← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 218

Sashe 104

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima kallon ta yayi take kuma sai ya 'dauke kansa yana gyara zama yace
" Yanzu dai na bata aron sunana cuz lokacin I'm in hurry zan yi late a office shiyasa nayi haka, duk time 'din data tuna sai ta sanar aje a canza mata..."

Zaitoon kam tun lokacin da ta ji Mufeeda na tare da Anty Madeena taji hankalin ta ya kwanta, gaba 'daya damuwar ta ta kau, dan tasan Anty Madeena sosai ta kuma san halayyar ta, sosai take 'kaunar Mufeeda tasan zata samu kula yadda ya dace a hannunn ta.

Washegari kuwa bai koma gidan Anty Madeena ba office ya wuce abin sa, yayin da Anty Madeena ta kwana da zullumi da tsanan ta tunani, sosai take ganin dacewar wasu abubuwa tsakanin Rayyan da Mufeeda, amma meyasa tun farko babu wanda ya lura da hakan sai ita, itan ma kuma sai yanzu, duk da ta jima tana kallon yanayi da zubin halittar Nadia da yaran yayan nata tattare da yarinyar amma bata sa aka ba sai da yau taga wannan ba'kin abin da ya kasance irin na Rayyan sak, domin tasan Rayyan tun yana tsumman goyon sa...ganin wannan ba'kin tambarin ya sanya duk tunanin ta hautsinewa.

Bazata ta6a jin natsuwar zucia ba har sai ta tabbatar da cewa wannan yarinyar ba jinin ahalin yayan ta bane ko kuma tasu...

Address 'din makarantar ya turawa Anty Madeena washegari tasa aka kai Mufeeda da komai da tasan zata bu'kata, yarinyar ma babu ruwan ta tana da saurin sabo dan har Mufeeda ta 'dan fara sakewa dasu ko da daren ma basu 'diga mata drop din baccin ba kuma bata basu matsala ba tayi baccin ta, sau 'daya kawai ta farka shima bata da'de ba ta koma.

Badi'a ma da'di kamar ya sumar da ita yau gata ga Mufeeda cikin gida 'daya.

Da safe ita taimata wanka duk da Nuwairah da Anty Madeena na 'ko'karin hanata amma ta turje.

Ita ta shirya Mufeeda tsab suka kuma fito tare aka wuce da su bayan an 'dauko Imran acan gidan su.

Abu wasa- wasa fa zuciyar Anty Madeena ya kasa barin batun, cikin ko wani da'ki'ka 'karin kusanci da kamanni take sake ji da gani game da Mufeeda.

Hakan sai yaso ya ta6a daily routine dinta, yini tayi tana tunani har lokacin tashi yayi aka dawo da Mufeeda data tabbatar shine ya tura.

Kasa hakuri tayi sai da ta kirashi awaya ta sanar da shi tana neman sa idan ya taso a aikin yace toh ba matsala.

Saboda yanayin da yaji maganar ta ma yasa ya kasa samun sukuni tun la'asar daya fito sallah bai koma office ba ya nufi gidan nata.

" Anty dan Allah ki bar wannan batun, na riga na san babu wata ala'ka tsakanin mu...meyasa kike takura kanki da tunani ne, Anty ko dai baki yadda dani bane dama tsawon lokacin nan..?"
Ya fa'da bayan jin bayanan da ya fito bakin Anty Madeenan.
Tace" Ko ka'dan Rayyan, abu guda da har Allah ya 'dauki raina bazan yi shaidar sa akanku ba kenan Insha Allahu, amma ni na kasa tantance wani tunani zanyi akai, hakika bazan ta6a samun natsuwar zuciya ba matukar ban tabbatar da cewa Mufeeda ba 'diyar kowa daga cikin ku bace, abinda ya fi 'daure min kai ma.shine yanayin kamannin ta da ya zo 'daya da Nadia kai da kuma Safaa...."

Jim yayi shi kansa maganganun Antyn sun fara shigan sa, amma baya so su shiga kansa su zauna domin yasan indai ba wani Rayyan din na daban bane Antyn ke magana shi kam yasan babu wata alaka.
Fawwaz ne ya sake zuwa masa tunani...sai kuma ya tuno kammanin Nadia da ya gani tattare da ita a safiyar jiya, ga kuma magangnun Anty Madeena.

" Yah Subhanallah...me ke shirin faruwa da shi ne wai...?"
Ya tambayi zuciyar sa yana mai cusa hannun sa cikin sumar kansa.

" Anty yanzu ya kike so ayi toh, ni har ga Allah bansan yadda zan 6ullowa lamarin nan ba, haka 'dazu da safe dana fito da ita zan kaita skul wallahi Anty kamar 'kiftawa naga kamannin Nadia saman fuskar ta har yaso sani cikin ru'dani amma daga baya sai na lura ba hakan bane.
Babu mamaki fa shai'dan ke son yi mana wasa da hankali dan ni nasan bani da alaka da su, kuma Sultan ban zargin sa sam bayaga haka ma ba yadda za'ayi Sultan ya haifi me kamanni da ahalin mu da yanayi da mu matukar ba da jinin ahalin mu suke tare ba nasan kin fini sani Anty...toh duk na rasa mai ma zance, kawai a watsar da batun, ki kwantar da hankalin ki dan Allah ki daina damun kanki da abinda Allah ne ka'dai ya tsara shi bamu san komai akai ba balle musan mafitar sa..."

