Sashe 111
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaitoon ma saurin juyawa tayi ta 6uya abayan pillar dinning zuciyar ta na harbawa.
Ban da salallami babu abinda take.
In dai abinda kunnuwan ta suka jiye mata dai- dai ne kenan Muhammad Arfan ba 'dan Rayyan bane na Sultan ne.
Amma abinda ta kasa fahimta shine shin Amrah da auren nata take ke6ewa da wani mijin ko kuwa ya lamari ya kene...Yah ilahi.
Ashe idanun ta ba 'karya sukai mata ba da suke hango kamannin Sultan tattare da jaririn.
Fata take abinda taji ya kasance mafarki ne ba gaskia ba...dan babu wanda zai ji wannan batu batare da girgiza ba.
Babu wanda yasan taji hatta Marwa kuwa, dan cikin ranta ta ri'ke shi tana fatan ya kasance ba gaskiya bane.
Tausayin Ammi take ji sosai, yadda take so da 'kaunar yaron nan, take kaffa- kaffa da shi ya zata ji duk ranar da ta san cewa ba jinin Rayyan 'din ta bane...tasan sai tafi kowa shiga tashin hankali.
Yah Rabb Rayyan fa, ya zaiji idan zamcen ya riske shi, tsananin tausayin su take ji matu'ka.
Anty Raihana ma fa sai shekaran jiya ta koma tun bayan haihuwa da tazo, kuma ta fahimci irin 'kauna da suke nuna wa yaron ko kuka sun tsani suji yana yi.
Sau tari tsakanin Amrah da yaron sai dai shayarwa amma wajen su Ammi yake yini, koda kaje gidan yana 6angaren Ammi.
Bassam 'din Anty Raihana kam ma cewa yayi shi dai bazai tafi ba lallai- lallai sai dai su koma da yaron da 'kyar aka shawo kanshi suka tafi yana kuka.
Ranar da ya cika kwanaki tara da haihuwa Rayyan da kansa ya kaisu Youheal Allura da tunanin maganar da Fawwaz yace zasu yi, anan ne Fawwaz ya samu daman ke6ewa da shi..Ya so ya fito kai tsaye ya bayyana masa halin da ake ciki amma 6acin ransa yake gudu, bayaga haka ma bai san 'karshe yanayin da Rayyan zai kar6i zancen ba shiyasa bai yi hakan ba.
Sai 'karya ya yiwa Rayyan da cewar an kawo sabon tsarin birth certificate yanzu kuma da shi suke amfani...kuma ba'a cirewa Arfan nasa ba dan haka ranar da suka shirya yi masa birth certificate din sai suzo shi da matar sa, akwai test akwai kuma sign da zasu yi.
Da mamaki Rayyan yake duban sa..." yaushe aka samo wannan tsarin kuma..?"
Inji Rayyan dake duban sa.
Fwwaz yace
" Just recently, bamu ma fara amfani da tsarin sosai ba but da yake tsari ne mai kyau that's why i prefer it than na baya, sai kuma naga dacewar mu fara a kanka..."
" Amma bani da labari..."
" ba lallai ka sani ba ai, tunda sai ka ga dama kake lekomu..." Fawwaz ya karasa yana murmushi.
" Toh why not ayi yau 'din kawai, tunda gamu gaba 'daya.."
" a a ba lallai sai yau ba if kun shirya kawai kai min magana...sai kuzo.."
" a a ayi yau 'din tunda gamu zan iya.mantawa ma kasan aiki na min yawa yanzu..."
" Hakane..toh bismillah...muke ko"
Fawwaz ya fada yana mikewa tsaye.
Cikin ransa yake fatan Allah yasa komai ya tafi masa a tsari kamar yadda ya faro.
Lab Fawwaz ya kaisu aka ja jinin su da na yaron da Amrah da Fawwaz yayi basaja da ita kawai.
Cikin gaggawa akayi aikin aka fitar da sakamako, a shirin Fawwaz cewa yayi da details 'din kan test result din za a cike birth certificate din.
Rayyan kam tuni ya fara mitar shi fa ya gaji, wannan tsarin yayi tsauri da yawa.
Ko da aka kawo result din hannun Rayyan aka damka su, Nurse da ta kawo bata wani 6ata lkc ba tayi waje abinta.
Bi yayi ya karanta amma tamkar ba likita ba gaba 'daya sai ya kasa fahimtar komai, ya karanta duk biyu ya kai sau uku amma still kansa ya kasa bashi abinda yake dai- dai.
Gani yake tamkar idanun sa ba daidai suke gane masa ba.
" Fawwaz wai me nake gani haka ne..?"
Yayi maganar yana mi'kawa Fawwaz papers din fuskar sa a yamutse.
Kar6a Fawwaz yayi shima ya duba ya kuwa saki hamdala cikin zuciyar sa dama burin sa kawai shine ace komai ya zo 'karshe Rayyan ya fahimta..sai kuwa gashi cikin sauki abin ke tafia.
" Toh ranka ya da'de aboki na Malam Rayyan, sakamakon fa nunawa yayi cewar babu ala'kar jini tsakanin ka da sabon jaririn ka....."
" Ya isa da Allah Fawwaz,
wannan wace iriyar magana ce....taya ma za'ai hkn ya kasance? su ma'aikatan lab din makafi ne ko kuwa menene da zasu canza mana sample da muka bayar...?"
Baya Fawwaz yayi ya jingina da kujerar sa yana sakin huci mai zafi...
" Amma dai kai kanka shaida ne bamu ta6a samun matsala irin wannan ba a wannan hospital 'din ko..?"
