Sashe 94
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwatsam bayan kwanaki ka'dan sai binciken Anty yakura yai tasiri har ya kai ta ga cin nasara inda ta binciko duk wani abinda ya faru da Nadia...acikin jerin wasu files da aka riga aka rufe babin su.
Har da Photon Nadia da aka 'dauka da 'dan jaririn ta data haifa kafin rasuwar ta mai tsananin kama da Rayyan tamkar an tsaga kara, sai kuma bayanan kwanakin da abin ya faru wuri da kuma lokaci duk acikin file din, already ma an riga an binne su domin an gane cewa musulma ce ita da jan lalle da take 'dauke da shi bisa hannayen ta duk biyu.
Wannan labari shi ya sake tada hankalin Rayyan jin cewa ta haifa masa cikin sa kafin barin ta dunia sun kuma koma ga mahalicci a lokaci guda, sai dai gefe guda kuma sai ya dan ji natsuwa sakamakon sahihin labari da ya samu harda photon su da aka 'dauka bayan rasuwar su aka yi amfani da shi cikin file 'din.
Ya nemi abasu photon da dake cikin file 'din bai kuma samu matsala da hakan ba.
Ranar da Rayyan ya dawo Kano yasha kuka da hawayen sa abinda bazai ta6a iya tuna rabon sa da yi ba.
A duk lokacin da yaga photon Nadiar sa kwance cikin jini da marigayin jaririn sa abun sosai yake ta6a masa zuciya.
Sai dai sanin da yayi cewa Allah shike kashewa yake kuma rayawa, yasa dole ya ha'kura ya cigaba da yi musu addu'ah da fatan Allah ya gafarta mata zunubanta da duk yan uwa musulmai.
Tun bayan bayyanar mutuwar Nadia a zahiri Da suka dawo gidan Ammi suka dan yi kwanaki biyu har yau basu sake komawa gidan su ba zaman gidan ya zam na dindindin.
Duk da ko ha'di babu da wannan na Ammi da kuma nashi daya ke kamar aljannar dunia amma hakan bai sa dai-dai da rana guda Rayyan yaji sha'awar komawa wancan gidan ba.
Kuma har gobe bai manta da Nadia ba da duka ahalin sa da ya rasa a duniyan nan, yasan cewa wannan ma 'daya daga cikin jarrabawa ce ta ubangiji, a kullum fata da burin sa shine Allah ya bashi ikon cinye dukkan jarabawar sa a duniyar nan.
Bayan rasuwar Nadia da wasu watanni aka wayi gari Amrah nada juna, sunyi farin ciki sosai sai dai 6angaren Rayyan bai ma san mai ze ce yake ji game da cikin ba, a zahiri da ba'dini yakan ji ne tamkar bashi begen cikin koka'dan.
Kamar wasa bai fi sati guda da bayyanar zancen cikin ba aka wayi gari babu shi Sultan yasa an mata allura cikin da yake na satikan da basu fi bakwai ba babu shi an wanke shi.
Rayyan bazai ce bai yi ba'kin ciki da lalacewar cikin ba, musamman da yake binciken likitoci ya nuna cewa cikin cire shi akayi amma ya kasa tuhumar Amrah akan sa sam.
Ya dai 'dauke mata wuta na wani lokaci da tunanin 'danyan kan tane yasa ta cire cikin bakomai ba.
Yasan Amrah akwai rashin wayo ita aganin ta har yanzu bata shirya hayayyafa ba ne bai san cewa duk bisa tsari da shirin Sultan take tafia ba.
Sultan ya riga ya dasawa zuciyar sa cewa bazai ta6a bari Amrah ta haifawa Rayyan 'da a duniyan nan ba matu'kar yana raye.
Sam ya mance da cewar Allah ke yin komai a duk inda yaso a kuma duk lokacin da yaso.
