Sashe 76
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana biyu da faruwar wannan lamarin babu wani abu da ya sake shiga tsakanin ta da Amrah, hasalima daina ganin ta tayi, ko ta shigo aikin ta basu haduwa da Amrah har ta kammala ta bar sashen ita kamma sai tafi sakewa da hakan, saboda ba kaunar tashin hankalin nan take yi ba sam a dole take biye mata...baya ga haka ma Ammi ta sake bata hakuri gami da garga'dan ta kan biyewa Amrahn, ta kuma fahimci Ammi, musamman sbd cikin da suke matukar tattali da Amrahn ke 'dauke dashi, kusan kaf ahalin ta lura duk wata kauna da soyayyar su kan cikin suka mika ta, ita kuwa bazata so tayi ta mata musu rai a banza ba, dan ta lura indai akam cikin nan ne toh kuwa ba sauki zata samu daga gare su ba duk kuwa da irin 'daga mata 'kafa da Ammi take bazata iya kawar da kai kan gudan jinin jikan ta da suke daukin zuwan sa duniya ba...hakan yasa ta yanke shawarar kiyaye komai da zai iya hada ta da Amrah kuma Alhamdulillah itama Amrah kamar tasan nufin ta sai ta ja baya.
Bayan kwanaki biyu...
Zaitun na kitchen tana ha'da musu abincin su na dinner ta fara jiyo hayaniyar Amrah, da sauri ta waiga ta ga Moopy na nan kitchen tana wasan ta kasan ta tiles, hakan ya tabbatar mata da cewa ba da ita take yi ba.
Ajiyar zuciya ta sauke gami da hamdala a fili.
Ka'dan da ka'dan ta fara jiyo hayaniyan na kusanto wa kitchen inda take.
Bata fahimci komai cikin maganar Amrah kasantuwar amsa kuwwa da maganar ke yi kuma ba cikin natsuwa Amrah ke maganar ba.
Har sai da Amrah ta iso bakin kitchen tana masifar wai Zaitoon ta fito mata da sarkar ta data sace mata in ba haka ba wallahi sai ta sa an mata 'daurin da babu uban da ya isa fitar da ita.
Sosai Zaitun tayi mamaki jin wai ita Amrah ke tuhuma da sata satan ma na sarkar Zinare ita kam me zata yi da wani abu wai shi sarka a rayuwar ta.
Duk kuma yadda taso fahimtar da Amrah abin ya faskara kokadan bata bata damar hakan ba sai ma sake azalzalar ta da take tana kumfar baki.
Abin takaici ko da mai gidan yaji hayaniyar su ya sakko ma ko tankawa Amrah bai yi ba balle ya tsawatar mata kan sharrin da take shirin kullawa Zaitun.
Kokarin ficewa ma yayi daga 6angaren Amrah ce tayi saurin dakatar da shi da fadin" Baby kace ta fito min da sarka ta in ba haka ba wlh sai na sa an 'daure ta..."
Ta karashe maganar tana wani jijjiga kamar wata jaruma.
Kallon Amrah yayi cikin ido sosai, bai ga alamun gaskia ko 'yar ka'dan tattare da ita ba, yasan ba mmk huce takaicin ta yasa ta biyowa ta wannan sigar...ba yau yasan Amrah ba, ba tun yau ya karanci yanayin ta ba.
Ga Zaitun ya maida duban sa da take tsaye wuri wuri da idanu waje, kallo 'daya yai mata ya 'dauke kansa ganin yadda idanun ta suka cicciko..." Ki bata abinta in ke kika 'dauka pls bana son wannan hayaniyar...".
Tamkar zatayi aman wuta haka take jin zuciyar ta, wai yau ita Zaitun Ahmad Kyari ake tuhuma da sata? sharrin sata fa..?
Shin shi talaucin hauka ne? Ko kuwa rashin galihu ne haukar? Koko rashin gata kawai yasa akai mata wannan sharrin?
