Sashe 125
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai nuna wa Amrah komai ba kamar yadda bakin sa bai furta komai kan abinda tace 'din ba a zahiri sai ma kya6e baki da yayi.
*****
'Bangaren Zaitoon kuwa sam hankalin ta yanzu ba akan su yake bama dan ba su ne gaban ta ba.
Kulawa da hakkin mutane biyu da nawin su ke rataye a wuyan ta shine ka'dai damuwar ta kusan ko wani lokaci.
Ita kanta Amrah tasan cewa Zaitoon duk na ankare da su amma sanin halin ta na kawar da kai yasa bata ta6a damuwa ko jin shakka ba, ta riga tasan mawuyaci ne maganar ta fita ta 6angaren Zaitoon in dai ba wani ikon Allah ba, sai dai duk da hakan ta kan iya takun ta dan bata so ko da wasa maganar ya fita wurin su Ammi da wa'dannan fitanannun 'yan uwan nasa..acewar ta...domin tasan da zarar sun ji to ta ka'de ne har ganyen ta.
Ita kam Zaitun wani.sa'in har na mamakin dalilin da yasa Amrah bata wani zama da mijin ta, duk kuwa da ba lafiya ce da shi ba amma duk wasu abubuwa da ya kamata ace ita ce a gurbin ko kuma suyi tarayya akan sa su biyu to bata bi takan su, duk ta barwa Zaitun sai dai tazo ta duba shi kawai tayi gaba tana kya6e baki.
Wani lkc Sultan ko su Huzaifa na zuwa su wanke masa jiki, idan ko suka yi masan itace ke tsabtace muhallin nasa, idan sun fito daga wankan kuma zata fita ne idan sun gama shirya shi sai ta dawo ta tsabtace bayin da sauran abubuwa, abinci dama ba'a maganar sa, watarana ita da Ammi suke hidimar idan tana kusa idan kuwa bata gari ta kance ta bar shi amana a hannun Zaitun, duk da tana tausaya mata sosai sbd rainon Mufee ga kuma kula da shi amma hakan sam baya damun Zaitoon.
Sau da dama ma har sai sun gama yi masa komai sun bashi maganin sa kafin Amrah ke zuwa ta zo wai duba shi, mama kam bata ta6a nuna mata 6acin ranta ba, may be dalilin ma kenan da ya sanya ta bada ragamar kula da shi a hannun Zaitun 'din gaba 'daya.
Magungunan sa kuwa kaf mama ke ajiye su sbd gudun abinda kan iya zuwa ya dawo sai za'a bashi sannan take 'dauko su, idan zata yi tafiya kuma a hannun zaitun take bada su, duk dama yanzu komai ajiyewa tayi saboda jinyar Rayyan in bata fiye zuwa ko'ina ba in ba ya zam mata dole ba toh ba kasafai take yin ta ba.
Watarana ne da sassafe aka yi mata 'kiran gaggawa akan wata goggon ta acan Jahar Maiduguri 'karamar hukumar Geidam, hakan yasa ta rikice ta hau shirin tafiya dan su ka'dai gare ta a yanzu dangin mahaifi da na mahaifiyar ta amma asalin mahaifan ta duk sun rasu.
Goggon tata dama ta tsufa gashi babu isashshen lafia..hakan ya ru'da mata tunani sosai, har bata tuna bawa Zaitoon maganin Rayyan ba hankalin ta gaba 'daya yy gaba.
Haka ta shirya ta fito, rashin sani ashe ma set up akayi mata babu abinda ya sami goggon ta tana nan dai- dai kamar kullum ba kamar yadda aka sanar da ita jikin yake ba.
An dai je gida an sassace musu wayoyi amma kowa na nan lafiyar sa 'kalau, shiyasa ma koda Ammin ta 'kira layukan su duk basu tafi ba numbern da aka 'kira tan ma baya tafia.
