← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 218

Sashe 119

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta cafko hannun. Raihana cike da jin dadi gami da nuna tsantsan farin cikin ta a fili take fadin.
" Allah yai miki albarka Raihana, wallahi tamkar kinsan menene acikin raina tsawon kwanakin nan, abinda kullum nk kwana nake tashi da shi kenan, amma gudun yadda za'a karbi zancen ya hana ni furtawa ga kowa sai gashi kema kinyi tunani irin nawa..."

Wannan magana ta Anty Madeena ita tasa Raihana ta dan saki ranta jin cewar tana da partner...tasan babu mamaki shawarar tata ta iya samun kar6uwa...

Ga Ammi Anty Madeena ta maida duban ta tana mai cigaba da fa'din..." Dan Allah Hajia Aseeyah a duba lamarin nan dai...magana ce muhimmiya, wallahi kuma na tabbata zata taimaka mana sosai wajen saukaka damuwoyin da muke ciki gami da tunanin mafita...."
Cike da zafin rai Ammi tana duban Anty Madeena tace.

" Lalle Madeena, ban ta6a tunanin shirmen ki na biyewa zancen yaran nan har ya kai hakan ba...taya kuke tunanin hakan zai faru ma? Kun ajiye matar ne, ko kuwa kun ajiye iyayen da zasu haifa maku yarinya haka nan kawai kuma su 'dauke ta su bawa majinyacin 'danku auren ta alhali kunsan halin da yake ciki, yana nan ne tsakanin rayuwa da mutuwa..babu wanda yasan mai gobe zata haifar...".

" Ji wani magana dan Allah...Haba Hajia Aseeyah! da kanki ma kike fa'din hakan toh me.kike tunanin wasu kuma zasu ce ...?"
Cewar Anty Madeena tana duban Ammi.

Marwa dake gefe banda kwalla babu abinda take sharewa, wai yau Yah Rayyan din su ne ake duk wannan muhawarar akan sa...alhali gashi can kwance bai masan wace duniyar yake ba.
Sosai take tausaya masa take tausayawa wannan hali da yake ciki.

Anty Madeena ce ta cigaba da fa'din" Nasan samun matar zai fi mana wahala dama, amman Insha Allahu bazamu rasa ba, mu bincika, wallahi ko min talaucin gidan su indai mun yadda da tarbiyar ta da kuma tsoron Allahn ta zamu iya jarrabawa mugani..."

" Madeena sai kace wata ba'kuwa cikin rayuwar nan, har yanzu baku saduda da sharrin mutane kun fita harkar mutane ba ashe Madeena?...bayan tabbatar da bayanin da gateman din gidan ki yayi har yanzu baki gama fahimtar cewa da shiri aka sa wuta a gidan ki ba ko sbd aga bayan ku duka? ...shin kinsan waye yayi ne..? Ko kuwa har kin mance kike si kice min...?
Me kuke sake nema? Me wata matar zata sake yi mana agidan nan...?"

" Hajia Aseeya ba haka nk nufi ba, taya ma zan iya mantawa, wannan abin ba abinda mutum zai iya mantawa cikin sauki hakan nan kawai bane but halin da Rayyan yake ciki abin dubawa ne, shine babban abin dubawa, wallahi tausayin shi a kullum karya min zuciya yake sai inga kamar muma da gudunmawar mu wajen guje masa bayan guje masa da Amrah tayi...yau idan ya tashi ya fahimci guje masa Amrah tayi ya kike tunanin zai ji a zuciyar sa Hajia Aseeyah? kina tunanin bazai ji zafin abin bane? Saukin da zamu samu shine kawai ya tara Amrah ta guje shi amma mun aura masa wata matar domin ta bashi kulawar da bai samu wajen Amrah ba..muma kanmu ai abin zai fi zuwa mana da sauki, in ba haka ba da wacce damuwar zamu ji?..ta rashin lafiyar sa ko kuwa ta rashin me kula mana da shi..".