Wani lokaci idan Sultan yayi wani abin sai ka rantse da Allah cewar bai ta6a zaman ajin islamiya ba nan kuwa har saukar alkur'ani sai da yayi kamar yadda duk 'ya'yan Alhaji Sa'ad Auta suka yi.
An wadata su da ilimi boko da arabi shine kawai ya fita daban sakamakon zuciyar sa da ya riga ya gur6ata ta da son zuciya da tsananin butulci da son kansa.
Ata'kaice Sultan ne munafukin gidan gaba 'daya, shi yasa aka kashe Abbah da Kawu Sufyan, ya kuma yi sanadin mutuwar Kabeer, Safaa da iyalan Kabeer din, 'karshe ya auri Marwa da burin kawai ta haifa masa 'ya'yan da zai yi tutiya su kuma zame masa tsani wajen mallakar dukkan dukiyar Familyn Alhaji Sa'ad Auta, yana kuma fita da Amrah wato matar RAYYAAN a 6oye sannan can 'kasar zuciyar sa ya 6oye soyayyar Zaitoon da ta kam shi tun ranar farko da ya ganta har zuwa lokacin da nasara zata cimmasa ta kasance tashi shi ka'dai, 'karshe yanzu ya zo ya nemi ran Rayyan bisa taimakon ma'akaitan sa sakamakon gani da yake kamar ya dace ace Rayyan ya bar dunia domin ya masa babakere bisa abubuwa da dama, kuma dole sai babu shi kafin ya samu damar mallakan komai da yk so ciki kuwa harda Zaitoona.
Domin matu'kar suna raye da kunya ya dubi tsabar idanun su yace yana bukatar auren Zaitoon bayan 'diyar su Amrah yake aure.
Wannan shine takaitaccen tarihin Alhaji Sa'ad Auta da iayalan sa, duk abinda kuka ga bai zo cikin labarin ba yana nan agaba ka'dan komai zai bayyana Insha Allah.
```~One love~``` 🫶
Back to labari........👇
( Ammi tasa ta tura Huzaifa ya nemo mata Rayyan bayan 'konewar motar sa...)
Salmerh😘
[21/10/2022, 3:25 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...56*
........Ammi bata iya ta sake 'kwakkwaran motsi ba har sai da taji tashin sallama da shigowan Rayyan bayan sa kuma Huzaifa ne.
Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sau'ke da ganin Rayyan lafiya 'kalau.
" Afternoon Madam.."
Cewar Huzaifa yana 'dan rissinawa.
Hannu kawai ta 'daga masa amma idanun ta na kan gudan jinin ta ne da ya koma gefe da ita ya zauna yana fitar da huci mai zafi.
Huzaifa bai sake 6ata lokaci ba yayi gaba abin sa domin yasan ko ba'a fa'da masa ba da kansa yasan ba'a bukatar sa a wannan zaman.
" Ammi barka da isowa..."
Yace bayan fitan Huzaifa.
Bata amsa shi ba illa duban sa kawai da take yi.
Jin zuciyar ta take tamkar na tafarfasa ta ciki saboda taraddadi.
Kallon 'kwayar idanun Rayyan ka'dai ya sake 'dimauta mata tunani, domin tasan shima 'din cikin yanayi na damuwa yake.
Bata masan me zata ce ba a yanzun saboda rsananin.karaya da taji tayi, ashe tsugunne bata 'kare musu ba tsoro take kar labari ya sake maimaita kansa.
Rayyan bai ankara ba sai gani yayi hawaye na sakkowa cikin idanun mahaifiyar sa.
Da sauri ya gyara zama daga kishingi'dar da yayi.
" Haba Ammi...haba dan Allah Ammi...idan ke da kanki zaki dinga zudfa hawaye akan irin wa'dannan 'kananun abubuwan ai 'kwarin gwiwar mu zaki kawar mana...ni banga abin damuwa ba tunda gashi Allah ya tseratar da ni...komai 'kaddara ne fa, kin manta ke ke tunatar da mu hakan, kuma kinsan 'karfen bature ba'a iya musu ai...."
