Sashe 211
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuncin ta ta yiwa curve da hannayen ta duk biyu tana murmushi tace.
" Shine kika 'ki zuwa in ganki ko Mufeeda?
" A ka qi kawo ta dai malama".
" Kuma kika cigaba da kukan nan tsab zan sanar da Ammi sai a ma daina kawo ta balle in kin ganta ki riqa kuka wa mutane....".
Marwa ta fa'da tana 'yar daria.
Duk da yake zuwan na bazata sukai mata amma irin tarbar da Zaitoon tai musu har sai ya baka mamaki a ahakan ma Ammi ta hana a sanar da su dan wai kar ta bawa kanta wahala wajen hidimta musu amma duk da hakan an yi ne amma ba a tsira ba.
sosai ta gwada bajintar ta, as there first visit to her house dole ta tarbe su da kyau ta faranta rayukan su...she was so exited.
Ko ba komai tsananin farin ciki da suka sanya ta ayau 'din yafi mata komai.
Duk inda tayi Marwa da idanu take binta, yayin da Mufee ke bibiye da ita tana cire 'kafa Mufee zata jefa nata, tun Marwa nayi mata tsiya har ta gaji ta 'kyalesu.
Lokacin da tazo ajiye musu zo6o ne kasa kasa Marwa ta furta, " wani abu na kasa ganewa fa Mamin Mufee?"
Hankali ta bata baki 'daya jin yadda tayi maganar tamkar tana 'kage da son jin amsar ta.
Marwa na gyara zama tace" Me Yaya yake baki kika canza baki daya cikin lkc kankani hakane.. kin ganki kuwa?"
Hararan ta Zaitoon tayi" Allah ya shirya Marwa, kin wani sa na nutsu zatona wani abin kirkin zaki fadi"
" Wannan ba abin kirki bane kk nufi? ba fa da wasa ba, Allah Mamin Mufee kin canza".
" Canzawa wata iri wai dan Allah?"
Inda tayi maganar cike da mmk tana mai sake duban jikin ta..kin yi haske kin murje abinki kamar bake ce waccan slim beauty din nan ba...kin dawo wata ta musamman again..gaskia asanar damu sirrin mu jarraba mu ma".
Ta 'karashe tana yar daria.
Itama Zaitoon dariyar tayi.
" Ki bari zan fada wa Yah Adam ya neman mk sirrin idan lkc yayi...".
Take Marwa ta ha'de rai da jin hk ta wani dame fuskar ta.
" Ke kuma kika jiyo, ni ban ta6a ganin inda laifin wani ya shafi wani ba sai a wajen antyn kin nan Mufee...shikenan a rayuwa babu jarrabawa sai kace duk an ha'du an zama daya...?...wani abin fa dole sai an bada 'kafa Marwa sannan ake gane inda al'amura suka fuskanta...muna dai rokon alfarma ayi hakuri a bamu dama muma mu jarraba sa'ar mu...".
" Hmm"
Kawai Marwa tace bata 'kara fadin komai ba.
Dama in kana son ta'kaita maganar Marwa toh sako mata hiran Adam ko wani makamancin sa cikin hirar ku...yanzu zaka ga taja ta fiske.
Tun ranar da ya sata ta ha'da sa da Mufee ta dan yi gardama ya fara shiga cikin rayuwar ta.
Lokuta da dama ta kan saka wayar ta flight mode sbd shi, sbd yawan 'kiran sa, dan ta riga ta fahimci manufar sa tuntuni, tun ma kafin ya kaiga furtawa, koda ya furta din kuma abin bai yi mata bazata ba amma ya sake worsening lamarin ta ne.
Ta kance ita a halin yanzu ba batun soyayya ko aure ne gaban ta ba, me ma zatayi da auren?
Wanda ta so ta kaunata, ta bada yadda da amincewar ta ha'intar ta yayi, ya rayu da ita zaman cin amana...ya cutar da ita, yayi mata illolin da har abada tabon su bazasu ta6a barin ta ba...me ta tsinta daga gare shi.
Banda bakin ciki da takaicin da suka kusan aika ta lahira.
Ta so shi ta 'kaunace sa amma yayi mata hakan balle wani can daban...tuni Sultan ya 'kona duk wani shaukin 'kauna dake zuciyar ta ya kuma yi watsi da tokar da yadda ha'de su waje guda zai yi mata matukar wahalan gaske.
Amma duk da haka Adam sai da ya cusa kansa cikin rayuwar ta, duk da yake akwai wani da sukayi schl tare shima ya nuna mata kauna amma tuni ta dakatar da shi, akwai dan gidan Alhaji Barau shima ya kasa samun fuskar ta duk da kuwa tasan Alhaji Barau makusancin mahaifinta ne amma hakan bai sa ta yi masa wannan karar ba, akwai wani ma Lameen shima tuni ta dakatar da shi amma shi Adam da ke isashshe ne bai tsaya bi takan maganganun ta ba, bai tsaya ya gama fahimtar manufan ta game da batun aure ko soyayya ba, bai tsaya yaji ra'ayin ta game da so ko 'kin sa ba kawai ya dangana kansa da manyan ta...aka kuma amince masa sbd nagartar sa da kuma kyakkyawan shaida da ya samu...
Shiyasa a halin yanzu tafi jin haushin sa fiye da kowa har cikin ranta.
" Ki dai bi a hankali dan Allah Goggo Marwa, kuma A cigaba da addu'ah shine mafita..kar a zafafa kuma kar a barmu cikin tararaddadi...dan Allah.."
Lokacin da zasu tafi kyaututtuka Zaitoon ta bawa yaran masu daraja, yayin da ta bawa Marwa wani ubansun turare mai kyau da tsada..ga sanyin kamshi.
