko 'kyaftawa.
Lokacin da ta hango tabarmar 'kafa ta 'daga da zummar zuwa wajen da hanzari sai taji sau'kan maganar sa cikin kunnuwan ta da wani irin sauti mai ratsa zucia.." Zaitoona!..."
Cak ta tsaya jun sunan ta da ya ambata.
" kin canza sosai.."!
Murmushi kawai tayi batare da ta juyo ko ta tanka masa ba.
Ita dai tana mamakin abinda yake kawo shi wajen Innar ta..kuma ko ita kanta Innar bata ta6a yi mata maganar sa ba.
Ruwa ta kawo masa bayan ta shimfi'da masa tabarmar..tana shirin mi'kewa tace" Innar tana sallah ne...".
Yace " Bakomai...ai gaki kafin ta idar...".
Bata ce uffan ba sai kawai tayi 'kasa da idanun ta.
'Yar murmushi yayi yace" Abu guda ne bai canza wajen Zaitoon ba.."!
'Daga idanu tayi ta dube shi sai kuma ta kau da kanta da sauri.
" Wannan alkunya da shiru- shirun sun kasa barin ki...".
" Hmm" tace 'kasan ma'koshi.
Ta dai fahimci wannan Adam 'din ba 'daya yake da Adam 'din ta na baya ba, ita kanta a halin yanzu jin ta take takure zaman da tayi kusa da shi, ga shi irin maganganun da yake yi mata ko ada bai mata irin su ba.
Tana mai wasa da yatsun hannun ta ta 'dora da fa'din.." Kunzo lafia?"
" Alhamdulillah..ya bayan rabuwa..".
Tace" Mun gode Allah..Hajia fa?"
" Tana nan..itama tana gaida ki..nayi mata albishir na ganki...tace itama tana nan zuwa da kanta watarana..."
Tasan abu ne mawuyaci dan haka kawai sai ta mi'ke tana fa'din" Allah ya bata ikon zuwa..zan kuwa yi farin ciki idan mutum kamar Hajia ta tako har garinnan sbd ni".
Ganin ta mike din ya sashi 'daga kai ya dube ta da hanzari yace " Shikenan?".
Kai ta 'dage masa itama ta dube shi...sannan ta bashi amsa" Zan dubo Innani ne ko ta idar..naji ta shiru har yanzu..."
"...Shikenan sai ita ka'dai?...ba ga ki ba, ga Feefy na, bazan yi hira da ku ba sai Inna Ka'dai...?".
Bata ce da shi 'kala ba kawai ta wuce cikin 'dakin ta, hakan nan kawai take ji aranta zata kare martaba da darajar auren da ke kanta, kuma ai ko ba komai Adam ba muharramin ta bane, matsayin tsohon saurayin ta yake da wata 'kaddara ta raba su.
Amma ita kanta bata san wani matsayi ko yanayi yake a zuciyar ta ba har suka rabu, domin har yau 'din nan bata ta6a jin wani abu game da shi a zuciyar ta ba..ita dai tasan tana bashi girma, tana kuma bashi daraja kwatankwacin yadda ya 'dauke su..ya mutunta su ita da Feefy, so ko ada 'din ma kyautatawar sa ne kawai yasa ta tilastawa kanta sha'kuwa da shi har ta amincewa auren sa bawai dan tana jin soyayyar sa ba.
" Yah Adam..."!
Ta fa'da tana murmushi.
Akwai wasu abubuwa da ta tabbatar har abada bazata ta6a mancewa ba a tsakanin su ko da kuwa ace bb soyayyar sa a zuciyar ta, Adam ya nuna mata 'kauna ya kuma 6ata wani 6angare cikin lokutan sa masu muhimmanci domin ta.
Shine ya fara 'daga darajar ta cikin sauran mutane tun bayan barowar ta gida.
Kwanciya tayi bisa katifar su, Mufee tazo gaban ta itama ta kwanta.
Cikin ranta take tariyo rayuwar su da Adam na baya" Ko ya Maman Abdul take oho..."
Ta tambayi kanta.
Canjin yanayin da ta fara fuskan ta daga gare shi ya sa ko tambayar ta su ma kasawa tayi... a hkn bacci 6arawo yy gaba da su ita har Mufeeda baki 'daya.
Bai damu da baccin nasu ba sbd yasan yana da isashshen lokaci daga yau har zuwa gobe, hakan yasa sam bai damu ba, hira ka'dan suka yi da Innani yace zai shiga cikin gari amma zai dawo washegari, Innah tace babu komai, ai ma yana 'ko'kari sosai..Allah ya ji'kan mahaifa.
Yace " Ameen Goggo..badan Mufeeda na bacci bama ai da ta rakani..."
'Yar daria Inna tayi masa tace" anya kuwa..? Wannan ma'kalematan zata yadda tabika kuwa..?"
Suka daria atare dukkan su.
Shi kansa ma fa'da kawai yake, amma sarai yasan halin Mufeeda da Zaitoon ba tun yau ba.
Daga haka ya wuce fuskar sa cike da annuri har ya tafi.
Koda Zaitoon ta tashi a baccin tayi mamakin irin bacci mai nauyin da tayi, domin sam bata san da tafiyar Shaheed ba, ba kuma tayi mamakin tafiyar tasa ba...dan dama tana da tabbacin wajen Inna yazo ba wajen su ba.
