← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 218

Sashe 34

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin hakan kwanakin da aka tsara na shiga kotu suka cika aka kuma shiga kotun. Zaitun ko iya daga idanu bata iyawa ta dubi mutane, yadda ma kotun ya cika makil dan sauraren shari'ar ta ina zata fara kallon su, da wani idanun ma, wara su me kyau ma bata iyawa sbd tsananin kukan azabtar da su da aka ringa yi, sau 'daya ta iya 'daga idanu ta dubi jama'ar bata 'kara ba kuma.

Baya da su alkali ne zaune, mutun ne wanda duba 'daya idan kai masa zaka fahimci nagarta da iya aikin sa.
Gefe da su kuma lauyoyi ne masu kare wanda ke kara da wadanda ake 'karan, yayin da nasu ya kasance lauyoyin gwabnati ne kadai zasu gwabza, tama yi mmk ganin cikin lauyoyi masu bayyana kawunan sun hadda masu kare su wai, ita mmkin ta in laifin suka yi dagasken gasken miye anfanin kare su kuma? wacce hujja za'a kare?

'Daya gefen nasu ma wasu manyan Lauyoyin ne daban suma, wanda suka amsa sunan su na lauyoyi hamshakai...wa'danda mafiya yawan su sun zo ne kawai dan saurarar karar ba dan su tofa wani abu ba.
Sannan da yawa sun koka da ganin yanayin Zaitun da karancin shekarun ta.
Can gefe guda kuma ga jami'an tsaro ga kuma masu tsaron Prison da kuma masu kare hakkin 'yan Adam...sai dai ba'a bar 'dan jarida ko guda shiga cikin kotun ba haka kuma ba'a bawa kowa damar 'daukan hoto ko video ba ko da a waya ne kuwa.

Adam Shaheed da ya kasance a sahun farko na masu sauraron karan tun zaman sa idanun sa na kan Zaitun kur...ji yake tamkar ya zubda mata 'kwalla ganin yadda ta koma, duk ta zama wata aba daban kamar ba Zaitun da ya sani ba, wannan yarinya sassanya me tarin hankali da natsuwa, duk wanda yayi mata irin wannan sharrin bai mata adalci ba, shi kansa ma baya jin har abada zai iya yafe wa mai shi...me tayi musu har haka..?
Sosai yk jin mafi tsananin tausayin ta cikin zuciyar sa, wanda sai ma a yanzu daya ganta yaji komai ya kwance masa, sabuwar kauna zazzafa da tarin tausayin ta suka sake diram masa, yana jin dole ne ma yayai wani abu, dole ya tunkari mahaifin nasa game da ita wannan karon ba da yawun kowa ba, da kansa zai je ya nemi wannan alfarmar dan ganin an ceto rayuwar Zaitun din daga fadawa wani yanayi.

Lokacin da Adam Shaheed ya zurfafa a tunani ga wasu mutane abin ba haka yk ba, da yawa na Allah wadai da halayya irin ta tasu Zaitun din ne gaba daya, yayin da wasu ke fatan ayi musu hukunci mai tsanani irin wanda zai sa na baya ma su kiyaye aikata laifi irinnasu, hukuncin da zai sa su raina kansu ko da agaba bazasu sake tunanin aikata irin hakan ba.
Da yawa kuma hankalin su yafi tafiya ga Zaitun suna tunanin abinda yaja hankalin ta ga irin wannan muguwar ta'asar musamman da ya kasance shekarun tane mafi karanci daga cikin shekarun masu laifin.

Daga kan Hameeda shari'ar ta fara inda aka sa ta rantse ta kuma tabbatar akan zata fa'di gaskiya akan duk wata tambayar da zata biyo bayan zaman kotun, Hameeda ta rantse cikin sanyi kamar yadda aka bukata, sunan ta shekarun ta da kuma sana'ar ta, duk ta fadi...tana da aure ko bata da, adadin yaran ta..duk ta basu amsa karshe aka tambaye ta dangatakar da ke tsakanin ta da Rasheed tace mijin ta ne...tana share kwalla daga karshe.
Zata sake magana lauyan ya dakatar da ita....tambayoyin shari'a suka biyo baya.

Daga kan Hameeda ga Zaitun tambayoyin suka koma...itama kuma sai da ta rantse, ta kuma basu tabbacin zata fa'di iya gaskiyar ta.
" Kotu na bu'katar jin sunan ki..."
" Suna na Zaitun Ahmad..."
Ta bashi amsa muryar ta can 'kasa, ga wanda bai san ta ba zai dauka duk tsantsan wahalar da tasha ne, amma ga wa'danda suka santa sun san cewa asali tana da sanyin magana bugu da kari kuma ga abinda ya farun ya kara saukar da ita.
"..Toh Zaitun Ahmad...shekarun ki nawa.?."
" Goma sha bakwai.."
" Kina da aure ne..?"
" a a bani da aure.."
" Toh mene dangantakar ki da Dr Rasheed kamar yadda kowa yk son ji..?"
Sai da ta 'dago ta dubi fuskar lauyan kafin ta sake maida idanun ta kasa ta cigaba da magana.
" Dr Rasheed taimako na yayi."....ta bashi takaitaccen bayanin taimakon da yayi mata.
" Idan na fahimce ki kenan daga ranar da ya taimake kin kuka ha'da kai kuka cigaba da satan dukiya da 'ya'yan al'umma...".
Da sauri ta 'dago kai ta dube shi kafin ma ta furta wata kalma wani daga cikin lauyoyin ya nemi alkali ya dakatar da shi daga irin wannan tambayar domin ya zama ne tamkar cusawa wanda ake kara ra'ayin amsa laifi bisa dole.
Alkali yayi na'am ya kuma ce a kiyaye.
Rigar da ke jikin sa ya gyara gami da sake duban Zaitun yace..." Kafin ha'duwar ki da Dr Rasheed din har zuwa daren ranar da ya taimake ki...a ina kike rayuwa kuma meya fito dake a daren ranar?"