Ita kanta marwa ya matukar birge ta ba dan kadan ba.
Wajen tafiyan ne aka samu matsala, dan Mufee ihu ta fara kamar wasa ta rungume 'kafafun Zaitoon...itama kawai sai ga hawaye.
Marwa rasa ma abin fadi tayi ta tsaya duban su.
Cikin sa'a kuwa sai ga motar Rayyan ta danno kai.
Shi kam cewa yy abarta kawai zai kaita da kansa an jima.
Da haka su Marwa suka wuce.
Koda labarin ya iski Ammi murmushi kawai tayi a fili tace" Ja'irar kaya kawai, wato ita nan taga uwar ta, aini wayon Mufeeda na bani mmk...
Badi'a dai bb fara'a tinda aka baro Mufee da kyar Ammi ta lallashe ta sannnan ta dan saki fuska.
Da tunanin dagasken za akai musu yarinyar har gida.
Mayarwan da Rayyan bai yi ba kenan sanadiyyan da rikon mufee ya dawo wajen su, ita dama Anty najin yadda suka yi tace a hada kayan Mufee kaf dan kuwa tatafi kenan, ba yau tasan halin kayanta ba indai Rayyan ne.
Ilai kuwa hkn ne ya kasance, biris suka yi suka zuba masa idanu kamar yadda yy dan kuwa cikin su kaf bb wanda ya tado zancen, nan ma suka fahimci ashe ko ada din ma da ya kyale kara kawai yk.
Bb abinda ya canza daga yawan baccin Zaitoon sai ma abinda ya karu, ga zazza6in tsakiyar dare, a kullum sai ya takura ta kusan sati guda kenan yanzu.
Rayyan tun yana kawar da kai har dai ya fara ha'de puzzle din waje guda ya kuma dasa ayar tambaya akanta.
Abinda ya fara dasuwa cikin ransa shi ya kusan haukata masa lissafi.
Had'nt been ya kasance gaskia da bai san irin farin cikin da zai tsinci kansa ba.
Amma a zahiri shi kansa yasan matar sa ta canza sosai, kama daga yanayin jikin ta, cimar ta da kuma yanayin tsarin halittar ta ba sai an fada masa ba.
*****
.......Angama maganar bikin Marwa har an saka rana wata biyu masu zuwa, Marwa tamkar ta yi bindiga sbd takaici, ba wai Adam ne bata so ko kauna ba, ita maganar auren ne baki daya bata muradi.
Domin hasalima duk da ba maganar kirki take yi masa ba amma duk ranar da ya shafe rabin yini batare da ya kira ta ba sai ta dan shiga damuwa, atimes har haushin kanta da kanta take ji sbd haka, kuma yanayin shigan sauri yai mata batare da ta shiryawa faruwar sa ba.
Haka nan kawai ta tsiri zuwa wajen Anty Raihana wai hutu, Adam yaso dakatar da ita amma ta 'kiya, kamar hadin baki kuma shima Rayyan yace a a bb inda zataje.
Tasha kuka har ta koshi, dan duk wanda ke tare da ita ma ya fahimci hkn.
Ammi ta 'kira Rayyan take bashi hakuri akan ya bar ta taje dan baki 'daya ya hargitsa mata autar ta.
Yace sam zai ma zo ya dauki Mufee anjima weekend din ya isa hk nan...daga nan ya kashe wayar sa.
Ammi tabi wayar da kallo kawai.
Sakkowa tayi a hknl ta tafi izuwa bangaren Marwa domin ban baki amma bata same ta dakin ba illa Mufee dake fama da Nursery Rhymes cikin waya...ta kuwa bada hankalin ta sosai akan wayar.
Ammi bata jima da shiga dakin ba sai ga ta ta fito daga bathroom da alamu wanka daga wanka take.
" ...Ammi da kanki har nan?...ai da kin aika sai naje in same ki acan.."
" No..Karki damu bakomai..dama batun tafiyar taki ne marwa...kinga yayanki yace sam bazaki ba, amma zan sake magana da shi Insha Allahu, kin sanshi wani lkc sai a hankali ga danzan kafiya da yake da...dan hk ki kwantar da hankalin ki kinji, ayi agama bikin nan lafia inyaso duk inda kk son zuwa sai kuje da mijin ki ba wajen Antin ki kadai bama hatta dangin mahaifin ki da nawa duk sai kuje...kinji daughter".
Marwa kawai kuka ta sanya tana mai zama gefen Ammin ta kwantar da kanta bisa jikin Ammi, kukan da yasa hatta Mufee da ke kallon waya dagowa ta dube ta.
Ammi kanta sai ta sake jin bb dadi, don dama tasan za'ayi hk..shiru kawai tayi ta zuba mata idanu, a hankali ta kai hannu take bubbuga bayanta alamar rarrashi...sau da dama Marwa na bata tausayi a gidan nan, bata fiye son ana takura ta ko tauye ta ba sam, bcuz yarinyar goes through alots a rayuwa, sannan tana da matu'kar ha'kurin da bata jin kaf 'ya'yanta ta haifi madadin ta wajen hakuri da kawar da kai bisa abubuwa.
Shiyasa tace dole zata sake magana da Rayyan.
Cikin kukan Marwa take fa'din
" Ammi ni dai abarni dan Allah inje, indai akan auren nan ne toh ni bana son shi, na fasa bana so ma na sake yin wani aure Ammi, maza duk macuta ne mahain'ta...Ammi ni har abada bana so in sake zama da wani...dan Allah kice Yayah ya barni inje.."
Ta karashe maganar hade da rushewa da kuka mai sauti.