← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 218

Sashe 1

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
( 'Yata ce)

*By*
*Salmerh MD*

🅿️....1

.........Duban farko idan kai mata zaka fahimci cewa matashiya ce mai karancin shekaru kasa da ashirin, sanye take da zanin atampan wanda daurin ya tsaya mata saman siraran kafafuwan ta sai hijab din ta na roba mai zanen blue da fari wanda shima dududu bai wuce tsayin hannun ta ba.

Tafiya take cike da sassarfa rungume da 'kullin kaya cikin wani ko'da'd'den zanin da ba se ka sha wahala wajen fahimtar cewa zanin ya jima yana shan ruwa ruwa ba musamman saboda kodewar da yayi.

Duk da cewa tana cikin yanayin tafiya ne na sauri amma hakan bazai hana ka fahimtar nutsuwar da Allah yayi mata ba. Akai akai zaka ga ta kai bayan hannun ta daya tana share 'kwallar da ke zuba daga idanun ta babu 'kakkautawa.

Tayi tafiya me dan nisa sosai domin daga inda take tsayen sam ko kusa ko alama bazaka iya hango alamun gari ko makamancin hakan ba.

Abu daya dake sata waigawa shine idan taji dirin tahowar mota daga bayan ta takan waiga wani sa'in har tsayuwa take yi ta tsurawa motar idanu har sai ta wuce inda take ga dukkan alamu kage take wajen ganin ta samu abin hawan amma hakan be yiyu ba.

Zuwa wannan lokacin tuni hawayen nata sun tsagaita sai dai har yanzun fuskar ta daure take babu wani alamun fara'a tattare da ita.

Bayan kamar shudewan rabin sa'a tana tafiyar batare da ta samu abin hawan ba, wata doguwar farar Bus ce ta taho wanda mutanen cikin ta basu haura mutane biyar ba. Ban yi mamakin tsayuwar da tayi ba bayan jin tahowar motar saboda na jima da fahimtar motar da zai tsaya ta hau tun dazun take dako.

Cak kuwa ta tsaya tabi motar da idanu, bansan dalilin da yasa har yanzun takasa budan baki tayi magana ko nuna alamu da hannun ta wajen tsaida abin hawan ba duk da cewa alamu sun bayyana asalin matsuwar ta da son ganin ta samu abin hawan amma hakan bai sa ta iya furtawa ko nuna alamun hakan ga matukan motocin dake faman zuwa suna wuce ta ba...sai dai bana raba dayan biyu cewa ta kasance bakuwa ce a wannan harkar shiyasa.

Kadan Bus din ta gitta ta cikin sa'a kuwa sai tsaya daga gabanta kadan take drivern Bus din ya sauko.
Cikin ranta ta saki hamdala gami da ajiyan zuciya afili.

"Uwargida ina zaki..?"
Drivern ya fada yana me bude mata bayan motar.

"..Inda kuka nufa.."
Tace dashi tana me kokarin taka motar ta haye.
Bai sake magana ba kawai ya ja marfin ya rufe ya koma mazaunin sa tare da jan mota suka yi gaba.

Karo na farko kenan a rayuwar ta da ta ta6a sanya kafa ta bar mahaifar ta, a iya sanin ta tunda mahaifiyar ta ta haife ta bata ta6a zuwa ko'ina ba...ta girma ta budi ido tayi wayo duk cikin garin su...sai gashi ayau kaddara ta rabata da mahaifar ta da kowa da ya kasance ahalin ta ne.

Duk da cewa kwanakin nan din wajajen nasu bai fiya lafiya ba amma sam bata ji hakan ya dame ta ba musamman da ta ga cikin motar akwai wasu mata guda uku da maza biyu...ta riga ta tsaida zuciyar ta akan kudurin ta na barin garin dan haka aranta take ji koma ina ne suka nufa a shirye take itama.

Rintse idanu tayi gami da dafe kanta. Yayin da dayan hannun nata kuma ta kai bayan ta ta dafe abinda ke goye abayan ta dashi bata sake daga kanta ba har sai da kunnuwan ta suka fara jiyo mata tashin hayaniyar mutane...amma baza ta ce ga tsawon lokacin da suka dauka suna wannan tafiyar ba.

Sai a lokacin ne ta dago kanta ga mamakin ta sai tayi arba da mutane, titina da kuma gine gine ba irin wanda ta saba gani a garin su ba..." _Duniya sabuwa_ ".

Ta furta cikin ranta tana mai gyara rikon da ta yiwa kunshin kayanta tare da daidaita zamanta da kyau dan kar ta takurawa abinda take goye da shi...duk dama tun farkon shigar ta zuwa zaman da tayi a motar ankare take ko da wasa hankalin ta bai bar kan abinda ke goye a bayan tan ba.

Motar bata zame ko'ina ba sai cikin tasha wanda ya kasance tasha ne babba shake da al'umma da kuma motoci kala kala ana ta hada hada.

Gani tayi an tsaya kowa na shirin sauka...itama sai tabi sahu ta sauka kamar yadda taga sauran sunyi...biyan kudin motar tayi adadin yanda matukin motar ya fada mata.

Mace daya cikin motar da tun duba na farko da ta mata ta fahimci sun hada alaka da ita 6angaren yare ita tabi abaya batare ma da matar ta ankare da ita ba...cikin rashin sa'a sai taga matar wani motan take kokarin shiga.

Inda taji wani da take kyautata zaton sune masu kula da hada hadan wurin yana fadin.." Hajiya mutun biyu daga nan har Azaren Bauchi...".