Saboda rasa abin fa'da kawai sai ta ringa bin su da kallo 'daya bayan 'daya hawayen ma ya kasa gangarowa.
Ba abinda yafi tsaya mata arai irin furucin Rayyan, a tunanin ta shi din yafi Amrah hankali, a tunanin ta zai dakatar da 'kudurin Amrah ne, amma sa6anin hakan sai ma biye mata da yayi..kenan sun taru sun ha'de mata baki ne, ko dai dama bakin su 'daya, ba mamaki tare suka yi shawarar hakan dan su tozarta ta dama tasan duk ba kaunar zaman ta gidan suke ba...baya ga haka meyasa daga fadin magana har ya hau ya yadda.
M
Toh ita a zaman tan nan idan ta saci sar'ka mai zata yi da shi? ina zata kai sar'ka cikin duniyar nan, in satan zata yi meyasa bata yi tun abaya ba sai yanzu..?
Meyasa basa ta6a fahimtar ne wai?, kan abubuwa da dama sai sun 'kalubalance ta?.
Shin zama da su dole ne ko kuwa 'daure ta akayi tare da su.
Amrah da kanta ta daga waya ta 'kira Ammi ta sanar da ita abinda ke faruwa tana cika tana batsewa.
Allah ma yasa Ammin na gari, cikin lokaci 'kan'kani ta bayyana 6angaren Rayyan cikin tashin hankali, rabon ta 6angaren Amrah har ta mance.
" Wai me yake faruwa ne...?"
Ammi da shigowar ta kenan ta jefa musu tambayar tana duban Rayyan dake zaune bisa kujera yana duban dramar tasu dan tun dazun ya rasa me ma zai ce ne.
'Yar takaitacciyar kalma zata raba husumar amma yasan Amrah zata birkice masa ne idan yayi hakan, dalili kenan da ya sanya shi komawa gefe yana duban su dan ganin karshen yadda abin zai kaya, kuma ma ko ba komai yau zai morewa kallon yadda Zaitun zata shiga taitayin ta duk da ma ya fahimci tuni tayi sanyi tun farkon maganar.
Gira ya dage sama yana fadin" haka na gansu Ammi wai Sar'kar Amrah aka sace...".
" Shine sai aka yi yaya...?"
Ta sake tambaya tana ha'de ranta gami da dawo da duban ta ga Amrah.
" Kar ace min zargin Zaitun ake da satan sarkar...?"
Shiru suka yi dukkan su yayin da Zaitun tayi 'kasa da idanun ta Amrah kuwa kawar da kai tayi tana wani girgiza jiki.
" Tambayar ku nake fa kun min shiru".
Ta sake fadi a dan zafafe.
Amrah ce ta bu'di cike da zafin kai tace.." ai wacce tayi satan ta san kanta in dai ba goye mata baya za'a yi ba kam..."
Ta 'karasa maganar tana kyabe baki gami da 'yan harare-harare.
Rayyan daga inda yake ya tsura mata idanu sosai yayi mamakin da yadda ta amsa maganar Ammi...bai ta6a ganin hakan da idanun sa ba sai yanzu.
Duk wasu abubuwa da Amrahn ke yi na kaucewa mu'amala tsakanin ta da Ammi yana sane amma wannan ba'kone a gare shi.
Tsaye ya mi'ke ya taho kusa da su da nufin kashe mata warning kan mahaifiyar sa.
Daidai lokacin da Ammi.ke sake fa'din..." Amrah ban san rigima fa, kin duba sarkar taki da kyau ne da kai tsaye zaki ce ga wanda kike tuhuma da rashin ta...?"
" Da ban duba ba ai bazan ce ita bace, ni dai kawai a fito min da sarka ta wlh ko na yi maganin mutum cikin gidan nan, dama nasan ba kauna ta ake yi ba tunda ake fifita wasu karere akai....."
Lafiyayyan marin da ya sauka saman kuncin ta ne ya hana ta dakatar da maganar da ta dauko...
