Sashe 155
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da haka fa fargabar da nake ciki koka'dan bai ragu min ba sai ma karuwa har abin na ban mamaki, sai kuma na fara tunanin 'kilan mutuwa zanyi ne shiyasa nake jin hakan, dan ko ciwon cikina 'kara tsanani yayi ba raguwa ba, a hakan nabi jejin na 'debowa Iyami ganyen duk da nasan take so na kamo hanyar dawowa gida, still ina tafiya ina hutawa ga gajiya, ga ciwo ga zafin rana fa nauyin abinda na 'debo banda jiri dake son kayar da ni..tafiya ka'dan ce ta rage in hawo bakin titi sai na ji 'kara garam mai firgitarwa, tsam na tsaya daga inda nake jiki na ya fara rawa bana iya hango bakin titin saboda yawan bishiyoyi amma daga inda nake kunnuwa na na iya jiyo abinda ke faruwa.
Ri'kon ledar na gyara a kaina na fara taku a hankali zucia ta cike da mamakin abinda ke faruwa..dan har takun gudu nake ji sai dai ba dayawa bane dan mutane ka'dan ne ke zirga-zirga cikin garin...ban kuma san me janyo gudun ba.
Tsoro ne fal zuciya ta amma nasan hankali na zai kwanta ne kawai idan na tsinci kaina cikin gidan mu shiyasa ban yi yunkurin dakatar da tafiyar tawa ba....
Cak na tsaya take ledar da ke kaina tayi 'kasa sakamakon rage 'karfin riko da hannu na yayi mata, 'dif-'dif na ringa jin zuciya ta na harbawa tana dukan tara-tara, daga inda nake ina iya sake jiyo yanda motoci dake wucewa suke gudu tamkar na neman tseratar da ransu, ga dukkan alamu kuma ba cikin natsuwa suke gudun ba.
Sake rirkicewa nayi gashi dama ba kuzarin kirki gareni ba, take ciki na ya sake hautsinewa da ciwo, cikin na dafe hawayen da tuntuni naso jin saukowar su suka ki yanzun ban ma san lkcn da suka fara min zarya ba, take na dur'kushe a wurin ina furta kalmar _innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Allahumma ajirni fii musibati wa aklifni khairan minha..._ ...na shiga uku ni Zatituna yau me ke faruwa ne agarin kuma?"
Cikin kuka na furta hakan a fili yayin da tsoro na ke 'kara tsanani.
Ban kai ga dawowa hayyaci na bisa ga tsoron da ya sarke ni ba na fara tsinkayo nishin mutum na kusanto inda nake amma ban ganin kowa.
A firgice nayi baya ina zare idanu amma na kasa 'dauke idanu na daga inda nake jiyo nishin a hakan kuma nake yin baya- baya alamun tsoro 'karara ya bayyana sosai kan fuska ta.
Jin nishin na sake tunkaro ni ne ya sanya ni yin baya da sauri ina sake rarraba idanu na.
Tsoro ya riga ya kashe min gwiwoyi na dan nasan abu guda mu 'yan wannan yankin ke fama da shi, matukar muka ji irin wannan guje- gujen to tashin hankali ne ya faru na 6ullowar 'yan ta'addah.
Ji nayi nishin na sake tunkaro ni sosai, take nayi baya gami da mikewa na ware 'kafa na fara gudu a rikice, cikin jejin na koma ina 'kiran sunan Allah a fili da zucia ta.
Sai da na 'dan yi nisa ka'dan da wurin kafin na tsaya na lafe bayan wasu gajerun bishiyu da suka ha'du sukayi duhuwar da na san zai iya 6oye ni.
A hankli nake sau'ke numfashi sbd tsoro, hannu na bisa 'kirji na ciwon cikin ma tuni na rasa inda ya shiga, ta tsakanin ganyen bishiyun nake le'ken hanyar da ke gaba na inda na biyo a lokacin jin zuciya ta nake tamkar zata fito kan hannu na, jiki na nasan da za'a tsaga mawuyaci ne a samu jinin kirki a ciki, wuri- wuri nayi da idanu cikin bishiyun tamkarr wata 6era...sai kakkarwa da ilahirin jiki na keyi.
Daga 'dan nesa ka'dan na fara hango wata mace na tahowa da 'kyar tana tafiyar hannun ta 'daya nakan tulelen cikin ta, 'dayan hannun kuma ta ri'ke zani da jakar ta da shi.
Dur'kuso tayi kan gwiwoyin ta ta ringa maida numfashi da 'kyar da 'kyar, yayin da gumi ke tsatsafo mata ta ko ina.
Ba bukatar tambaya, domin da ganin ta kasan ba 'karamin galabaita tayi tashin farko za kuma ka fahimci cewar cikin wahala take wanda bata saba shiga irin sa a zahiri ba.
Sai a lokacin na fahimci hawaye na gangaro min sosai bayan na tsura mata idanu sosai, bazan yi 'karya ba har ga Allah ta bani tausayi domin wani gaban yafi gaban wani, ko kusa ko alama ciwon ta ya bambanta da nawa...tuni kuma ganin ta yasa nawa ciwon tafiya sbd tsananin tausayin ta da naji.
Tsakani na da matar akwai 'dan tazara amma hakan bai hanani 'kare mata kallo gaba 'daya ba...da alamu ta gaji ne da gudun dan sosai ta galabaita ta fita hayyacin ta gaba 'daya.
Ni kam banda kuka babu abinda nake yi cikin bishiyun tsoron fitowa nake yi dan har yanzun ban daina jiyo guje- gujen motoci da mutane ba.
A hankali naga ta sake mi'kewa cike da 'karfin hali, a 'ko'karin ta na ganin ta tseratar da ranta daga abinda yasa ta gudun tun a farkon fari.
