← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 218

Sashe 8

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda yayi da Hajja kuwa kin amince masa tayi karshe ma tace da kudin da zai yi auren gwamma yaje ya karasa ginin gidan sa su koma can ta rabu da alakakai in kuma ba zai yi hakan ba toh ya biya mata kudin jirgi ta koma ta sake sauke farali dama ta dade da zuwa tun mahaifin ta na da 'dan abin hannun sa lokacin ya biya musu ita da mahifiyar ta suka je farkon auren ta da mahaifin Baban Abdul din tunkan ta san zata haife shi ma.

Kwana biyu kwarara Baban Abdul bai kara yi cikin gidan ba ya kara gaba saboda haushin Hajja ta hana sa cika burin sa na auren Zaitun.

Ita kuwa daga lokacin rayuwa ta kara yi mata dadi dan babu me takura mata yanzu, Hajja ce kadai taga ta sake ninka tsanar da tayi mata abaya amma dayake tasan dalilin sam hakan bai dame ta ba.

Daga karshe ma daina ganin Hajja tayi a gidan bata san ina ta tafi ba bata kuma tambayi Mmn Abdul ba dan itan tun asali ba gwana bace wajen cusa kai in da ba hurumin ta ba.
Zuwa lokacin kuwa tuni Maman Abdul ta yaye Ahmad shiyasa Mufeedan ta ke samun cikakkiyar kulawa.

_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️...4

......Bata yi kasa a gwiwa wajen fara bawa yarinyar kunun ba sai dai me kokadan Feefy bata son shi, idan ta bata ma ta rinka amai kenan sam ta rasa dalilin hakan..gefe guda kuma tsananin tashin hankali take shiga idan taji ko ta ga yarinyar cikin wani irin yanayi.

Maman Abdul ce ta bata shawaran cigaba da bata a hakan inda a hankali zata saba da shi tunda watannin ta sun riga sun kai gejin da zata iya sha din.

Inda tace ai ba dan ma shakkan zuciyar Zaitun da take ji ba da tuni yarinyar ta jima da fara cin abinci dan ko ba ita ba hatta su Siyama sun so su fara bata abinci idan suna ci amma Maman sun ke hana su.

Ido Zaitun ta waro kan Maman Abdul din.." bakya ganin tayi karama ne Maman Siyama watannin ta hudu ne fa kacal ko zama me kyau ma yaushe ta fara shi, ni da cewa ma fa sai ta kai watanni takwas kafin in fara bata abinci".
"..ahh haba har watanni takwas be yi yawa ba Zaitun, wai ni tausaya miki nake ne duba da yadda kike ta fadi tashin nan.."
"...saboda ita duk nake yi ai Maman Siyama"
"Nafi kowa sanin hakan Zaitun shiyasa nake so ki dan sassauta afara bata kunun yanzu muga yadda hali zaiyi.."
Zaitun bata sake musu wa Mmn Abdul din ba, dan tasan duk abinda matar ke dora ta akai bai ta6a cutar da ita ba, bata ta6a dana sanin bin shawaran Mmn Abdul ba dan haka wannan din ma tana da yakinin Insha Allahu bazata yi ba.

Kudi kawai ta bawa Mmn Abdul din ita ta aika aka siyo gyada ta gyara aka marka'da mata dashi ake yiwa Feefyn kunu amma ba'a saka mata tsamiya shiyasa duk ranar da Zaitun ta samu sukuni ta kan kara mata garin madara akai.

Cikin rashin sa'a Mufeeda sam bata son kunun nan in an bata dawo dashi take yi in an matsa akai mata dura kuwa..haka zata harar da shi gashi ta rika kuka kenan taki yin shiru.

Hankalin Zaitun tashi yake idan taga hakan, cike da marairaita idanu ruwa ruwa ta dubi Mmn Abdul tace" dan Allah a daina bata haka nan Mmn Siyama ki ga fa yadda take kuka.."
" Ki bari a hankali zata saba ne, ba'a biye ta yara Zaitun in ba ke bama har tsawon wani lokaci zaki dauka kina wannan hidima da celarac da madaran bacin ina da tabbaci ko cikin ki baki bashi kula yadda ya dace kwatankwacin yadda kike bawa yarinyar nan, dubi kanki fa Zaitun sittirar kirki baki sawa baki damu da duk wani farin ciki ko jin dadi naki na kanki ba, takalmi idan kika siya kika fara amfani dashi ke da canza sa har sai ya daina amfanuwa a kullun ke dai Mufeeda! Mufeeda!!..babu abinda Mufee ta rasa a yanzu, kema ki ringa yiwa kanki adalci dan Allah Zaitun".

Jikin Zaitun sanyi yayi sosai..tarasa meyasa a kullun Mmn Abdul ke gani kamar ta zurfafa a kaunar da take yiwa Mufee ne, bata san cewa ita din ita ce jigon farin cikin ta ba ne, baya ga hakama alkawari ta daukan ma kanta cewar zata zame mata Garkuwa, ta kula da ita gami da bata kariya ta ko wani irin fanni matukar hakan bazai sa ta sa6awa mahaliccin ta ba.

Kalaman Mmn Abdul sosai ya sanyatar mata da jiki, hakan yasa bata kara magana ba ta jure kawai aka cigaba da bawa Mufee kunun nan ahakan kuwa tun bata so har tazo ta saba da shansa.