" Wannan duk na Allah..mu bar masa komai a hannun sa Insha Allah babu wani abu da zai faru...".
Cewar Ammi.
Raihana ce ta sake fadin..." Duk da hakan dai Ammi a duba lamarin...kinfi kowa sanin cewa Yah Rayyan na bukatar wani kusa da shi yanzu..."

" Hmmm....."
Ammi ta saki ajiyan zucia mai 'karfi, daga hakan kuwa bata sake fa'din komai ba.

Washegari da safe ma babu wanda zai goge masa jiki ya shafa masa magani dan babu Sultan, dole Ammi ce tayi da kanta...Anty Raihana ta tayata.
Ko lkcn da Fawwaz yazo ma tuni sun gama masa komai dan Ammi cewa tayi bazai yiwu su 'daura masa dukkan nawin kulawa da Rayyan din akansa ba.

Har aka kwana biyu ita da kanta ke masa komai, ba kuma su sake tada zancen ba dan Ammi bata 'kara basu fuskar maganar ba.

Sosai suke tausaya mata sbd sunsan ba dadin jikin ta take ba itama amma tsoro da fargabar halayyar mutane yasata saduda take ta hidima da shi...burinta a kullun taga ko da dan yatsansa ne yayi motsi amma yaci tura.

Dole Anty Madeena ta sake tada batun Raihana ma ta tayata.
Marwa dai bata ce komai ba da yake ba sa'annin ta bane su duk, kuma ba'a musu tarbiyar tsoma baki cikin maganar manya ba, tana nan dai ta buga tagumi a gefe tamkar yajin 'kosai.

Ita kanta tana da tata shawarar cikin ranta amma bata san waya kamta ta tunkara ba hakan yasa ta rike abinta cikin ranta take binsu kawai da idanu.

Cike da ginshira da zancen nasu Ammi da rabon ta da fara'a cikin gidan tun kafin kwamciyar Rayyan, ta dube ta sannan tace.
" Hakane Madeena, amma please ku bar batun matar nan tukunna muyi ta lafiyar sa first, kowa tsoro yake bani a yanzu, ita kanta Amran ma ba sanin zuciyar ta muka yi ba, tunda ga 'karamin misali tun tafiyar ta su ko a waya ai bata kira taji ya jikin nasa ba balle muyi tunanin dama can bada san ranta tabi mahaifiyar tata ba, toh itama da take matar sa, suka yi zama da ita na wasu shekaru balle ace wata sabuwar matar daban da bata san waye shi ba, bata san ya halin sa yake ba kuna tunanin zata fi kaunar sa har ta kula da shi yadda muke so ne? bana tunanin wannan abin me yiyuwa ne Madeena bayaga haka ma zucia ta bazata ta6a iya jin yadda ko sakewa da ita ba matu'kar Rayyan 'dina na kwance bazan iya kwantar da hankali na in barshi da wata can daban wai matar sa ba...."

Wani abu ne ya tsikari zuciyar Marwa da yasa ta dubi Ammi da sauri, sai yanzu ta fahimci Ammi, ba wai auren ne bata so ba kawai tsoron mutame take a halin yanzu...tsoron da bazai iya barinta amincewa da yi masa auren ba duk da yake tasan cewa auren ne kadai mafita a hakin yanzu.

Bakin ta har na rawa wajen fa'din...
....." Ammi...
Sai kuma tayi shiru zuciyarta ya gama cika da fargaba.
Yayin da hankalin su da idanun su duk ya koma kanta.
" Ammi har Zaitoon ma baki yadda da ita ba kamar sauran...?"
Ta fa'da da sanyin sautin da ke tafe da tsananin fargabar maganar tata.
Dukkan su duban su suka kai gare ta hatta Ammi da tama kasa fa'din komai.