" Hakane Rayyan...Amma baka yadda cewa tun kafin Allah ya halicci cuta ya halicci magani ba, sannan ya halicci tsanani ya kuma kawo sau'ki..? Baka ganin cewa Allah da kansa ya bamu hanyoyin da zamu samawa kan mu mafita kan duk wani damuwar da ta dame mu...?"

Shiru yayi yana duban ta...duk yadda ya kai ga raina lamarin abin nema yake yafi karfin sa, dagaske ba haka yaso ba, meyasa Anty Madeena zata tashi hankalin ta ta kuma tada mashi, baya ma 'kaunar su Ammi suji wannan labarin dan suma duk hankalin su kan batun zai koma suyi ta zargin sa alhali yasan shi bai aikata komai ba, bayaga hakama baya so hankalin su ya tashi kwatantacin yadda yake ganin Anty a halin yanzu...tuni ma yafara regretting kawo Mufeeda gidan ta, da yasan hakan ne zai faru da bai yi azar6a6in kawo ta ba, da yasani da office 'din san kawai ya wuce da ita yafi mashi.

" Mafitar mu ba haramtacciya ce, ba kuma rashin yadda da hukuncin ubangiji bane face dan samun masalaha da natsuwar zuciya, kai Rayyan kana ganin akwai ranar da zanji kwanciyar hankali ne matukar ban tabbatar da wannan 'diyar bata da ala'ka da mu ba zahiri...?"

" Toh Anty how, ni ne nace bani n bane, Sultan it's impossible, toh Anty Raihana ko Marwa kin san babu ko 'daya..bama zai yiwu ace su ba toh miye abin damuwa akai..?"

" Abin damuwar yanayin Nadia da ke tattare da ita..".
Shiru yayi ya zubawa Antyn idanu.
" Idan kuma ance Nadia who next..? It's u Rayyan..."
" Anty kin manta Nadia ta rasu ne..?"
" Ban manta ba kamar yadda ban manta yanayi da halin da ta rasu ciki ba, Allah ka'dai ne yasan komai dan haka na riga na gama yanke shawarar asbiti zamu je, idan aka tabbatar min baku da ala'ka sannan hankali na ya kwanta fiye ma da yadda kake zato...".

Salmerh 😘
[27/10/2022, 1:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
*Serlmerh-md*

🅿️ *...61*

........" Ina Marwa ta shiga ne? Marwa!..Marwa!!..."
Ammi ke cigiyar ta tana 'yan dube- dube amma bata ganta ba.
Bayan kamar mintina biyu sai ga Zaitoon ta hawo saman nata da sallama a bakin ta hannun ta 'dauke da wani kyakkyawan bowl da spoon bata dire shi ko'ina ba sai gaban Ammi.
Sai da ta dai- dai ta zaman glass bowl 'din da kyau sannan ta koma gefe ta zauna daga gefen kujerar Ammi fuskar ta babu yabo babu fallasa.
Ammi ma gyara zaman ta tayi gami da 'dago bowl din a hannun ta tana fa'din" banga Marwa ba hala itama tama can kitchen 'din ne ko..?"

" A a Ammi inaga dai 'dakin ta take fa.."
" Ok...wai da so nake taje ta duba min Amrah ya tashi, amma bari dai ta shigo tukunna...".

" Ko dai in 'kira ta ne kawai Ammi..?"
" a a barta zata shigo ai..."

Shiru ne ya 'dan ratsa wajen na 'yan wasu da'ki'kai...kowa sakar zuci yake amma daban, Ammi tunanin Amrah take da yanayin girman cikin ta sosai take tausaya mata, yayin da Zaitoon kewar Mufeeda ke nu'ku'rkusar ta.

A hankali Zaitoon ta 'dago tana duban gefen Ammi bakin har na 'dan rawa tace.." Amma Ammi yau in an tashi su Mufeeda gida za'a kawo ta ko...?"

'Yar murmushi Ammi tayi tana tauna fruits din bakin ta a hankali, sai da ta gama taunawa kafin tace..." Ha'kurin Zaitoon ya 'kare kenan...?"
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, yayin da Ammi ta cigaba da fa'din.." Nima nan bansani ba wannan hukunci duk na Rayyan ne, amma may be ya dawo da ita yau 'din jiyan ma ai kinji yace ayyukane sukai masa yawa shiyasa kawai ya barta acan ya koma office. "
" Hakane Ammi...Allah ya taimaka ya bada sa'a..."
" Ameen Ameen...ai naga ma kinyi 'ko'kari fa, tun jiya an yini an kuma kwana ana sake shirin wani yinin batare da kuma Mufeeda ba ai dole a jinjina miki...."
Ammi ta fa'da tana 'yar dariyar zolaya...dayake dama ta saba jan mutane ajiki, bata da girman kai sam Ammi, da kowa ma zata zauna tasha hira abinta in taso tsokanar ka ma duk yi zatayi.

Itama Zaitun murmushi tayi kana tayi 'kasa da kanta.

" Zaitoon kenan tsananin son da kike wa yarinyar nan ya zarta kowa a zuciyar ki da alama fa..?"

Murmushin ta kawai ne ya 'kara fa'da'da wanda kai tsaye ta aika shi ga Ammin cikin bayyana amsar tambayar ta yayin da Ammi ta cigaba da fa'din" na jima da fahimtar haka na kuma kasa ganewa, ko ince kin kasa sanar da ni sahihin labarin ki har yau balle in tabbatar da abinda zuciya ta ke raya min, amma tunani na yafi tsayawa akan cewa rasuwa mahaifin ta yayi shiyasa kk ninka 'kaunar da kike yi masa akan ta ko?
Chapter 104 · 0% Book details