Watannin su shida a gidan fitinar Baban su Siyama ya ishe ta sosai, dan har kara ramewa tayi saboda damuwa, tuntuni ta fara tunanin barin gidan amma zuciyar ta ta kasa tsaida mata inda ya kamata bayan nan din, kuma ma takan tambayi kanta da wani kudin zata sake neman hayar, ko nan din ma albarkacin wancan kudin dake hannun ta ne kuma tuntuni da jimawa labarin su ya shude, 'dan wanda ake biyan ta wajen aiki kuma hidimar kanta da ta Mufee ba barin kudin yake sukai wani lokacin ba, dan ma ahakan Mufeeda kadai take siyawa abinci ita kam lissafin cin abincin ta a cikin kudin duk babu shi.

Da gari ya waye idan ta tashi ta dama kunun Mufee ta juye cikin 'yar teaflask din da Mmn Abdul ta bata shawaran siya ta kuma bata shawaran siyan karamin kettle tunda ba girki take yi ba duk wani hidimar ta ta ruwan zafi ce.

Wankan ta da na Mufee sai 'yan wankin kayan da Mufeen ta kwana da shi da yake koda wasa bata yadda ta rabu da omo a dakin ta da sabulu sai dai in abin yafi karfin ta ne.

Da zarar ta gama da yarinyar shikenan sai ta shirya ta wuce wajen aikin ta tuni ta cire batun yin breakfast a tsarin rayuwar ta..abincin da ake basu na rana a wajen aikin shine kullun mahadin breakfast da lunch dinta, ta jima da sabawa cikin ta da hakan.

Sai kuma in ragowar na siyarwar ya rage zuwa lokacin tashin su Hajiya Talatu nada halaccin bar musu su raba tsakanin su duk da irin hakan ba kullun yake faruwa ba amma duk ranar da hakan ya farun ba karamin faranta ran Zaitun yake ba.

Duk iya zaman ta a wurin kuwa mutun guda daya tak ta saba da shi wato _Adam_.

Adam ya kasance 'da ne ga kanwar Hajiya Talatu da ta rasu shekaru ashirin da biyar baya wanda bayan rasuwar mahaifiyar sa rikon sa sai ya dawo hannun Hajiya Talatu kuma shi kadai gare ta Allah bai ta6a bata haihuwa ba, tayi aure har mazaje uku amma bata samu rabo da ko guda daga cikin su ba, shiyasa gaba daya ta hakura da maganar aure ta kama sana'ar ta wanda aganin ta yafiye mata yawon auren duba da cewa shekarun ta sun riga sun ja me kuma zata sake nema bayan taga ta inganta rayuwar marayan danta guda 'daya tilo da Allah ya bata.
Dalili kenan da ya sanya ta dauki son duniya ta daura akan Adam.

Farkon zuwan Zaitun wajen bata ta6a ganin sa ba ashe baya gari ne lokacin yana can kudancin kasar nan wajen bautar kasa..dan Hajiya Talatu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta bashi ilimi ingantacce.

Bayan dawowar sa ne Zaitun ta lura da shi da kusan kullun sai yazo wajen musamman da rana yakan zo yaci abinci ya kara gaba.

Kuma sau tari idan Hajiya na bukatan wani abin shi take kira ya siyo mata na kayan abincin da ake amfani da shi a wurin ko wani abu daban...sosai Zaitun ta lura da sauqin kan da Adam ke da shi da kuma haba haba da jama'ah dan duk lokacin da yazo wurin sai yayi musu sannu da aiki bai ta6a binsu da mummunan kallo ba duba da cewa karkashin mahaifiyar sa suke aiki.

Zaitun bata ta6a zaton Adam ya san da zaman ta a wurin ba sai ranar da ya kasance bata zo wajen aiki ba sakamakon zazza6in hakori da Mufeeda ta tashi da shi.

Daga chemist da ta kai yarinyar ta yanke shawaran zuwa wajen aikin ta tai bayani dan kar Hajiyan taga shiru kuma ba wani bayani.

Bayan ta gama da Hajiyar ta fito ne kan hanya suka ci karo da Adam inda ya bita da kallo..." wannan ba Zaitun bace..?"
Yayi tambayar yana me juyowa ya dube ta cike da mamaki yake sake yawo da idanun sa kan Zaitun din.

Tsayawa tayi tace nice tana kakalo murmushin da iya fuska kawai ya tsaya mata dan ita kadai tasan irin halin da take ciki hakan ma dan mai Chemist din da taje dazun ya kwantar mata da hankali da faddin ai ba wani abu bane zazza6in fitan hakori ne kuma shike sata gudawan da ta kwana tana tsula tsulawa, shine ya tashi hanakalin Zaitun gari na karasa wayewa ko Mmn Abdul bata san da fitar ta ba balle tasan abinda ke faruwa.
" Ina kwana" tace da shi tana mai kawar da duban ta daga gare shi dan ba saba magana tayi da shi irin hakan ba sam- sam ma bata san cewa har sunan ta ya sani ba inba yanzu da ya ambata taji ba.
Adam bai bi takan gaisuwar da tayi masan ba illah tambaya da ya sake jifan ta da shi.." Ina zuwa haka ko yau din babu aikin ne...?"
" a a akwai ni din ce dai bazan samu daman yini wajen aikin ba..."
Bata ma kai ga rufe baki ba yace " saboda me..hala matsala aka samu tsakanin ki da Hajiyar ko..?'
" Da alamu wannan ya kware wajen zayyano tambayoyi."
Wannan maganar cikin zuciyar ta ne tana me yatsina fuskar ta.
A fili kuwa kai ta girgiza masa.." ba haka bane...'YATA CE bata jin dadi shiyasa".
Chapter 8 · 0% Book details