" Shine a kaina za'a fara samu...?
Yayi maganar yana mi'kewa tsaye cike da zafin rai.
" Ina kuma zaka...?"
Fawwaz ma dake mi'kewan ya tambaye sa da mamaki.
" Lab din zanje inji dalilin su na yin haka..."
Yayi maganar batare da ya dakata da tafiya ba.
Bayan sa Fawwaz ya bi da hanzari yana ro'kon sa kan ya dakata amma Rayyan ko kula sa bai yi ba tamkar ba dashi yake magana ba.
" Dr Rayyan kayi ha'kuri mana, in Test 'din ne baka yadda da shi ba sai mu sake yi da kan mu ni da kai ai zamu fi tabbatarwa...kuma zuciyar ka zata fita a wasi wasi.
Hakan kuwa akayi sabon gwaji suka sake Fawwaz da kansa yaja jini shi da Rayyan sukayi aikin sai dai tuni akalar test din ya sauya salo daga birth certificate zuwa na DNA test 'karara.
Koda sakamako ya fito ya zam exactly kamar na farkon ne babu kuskure ko guda.
Tsaye Fawwaz ya mi'ke " Ai dama na fa'da maka, komin mu na tafia ne bisa tsari, ina tabbatar maka da cewar babu kuskure cikin wancan sakamakon tamkar dai yadda nasan baka ga alamun kuskure cikin wannan ba..."
" Fawwaz kasan me kake fa'da kuwa, dubi fa kaga abinda sakamakon nan ke fa'di shine babu kuskuren?.. ana maganar Arfan ba jini ba ne kake cewa babu kuskure...?
" Tabbas kuwa.."
Fawwaz ya tabbatar masa.
" Toh na waye...?"
Rayyan ya tambaya cike da mamaki.
" Mu koma office first..."
Cewar Fawwaz yana juyawa.
Amrah dake nan cikin sauran Nurses suna hira har ta gaji da zama bata kuma san me ya ri'ke Rayyan har haka ba...kaddai patient ya tsaya dubawa ya barsu yashe a reception sai faman 'diban jinin su ake babu 'kakkautawa.
Ko dai yau aikin likitacin nasa ya tashi masa ne akan su...?"
( Mace ki jira dai madam zaki ga aikin likitanci).
Koda suka koma office Fawwaz zama yayi bisa kujerar sa, haka ma Rayyan yana duban sa.
" Fawwaz plz tell me me ka sani akaina kake 6oye min, I can see something in ur eyes that worth bcuz birth certificate kawai ake wannan abin but somthing else, which I did'nt know..pls tell me ka cire ni a duhun da ka sani...."
Tsaye Fawwaz ya mi'ke ya nufi jikin window yana mai cusa hannayen sa duk biyu cikin aljihun wandon sa.
" Yes Rayyan i owe u these...Hakika na san wani abu akan ka Rayyan, but nasan ba lallai ka fahimce ni ba, ba lallai ka yadda da zance na ba...ni kaina lamarin ya girgiza ni, ya kuma bani tsoro, da ace labari aka bani lallai bazan ta6a yadda ba but I heard it with my own ears, kuma ko ban fa'da maka yanzu ba ina tabbatar maka da cewar watarana dole sai na fa'da maka...amma hausawa sun ce da sassafe ake kamun fara...bana so ka rayu cikin duhun da tunanin ka bazai iya fiddaka kwana kusa ba...".
" Ban fahimce ka ba fa me kake son fa ne wai..straight to the point plss..."
" I heard ur wife saying....."
Nan ya labarta masa duk abinda yaji da ranar da kuma lokacin da duk yaji abin, Rayyan mutuwar zaune yayi yana duban fawwaz, yama kasa bawa maganar matsuguni a zuciyar sa balle ya samu damar yin nazari akanta.
Cunkushe yaji zuciyar sa gaba daya banda wani 'daci da juyawa da kansa ke yi.
Da yaga alamun Rayyan kamar bai yadda ba Fawwaz sai ya 'daga wayar sa ya 'kira waccan Nurse 'din akan tazo bata aiki ma a lokacin amma da ganin 'kiran ogan nata batare da 6ata lokaci ba ta shirya ta taho.
Rayyan na ganin ta ya gane ta tabbas tare da ita suka kar6i haihuwar Amrah ranar can, ita ce kuma tace ya tafi zata kimtsa su.
Fawwaz ne ya tambaye ta tsakanin ta da Allah ta kuma tabbatar da cewa tabbas sun tattauna da Amrah kan hakan dan ta fa'da mata ne out of guiltiness neman mafita take a lkcn.
Rayyan ji yayi jikin sa ya mai nawi, Salati kawai ya fara saki a zuciyar sa.
Fawwaz ne ya sallami Nurse tayi gaba abinta tana tunanin toh wa ya kai masa zancen shi kuma, ita dai har ga Allah batayi niyyan tonawa ba amma da aka riga aka kai wannan level din bata da yadda zata yi domin 6oyewar ta kan iya zama wani abu daban...bata kuma san iya inda zancen zai tsaya ba, bata ta6a nufin kowa da sharri ba sannan bata cusa kanta cikin lamarin mutun ko dan gudun abinda zai iya zuwa ya dawo amma Amrah 'karfi da yaji ta cusa ta cikin lamarin da kan iya zame mata matsala watan wataran...fatan ya tsaya iya haka nan.
" Fawwaz kasan babu irin wannan tsakanin mu, Pls ka fada min ba gaskiya bane wannan maganar, ba gaskia yarinyar nan take fada ba....".