A gigice ta bar gidan bayan ta bawa Zaitun amanar Rayyan, ita kan ta Zaitun Kukan take yi sosai sbd tausayin Ammi, ta rasa wannan wacce iriyar 'kaddara ce, ta shiga halin 'dimuwa abaya wanda take tunanin bb ce ta sanya hakan sai dai zuwa yanzun ta fahimci masu halin ma idan suka tashi shiga damuwa bada wasa suke shigan ta ba...a yanzu ne Zaitoon ta fahimci ita rayuwa komai mukaddari ne..kuma jarrabawa, sannan Allah na jarabtan bayin sa ba wai dan baya sansu ba sai dan ya gwada imanin su...ya kan jarabci duk wanda yaso ne cikin bayin sa batare da ya za6i nasaba, arziki ko akasin hakan ba.
Ammi bata jima da tafiya ba Sultan ya zo da kansa, fuskar sa babu yabo babu fallasa ya duba jikin Rayyan sannan ya fita, har ya fita kuma ya dawo ya dubi Zaitoon.
" Magungunan sa fa...?"
Tace" Ammi.bata bani ba, ina jin ta mance ne...".
Kai ya jinjina wata 'yar murmushi ya subce masa.
Sai yace.." Ok..bari a 'kira ta kafin su tashi sai ta fa'di inda suke ko kuma a siyo wasu a cigaba da bashi, bai kamata a yanke bashin ba dan bata nan..."
Yayi maganar yana juyawa ya fita yana mai ciro wayar sa a aljihun dake gaban rigar sa.
Zaitoon kam kai ta jinjina tana mai maida duban ta izuwa gare shi.
Tausayi yake bata sosai, gashi nan kwance kamar kace wane tashi amma babu dama... _Allah gwanin baiwa...._
Ta jinjina cikin ranta.
Bayan tafiyar Sultan bada jimawa ba sai ga sa'ko yazo ta hannun masu kula da shi wato su Huzaifa, a parlor suka tarar da ita, su biyu ne sun sha suit ba'ka'ke da ba'kin gilashi ko za'a kashe ta kuwa bazata iya yi musu kallo biyu 'kwa'k'kwara ba balle har ta iya gane su saboda yanda suka ha'de rai kamar masu kawo sakon mutuwa.
Wasu sabbin magunguna taga sun bata da bazata iya tantance su ba, akwai na ruwa dake farin kwalba shi yafi 'daukan hankalin ta sai dai girman kwalbar ya gaza wanda take gani Ammi ke bawa Rayyan sosai, sannan an kwaye takaddar jikin kwalbar haka zaka hango kalar ruwan dake ciki, bata san dalilin kwaye takaddar kwalbar ba, tana son sani amma kuma bata iya ta bu'de baki ta tambaye su dalilin ba.
Sai da ta kalli kwalbar kafin ta 'dan 'daga kai ta dubi 'daya da ya gaza 'dayan a tsayi ka'dan yana gyara gaban rigar shi ganin ta kalle shi sai yace" Inji Hajia ne wai a ringa bashi sau uku arana kafin ta dawo".
'Kasa tayi da kanta tana mai sake duban kwalbar dan shine a hannun ta tare da girgiza kai tana mai kimtsa bakin ta, a lokacin sam batayi wani tunani na daban ba, saboda tasan Ammi bata bar mata magungunan nasa ba 'kila shiyasa ta aiko da su yanzu.
Motsin bu'de 'kofa suka ji sai taga sun yi saurin waigawa suna masu shirin ficewa cikin hanzari..Zaitoon kam bin su tayi da kallo har lokacin da Amrah ta 'karaso ta samo ta tsaye a wurin da take cikin takun nan nata mai birgewa...tana tafiyar take fa'din.
" Ke kuma fa..kin wani yi tsaye tamkar wata dogari?..koda yake babu bambanci ma...tafiyar kusan 'daya ce..."
