Sashe 78
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bata amsa shi ba illa kokawa da hannun sa da take a kokarin ta na son 'kwatar nata hannun.
Tsayuwar sa ya gayaa jikin mota, daga nesa idan ka hango su sai ka zaci maganar arziki suke yi tsakanin su.
Gashin kansa ya shafo da 'dayan hannun sa yayin da 'daya hannun yake ri'ke da tsintsiyar hannun Zaitun har a lokacin bai saki ba.
" Wai ina zaki je ne?...kin gaji da zama waje 'dayan ne za'a 'dora? ko kuwa guduwa kike son yi bayan daf kike da kashe min aure na..?
Hararar sa tayi
Sai ya yi kamar bai gani ba.
" Ai in kinga kin bar gidan nan toh aure na bai daina lilo ba, Toh ma Ammi tasan kin fito ko kuwa..?"
Cike da haushi tace
" Wallahi idan baka cika ni ba sai na maka ihun kwarto...".
Idanu ya zaro sosai..." ohh really...mene ma kwarto?...ohh na gane, ki gwada mana, kowa yasan ni ba kwarto bane akaf unguwar nan kuma ko zanyin ma ba dai da irin ki zanyi ba..baya ga haka ma ni da ke waye mai shaidar da zata bayyana kwartancin?".
Ya 'karashe maganar yana sakin wata 'yar dariyar mugunta.
Wani fizga ta yiwa hannun nata dake hannun sa tana fa'din" Ni dai wlh ba 'yar iska bace sai dai ko kai da ka rike min hannu..." wannan maganar ya sanya ya 'daga 'daya hannun sa kamar zai mareta sai kuma ya fasa..kan hannun nata dake hannun sa ya sauke idanu.
Shi da kansa mamakin kansa yake yau din da har ya biye mata har haka, me me ruwan sa da ita? Amma haka kawai yaji zuciyar sa bai yadda ya barta ta tafi da wannan lokacin ba.
Ba 'karamin girgiza Zaitoon tai ba da ganin ya 'daga hannun sa da nufin marin ta, gashi ya tsare ta idanuwan sa masu mugun shigar da ita taitayin ta...bata manta marin da ya saukewa Amrah ba...ita bata taso ta saba ganin ana bugun mutum ba haka kuma itama baza tace ga ranar da aka mare ta irin hakan ba shiyasa take jin tsoron ranar da hakan zai faru gareta amma duk da hakan bata yadda ta bayyana firgicin ta gare shi ba.
" Shiga mota mu koma gida..."
'Karfin halin magana tayi tana sake ha'de rai
" Wani gidan..kenan..? Babu inda zan koma ni, gidan da bashi da maraba da bakin kura, gidan da banda zalunci da 'karairayi babu abinda aka iya a cikin sa, ka cika min hannu nayi tafiya ta, nagaji da azabtar min da 'diya da cutar da mu da kuke yi a gidan ku..kuma ka fa'da wa matar ka ni kaf gidan banga abin sata ba balle har nayi sha'awar daukan sa, nafi 'karfin in 'dauki abinta wallahi koma menene shi..."
Kallon cikin idanun ta ya tsaya yi har ta dasa aya, duk da duhun maghrib da ya fara shigowa amma hakan bai hana shi ganin fuskar ta da kyau ba, mamakin kalaman ta yake da ya tabbatar tsantsar gaskiyar abinda yake zuciyar ta take furtawa....
Kansa ya kawar gefe yana 'yar daria da kokadan bata bayyana saman fuskar sa ba , bai kuma bari Zaitun ta fahimta ba.
" Kika ce babu abin sata a gidan?"
" Ban ta6a ganin sa ba...".
Ta bashi amsa ranta a 6ace itama.
" Na yadda babu 'din, amma ina jiye mk ranar da zan kamki da satan wani abu kuwa..tsaya ma tukun na kin tabbatar baki sato komai yanzun bama ko...sai na tabbatar sannan zan yadda dake, har kuma yanzu na.kasa tabbatarwa musamman saboda yadda naga kike tirjewa da son kika ga kin wuce..kodai sarkar matartawa za'a je a siyar...?"
Bata bashi amsa ba illah harara da ta banak masa sai lokacin taji hawaye.
Shima da ganin hakan sai ya 'daule kansa.
Ji yake tamkar yayi ta sheka daria amma bazai iya gaban yarinyar ba.
Wayar sa ya ciro agaban rigar sa ya danna 'kiran Ammi.
Ko da ta 'daga sunan sa ta fara ambata yace.." Na'am Ammi barka da Yamma, ina wannan maid 'din taki, mamar yarinyar nan...?"
" Ohh Zaitoon...?" Wlh nima cigiyar ta nake yanzu ina tunanin can 6angaren naka take ma dan bata nan..".
" Ok shikenan...".
Idanun sa akan ta ya cire wayar daga kunnen sa..." Ammi bata san kin fito ba, oya shiga mota mu koma gida...."
Kuka mai sauti ta sanya tana fa'din" wallahi ni babu inda zani dole ne sai an zauna tare da ku...?"
" Ba dole ba ne...amma waye ya kawo ki Kano ne...?"
" Ina ruwan ka ai dai bakai bane toh...?"
Wani killer smile yayi, sannan yace" Wanda ya kawo ki kano shine mamallakin ki a yanzu dan haka shiga muje, in ma bazaki fa'da ba ai ni sani...".
Zata sake magana ya cicci6e ta ita har yarinyar bayan ta ya santa su abayan motar sa yana fadin mutun sai shegen nauyi da taurin kan tsiya...".