Kamar yadda ya fa'da washegarin ranar ya dawo da misalin 'karfe goma da 'yan mintina.
Shaheed sam baya da shamaki da gidan Innah, hakan yasa sallama kawai yake yi ya shigo gidan kansa tsaye bayan an amsa shi.
Doguwar ba'kar riga ce jikin ta da wata jar hula taja shi baya sosai dan kusan rabin kanta ma waje yake baki 'daya.
Wankin kayan Mufee take yi da wasu nata 'kalilan tana kuma yin abinta ne hankali kwance, yayin da Mufee ke faman takura ta da fitinar itama sai tayi wankin, tun tana hana ta tana qi da 'yar rigima har ta ha'kura ta 'kyaleta, ta kuwa ji'ka jikin ta sosai da ruwan wankin.
Lokaci- lokaci takan ce Mufee bazaki bari ba..? Dubi yadda kk ji'ke jikin ki a banza?"
Mufee ko gezau tamkar ma ba da ita take ba..sosai take jin nisha'di da wasa da ruwan..ita kanta Zaitoon nisha'din take ji a zuciyar ta da bata san na menene ba.
Cikin rashin sa'a adai- dai lokacin da Zaitoon ta sakan kance tana wankin ta gami da surutu wa Mufee akaro na babu adadi shima ya doka sallamar sa har sau biyu..duk Zaitoon bata ji ba.
Shigowar sa gidan yayi dai- dai da lokacin da take sake fa'din" wallahi in mura ta kamaki allura zan kai ki ayi maki babu ruwana..?"
Sai ji tayi bazata anbata amsa" Ni kuma inada tabbacin bazaki ta6a iyawa ba..."!
Ya fa'da yana murmushi.
'Daga kai tayi da sauri nan tayi arba da Adam tsaye yasha kyau har ya gaji.
Fuskar sa sanye da farin gilashin da ya matu'kar 'kawata zubi da tsarin sa.
Bata san lokacin da itama ta murmusa ba.
Tana 'ko'karin cire hannu a ruwan ya 'karaso..." Kar ki damu, cigaba da wankin ki...ai ni ba ba'ko bane da kaina ma zan nemo abin zama.."
Ya fa'da yana zama bisa wata kujerar da ya hango kusa da ita.
" Toh ruwa fa..?"
" Bani da bu'katar komai Malama ta..".
Suka yi daria atare.
Cigaba tayi da wankin ta.
Cikin ranta tace " Yah Adam kenan..toh dama akai akai yake zuwa gidan nan ne..ko de yana da alaka da mai gidan Innani ne...? Babu mamaki hakane..."!
Tayi tambaya kuma ta bawa kanta tabbacin amsar ta.
Hannun Mufee ya kamo..." Ke kuma yarinyar Daddy bakijin magana ko?..nima da kk gani bazan hana malamar nan kaiki allura ba..gara ma ki kiyaye ki riqa jin magana kin ji ko...?"
" Yah Adam tuna min kake da wani abu can baya idan kace min malama.."
'Dagowa yayi ya dube ta sosai suka ha'de idanu, dama hakan yafi bu'kata tuntuni amma sai tayi saurin mayar da kanta 'kasa ta cigaba da wankin sannan tace.
" Da ace a rayuwa ta na samu matsayin zama malama kwatankwacin yadda kk fa'da yanzun, da na gama jin da'di..."
" Idan hakan kk bu'kata har yanzu baki makara ba Hajia ta..zan iya miki al'kawarin zama malama daga yanzu har 'karshen rayuwa ta..indai ilimi ne baki da matsala da shi har sai kin gaji..."
Sai tayi murmushi.
" Wani abin kafin ya faru 'karshen sa ke fara bayyana Yah Adam...ha'ki'ka nayi rashi cikin rayuwa ta gagaruma...bazan ta6a mantawa da kai ba domin kaine malami na biyu da ya tallafi rayuwa ta...ko hakan ma nagode..."!
" Ina kuma so in zamto na 'karshe a wajen ki idan kin bani dama Zaitoon...?"
Ya fa'da yana mai mayar da hankalin sa sosai agare ta.
Mufee dake wasa da agogon hannun sa take shirin 6allewa ya kalla, adaidai lokacin itama Zaitoon ta 'dago idanu sbd jin sigar da yai magana sai ya mata wani iri.
Idanun ta ta sau'ke akan hannun nasa..abinda tayi niyyan fa'di ta fasa..inda akalar maganar tata ta sauya daga wacce tayi niyya zuwa" Indai Mufee ne tsab yanzu sai ta lalata maka agogon nan idan baka hanata ba.."
" Sai kuma akace mk hakan matsalar ki ce ko..?"
Kai ta girgiza...sai yace" Toh babu ruwan ki da yarinya ta.."
Bata ce komai ba ta cigaba da wankin ta.
Sai ji tayi yace" Sannu da hidima.."!
" Ta me fa..?"
Ta tambaye shi batare da ta 'dago ba.
" Wankin kayan Mufee na mana.."!
" Wannan kuma...ya riga ya zame min jiki ai.."
" Allah ya baki lada Malama ta...ni ma bari in ta6a wannan ladan ko ta yau ka'dai ce kar ta wuce ni..."!
Da sauri ta 'dago sai gani tayi yana tattare hannun riga yayin da agogon hannun sa ke hannun Mufee tana ta faman kokawa da shi.