" Yawon bara nake kuma anan titi nk rayuwa nk kwana bamu da muhalli...".
Zaitun cikin ranta ta yanke shawaran fa'din hakan sbd bata so sunan kowa ya fito balle har a shigo da wata ko wani cikin irin wannan azabar da su suka sha, dan taga a bakin Hameeda aka ji sunan Dr Rasheed shima aka kawo shi.
"..kika ce baku da muhalli...ke da waye kenan kike nufi ...?"
Taji ya sake tambayar ta.

Shiru tayi dan ita har ga Allah tsananin son ganin Mufee take bata san inda aka kaimata yarinya ba, duk yadda taji zuciyar ta ta bushe haka tuno Mufee da da tayi ya sanya hawayen ta saurin saukowa.
Sai da ya sake maimaita tambayar kafin ta bashi amsa .." Ni da 'yata ne..".
Da mamaki yace " 'diyar ki, kuma kince baki da aure...?"
"...Erh...'yata ce kawai...".
Wancan lauyan ne ya sake mi'kewa da sauri yana wa alkali ishara da cewa lauya mai tambaya yana 'ko'karin shiga hurumin da ba nasa bane cikin tambayoyin sa.
Alkali yace a kiyaye.
Daga haka ya barta da tambayoyin yayin da kotu ta 'dauki 'kananun surutai jin cewa Zaitun 'din har nada yarinya...dan kowa yaga karancin shekarun ta, amma jin cewa a bakin titina take kwana ya hana da yawan mutanen mamaki sai dai jimantawa da alhinin irin zamanin mu ta yanzu.

Daga Zaitun Dr Rasheed aka yiwa tambayoyin kuma Alhamdulillah duk abubuwan da su Zaitun suka fa'da shima 'din haka yace sai dai abinda ya 'dauki hankalin mutane cikin amsoshin tambayoyin da akai masa, tashin farko Dr Rasheed ya bayyana sunan......

Vote
Comment
Share
Salmerh 😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...23*

...... _Alhaji Jibrin Adam 'Dan- maliki_ matsayin ubangidan sa kuma me 'daukan nauyin duk wasu makaman da yake amfani da shi.

Sosai kowa yy mmk, take kotun ta 'dauki surutai da kananun maganganu da 'kyar aka samu komai ya daidaita, Adam dake zaune ta gaba- gaba kusan suman zaune yayi da jin wannan furucin, ba 'karamin shiga tashin hankali yayi ba, duk da cewa baya shiga harkar sa amma ai jini ba karya bace..kuma duk inda akaje aka dawo dole dai jini yafi ruwa kauri...baya ga haka ma burin shi fa? mutumin da yake da burin samin sa kan saka hannu cikin maganar dan ya taimaka wajen wanke laifin Zaitun sai kuma yaji sunan sa...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..kawai yk iya maimaitawa.

Karshe dole aka 'dage shari'ar har sai zuwa nan da wasu kwanaki kimanin goma sha hudu, domin sake kaurara bincike game da sabon furucin na Dr Rasheed.

Hankulan jama'ah duk ya dauku ga sunan da Rasheed ya ambata, kasancewar sa wani kusa ne a gwabnati bayyananne kuma sananne ga mafiya yawan al'ummar jahar, kuma da yawa ba'a yi masa kallon gur6attace shiyasa akai matukar mamaki.

Tuni an mance da zancen su Zaitun an koma kan 'Dan- maliki, dama haka jama'ah suke, abu 'kalilan ke 'daukan hankulan su ga abu haka kuma wani 'kalilan 'din ke sake juyar da hankalin su zuwa wani waje.

Wannan karan wata ma'ajiya aka maida su a Prison dake babbar karamar hukumar jahar tasu...wuri mafi tsamani da muni ga jikkunan su kuma illa ga numfashi da lafiyar su.

Irin kukan da Zaitun tayi ranar baya ta6a misaltuwa, tayi kuka kuka me tsamanin gaske, ganin kwanakin shan wahalar tasu a kullun da'da yin gaba yake yi bbu kuma alamun sassautawa balle suyi tunanin 'dan lokaci ne.
Kullun sassauci baya zuwan musu sai dai tsanani...
Haka kawai in tana zaune sai kaji tana fa'din" Allah! Yah Allah!!, Yah Malikal mulk Yah Zuljalal wal ikhram...tsabar yadda damuwar ta takai ma'kura sai ta rasa mai ma zata furta ne, me zata roki ubangiji yayi mata a wannan halin, kawai sai ta saki kuka me karya zuciya mai azabtar da ruhi da gangar jiki, ita ka'dai tasan halin da zuciyar ta take ciki...wai ita ce yau a prison, itace tayi zaman cell tsawon kwanaki itace akai ta jiba bisa tuhuma akan laifin da ko cikin mafarki bata fatan ta tsinci kanta a ciki balle a zahori, itace yau dubban al'umma ke mata kallon mai laifi, itace ake shari'ah da ita a kotu da bata tunanin ya wanzu a doran 'kasa ba, itace itace abin da yawa fa...hakan kadai idan ta tuna yakan yi mata zafi matuka, zafi ma me kona zucia....

Abu biyu ke mata kai kawo, bata san inda Mufeeda take ba bata kuma san wa zata tambaya game da yarinyar ba, dan rashin ganin Mufeeda shine ya sake ta'azzara yanayin da take ciki.
Chapter 34 · 0% Book details