Bata yi kasa a gwiwa ba wurin shiga motar kamar yadda taga matar ta shiga duk da cewa kuwa bata san inda tafiyar zata tsaya mata ba kamar yadda bata san mafarin ta ba...amma hakan bai sa ta fasa tafiyar ba.

Fatan ta kawai shine Allah yasa wannan kaddararriyar tafiyar ta sada ta ga Alkhairi ba Sharri ba...nan ma haka ta biya kudin motar adadin da akace mata ta biya.

Sunyi tafiya kusan ta sa'o'i uku kafin taga an sake tsayawa kowa na nemawa kansa hanyar barin motar..itama hakan tayi sai dai wannan karan bata yi yunkurin sake bin matar ba tana tsaye a wurin taga duk wadanda suka zo a motar kowa ya kama gaban sa...wasu da kafafun su suka yi gaba yayinda wasunsu suka hau adaidaita kamar dai matar nan da ta biyo wanda hakan ya kasance nan ne karshen ganin ta da matar.

A fili ta saki ajiyan zuciya, Gabas, yamma kudu da arewa ta waiga bata ga ta inda zata fara ba.

Duk da hakan a wannan lokacin da take tsaye gefen titin tana da tabbacin tayi tafiya, tafiya mai nisan gaske nisab da ko ba'a fada mata ba ita kanta tasan tayi nisa da gida, sam takasa jin farin ciki cikin zuciyar ta duk da cewa ita da kanta ta za6a wa kanta hakan amma ji take tamkar ta raba rayuwar ta ne gida biyu.

Safayau taje jin kanta sam ba nawi..yayin da cikin zuciyar ta take jin ta cunkushe da nawin da bata hango ranar warwarewar ta kwana kusa ba.

Jiri taji yana shirin diban ta idanun ta duhu duhu yake gani yayin da taga komai na kokarin canza mata yanayi...dai dai lokacin kuma da abinda ke goye a bayan ta yayi mutsumutsu akaro na barkatai da ita kanta bata san ko na sau nawa bane sai dai wannan din da alamu hakurin ta ya gaza ne.

Tuni ta dawo da tunanin ta daidai ta riga tasan matsalar, tasan me ke damun su daga ita har abinda ke bayan tan...bakomai bace face yunwa..dan tasan rabon su da saka wani abu a cikin tun kafin barowar su gida.

Dube dube ta fara can ta hango wata bishiyar dalbejiya yalwatacciya, batare da tunanin komai ba ta nufi karkashin bishiyar ta yada zango...Kullin kayan ta fara ajiyewa kafin ta kai ga zama kuma sai ta sa hannu ta kunce abinda ke bayan ta ta dawo da shi ta gaba sannan ta dage hijabin ta gaban tana zama, nan idanu na suka ci karo da wata kyakkyawar halitta, wanda duba na farko ba sai ka kara ba zaka fahimci cewa yarinyar kyakkyawa ce, yarinya ce 'yar karama wadda akalla bazata wuce sati uku zuwa hudu da haihuwa ba.
" Sarkin bacci kenan..."
Ta fada tana murmushi tare da gyara rikon yarinyar.

Matukar mamaki ne ya kama ni da ganin murmushin ta akaro na farko, domin yinin yau din kaf ban ga murmushi ko sakin fuska dai dai kwayar zarra kan fuskar ta ba, sai yanzu da ta yi arba da fuskar 'yar yarinyar nan dake hannun ta.

Ga mamaki na sai naga ta kunce kullin kayan ta ciro gongonin madara ta yara, Pure watern da tun kafin ta sauka a mota ta siya da niyyan sha amma bata sha din ba da shi ta dama madarar ta bawa yarinyar nan tasha abinta yayin da ita kuma ta tsaida mai awarar da ta ga na wucewa ta gefen ta shi ta siya taci tare da korawa da guntun ruwan pure watern nan.

Sake maida goyon ta tayi abayan ta ta dauki kayan ta ta cigaba da tafiya a hankali duk da yake bata san inda ta nufa ba amma dole ne tayi tafiyar.

Karshe wata bishiyar ta sake yada zango sai sai wannan din ba bakin titi take kamar wacce ta baro ba.

Ruwa ta sake siya tayi alwala da shi tayi sallah batare da cire goyon ta ba.

Wannan bishiyar nan ta maida wajen zaman ta, sai idan dare yy kuma ta koma wani lungu ko wata runfa ta kwana rungume da yar ta ajikin ta baccin kirki ma bata iyawa hankalin ta duk akan yarinyar ne tana gadin ta har gari ya waye da rana kuma ta dan kara kekkewayawa idan taji yunwa ta siyi abinci taci..da haka har ta saba da wata mai sai da abinci kusa da wurin kadan.

Rashin baccin da ta ke fuskanta yaso ya sa mata ciwon kai mai tsanani amma sam bata sashi aka ba da haka har ya gaji yayi nasa wuri.

Wannan mai sai da abincin ta fara magana da ita tun zuwan ta garin kwana biyu kenan yanzu, inda ta roke ta cewa ko zata bata aiki a wajen tana yi mata, matar da farko kin amincewa tayi tace babu wani aiki sai dai daga baya kuma sai ta tuna ashe me mata wanke wanke wata me kamawan nan ne za'ayi bikin ta.

Hakan yasa tayi saurin dakatar da ita tai mata bayani akwai aikin wanke wanke in zata yi amma zata fara aikin ne bayan kwanaki ashirin da takwas masu zuwa inda ya kama kusan sati uku kenan kafin zuwan ranar.
Chapter 1 · 0% Book details