← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 218

Sashe 188

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahalin Amra sun 'dauki fin sati biyu suna cikin yanayin zulumi, kunci da damuwa suma..Amra duk tayi sanyi ta rame kamar ba ita ba, dama ba wani auki gare ta ba sai ta 'kara zama very slim sai haske da ta 'kara, cikin lokacin Rayyan yazo har gida ya kawo mata takaddar sakin ta, ko neman ta bai yi ba balle Arfan da ya turo tun satin da ya wuce tare da mai kula da shi, bai nemi jin komai daga gare ta ba kawai ya bada takaddar ta a hannun mahaifin ta bayan gaisuwar mutunci da sukayi ya yi tafiyar sa.

Tasan shikenan yanzu kam ta'kurunkus komai ya 'kare mata ne, ta faru ta 'kare tsakanin ta da Rayyan tunda har da hannun sa ya rubuta mata saki har guda biyu...ya kuma 'kara da fa'din idan ta samu miji tayi auren ta.

Gaba 'daya jikin ta yy sanyi, wannan karan hatta Ameera bata iya labartawa ba, sai dai tayi ta kuka kullum bayan ta rufe kanta a daki...tayi kuka har kuka ya zame mata jiki..kwallan ta suka daina zuba sai dai tayi na zuci.

Tayi nadama, tayi Allah wadai da hali irin nata, nadamar da bata jin zai yi mata amfani shine ya shige ta tun barowar ta asbitin mahaukata.

Takaicin kanta sosai da sosai take ji, da ganin rashin wayon kanta da kanta.

Ibada kuwa yanzu sai dai a koya daga wajen ta sbd yadda ta du'kufa rokon Allah gafara sai abin ya baka mmk, a kowani lkc burin ta shine Allah ya yafe mata kurakuran da ta aikata.

Mahaifinta kuwa kullum indai yana gari sai taje ta gaida shi duk da ba amsawar kirki yake yi mata ba amma bata fasawa bata gajia da zuwa wajen sa..ta riga tasan koma menene ita tajawa kanta.

Amra duk tayi sanyi rayuwa ta juye mata..juyi irin na waina a kasko...Kusan hakan ke faruwa kuma a 6angaren Mummyn ta.

Ammi kanta bata san Rayyan yy sakin ba sai da ta fara mitan yawon da iyalan sa ke yi ya isa haka, sbd kullum basu nan yau suna can gidan gobe suna nan tace abin ya ishe ta haka nan yaje ya dawo da su gida yafi.

Toh kawai yace amma bawai dan zai yi hakan ba.
Tun Ammi nasa ran ganin su har ta fahimci bashi da niyya da kanta ta fara saka rana nan ma sai yake zamewa da kawo uzururruka adai dai lkcn da yasan zata yi masa zancen. Ko kuma sai ya tsiri tafia ba gaira bb dalili inyayi kwanaki sai ya dawo yace an 'kira shi a wani gari aiki ne, ko kuma yace branch na companyn su ke neman sa.

Tun Ammi bata fahimta har ta fahimci dojewa kawae yk,
Sai da tayi dagasken gaske kafin ta samu ta ritsa shi akan maganar dan ta gama harbo jirgin sa tun ba yau ba, gashi ko maganar taso suyi da Antyn sa itama bata samun kyakkyawan goyon baya sai dai ta kyabe baki tana kawar da kai...da alamu dai bakin su 'daya da shi.

Abin ya ishi Ammi..dan haka a ranar ta ce ya shirya da ita suje nan ya so zamewa itama ta tirje ta toshe kowacce hanyar zamewa.
Dole fa aranar sai da ya fito fili yy mata bayanin ai ya saki Amra tun ba yau ba.

Ammi sosai kalmar sakin ya doke ta a uzubillahi minash shaidanir rajim...ta furta kamar wani abu ne ya tunkare ta.

Ai kuwa ta inda take shiga bata nan take fita ba ta ringa masifa, ta yi ta fa'da tamkar ta ari baki, inda ta ha'da hadda Anty Madeena akan ai ita ke goye masa baya yake komai, ya kashe auren Marwa shima gashi ya kashe nashi sun zama 'daya...banda shashanci mene amfanin hkn toh.

Ita a ganin ta bai kamata yy gaggawan sakin ba, ai har abada Sultan nasune, dan bayan wani yanayi ya same sa bai kamata ace sun juyawa zuri'ar sa baya ba, yadda kowa yake gani ya kuma a kuma ce Arfan nasu ne meyata bazasu cigaba a hakan ba, su tallafi yaron kamar yadda suka tallafi Sultan..Rayyan yace" Allah ya kiyaye Ammi...kina nufin har kin manta abinda Sultan yai mana agidan nan da har kk tunanin a sake maimaitawa? mu sake kwaso wani mu kawo cikin mu muyi rainon makashin 'ya'yan mu ko Ammi...?"

Kai Ammi ta girgiza sannan tace" ance maka duk an taru ne an zama iri 'daya Rayyan...kenan dan ka aikata alkahiri an saka maka da sharri sai ka bigi 'kirji kace ka daina yin alkhairi ga kowa kenan har abada a duniya..?
Rayyan ka lura mana...a kullum hanya ake hawa, accident ake, mutuwa ake amma hkn ya hana a daina tafiye-tafiye ne Rayyan? Bb abinda wani 'kalubale na rayuwa zai hana a cigaba da aikata shi..
Ai duk abin da za a yi duk rufin asirin junan mu ne, Sultan Namu ne, haka ma arfan har abada namu ne..."!
Ta kuma ce tunda har ka riga ka saki Amra batare da ko shawara da ni kayi ba, batare da sanina na ba..ya riga ya wuce ya wuce kam domin bani da ikon dawo da zancen baya amma ka sani ka.kuma maimaita irin wannan kuskuren Rayyan zan yi mummunan sa6a maka...kuma ka shirya zuwa jibi da yaddar Allah zamu wuce garin su Zaitoon baki 'dayan mu, Raihana ta riga ta wuce tun kafin itama a kashe mata auren tunda naga yanzu kisan aure kafi gwanancewa akai...dan haka tafiyannan bb ita.."

