Sashe 199
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ace ba a riga an 'daura mata aure ba bazai ta6a janyewa ba, da bazai ta6a cire rai da samun ta ba, dole zai gwada tashi sa'ar ne har sai yaga abinda hali zai yi, amma a halin yanzu bashi da wannan damar, da ce bbata riga ta zama mallakin wani ba da sai inda 'karfin sa ya 'kare, da bazai ha'kura hakanan kawai ba...zai yi addu'a..kuma ai yana da Goggo.
Wannan labari da kunnuwan sa suka jiye masa ayau, kusan shine labari mummuna na biyu da ya shiga kunnuwan sa akaf din rayuwar sa.
Na farko tarihin mahaifin sa ne..na biyu kuma labarin auren Zaitoon ne, dan ko lokacin da ya rasa a wancan karon bai cire rai da samun ta kamar yanxun ba, a wancan lokacin kwana yake ya tashi da tunani da tsamanin ganin ta duk da bashi da tabbaci.
Amma wannan karo 'daya aka yanke masa kauna da samun ta, karo 'daya komai da ya fara ginawa cikin ransa ya rushe kaf.
Bazai ta6a yadda a kashe mata auren ta sbd son zuciyar sa ba...Zaitoon na tare da shi ko akasin hk dole zai mata fatan alkhairi..ba yaga hk ma a halin yanzu jinin jikin sa take...hkn ma Alhamdulillah bai yi hasara ba, bai kuma bar wani ba'kin ta6o abaya da zai hanata yi masa kallon 'dan uwa babban wa agare ta ba.
Sai dai duk da haka zai fi so ace shine da ita, zai fi so ace shi ya mallake ta ba wani can daban da babu ma wanda yasan asalin sa ba.
Ya bawa Innani shawarar da yasan ta dace, ya bata shawarar da yasan ko bayan bashi baza a kuka da kalaman sa ba, ya kuma nemi a raka shi gidan mahaifin Zaitoonan domin shima ya duba shi da jiki.
Sun yi gaisuwar mutunci tamkar ansan juna dan shi Adam badai raha da sakin fuska ba.
Haka yy kokari sosai wajen danne duk wata ddamuwar da ke cinsa aransa.
Sun tattuna sosai a tsakanin su wanda duk ya gama fahimtar manufar kowa, ya fahimci Bukar sam baya ra'ayin sake tafiyar Zaitoona Kano zaman aure..haka kawai sai ya 'danji sanyi a aran sa...shi dai bai matsa ba..amma koma mai zai faru falillahil Hamdu.
Atare shi da Bukar suka 'dunguma wajen Baffa Liman anan ne suka so samun matsala da shi ma dan shi baya da fahimta sam, duk da dai dama maganar su yazo 'daya ne da Yah Bukar da Baffa Liman kusan ra'ayin su guda ne sai dai kawai manufa ce daban..a fahimtar sa.
Kuma ko da wasa bai bari 'daya cikin su ya fahimci 6oyayyan matsayin Zaitoon awajen sa ba.
Yazo musu ne kawai a matsayin 'dan uwan ta na jini.
Adam yy kokari sosai wajen ganin ya janyo hankulan su duk su biyun, sosai ya ajiye son kansa, soyayyar da yake yiwa Zaitoon din ma ajiye ta yy itama wuri guda kawai ya sa aransa zai yi domin Allah domin ya fahimci cikin mahaifan Zaitoon akwai wadanda son zuciyar su kawai suka sa agaba.
Shi kansa bazai so a salwantar masa da farin cikin 'yar uwar sa ba...tun anan ma ya yada makaman ya'kin sa ya saduda..yana fatan wa kansa canji da wata daban mafi alkhairi...amma da Baffa Liman yace sam, shi fa bai yadda da wannan aure na Zaitoona ba.
Bukar yace shima dai bawai har zuciar sa ba amma indai ya fahimci Zaitoon na so bazai hanata komawa ba sbd bazai so tauye mata hakki ba, bazai so ya sake saka ta cikin 'kunci bayan wanda ta fuskanta a baya ba.
Sai da aka kai ruwa rana kafin Yah Bukar yayi na'am da batun amma da shara'din amincewar ta tukunna.
Shikan sa Adam ma yafi son hakan, domin wata zuciyar tasa na sanar da shi cewa shi Zaitoon take so ba wancan gayen ba...yana ji tamkar nasara na tunkaro shi ne cikin sauki.
Bayan kwana biyu ya sake dawowa duk dai akan maganar.
Yayin da duk tsawon lokacin nan babu Rayyan babu alamar sa.
Hajan.sai ya fara kawo kokonto a zuciyar Yah Bukar amm sbd kar ya mayar da magana baya sai yaja bakin sa yy gum.
'Karshe dai Bukar kasa rike abinda kke ransa yy sai da ya furta shi, yace shi bai ga alamar wannan miji na Zaitoon ya damu da ita ba, yace idan aka cigaba a haka yana tsoron abinda zai je ya dawo, domin mutum abin tsoro ne, yace kar fa suyi kuskuren tura yarinya inda rayuwa zatai mata bakikirin sbd wai halacci, in kuwa hakan ya faru har abada zai ri'ka ji aransa tamkar bai yiwa Zaitoon bikin yar gata da ya jima yana tsarawa aransa ba...zai rika ji tamkar sadakar ta ya 'dauka ya bayar haka nan kawai ba auren daraja ba.
Abbah ne ya taushe shi da fa'din yy ha'kuri ai komai mu'kaddari ne daga mahalicci, ba kuma komai da muke so muke samu kamar yadda muka tsaraba ba, dole akwai shirin ubangiji da ya riga ya rinjayi namu shirin kuma dole mu bisa.