Ta 'karashe maganar tana mai zama bisa 'daya daga cikin kujerun parlorn.
Zaitoon bata kula ta ba kawai tayi 'kasa da kanta tana mai fa'din" Barka da safiya".
Bata tanka ta ba sai ma kya6e baki da tayi tana sakin huci.
" Ya jikin nasa? ashe Ammi ta wuce Borno?"
" Erh" Ta bata amsa da fa'din haka a a takaice.
Baki ta kuma kya6ewa batare da furta komai ba kawai ta 'dauki remote, kallon ta Zaitoon tayi a tsanake, cikin ranta take ayyana mamakin da Amrah ke bata, ga dukkan alamu ko jikin mijin nata bata je ta duba ba ta wuto nan wurin tana wani tambayar ta.
Tana canza channel take sake tambayar..." Wai har yanzu ko motsi bai yi ba...?"
" Kije ki duba shi da kanki zaki tabbatarwa ..."
Zaitoon ta bata amsa batare da ta kalle ta.
A fusace ta waigo gare ta tana kankance idanu.
" Toh ban yi niyya ba...isashshiya, in kuma za'a sani dole ne sai inji...".
" Hmm..."
Tace a hankali, bata san ma meyasa ta bata amsar farkon ba, bata san ya akayi amsar ta shiryu cikin ranta har ta iya furta shi ga Amran ba.
Sai daga baya ta fahimci haushin Amran ya bata kwarin gwiwar amsata...gashi kuwa taji zafin sa.
Wani 6angare na zuciyar ta ke bata shawarar bata hakuri, yayin da wani 6arin zuciyar ke yi mata garga'din kar tayi.
Kwalbar dake hannun ta ta dam'ke sosai sannan ta wuce 'daki inda Mufee ke bacci, ba yanzu zataje 'dakin nasa ba tunda ta riga ta gama yi masa duk abinda zata masa, yanzu kuma Dr Fawwaz ya rage yazo ya 'kara dubashi ko yanzun ma da su ka ganta palor aiki ta gama parlorn tana shirin wucewa suka tarar da ita.
'Karfe takwas zuwa tara baya wucewa batare da Dr Fawwaz ya iso gidan ba, tasan haka amma bata san mai ya dauki hankalin ta ba har kusan 'karfe goma sannan ta tuna da lokacin da ya kamata ta kasance a dakin nasa, da sauri ta tashi ta fito Moofy na biye abayan ta dan ta riga ta tashi a baccin kuma idan ta barta ita ka'dai kuka zata yi...hannun ta ri'ke da ledan magungunan da aka kawo mata cewa nasa ne...ita dai haka nan kawai taji zuciyar bata yi na'am da su ba koka'dan.
Da sallama ta shiga 'dakin duk da tasan ba lallai ne ta samu amsar sallamar ta ba indai ba Dr Fawwaz ne ya iso ko su Sultan ba, shima Sultan yanzu haushi ta yake ji ko zai amsa sautin muryar sa da 'kyar yake fita...jin shiru babu amsa yasa ta fahimci babu wanda ya iso kamar yadda take tunani.
A hankali ta 'karaso cikin 'dakin kanta na kallon 'kasa dan sau tari bata fiye son kallon inda yake karaf 'daya ba kasantuwar tsananin tausayin sa da kullum ke 'kara hauhawa mata a zucia...idan ta juri kallon sa a hakan abu na gaba da zata tsinci kanta ciki shine zubar hawaye da karayar zucia.
Sai ji tayi an bu'de 'kofan bathroom dake 'dakin, tsaye ta mi'ke cikin ranta take ayyana suma sun makara kamar ni kenan..basu zo da wuri ba ne ko kuma aikin ne bai 'kare musu da wuri ba....duk zaton ta wani cikin masu zuwa duba shi ba ne.
Salmerh😘
[23/11/2022, 7:04 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...73*