Ba kowa bane kuwa face Rayyan da tuni ya hassala ganin yadda take bawa Ammi amsa tamkar sa'ar ta.
Sai dai yana shirin kara mata wani.marin Ammi tayi saurin rike masa hannu ramta 6ace" Haba Rayyaan, miye hakan kuma...baka da hankali ne mace zaka yiwa irin wannan bugun, kuma ma a gabana...?"
Bai bi takan maganar Ammin ba, tuni idanuwan sa sun koma jajajir kuma still Amrah yake kallo duk wani mutsa mutsan 6acin ransa sun gama bayyana saman fuskar sa..da 'daya hannun sa da Ammi bata rike ba ya nuna Amrah" Ke har iskancin naki yakai haka Amrah...Ammi ce fa, mahaifiya ta....?".
Ya ma kasa magana illah dafe kansa da yayi da hannu 'dayan tsabar yadda ransa yakai kololuwa wajen 6aci har kansa na mai sara.
Ammi bata bi ta kan shi ba kamar yadda bata bi takan abinda ya furta ga Amrah ba..abu biyu kawai ke gaban ta a yanzu...shine bugun Amrah da yayi sai kuma maganar da asali ya kawo ta 6angaren.
" Bana son shashancin banza Rayyan, I always says ka koyi sarrafa fushin ka ko ban san isa na hana ka abu ba..?"
Da sauri ya 'dago ya kalle ta yana mai dauke hannun sa da ke kansa.
Da kyar bakin sa ya iya furta
" Haba Ammi..."
" Daga yau..duk hukuncin da zaka yi kar ka sake ka sake 'daga hannun ka dan bugun mace kana jina...?"
Kai ya 'daga mata alamar yaji..." Shin ka mace waye Amrah ne? Mancewa kayi da yanayin da take ciki ne...?"
Shiru bai ce komai ba illah Amrah da ya juya ya kalla da ke dafe da kuncin ta har yanzun hawaye kawai ke mata zarya.
Kan cikin ta ya sauke idanun sa take yaji mugun tausayin ta ya tsirga masa," uwar 'ya'yana ce..."
Zuciyar sa ta furta masa take ya lumshe idanu yana jin gaba 'daya tamkar wani ne bashi ba" Ammi tafi kowa kauna da burin ganin 'ya'yan su a duniyan nan bazai so ya ringa 6ata mata ba."
...a fili ya furta" I'm so sorry Ammi...".
Yayi.maganar ne yadda shi da ita kadai zasu ji musaman sbd kusancin dake tsakain su sai ko Amrah dake daura da su amma zurfafa tunani da tayi ma bai bari taji abinda ya fadan ba sai dai na Ammi da ta dan yi da sauti kadan tana duban sa.
" Oya je ka sha ruwa yanzun nan..".
Ammi ta bashi umarni inda tayi maganar tana mai sakin masa hannu.
Ga Zaitoon ta maida duban da tuni ta durkushe saman gwiwar ta tana kuka 'diyar ta na jikin ta ta lafe itama...tun lokacin da Rayyan ya saukewa Amrah mari Zaitoon ta durkushe dan gaba daya tsoro da fargaba ne suka shige ta, sai a lokacin kuma hawayen ta suka 6alle gaba 'daya, abinda bata ta6a gani ba, abinda bata ta6a zaton zai faru tsakanin su ba musamman sbd irin kaunar da ta tabbatar suke yiwa juna, yau ita kam tata ta kare, akan ta Rayyan ya daga hannu ya mari Amrah?, duk akanta suke wannan 6acin ran, hatta Ammi da ta shigo fuskar ta babu alamun walwala koka'dan....
Gani.take tamkar zasu yi gunduwa gunduwa da naman ta ne yau din nan, dalili kenan daya sanya ta sake matse 'diyar ta ajiki sosai tana fadin" Yau Zaitoon ina kika kawo ku...?"