Watsa hannuwa yayi yana fa'din wash hannu na da gangan duk da yasan ba gaskia yake fa'da ba, ita har 'yar tata da ya 'daga weight din su bai taka kara ya karya ba.
'Kofar motar ya mayar ya rufe da karfi shima ya shiga gaba.
Kuka sosai Zaitun take ta kifar da kanta bisa cinyoyin ta.
" Aimin shiru ko nayi bugu bana son hayaniya..dan ma kin samu na saki a motata.".
" Ni na ro'ki a sani cikin mota ne toh..?"
Kin kulata yayi kawai yayi murmushi itama bata sake tanka saba yaja motar yayi gaba, tafiya ka'dan yayi suka iso 'kofar gate gidan su ya danna horn
Mai gadi yaja gate ya fara tura hancin motar ciki dai-dai saitin maigadi ya ja ya tsaya yana ya fito sa da hannu.
" Ranka ya da'de barka da dawowa".
" Yauwa Emma ya akayi ka bar wannan yarinyar tafita batare da binciken komai akanta ba...kasani ko sata tayi zata gudu...?"
" I'm so sorry Oga, she said she ll buy rechard card nd come back now...".
" Ok..kar ka sake wannan gangancin kaji, duk wanda kaji.baka yadda da shiga ko fitan sa ba ka kira ka sanar dani before letting every body out kana ji na ko...?"
" Yes Oga..Thank u...".
Gaba yaja motar ya isa wajen Parking sannan ya bu'de ya fito itama fitowa tayi.
" Allah sai ya sakamin sharrin satan da akai min...".
Bai tanka ta ba sai ma gira da ya dage kawai ya nufi 6angaren sa.
Ita kuma jikin ta sanyi 'kalau ta nufi 6angaren Ammi.
*Drop ur Comment pls*
Salmerh😘
[12/10/2022, 12:27 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...49*
........Fa'da sosai Ammi tai mata kan yanke shawarar tafiya da tayi batare da ta sanar da ita ba, ita Ammi a sonta daga nan gidan Zaitun bazata sake zuwa ko'ina ba sai gaban iyayen ta, tafi so ta damkata a hannun su kamar yadda ta yiwa kanta alkwari tun farko.
Meyasa Zaitun din bazata yi hakuri ba, ita kanta tasan ba gaskia Amrah ke fadi ba kuma ko awajen bata goyi bayan ta ba meyasa daga baya Zaitun din zata yi fushi ta tafi.
Tana ganin kamar batai mata adalci bane ko me take nufi.
Hakuri Zaitun ta bawa Ammin sannan ta sake komawa dakin su da ta baro.
Ta 'dauki tsawon kwanaki kafin walwalar ta ta dan dawo dai- dai, ba komai yafi tsaye mata ba face zancen satan nan, Ammi kuwa bata tashi sanin cewa Amrah bata gidan ba har sai da aka shafe tsawon sati guda.
Rayyan ne da ya shigo 6angaren ta take tambayar sa Amrah fa tace har yanzu fushin take yi dani ne naga bata leko nan ba, ka sanar da ita nace tayi hakuri ba nufi na in 6ata ranta ba ne.
" Ammi ai Amrah tun ranar can bata kwana gidan nan ba.."
Ya bata amsa a ta'kaice
Yana shirin mi'kewa.
Gira sosai Ammi ta ha'de tana duban sa" Me kake nufi Rayyaan..?"
" Ta tafi gida naje bayan kwanaki biyu da tafiyar tata amma ban samu ganin ta ba.."
Shima fa'da sosai Ammi tayi masa na rashin sanar da ita da wuri da bai yi ba ta inda take shiga bata nan take fita ba, tace meyasa zai yi kan irin wannan maganar bacin yasan yanayin da Amrahn ke ciki, kai ko 'dar ma bakaji, taya zaka bari har sati guda bata tare da kai bayan kasan da 'karamin ciki ajikin ta, idan wani abu ya samu cikin fa..."
" Ammi ni bazan iya zarya ana cimin zarafi haka nan kawai ba, 'karshe ma nayi magana Amaran yanzu haka bata Kano tana Kaduna nayi bincike kuma na tabbatar da hakan ne dagaske...babu yadda zanyi ne Ammi, umarnin mahaifiyar ta take bi itama."
" Kuma da aure da cikin duk take wannan yawon..?"
Ammi ta tambaya cike da 6acin rai.
" Rabu da su Ammi..in hauka suke ji na 'dara su, na riga na sanar da ita, ko kwarzanen abu ya samu cikina I would not hesitate in 'daure mutum babu ruwa na, nd tasan zan aikata.."
Tsaki Ammi tayi ta wuce sama.
Washe gari tana da tafiya agaban amma ta soke shi zuwa rana ta gaba.
Da kanta taje gidan su Amrah dan ganawa da mahaifan ta kan batun amma kamar yadda mahaifiyar Amrah ta shaidawa Rayyan haka ta shaida ga Ammi.
Sosai ran Ammi ya 6aci, sai taga ma kamar raina musu hankali kawai suke son yi, bayaga haka taya za ace sai su ne zasu bata dokar yadda rayuwar gidan ta zai kasance, kamar dai yadda Rayyan ya bar gidan cike da 6acin rai haka ma Ammi, inda duk suke yin tafiyar su batare da an tsaida magana guda muhimmiya ba.
Tun faruwar lamarin can Zaitoon bata sake aikin komai cikin gidan ba, wannan karon koda Marwa ta dawo gidan Ammi ta tare gaba daya, dan Sultan yayi wata doguwar tafiya zuwa kasar senegal.
Sosai suke samun time susha hira yadda ya kamata da Marwa.