Suka ce haka ne, amma dai a bari aga nan da dan wani lokaci idan babu canji sai asan abinyi.
Duk da haka Bukar ya kasa yin shiru mita kala kala yake yi...tun daga kan batun Rayyan har na rashin samun daman gatantawa er uwar sa da bai yi ba.
Adam ne yace to ko za'a sake biki ne Bukar sai hankalin ka ya kwanta idan ka tabbatar kayi bikin ta kuma ka mi'ka ta 'dakin mijin ta da kanka hala zaka fi jin kwanciyar hankali".
ya fa'da yana yar daria.
" kaga ko mu ma akwai tamu rawar ganin da muke so mu taka a matsayin mu na 'yan uwan ta ai".
Suka 'dan yi daria.
Abban su kuwa yace sam suma yi hakuri dan bb wani biki da za asake, duk shirme ne kawai ba wani abu ba...yace indai biki ne su tari na khausar dake zuwa nan bada jimawa ba.
Dole suka ha'kura suna murmushin 'karfin hali.
A wancan ranar Adam bai yadda ya bar garin ba sai da ya tabbatar ya bada ku'da'de isassu wa Bukar sbd ganin yanayin jikin Abban su Zaitoon yace akai shi asbiti a duba lafiyar shi sosai.
Zaitoon da taji labari sai da tayi kuka, shiyasa har kullum tasan darajar Adam na daban ne aran ta, yakan yawaita cika mata burikan da take faman sa'ka su cikin ranta tun kafin ta kai ga furtawa.
Ha'ki'ka shi 'din 'dan uwane abin alfahari makwafin yayanta.
Tun ranar da ta samu labari cewa shi 'din 'dan uwanta ne take jin ta cikin farin ciki...ta godewa Allah daya azurta ta da samun gwarzayen yayye masu so da 'kaunar ta har guda biyu.
*****
Rayyan bai sake waiwayen su ba haka ma Ammi bata sake yi masa maganar su ba.
Sai da aka cika kwanaki tara cif bata ma san yaje ba sai bayan ya dowa taji lbr.
Ranar da ya sake komawa ma shi kadai ya kama hanya.
Can gidan mahaifin ta ya fara dira suka yi gaisuwa sama sama da Iyami suka sanar da shi ai suna can wajen Innar su...yasan dama suna can din, dama kawai yazo nan 'din ne sbd bin umarnin zuciyar sa.
Ko da ya tambayi Abbah kuwa Iyami kawai ce masa tayi baya gida.
Shima bai bi taktakan batun ba yy musu sallama ya fito bayan yayi mata goma ta arziki.
Bai nemi rakiyar kowa ba da yk ya riga yasan gidan Innan.
Cikin rashin sa'a Inna ce ka'dai a gida, su Zaitoon na gidan Dije 'kawarta tun zuwan ta basu ta6a zuwa ko'ina ba illah gidan mahaifin ta kuma ko can din ma ba kullum take zuwa ba yau shi ne fitar su na farko zuwa wani wuri daban..shima 'din gorin Dije ne ya ishe ta akan ta'ki zuwa taga gidan ta..shine ta shirya suka je.
Bayan sun gaisa da Innani ta bashi ruwa sai ta sanar da shi ai sun je gaisuwa amma bazasu da'de ba yanzu zasu dawo.
Wani takaici ne yaji ya turnu'ke shi, take yayi kicin- kicin da fuska...wato ma ita hankalin ta kwance har ta samu 'kafar yawo agari, to inma tana tunanin zai sawwa'ke mata ne ta samu filin zama da yawo ko hira da nishadi da wasu mazan shi bazai ta6a sakin nata ba, sai dai koma me zai faru ya faru a shirye yake...in bama ta raina shi ba da auren nasa take biye- biyen gidaje batare da sanin sa ba bayan tasan bb abinda yafi tsana irin hakan..da yake ta riga ta raina sa kenan ko me...?"
Ko dayake bazai yi mamaki ba, wacce ta iya zama babu ko 'kwakkwaran mayafi tana hira da daria da wani namijin toh menene sabo kuma dan ta tafi yawon ta batare dda sanin sa ba.
Gashi Inna ba zaman hira tayi da shi ba balle sake saken zucin da yake su tsagaita..Rayyan har ya fara tunanin kawai yayi tafiyar sai dai sam ya kasa...haka nan kawai ya sawa ransa tsayawa yaga iya tsawon da'dewar su, kuma wata zuciyar tasa na kwa'daita masa so da muradin ganin duk su biyun ayau.
Domin ba zai ce Mufee ka'dai idanuwan sa ke bu'katan gani ba, a ha'ki'kanin gaskia hatta ita uwar Mufeen yana da muradin ganin ta, yana kuma da tarin tambayoyin da yake son yi mata su wanda yake ji dole sai ta amsa masa su.
Dalili kenan ma da ya sanya ya bi umarnin zuciyar sa akan ya tsaya ya jirayi dawowar su.
Baya ga haka ma bazai iya irin wannan doguwar tafiyar kuma ya koma batare da ya cikawa idanun sa da zuciyar sa mura'dan su ba.
Rayyan baki 'daya ya cika tamkar zai yi bindiga, fuskar sa ka'dai idan ka kalla kasan bb annuri dai- dai da mis'kala zarratin akan ta, dama tun asali fara'ar bata wadaci fuskar ba da ya ha'du da wannan yanayin kuwa abin kawai sai wanda ya gani.
Gashi mijin Innani ma bayanan yy tafia balle ya samu abokin hira.