Da sauri Ammi ta tareshi.
" Kaimin shiru Rayyan, bana san wannan rufa rufar...irin wannan abin ne kake 'kira da suna 'kananun abubuwa? a tunanin ka idan 'kananun abubuwan da kake ikirari suka cigaba da faruwa har akwai wani sauran 'kwarin gwiwa da zai mana saura ne? mu kam mu labarin mu.shudewa zaiyi talkmore of wani 'kwarin gwiwar mu...?"
Sosai jikin Rayyan yayi sanyi, da duk hannuwan sa biyu da ri'ke kansa da yake ji na juya masa sam yama rasa ya zai yi da Ammi a wannan yanayin baya son wannan 'kwallar tata sam, a cikin 'kirjin sa yake jin ciwon su.
Cike da raunin murya yace" Ammi pls..ki bar kukan haka nan dan Allah.."
Bata kula da maganar sa ba illa cigaba da magana da tayi..." Tsoro nake ji Rayyan, kai kasan abubuwan da sukai ta faruwa a gidan nan bana so wani abu ya same ku, a yanzu ku ka'dai nake dashi kuma kune farin ciki na..taya kake tunanin zan iya kwantar da hankali na bayan irin wa'dannan abubuwan na cigaba da faruwa...?"
Hannun ta yayi saurin kamawa" Ki kwantar da hankalin ki Ammi, Insha Allah babu abinda zai faru da mu, kin manta yaranki are kinda warriors? Insha Allah together we would succeed tare zamu rayu har 'karshen rayuwar mu..."
Wannan kalmar ce ta sanyaya ranta har yasa ta murmushi.." Rayyan bani labarin abinda ya faru pls.."
Shiru yayi ya kalle ta, a yadda yaga ta 'dan saki rantan nan baya 'kaunar abinda zai sake dama mata yanayi balle har ace shine da kansa ya furta mata da bakin sa.
Tsaye ya mi'ke ya shiga kitchen Ammi ta bishi da idanu, nan ya kawo mata ruwa mai sanyi da cup ya tsiyaya mata ta sha, yana shirin 'karawa tace a a.
Yana ajiyewa kan center table yake cewa" Ki kwanar da hankalin ki Ammi komai ya riga ya wuce ai, bagani zaune agaban ki lafia ba...?"
" Hakane Rayyan but u must tell me saboda gaba, dole musan yadda zamu 6ullowa lamarin ba akan ka ka'dai ba har da sauran 'yan uwan ka, karka manta akwai Sultan, akwai Marwa akwai Raihana sannan ga ni kaina toh idan bamu san ta inda matsalar ke tasowa ba ta ya zamu magance ta...?"
" Ammi ai kowa da kalar 'kaddarar sa..."
Bata ma bari yakai aya ba ta dakatar da shi da 'kiran sunan sa.
" I said u must tell me dole in san komai Rayyan..."
Dole ba dan yaso ba ya bata labari beriefly kuma bai fa'da mata yadda suka yi da Zaitoon ba, domin in tasan cewa yes akwai hannu aciki dole hankalin ta zai 'kara tashi ne.
Duk da 6oye matan da yayi sai da Ammi ta nuna damuwar ta 'karara sosai tayi mamakin faruwar lamarin, motar da abin ya faru sabuwa ce dal 7months mai kyau ma bata cika yana hawan ta ba, marcedes benz ce kuma ta tattabatar lafiyayya ce shi kansa ya sani domin ko da wasa Rayyan baya yadda ya hau motar da yasan bata cika lafia ba balle ta bashi matsala bayan fitar sa daga gida.
Amma wannan 'din abin da mamaki ace kamawa tayi da wuta hakan kawai bisa titi.
Ganin Ammi na 'kokarin zurfafa tunani ne ya sanya shi fa'din" Ba'a mamaki da ikon Allah Ammi right...?"