Ba ita ka'dai ba hatta Raihana da Anty Madeena ma basu ta6a kawo Zaitoon cikin ransu ba maganar Marwa duk sai ya ankarar da su.
" Zaitoon..!"
Ammi tace tana duban Marwa....yayin da su Raihana duk suka zuba mata idanu.
" Erh Ammi...Zaitoon, kinsan ta Ammi, kinsan halin ta, kin kuma san wani irin tarbiya gare ta Ammi, kinsan abinda zata aikata da wanda bazata iya aikatawa ba, kuma na tabbata Zaitoon bata yi kama da maciya amana ba, Ammi tun zaman mu da ita bata ta6a aikata wani abin Allah wadai ba da kanki ke shaida ce kan haka Ammi, me zai hana a tuntu6e ta ko zata amince ta aure shi, ba wai dan mun gaza ba ko.itama ta gaza bisa ayyuka da hidimar da take yi mana a gidan dama wanda shikan sa take yi masa ba sai dai dan cike wasu ka'idoji ....".

A zafafe Ammi tace
" Baki da hankali ne Marwa? Kin san abinda kike fada kuwa...?"
" A a Ammi, wallahi shawarar Marwa kan hanya take, koba komai duk munsan Zaitoon, kuma mun rayu da ita, nasan ko dan halacci bazata 'ki amincewa da maganar nan ba..."
Anty Raihana ce ta kar6e maganar da fa'din haka.

Ga Raihana Ammi ta maida duban ta da ta gama wannan maganar.
Rai 6ace sosai tace
" Kuma dan bamu da adalci sai mu tauye ta? sbd muna tunanin munyi mata halaccin da ya kamata ta saka mana sai mu ce ga abinda muke so tayi mana ko...?".
" a a Ammi..."!
" Yi min shiru da Allah...Ni ban ta6a tunanin Zaitoon watarana ta biyani abinda nai mata ba, ba ita kadai bama ban ta6a yiwa wani wani abinda da zan nemi sakayya a wurin sa ba kuma bana fatab hakan har abada, dan Allah ku kyale ni, ku sarara da wannan batun dan Allah ku cigaba da addu'a kuna nemawa dan uwan ku lafia yafiye min wannan maganar da kuke yi yanzu....".

Anty Madeena de bata tanka ba, banda murmushi babu abinda take yi domin a sarari take hango mafita, mafita ma kuwa mai 6illewa.

_Afuwan pls readers...nasan anyi hakuri sosai dani amma a 'kara..bani da time ne sosai shiyasa kukaji shiru amma amma Insha Allahu idan na samu time ko anjima zuwa dare ko gobe zaku sake jina._

*Thank u for your care and calls, Allah ya bar 'kauna, Allah bar zumunchi, Allah ya albarkaci zuri'a...nagode sosai 'yan uwa.*🤝💝

Salmerh😘
[15/11/2022, 10:06 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...69*

........Yadda Ammi tayi kicin- kicin da fuska yasa babu wanda ya sake samun damar tada wancan maganar yayin da Anty Madeena tayi shiru dagangan ta dai fara shirin ta ta 'kasa- 'kasa ba tare da kowa ya fahimci manufar ta ba.

Da wayo sai da tayi abinda sauran masu aikin 6angaren nasa duk suka bari illa Zaitoon, batare da sun farga ba kuwa Anty Madeena tayi nasarar fara saka ta yi masa wasu hidindimu a 'dakin da yake kwance.

'Karshe tayi magana da maigidan ta ta kuma fahimtar da shi game da halin da ake kici ta kuma bashi dalilai kwarara ya kuma.gamsu dari bisa dari, domin dama asali Anty Madeena Zara take awajen sa sam bai ha'da ta da kowa ba, da kansa yazo ya samu Ammi as in shawara ya bata bakomai ba, nan fa kan Ammi ya 'kara 'daukan zafi, gefe guda kuma sai taga a hankali hidimar Rayyan 'din na komawa hannun ita Zaitoonan bata kuma san dalili ba.
Chapter 119 · 0% Book details