Ganin yadda matar ke tafiya da 'kyar tana dafe cikin ta ne ya sanya ni jin tausayin ta sosai ya 'kara kamani, musamman da na tuno yadda nima nasha wahala da ciwon ciki jiya duk nasan nata yafi nawa, amma nasan babu sau'ki kuma da alama ita ma wannan 'din ciwon cikin ke damun ta tunda cikin take dafewa.
Yadda na tsura mata idanu kai kace wani abin nake son karanta a jikin ta, anan na fahimci ciki ne babba jikin matar kuma shike galabaitar da ita.
Wannan karon kam danne tsoro na nayi na fito cikin bishiyun na tsaya na zubawa matar idanu.
Ganin kamar 'karfin ta na yin 'kasa sosai ne ya sanya nayi saurin isa gare ta da sassarfa, ina jin tsoro amma tausayin ta sai ya danne komai dake zucia ta.
Ji kawai nayi baki na ya furta " sannu kina ambaton sunan Allah ko da cikin zuciyar ki ne..."
Na fadi hakan ne bayan na kamo hannun ta da ni kaina naga karfin halina a wannan wajen.
'Daga hannun ta nayi anan na tabbatar ko gani mai kayu bata yi dan har na kama hannun nata na kaita gefe bata san waye ba..banda hawaye babu abinda nake ganin yake fitowa daga idanun ta, da alamu ta riga ta cire rai da sake rayuwa a duniya ma.
'Karkashin wata babbar bishiyar gamji muka zauna kowa na sau'ke numfashi sama- sama amma na matar cike yake da zafin ciwon da ita kadai tasan yanayin sa..har a lkcn kuma hannun ta na dafe da cikin ta ne.
Ganin yadda nishin matar yaki 'karewa ne ya sanya ni matsawa kusa da ita gami da sake furta" Sannu Hajiya..."!
Inda na furta hakan cikin sanyin murya me tafe da fargaba.
Jin magana ta ya sanya wani hawayen sake gangaro mata, ahankali kuma ta kamo hannu na sannan ta bu'de idanun ta ta kalle ni, sai a lokacin muka ha'da idanu, duba 'daya nayi mata na fahimci rayuwar mu da ita da bambamci bayyananne...akwai tazara sosai tsakanin rayuwar mu da ita, tazarar nisan da zan iya 'kiyasta shi da nisa kwatankwacin tafiyar da ke tsakanin Borno da Lagos...sam babu maha'da.
Ban sake tabbatar da hakan ba sai da na sanya idanu na cikin nata.
A hankali na lumshe idanu na kuma bu'de su jin yadda take sake ri'ke min hannu na, taushin hannun matar na musamnan ne, hutu sosai ke jikin ta hutu, hutu irin wanda ya amsa sunan sa hutu....
Da kyar nayi gathering courage wajen furta" Hajia dan Allah ki daina kukan haka nan...ni bansan me ya faru ba har yanzun, kawai nima.. tsorata nayi jin motsin ki kuma ya sake firgita ni...me yasa ake gudu bakin titi dan Allah ki sanar da ni...".
Na 'karashe maganar murya ta na rarrabewa.
Kai ta girgiza min da sauri tana sake maida idanun ta ta rufe ruf, da alamu wani abu ke cin zuciyar ta wanda ni banda masaniya akai sam.
Banyi zaton zanji muryar ta ba dan har a lkcn banga alamun zatayi magana ba.
Ga mamaki na sai naji ta kara ri'ke min hannu na da kyau..cikin sanyin murya wanda ke fita da kyar ta fara fa'din" Ya hanani, sai da ya hanani tafiyar nan fa amma na nace masa.."
Bakin ta rawa ya fara da alamu tana danasanin kin bin maganar wanda take maganar akai din ne...."
" Ni nace sai nazo naga Ummah ta..ashe rabon wahala ya kawo ni..."
Daga haka ta rushe da kuka sosai, nima hawaye ya fara sakko min saboda tausayin matar duk da har yanzu ban gama fahimtar me take nufi da maganganun ta ba.
Cikin kukan nace da ita.." Hajia ki kwantar da hankalin ki bawa baya ta6a wuce 'kaddarar sa..."
Cak naji kukan ta ya tsaya sai hannu na da ta sake rikewa cikin nata tana sakin nishi mai 'karfi idanun ta a rintse.
Ba 'karamin firgita ni tayi da wannan yanayin ba, take na sake rikicewa dan bansan me hakan ke nufi ba, tunowa da nayi anacewa hadda mata cikin 'yan ta'addan kuma sai ya sani marairaicewa hawaye na na sake sau'kowa a guje, rintsattstun idanun ta na kalla da fuskar ta da ta ke ta faman yamutsewa tana cije baki.
Sake tsorata nayi ganin yanda ta 'kwakumo ni jikin ta ko motsin kirki ban iyawa...cikin kuka na fara ro'kon ta" Hajia dan Allah kiyi ha'kuri kar ki cutar da ni, wallahi banda kowa bani da komi...Hamma na bazai ji dadi ba idan kk kashe ni, kinga ni tausayin ki ya sani zuwa inda kike, dan Allah ki rufa min asiri kar ki cutar da ni.....".
Me kuke tunanin zai faru?
Share ur views pls...ina so inji inda tunanin ku ya nufa....
Salmerh😘
[2/1/2023, 10:23 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...88*
........Ban kai ga rufe baki na ba kunnuwa na suka jiyo min abinda ya sake firgita ta 'yar natsuwar dake tare da ni, wato kukan jinjiri, wanda zuwa lokacin garin yayi tsit da alamu kowa ya nemi mafakar da zata zame masa garkuwa, banda sautin kukan babu abinda ke ratsa ilahirin dajin dama wani sashi na garin na mu gaba 'daya.