'Yar murmushi kawai yy...dan yasan Ammin zafi kawai ta 'dauka shiyasa ta fa'din hakan amma ai shi bai ga laifin abinda ya aikata ba, duk 'din su idan yace kowa ya cigaba da zaman auren sa ba shi ba, ba Marwan ba gaba 'daya zaman zargi, raini da rashin ganin darajar juna za'a yi, toh menene amfanin zaman auren da zai kai ka aljanna ba sai dai yaja ka izuwa wuta..Ai Allahn da ya halatta aure shi ya halatta saki.

Wasu maganganun Ammi dariya suke bashi yayin da wasu ke sanya shi nisha'di matu'ka, Ammin sa akwai hikima yana kuma jinjina mata sosai.
Babban abinda yafi tsayawa da burgesa sa cikin maganar Ammin shine batun zuwa wancan garin, bai kuma san dalilin sa na jin da'din ba...tsintar kansa kawai yy cikin tsantsan farin ciki marar misaltuwa.

Kamar yadda Ammi ta tsara tafiyar hkn ne ya faru, domin hatta Rayyan bai nuna za'kewar sa kan batun tafiyar ba gaba 'daya ya barta a hannun su balle Zaitoon da fargaba da tararradin abinda zata je ta tarar acan shi yafi tsaya mata.

Tsoro take ji sosai sai ma yanzu da kwana 'daya ya rage ayi tafiyar take jin ta cikin wani tsananin tashin hankali, most especially idan ta tuna da batun wannan auren na kanta tsoro da fargabar ta kara yawaita yake, ba kowa take kuma jin shakka ba kuma face Yayan ta, da wani idanu zata dube shi tace masa da aure akan ta bacin babban laifin da ta aikata gareshi na tafiyar da tayi batare da ya san da tafiyar ba balle inda ta shige.

Bata yi 'kasa a gwiwa ba sbd fargaban da take ji ya riga ya rinjayi komai.
Ammi ta samu kan batun auren inda ta ro'ke ta akan dan Allah ta sa ya sawwake mata auren kafin su tafi domin bata so tajewa mahaifan ta da igiyar auren wani akanta alhali ba sune sukai mata auren ba, aganin ta laifin ta 'kara ninkuwa zai yi awajen su.

Murmushi kawai Ammi tayi mata, tace da ita" toh" kawai amma ba wai dan zata cikawa Zaitoon 'din burin ta ba domin sun riga sun gama magana da Rayyan akan haka, kuma shima hujjojin sa abin dubawa ne haka ma na ita Zaitoon, sai dai dole na wani ne zai rinjayi wani, shi aure sittura ne ga kowa ce 'diya mace, abu guda da zai iya sa ta bada goyon baya wajen raba wannan aure shine rashin amincewar mahaifan ta, ma'ana in suka nuna basaso...amma baya ga haka fatan zama me 'dorewa take yi musu, zama mai cike da farin ciki da walwala har zuciyar ta, duk da a har yanzu bata ga ko 'dis 'din alamu daga Zaitoon daya tabbatar mata da cewar tana na'am da shi ba amma tasan with time watarana zata so shi da iznin Allah.

*****
....." Innalillahi wa inna ilaihir raji'una...."
Ta fa'da tana tafa hannuwa, salallamin bai dire ba sai da ta kai aya iya yanda yazo bakin ta, kafin ta 'karashe da nuna shi da 'dan yatsan ta.

" Kana nufin kai jinin Jibirilla ne...?"
Da kai ya amsa ta yana mai sakin 'kayataccen murmushin da ya sake 'kawata fuskar sa cike da annuri da farin ciki, duk da Goggon nasa ba cikin natsuwa take ba amma shi kallo 'daya yy mata ya fahimci ita 'din dagaske jinin mahaifin sa ne, duk bakar wahalan da ya sha kafin zuwan sa gare ta a yanzun duk babu su sun kauce, kallon Goggon nasa kawai ya gama wanke masa komai.
Kuka kawai ta sanya ta kuma rufe fuska da dan hijabin da ke jikin ta.

Shi kansa kukan yake jin yi amma ba hurumin sa bane a yanzu domin cikin tsananin farin ciki yake marar misaltuwa.

Hannu ya mi'kawa Bello dake bayan sa ya kuma yi masa alamar shan ruwa da hanzari ya nufi mota dan 'dauko masa ruwan.

Hafiz dake kishingi'de cikin motar a mazaunin driver da sauri shima 'din ya 'dago ya dube sa.
" Ya akayi Bello an dace ne?"
" Naga alamun hakan"!
Cewar Bello yana 'ko'karin farka ledan ruwan ya zaro roba guda babba yana jinjina shan ruwa irin na wannan mutumi, daga ha'duwan su zuwa yanzu bazai iya irga robar ruwa nawa ya 'di'd'dikawa cikin sa ba tamkar mai hanjin roba.
Chapter 188 · 0% Book details